← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 170 OF 179

Sashe 170

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu fa ba lokacin Yin nishaɗi bane, Yakamata Mu nemi mafita, Ni dama tun farko raina bai bani cewar Akwai wasu makullai ba, Mu ɗin dai mune makullan, Ƙofa ce kaɗai zamu gano, Saboda a jawabin da tsohuwa Tamira ta yi mata cewa ta yi Mu ɗauka cewa mu ɗin makullan Wata ƙopa ce guda ɗaya wadda zata sama mana farin ciki, To kunga anan tana nufin we're the keys da zamu buɗe ƙofar" Angel ce ta yi jawabin

"Ni kuma aganina akwai makullan, Ma'anar abunda ta ke nufi, Mu zamu haɗa hannu don mu gano su, Sa'annan waɗannan munafukan tagogin da suka zuba mana ido suna kallon mu, Ina zargin ƙofar tana A cikin su," Deeja ce ta yi maganar, Kowa sai tofa albarkacin bakinsa ya ke yi kamar masu gabatar da shirin wasa ƙwaƙwalwa.

"Ni ma nafi hasashen acikin su ne za'a samu ƙofa, saboda su kaɗai ne hanyoyin da zasu Iya 6ullewa wajen ɗakin nan" Acewar Hibba.

"Ku dakata, Kada Mu ɗaura buri akan waɗannan Tagogin, Har yanzu fa akwai wuraren da bamu Bincika ba, Na farko akwai ƙarƙashin gadajen mu, Da kuma ɗakin tsohuwa Tamira" Yasmin ce ta yi maganar, Rubina tace"Ai babu ta yadda za'ai mu iya buɗe ɗakin Tsohuwa Tamira, tun da mu ke bamu ta6a shiga ɗakin ba, saboda kullum agarƙame ya ke kuma babu makulli ta waje balle muyi tunanin balle shi mu shiga"

Gaddama ce ta 6alle atsakanin su kamar za su yi faɗa kowa Ya kafe akan tashi shawarar, Sai tada jijiyoyin wuya suke Yi, Ko yunwar cikin su basa Ji ga Jikinsu da ke ta tsami saboda rashin wanka, Hayaniyarsu ta cika ko'ina, ganin zasu hargitsa mata lissafine yasa ta dakatar dasu ta hanyar daka masu tsawa, Nan fa kowa yaja bakin shi yai shiru, Hankalinsu ya koma kanta, Miƙewa tayi tsaye kamar malami agaban ɗaliban sa, A tsanake ta soma magana.

"Idan har mu ka rasa natsuwar mu to kuwa ba zamu ta6a Iya gano ƙofar nan ba! Mu kan mu hankalin mu ba a kwance ya ke ba, ta ya ya ku ke tunanin zamu Iya gano ƙofar bayan mun ƙi haɗa kan mu, mu sanya natsuwa wurin bincikota"? Ta jefa masu tambayar tana ƙare masu kallo, duk sunyi ƙuri da idanuwansu,

"Maganarki gaskiya ce Angel, komai yana buƙatar kwanciyar hankali da natsuwa, Yanzu ki faɗa mana me ya kamata mu yi? Tun da kinfi mu kaifin basira"

Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, Jin an wasa ta, Miƙa ma Jamimah furennin dake a hannunta tayi tare da cewa"Ruƙe mini su My little sis" Kar6ar furannin Jamimah ta yi a hannunta.

"Abu na farko da yakamata Mu fara yi shine mu tsaftace jikin mu, ta hakanne zamu Ji daɗin Jikin mu brain ɗinmu ta yi fresh, mu samu natsuwar fara yin bincike na hankali, nasan kafin mu kammala Yin wanka Giants sun kawo mana Ganye, Idan mu ka Ci mu ka ƙoshi Sai mu fara wasan Ƴar 6urun 6urun kamar yarda na tsara mana, don kada ayi zargin wani abu tunda suna kallon duk wani moving ɗin mu"

Tun kan ta ƙarasa yin maganar, murmushi ya bayyana akan fuskokin su, gaba ɗaya sun yi amanna da maganarta, without wasting time kowan nan su ya miƙe tsaye, ɗaya bayan ɗaya suka fuce daga cikin toilet ɗin, Ya rage saura Angel da Jamimah, Kallon Juna su ka yi atare suka sakar ma Juna murmushi"My Genie, Ƙofar da zamu gudu ku ke nema mana?

