← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 179

Sashe 69

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba ka yi mini kama da maƙaryaci ba, duk da bana yarda da mutun ta yanayinsa, pls tell me the truth kawai inaso na sani ne, saboda kafin na shiga toilet ɗin sai da na tabbatar na barka a kwance kana bacci kafin na shiga ciki, Kuma ko bayan dana shiga saida na Haska ko'ina babu mutun, amma wani abun mamaki sai gaka acikin toilet ɗin, wanda nayi Imanin bata ainihin ƙopar ka shigo ba, Kuma baka Biyoni abaya ba" Cikin tuhuma take yi mashi maganar,

muryar shi a sanyaye yace" Bazan iya baki amsa ba, saboda ni kaina bansan ta ina na shiga ba, abunda na sani shine Na sanyawa raina inason nabi bayanki ne, kuma na samu kaina Acikin toilet É—in shine kaÉ—ai abunda zan Iya tunawa amma bayan wannan bansan komai ba"

Zuba mashi ido tayi tana kallonshi, har cikin ranta ta yarda da maganarshi, domin kuwa babu alamun wasa a fuskarshi ya bata amsar, kwara tabi komai asannu wurin yin bincike, Idan ba haka ba, zata iya tarwatsa lissafin kwakwalwarta ne,

Ƙaƙaro murmushi ta yi akan fuskarta, yayin da take kallon shi,

Mayar mata da martanin murmushin yayi Calmly yace" kin sanya damuwa aranki, Jiya kinyi kuka kuma baki yi bacci ba Why? Akan su Parveen ne"?

Jinjina mashi kai tayi alamar eh, ta ƙara da cewa"na damu dasu sosai, Ina ji araina kamar baza a dawo mana dasu ba, shiyasa zuciyata ta karaya har nagaza runtsawa"

Duƙowa taga ya yi saitin fuskarta, har saida ta ɗan tsorata, Zuciya da saƙe saƙe sai tayi tunanin ko kiss zaiyi mata, ƙiris ya rage tsinin hancinshi ya gogi nata, runtse ido tayi tana jin me zai mata

"Ki kwantar da hankalin ki, Zasu dawo na yi maki alƙwarin hakan," ɗagowa tayi tare da kallon shi,
"Taya akai kasan cewa zasu dawo"? Tayi tambayar tana kallon cikin idanuwanshi,

Murmushin gefen fuska ya É—anyi, Can kuma yace"Kin manta anzo an É—auke ni, Kuma an dawo dani, Suma zasu dawo ne"

Girgiza kai angel tayi"amma koda aka dawo dakai, baka Acikin hayyacin ka, kamar an ƙara maka Ciwon Ajikin ka, danish zaka Iya tuna ina aka kai ka bayan an ɗauke ka daga Cikin mu"? ta jefa mashi tambayar,

"Angel, ba zan iya tuna komai ba, tun bayan da giants suka É—auke ni bansan meya faru ba, har sai ranar da suka dawo dani cikinku tukunna na iya tuna wanene,"

Shiru angel ta yi bata kuma cewa komai ba, Lamarin ne yafi ƙarfin tunaninta, Wata irin Murɗaɗɗiyar sarƙaƙiyace Acikin Kurkukun mai wuyar fassaruwa,

Miƙa hannu danish yayi tare da ruƙo nata hannun acikin na shi, Magana ya soma yi idonshi acikin nata"angel, ina neman yafiyarki, for everything that happened because of our misunderstanding, I hate you for no reason, but now I can say that I love you more than anyone........" kalaman shi ba ƙaramin sanyaya mata zuciya su ka yi ba, sai taji tamkar an yaye mata damuwarta na ɗan wani lokaci,

ƙayataccen murmushi ta saki tana motsa lips ɗinta, alamar tana so tace wani abu amma ta kasa furtawa, sam batayi tsammanin jin hakan daga gare shi ba, ta yi farin Ciki saboda yana ɗaya daga Cikin nasarar da take so ta samu na Jituwa atsakaninta da kowannan su, tana so ta shiga cikin zuciyoyinsu sosai ta yarda zata samu damar janyo ra'ayinsu, yanzu saura mutun biyu ya rage mata haris da deeja, taci alwashin Idan aka dawo da deeja bazata ƙara bari faɗa ya haɗa su ba, Shi ma haris ɗin bazata biye mashi ba, xata jasu ajikinta,

