← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 179

Sashe 50

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matashin murmushi tsohuwa ta saki, Yayin da idonta ke akan angel tace"duk yadda kika É—auka haka ne," ta6e baki angel ta yi, su haris duk suna sauraronsu batare da wani ya sanya baki ba,

"Danish zai dawo zuwa gobe, iya amsar da zan iya baku kenan, kowa yaje ya kwanta" tana kar ƙarshen maganarta, ta juya tana dogara sanda ta shige ɗakinta tare da jan ƙopa ta datse,
"Wannan munafukin É—akin ko menene acikinsa, wata rana saina san yadda nayi na kutsa kai cikinsa," angel ce ta yi maganar acikin zuciyarta, kafin ta kalli su hanna tace"har yanzu kun yadda da matar nan"?

Jinjina kai su kayi alamar eh, harish yace"Tsohuwa bazata ta6a yi mana ƙarya ba, danish yana kar6ar treatment ne, Idan ma akwai wanda ya kamata mu ga laifin shi to ke ce Angel, jiya kamar xaki kashe shi duk Kika yakushe wuyan shi hada cizo saboda tsanar da ki ka yi ma shi" rai a6ace haris ya yi maganar tare da jefa mata harara,

Ya yi tunanin zata mayar mashi da martani, amma sai yaga tana nannaÉ—e hannun rigarta, tuni yasha jinin jikin shi

"Wlh duk wanda ya kuskura ya ƙara ɗauramun alhakin ciwon danish, Sai na yi mashi jahilin Bugun da zai gaza ta shi" A harzuƙe ta yi maganar, nan da nan kowa yasha jinin jikin shi,

Murya na kerma azeeza tace"dan Allah kowa ya yi haƙuri, nidai bana son tashin hankali, tun da tsohuwa tace mana gobe zai dawo to mu haƙura muje mu kwanta mana"

Sai da batool ta lalla6a kowannan su kafin ta samu, Suka nufi gadajensu kowa ya haye sama ya kwanta

Ya rage saura angel kaÉ—ai a tsaye tana binsu da kallo, Yayin da tunaninta gaba É—aya yana akan Danish,

GyaÉ—a kai tayi tare da juyawa ta koma saman gadonta, har dare ya tsala bata runtsa ba, Allah na gani ta damu da rashin danish acikin su, tana ji aranta kamar wani abun ne zai faru da shi, ko a wani hali yake a yanzu oho Allah wa'alamu,

Lokacin da kowannan su ya yi bacci, tana cikin saƙe saƙe acikin zuciyarta, tajiyo motsin mutun, da sauri ta ƙyalla idonta don taga wanene

Wannan mutumin ne me jajayen kaya har ƙasa, hannun shi ruƙe da kaskon turaren wuta, sai yawo yake yi acikin ɗakin su, yana tafiya yana karanto wasu ɗalasimai, hannun shi ɗaya ruƙe da kaskon turaren wutar ɗayan hannun kuma yana amfani da shi wurin kora hayaƙin zuwa kowani sashe na cikin ɗakin,

Mamaki ne ƙarara akan fuskar angel ga tsoro tana ji, da sauri ta ƙudundune cikin bargonta, ta sanya tafin hannayenta ta toshe hancinta da bakinta kamar yadda ta yi jiya. Aranta tace"Yau ma ya dawo kenan"

Ya jima acikin ɗakin nasu yana turara masu hayaƙin, kafin taji tsit alamar ya tafi, da sauri ta yaye bargon tana faman sauke ajiyar zuciya,

Saukowa ta yi daga saman gadon jikinta na kerma, hasken fitilun nan guda uku ne ya ɗan haskaka Cikin ɗakin, fitila ta ruƙo a hannunta tana haska wurin gadajensu,

Kamar yadda tabi kowanansu jiya har gadon shi ta tottofe shi da addu'a, haka yau ma tabi gadajen su ta yi masu addu'o'i,