Ɗaga mata kai Angel ta yi alamar eh, Dariyar Farin Ciki Jamimah ta saki har fararen haƙoranta sai da su ka bayyana, Bin ta da kallo Angel tayi dariyarta ba ƙaramin burgeta ta yi ba, sai da ta tsagaita da yin dariyar ta kuma cewa"Genie Zamu Koma Gidan ku da zama ko? Kuma can babu giants sannan ba zamu ƙara cin ganye ba ko"? Maganar da jamimah ta yi ba ƙaramin ta6a mata zuciya tayi ba, yadda suka ƙwallafa rai akan son zuwa gidan daddynta ba ƙaramin karya mata zuciya ya ke yi ba, duk idan ta tuna cewa ba lallai bane su samu damar tsira dukkan su ba koda ace sun samu ƙopar, wata'ƙil ma babu wata ƙofa tunda hasashene kawai suke yi basu da tabbaci akanta.

"My genie kin yi shiru, pls ki amsa mini, inaso inji a ƙagare na ke," yadda ta ke yin maganar farin cikine tsantsa akan fuskarta, tuni idanuwan Angel sun cicciko tab da ƙwalla, sam ta kasa buɗe baki ta amsa mata.

"Genie Am talking to u pls ki amsa mini, idan ba haka ba zan cinye furannin da ke a hannuna" Ta yi maganar tare da yin kamar zata cinye su, Nauyayyiyar ajiyar zuciya Angel ta sauke tare da cewa"Kada mu 6ata lokaci My little sis, Zan yi maki wanka amma kafin nan ki taya ni mu mayar da ƙasar tukunyar nan sai mu mayar da furennin" Amsa mata tayi da toh.

Ba tare da ta ƙara tambayar Angel ba, Atare su ka zuƙunna jamimah ta kwantar da furennin a ƙasa, kafin su ka sanya hannu Suna ɗibar ƙasar da ke a ƙasa suna zubawa cikin tukunyar fulawar bayan sun kammala Angel ta ɗauki furennin ta tsirasu Cikin ƙasar, har ta yunƙura zata miƙa Karaf idanuwanta su ka sauka akan wasu furenni guda biyu da ke yashe ƙasa, ƙura masu ido ta yi tana kallonsu Jamimah sai magana take yi mata amma sam bata Jinta,

Wani irin faɗuwar gaba taji tamkar zuciyarta zata faso ƙirjinta, a matuƙar ruɗe ta ke kallon Furennin, Ganyen jikinshi ya bushe ƙasa ya mutu, bakomai ya faɗo mata araiba face Majnoon da Unaiza da suka rasu, Zazzare idanuwanta tayi Hannunta ɗaya dafe da ƙirjinta, Nan take ta fahimci cewa furennin su ne suka mutu, Tun da basa araye that mean sauran furennin dukkan su rayukan ƴan uwansu ne akai, A hanzarce ta ɗaura eye balls ɗinta kan Dogon furen nan Muryarta Na rawa ta furta"DA...NISH!"

Zungurar hannunta jamimah tayi hakan yasa tayi firgit ta dube ta

Fuskarta a ɗaure tace"Kin shanyani Genie, ko ba za ki mini wankan bane? Inje inyi da kaina" Yawu ta haɗiya zuciyarta duk ba dadi, Furen Danish ya tsaya mata aranta, musamman da ta tuna da Lokacin nan da ta tarass Ganyayyakin jikinshi Sunyi baƙi sosai, tana ji aranta cewa wani mummunan abune ya faru dashi wanda silar hakan yasa furen shi canza launi,