"What are u thinking about"? Jin voice É—in danish yasa ta É—anyi firgit ta kalle shi, still idanuwanshi na akan fuskarta,

" baki bani amsa ba," ya tambaya yana sauraranta,

"Dama ni ban ruƙe ka azuciyata ba, Ni baka yi mini laifin komai ba, dani dakai tamkar ƴan uwana ne jini," ba ƙaramin daɗin kalamanta yaji ba, har cikin zuciyarshi yaji sanyi, zame hannunshi yayi daga Cikin nata, ganin ya lumshe eyes ɗinshi yasa tayi tunanin ko bacci zai koma ne,

Yunƙurawa tayi tare da miƙewa daga gaban gadon shi, A dai dai Lokacin Batool ta fito daga sashen makewayinsu, itama fuskarta a kumbure, suna haɗa ido da angel ta nufeta, rungume juna su kayi kowa yayi shiru, batare da sunyi magana ba,

Azeeza dake zaune saman gadonta, farkawarta kenan idanuwanta na akansu,

Sun É—auki lokaci kafin suka raba Jikinsu daga na Juna,"

"Idanuwanki sun nuna alamun baki yi bacci ba jiya, meyasa"? Batool ce tayi mata tambayar,

"Taya xan iya runtsawa, alhalin ƴan uwana suna Acikin mawuyacin hali, anzo an raba ni dasu, an kaisu wani wurin, dole na damu, Nayi kewarsu sosai, Na gaza jurewa ne....." kukane ya ciyota, da sauri ta duƙar da kanta ƙasa, sam bataso ta nuna rauninta agabansu, saboda zata ƙara karya masu zuciya ne, sai dai duk ƙoƙarinta na hana kanta yin kukan hakann ya faskara, ita dai sam hankalinta bai kwanta da ɗaukar su parveen da akayi ba,

Dafa kafaɗunta Batool ta yi da hannayenta biyu, Cikin sigar lallashi tace"pls angel, u should stop shedding your tears, kina ƙara sanya mana damuwa ne, ke da kike ƙarfafa mana gwiwa yau ke ce da kanki ki ke zubar da hawaye to mu me zamu yi kenan"? Idon batul cike tab da kwalla tayi maganar,

Ta wutsiyar idonta ta hangi azeeza dake a zaune ta kasa kunne tana sauraronsu, da alama baccin bai sake ta ba, bata fahimtar me suke tattaunawa,

Sanin raunin azeeza yasa tayi saurin sanya tafukan hannayenta, ta share hawayen da suka wanke fuskarta, murmushi tayi wanda kai zuci ba takalli batool dake kallonta tace "Nadaina batool, bazan ƙara ba, kema kada kiyi kuka" jinjina kai batool tayi"Nima bazan bari hawaye na su zuba ba, Angel inaso mu haɗa hannu wurin taimaka ma sauran ƴan uwanmu, mu dinga lallashinsu muna basu baki har Allah yasa adawo dasu Parveen, Inaso mu sama ma junan mu farin ciki koda kuwa babu wani acikin mu, kamar ke da kika jure rayuwa batare da Mahaifinki ba, haka nakeso muma mu ƙarfafa zuciyoyin mu, mu yi rayuwa da sanin cewa wata rana samu iya rasa wani,

Tun da batool ta soma magana angel ta natsu tana kallonta, acikin zuciyarta tana Jinjina Ma batool, Yarinyar akwai tawakalli, Tana da hankali da tunani, Allah yayi mata baiwar iya sarrafa harshe wurin tsara kalamai masu kwantar da hankali, Haƙiƙa Iyayensu sunyi babbar asara Na rashin ya'ya kamar su,

"Angel kinyi shiru baki ce Komai ba, Ina ta surutu Ni kaÉ—ai," ajiyar zuciya angel ta sauke tare da kallon Batool tace"Am sorry Sister, naji maganganunki, sunyi mini daÉ—i sosai kuma in sha Allahu, zamu yi hakan, Zamu haÉ—a hannu wurin sama ma kanmu farin ciki,"