A daidai bakin gadon danish ta tsaya tana kallon shimfiɗarshi, bakomai ya faɗo mata aranta ba face jiya da tazo yi ma shi addu'a, ya damƙo hannunta yayi tunanin wani mugun abunne take yi mashi, ɗan abunda ya faru jiya atsakaninsu ya tsaya mata arai, matsawa tayi zuwa gefen gadon ta tsugunna tare da leƙa ƙarƙashin gadon tana haskawa da fitila, ganin babu wuƙar anan, yasa tayi tunanin ɗaga katifarshi,

koda ta ɗaga ƙarƙashin Katifar bata samu wuƙar anan ba, ba ƙaramin takaici taji ba, taso ace Ta gano inda wuƙar take kota samu ta lalata glass ɗin dake ajikin windon toilet ɗinsu,

Allah kaɗai yasan inda ya jefa wuƙar, wata'ƙil ma, ya maida ma tsohowa ita, guntun tsoki taja, yanzu shikenan narasa damar da nake ita? Babu wani makami da zan iya yin amfani dashi wurin rotsa gilashin, kodai naje toilet ɗin In ƙara dubawa? tana yin wannan tunanin ta miƙe da sauri ta nufi Cikin toilet ɗin, Ta tura ƙopar ta shiga daga Ciki, tana haska ko'ina da fitilar hannunta,

Abu biyu ne Yazo mata aranta, na farko Bokitin da ke acikin toilet ɗinsu Na ƙarfe ne, Na biyu kuma wannan tukunyar fulawar dake ajiye Jikin bango, waswasi ta shiga yi kodai tayi amfani da bokitin? ƙwara shi akan tukunyar fulawar, saboda Zata Iya rugujewa azo kuma buƙata bata biya ba, Anyi asara kenan,

Bata kaiga yanke shawarar dame zata yi amfani ba, ba zato ba tsammani Taji saukar hannun Mutun saman kafadarta, awani irin Firgice tayi kwakkwaran juyi Ta daddage ta É—aga fitilar hannunta zata kwaÉ—awa mutun daya dafa kafaÉ—arta, wani irin ihu batool tasaki a tsorace take faÉ—in"wayyo! Ke ni ce fa, batool ce,'

Nauyayoyar ajiyar zuciya angel ta sauke, Tare da janye fitilar, ta daidai ta natsuwarta, ba ƙaramin dariya batool ta bata ba, ganin yadda ta gigice,
"Allah ya taimake yau, da kin kwanta jinya,"
Dariya batool tayi"Kin ban tsoro me kike yi acikin toilet ne"?

"Ke zan tambaya, dama baki yi bacci ba,? Taya akai kika faÉ—o mun Cikin toilet batare da neman izni ba, yanzu da ace wani uzirin nake yi fa?

Hannu batool ta sanya tana sosa kai, tace"raina ya bani cewa ba abunda kike yi ne, shiyasa na shigo Ciki, Kuma na ganki Ɗazu zuƙunne agaban gadon Danish bansan me kikeyi ba, Amma ina hasashen wuƙar shi kika je nema halan"

Yatsina fuska angel tayi"I don't know why kin sa mun ido, " ta yi maganar da zolaya,

Batool tace"saboda na damu dake"
Ruƙo hannunta angel tayi tare da janta suka fito daga Cikin toilet ɗin, a bakin ƙopar fita daga area ɗin suka ɗan tsaya suna magana,

"Na duba ko'ina batool banga wuƙar ba, kodai ya maida ma tsohuwa ne?"

Girgiza kai batool ta yi "I don't think so, nafi tunanin yayi mata wani mugun 6oyan ne, shiyasa na baki shawarar ki shirya dashi, Ku samu kusanci sosai, ta hakanne zaki samu damar sanin inda ya ajiye wuƙar,'

Tur6une fuska angel tayi"Anya zan samu yardar danish, Kin fa ce yana da wuyar yarda da mutane, balle ni kuma daya É—aurawa karan tsana,"

"Ki jaraba ke dai, Danish yana da sauƙin kai sosai, ya danganta da yarda kika tafiyar dashi, amma wani hanzari ba gudu ba, har yau baki faɗa mini me zaki yi da wuƙar Ba!? I ave to know,'

Ta tsareta da ido tana jiran jin amsar da zata bata, Æ´an kame kame angel ta shiga yi don batasan batool ta gane ainihin abunda zata aikata, tasan bazata bari ba, zata yi kokarin dakatar da ita ne

Ganin tana ƙoƙarin ƙara tambayarta yasa tayin saurin katse mata hanzarinta da cewa
"Ko kinsan akwai wani mutumi da ke zuwa É—akin mu tsakar dare yana yawo da kaskon turaren wuta a hannunshi?