"Genie!!" jamimah ce ta ambaci sunanta da karfi ganin ta ƙara shiga zurfin tunani, Numfasawa tayi tare da ruƙo hannun Jamimah, Cikin sanyin murya tace"Am sorry Muje inyi maki wankan" Tayi maganar tare da janta zuwa gaban fanfo, Ta cika bokiti da ruwa ta ɗauko kwandon soso da sabulu, Bayan ta cire mata kayan Jikinta ta ɗaura su saman igiya, wanka ta ke yi mata amma hankalinta gaba ɗaya yana akan dogon Furen nan, A shiririce ta gama Yi mata wankan hada sumar kanta ta wanke mata, bayan ta kammala bata mayar mata da uniform ɗin jikinta ba, saboda sun yi datti, sai tace mata ta koma ɗaki ta Ta lullu6e da bargo kafin kayan da zata wanke mata su bushe saita maida su a jikinta, bayan fitar Jamimah daga Cikin toilet ɗin, komawa Angel tayi gaban tukunyar fulawar ta zuƙunna tana ƙarewa Dogon furen kallo, Yayin da zuciyarta ke harbawa da sauri da sauri, Yatsun hannayenta na kerma ta ɗaurasu kan furen tana shafa leaves ɗinsa, Har cikin zuciyarta ta ke jin kamar sumar kan Danish ta ke shafawa, A hankali ta rufe idanuwanta a yayin da ƙwaƘwalwarta ke tariyo mata Rayuwar su ta baya dashi, baza ta ta6a manta Rana ta farko da ta fara Yin tozali da kyakkyawar fuskar shi duk da bata a cikin kwanciyar hankalinta sai da gabanta ya faɗi ganin irin baiwar kyan da Allah ya yi mashi, Tana matuƙar ƙaunar danish, Jin shi ta ke yi tamkar oxygen ɗin da ta ke shaƙa don ta rayu, taya hankalinta zai kwanta? Bayan ta riga da ta gane furen Masoyinta ne, idanuwanta sun yi maraicin shi, zuciyarta sai azalzalarta ta ke akan ta nemo shi aduk inda ya ke, don taga awani hali ya ke ciki, ya idon shi ya ke? Meya faru dashi da har furen shi Ya canza Launi............"

💔PRISONERS💔

Hankalin su Yaƙi kwanciya Jin shiru Angel bata fito daga Cikin toilet ɗin da ta shiga ba, Tun suna saran fitowarta har sun fara tunanin Anya kuwa lafiya? Ita kaɗai ya rage ta fito su fara wasan Ƴar 6urun 6urun, don su gano inda ƙofar nan ta ke, tun ɗazu Giats sun kawo masu Ganye kamar kullum tare da ruwan zafi, babu wanda yasan da cewa An kawo masu abinci.

Jamimah kaɗai ta rage a cikin ɗakin nasu, kwance saman gado ta lullu6e jikinta da bargonta, Jin motsin shigowar Giants, ta yi hanzarin yaye bargon data lullu6a dashi ta yi ɗaurin gaba har yana jan ƙasa saboda rashin tsawonta, Ahaka ta nufi ƙarƙashin gadon batul ta ɗauko kwandon abincinsu taje ta zuƙunna agaban dining Carpet ɗinsu, ta kwashe ganyan Ta zuba masu Acikin kwandon, bayan ta kammala kwashewa, Giants suka Ɗauki farantan tare da fucewa daga Cikin ɗakin, Zama Jamimah tayi saman carpet ɗin, ta soma ɗibar ganyen tana Ci yadda kasan ƴar akuya, Kunnuwanta har motsawa su ke yi saboda daɗin da ya yi mata.

"Angel ke fa mu ke jira! Tun ɗazu kowa ya fito daga wanka, Saura ke kaɗai kin shige toilet kin garƙame ƙofa kin barmu a tsaye" Deeja ce ta yi magnar

Batul tace"Ko dai ta fito daga wankan ne bamu sani ba? ta yi tambayar tare da yin saurin juyawa ta shiga É—akinsu, Jamimah ta hango zauna tana cusa ganye abakinta, babu alamun Angel acikin É—akin, dawowa ta yi sashen toilet É—in tun kafin su tambayeta ko ta ganta, ta riga su cewa Na duba bata a ciki,

Nan fa hankalinsu Ya É—ungunzuma
Chapter 170 · 0% Book details