Muryar azeeza ce ta katse su da cewa"Wai har yanzu ba'a dawo mana dasu parveen ba? Jiya har mafarkinsu nayi," saukowa tayi daga saman gadon ta nufi su angel dake a tsaye ta ruƙe qugu tana kallonsu,

"Ba'a dawo dasu ba Azeeza, Mu ƙara haƙuri zuwa anjima may be Giants su kawo mana su" Batool ce ta bata amsar tambayarta,

Ta6e baki azeeza tayi tare da cewa"Ni dai indai ba'a dawo mana dasu ba, Bazan ƙara Cin abinci ba" maganartace ta basu dariya,

Sauran ƴan uwansu dake bacci ɗaya bayan ɗaya suka dinga farkawa, duk wanda ya buɗe ido saiya tambayi su deeja, Angel da batool ne ke kwantar masu Da hankalinsu akan su ƙara haƙuri zuwa anjima, lokacin da kowa Yayi wanka, Suna a zazzaune saman gadajensu, Sai ga giants sun shigo kawo masu abinci, Bayin Allah duk sunyi tsammani za'a zo masu da ƴan uwansu amma sai suka ga akasin,

Koda suka koma saman dining carpet domin Cin abinci, saboda damuwa, kaɗan suke tsakura suna ci ba don suna jin daɗin abincin ba, Angel hada ƙoƙarin mikewa taje karkashin gadon batool ta ɗauko kwando, tazo tana kwashe kingin abincinta, Yasmin tace"meyasa ba zaki ci ba? Bafa Ki ci dayawa ba'? Angel tace"su parveen zan ajiye mawa, kada su dawo da yunwa anjima, Jin abunda tace ne yasa suma suka rage sauran nasu abincin don a ajiye ma su parveen, angel ta kwashe duka cikin kwandon, Taje ta 6oye a karkashin gadon batool,

Bayan tafiyarsu Giants, Hanna ta basu shawarar su motsa Jiki Ko sun samu Lokaci yayi saurin wuce wa duk don saboda tsammanin za'a dawo masu da ƴan uwansu yau, bayan sun kammala motsa Jikin nasu Kowa Ya gaji sai uwar xufa ke tsastsafo masu, A dole suka je toilet kowa ya watsa ruwa a jikin shi, ba ƙaramin ɗaɗi suka Ji ba, saman gadajensu suka koma kowa Ya hau ya zauna fira suka soma yi atsakanin su, wani irin bacci ne yazo ma angel batare data shirya mashi ba, dama jiya ana binta bashin baccin da batayi ba, gyara kwanciyarta tayi asaman gadonta, tare da jan bargo ta lullu6e kanta, Cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awon gaba da ita,

*ANEELERH*

Almajirai ne daddabe a gaban motarta, sunyi dandazo suna jiran Ta basu sadakar kuɗi kamar yadda ta saba basu a duk lokacin da tazo zata wuce ta wurin makarantar allonsu, Sai faman zumuɗu almajiran suke Yi, Kayan Jikinsu duk sun yayyage, kowannan su na aruƙe da kokwan bararsa,

Zuge glass ɗin motar ta yi, almajiran sai kallonta suke yi, tana a zaune saman driver seat, Jikinta na asanye da atampa, riga da skirt sunbi shape ɗin jikinta, Ta yafa mayafi akanta, ba ƙaramin kyau ta yi ba, Yayin da baby junaid ke akwance saman passenger front seat, Kayan sanyi ne ajikinshi sunyi matuƙar yi mashi kyau, baccin shi yake yi hankali kwance, ga wani irin ƙamshi dake fita ajikin shi,

Ƙoƙarin Zaro kuɗi take Yi acikin ƴar purse ɗinta Bendir guda ta ciro na ƴan ɗari biyar biyar, zarowa ta dinga yi tana miƙa ma almajiran, Sai murna suke yi, suna kai hannu suna karba tare da yi mata addu'o'e Sai da ta kammala raba masu, tana yunƙurin Zuge glass ɗin motar, taga an zuro mata hannu, ras taji gabanta ya faɗi ganin hannun babban mutun sanye cikin baƙar safa,
Chapter 69 · 0% Book details