Tayi maganar a kokarin ta nata gusar mata da zancen wuƙa,

"Yaushe kika ganshi"? Angel tace"ko yau yazo, jiya ma na ganshi, idan yazo Sai yaita yin magana cikin wani irin yare mara daɗin ji, sannan yana bin kowani gado yana kora hayaƙin zuwa kowani sashe na ɗakin mu,"

Maimakon taga mamaki akan fuskar Batool, sai taga ta saki murmushi tare da cewa" kada ki damu kanki angel, tsohuwace ae kullum idan dare ya tsala sai ta shigo ɗakin mu, ta turara mana hayaƙin Kariya,"

Maimaitawa angel tayi'hayaƙin kariya kuma? Jinjina kai batool tayi eh, mun ta6a tambayarta hayaƙin menene tace mana hayaƙin kariya ne daga sharrin baƙaƙen aljanu domin kuwa akwai su acikin kurkukun nan, kuma hayaƙin yana da waraka acikin shi, shiyasa zaki ga ko ciwo bamu cika yi ba"

Angel tace"Ni a iya sani na, idan har za'a ba mutun kariya ba hayaƙi yakamata ayi mashi ba, addu'a ya kamata ayi ma shi, sam ni ban yarda cewa hayaƙin kariya bane, dole akwai wani 6oyayyan sirrin a tattare da shi,"

Kafin batool ta kuma cewa wani abu, suka jiyo sautin shessheƙar kuka daga can cikin ɗakin su,

"Wanene ke kuka"? Angel ce tayi tambayar tana kallon batool,

Batool tace "Muje mu duba, ina tunanin Aziza ce, "

da sauri suka fito daga area É—in toilet, suka faÉ—o cikin É—akin, haskata Angel ta yi da fitilar hannunta, a tsaye suka ganta tsakiyar É—akin sai kuka take yi tana laluban hanya saboda lalurar da take fama da ita, ta makantar dare (nyctalopia) bata iya gani idan dare yayi, ko kuma idan babu wadataccen haske, haka suke fama da ita, in ta farka zata shiga Cikin toilet, sai ta dinga kuka tana ambaton sunayensu har sai wani ya farka acikinsu ya rakata,

Tun lokacin da angel tayi noticing lalurar yarinyar, sai da tayi ma batool magana ta tambayeta tun yaushe take fama da ita? Batool ta bata amsa da cewa"tsohuwa tace haka aka halicce ta, da zarar dare yayi ganin ta ya ke ɗauke wa, koda an kunna hasken fitila biji biji take gani" tun daga wannan lokacin angel take jin tsananin tausayinta, tana matuƙar jin yarinyar acikin zuciyarta,

*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*

Ƙarasawa suka yi inda aziza taka a tsaye Angel ta ruƙo hannunta,

"Its ok stop crying muna atare dake, Ina zaki je ne"?

Cikin shessheƙar kuka tace"Fitsari nake ji ya matse ni,"

Bari naje na rakata, takai ƙarshen maganar tare da ruƙo hannun azeeza, suka nufi toilet, gefen gado batool ta koma ta zauna tana jiran fitowarsu, badajimawa ba Angel ta fito hannunta ruƙe dana azeeza, har saman gadonta takaita sai da taga ta kwanta, ta janyo mata duvet ɗinta ta lullu6a mata shi saman jikinta, tana jiyo muryar azeeza ta cikin bargon tana faɗin"I luv u so much angel," murmushi angel ta saki tare da cewa"Luv u too my sister, Allah ya kare mun ke, ki amsa da ameen" tana jiyo muryarta tana faɗin"Amen" ba ƙaramin daɗi taji ba, wuce wa tayi zuwa nata gadon ta haye ta zauna tare da jingina bayanta,

"Ba zaki kwanta ki yi bacci ba"? Batool ce ta yi mata tambayar,

"Zan kwanta, Ina yin addu'a ne ko baki gani ba" kallonta batool tayi ganin ta É—aga hannayenta biyu sama tana magana cikin harshen da bata sani ba, da larabci take yin addu'ar,
Chapter 50 · 0% Book details