Sashe 172
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Jikin su ba ƙwari, Muna ƙara masu ciwon nasu, Mun ishe su da surutu, Mu taimaka masu Su shiga cikin ɗaki su kwanta," Hibba ce ta yi maganar, Ruƙo hannun haris Deeja tayi a cikin nata, Ba ta yi tsammanin zai motsa ba sai ji ta yi ya sanya hannu ya dafa kafaɗarta, Hakan ba ƙaramin kwantar mata da hankalin ta Yayi ba, A hankali su ke yin tafiya suna tunkarar cikin ɗakin, Ruƙo hannun Naufal Parveen tayi da taimakon ta ya dinga ɗyangyasa ƙafar shi suka nufi gadon shi, Yayin da Batul ta ruƙo javed ya kwantar da kanshi saman kafaɗarta a haka suka nufi cikin daki, Ita kuma Hannah ta taimaka ma Mubeen, Ya rage saura Gabriel da Azeeza ke a rungume dashi, ta rasa ya za ta yi ta taimaka mashi su shiga ɗakin, Gaba ɗaya su Hibba sun bar bakin benen babu wanda Ya lura da Gabriel da su ka bari saboda babu shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu dashi, Sunfi Jinsu Javed shiyasa Hankalin su yafi karkata akansu.
Tana so ta taimaka mashi sai dai bazata Iya ba, Saboda tsayin dake gare shi Ga ƙirar Jiki, tsawonta daƙyar Ya kai waist ɗin shi, ruƙo hannun shi ta yi a cikin nata tare da jan shi don su shiga ciki ko motsi wannan baiyi ba, hakan yasa ta fashe da kuka tare da ɗaga murya tana yi ma su batul magana "Wai bazaku zo ku taimaka mashi ba? Kun barshi shi kaɗai a tsaye" babu wanda Ya juyo ya kalle ta Hankalin su ba akanta ya ke ba, Tsagaitawa tayi da yin kukan tare da kallon fuskar shi wata irin zufa ce ke tsastsafo mashi, Ya galabaita sosai, Cikin shessheƙar kuka ta ambaci sunan shi, bai amsa mata kiran da ta yi mashi ba, Sai dai taga Ya zuƙunna saman matakalar benan Yana faman Fitar da numfashi mai ɗumi.
"Ka tashi mu shiga ciki, Inaso na taimaka maka" A hankali yake bin ta da kallo fararen idanuwan shi sun canza launi zuwa ja, daga gani ba ƙaramin jin jiki ya ke yi ba, azeeza sarkin tausayi hada sanya Ƙasar rigarta saman fuskar shi tana share mashi gumin da ke tsastsafowa, acikin zuciyarta ba ta ji dadin yarda su Batul suka manta da zancen shi ba, Shi kaɗai suka ware, marairaice mashi fuska tayi "Pls ka tashi mu je ka kwanta, baka da lafiya fa, Nasan baka jin dadin Jikin ka,......" tunkan ta ƙarasa maganar Gabriel ya yunƙura ya miƙe, Daurewa kawai ya ke yi don ba ƙaramin jiri yake gani acikin idanuwan shi, ƙoƙarin Yin tafiya yayi Ƙafarshi ta Hagu taƙi bashi haɗin kai, Gaba ɗaya Ya tafi zai kife ƙasa, Azeeza ta fasa uwar ƙara haɗi da ambaton sunan shi, hakan ne ya jawo hankalin su Parveen ga kallonta A lokacin har sun taimakama su Haris sun kwanta saman gadan su, Da gudun gaske suka nufi Gabriel dake ƙoƙarin faɗuwa, Da ya ke Namiji ne Allah yayi shi da ƙarfi bai bari Ya faɗi ƙasa ba, Handrail ɗin benan Ya dafe da hannun shi, Sai faman Huci ya ke fitarwa, Nannaɗaɗar sumar gaban goshin sa duk ta rufe idon shi, Koda su parveen suka ƙaraso ganin ya dafe Hannun benan yasa suka sauke ajiyar zuciya, Azeeza kamar jira ta ke yi su ƙaraso ta dinga surfa masu bala'e akan sun tafi sun bar ta da shi, bayan sun san ita ƙarama ce, da ace ya faɗi kasa kanshi ya bugu me suke tunanin zai biyo baya, Faɗa sosai ta rufe su dashi, ta inda take shiga bata nan take fita ba, sai faman tada jijiyoyin wuyanta take yi duk akan Gabriel.
"Allah ya huci zuciyarki Azeeza bada son ranmu muka ƙyale shi ba, Hankalin mu ba a kwance Ya ke ba, Amma yanzu kiyi haƙuri, zamu shiga dashi Ciki" Fuskar Yasmin a hautsine tayi mata maganar, ɗaure fuska azeeza tayi hada ruƙe qugu tana binsu da kallo.
Parveen da Yasmin ne suka taimaka wurin ruƙo Gabriel Suka nufi Cikin ɗakin dashi, agaban gadon shi suka sake shi ya hau ya kwanta, Daga gefen shi Azeeza ta hau ta kwanta tana ƙare mashi kallo mai nuni da tsantsar ƙaunar shi kewar shi da Tausayin shi.
a 6angaren Haris Deeja ce zaune saman gadon shi, Eve da yasmin suna zazzaune gefen gadon shi, Sai sannu su ke yi mashi, Sam ya kasa amsa masu, Sai dai yabi su da ido,
Javed Yana a kwance saman gadon shi, Batul da Sarah ne Zaune gefe da gefen mattress É—inshi, Ji su ke kamar su É—auke masu ciwon Jikin su saboda tsabar tausayinsu da su ke Ji,
Idan muka koma 6angaren Naufal Shima Yana kwance Ya lumshe idanuwan shi, Parveen da Hibba suna a zaune saman gadon nashi, suna yi mashi sannu.
A yayin da Hannah da Rubina suke akan gadon Mubeen, hakan ba ƙaramin sanyaya zuciyoyin ƴan uwan nasu yayi ba, Ganin yadda suka nuna damuwa akan su,
"Yanzu ya zamuyi? Ko abinci babu da zamu Iya basu nasan dole suna jin yunwa," parveen ce ta yi maganar,
"Ko ruwa ne mu fara basu Mu ga idan zasu sha" a cewar Batul, Jin suna maganar ruwa yasa Jamimah ta nufi ƙarƙashin gadon batul ta lalubo robobin ruwa taje ta miƙa ma Deeja, Bayan ta kar6a taje ta miƙa ma parveen kafin ta nufi Batul ta bata ɗaya" da sauri ta koma ta ɗauko sauran robobin ruwan guda biyu Ta kaima Hanna ɗaya, sannan ta nufi gadon Gabriel Ta miƙa ma Azeeza, Hannu tasa ta kar6i robar ruwan tare da miƙewa zaune ta cire murfin kallon shi tayi, Still idanuwan shi Na akan fuskarta,
"Ruwa ne ka tashi ka sha" tayi maganar tana nuna mashi robar ruwan, Da ƙyar ya yunƙura Ya tada kanshi saman pillow, Yatsun hannun shi sai kerma suke Yi ya gaza iya ruƙe robar, hakan yasa ta kafa mashi ita saitin bakin shi ya soma kur6ar ruwan Yana bi ta makoshinsa, A tsanake Azeeza ta ke kallon fuskarshi Ya canza sosai, kamar ba Gabriel ɗin da ta sani ba.
Bayan kowannan su Yasha ruwan, Jamimah ta tattara robobin ta maida su ƙarƙashin gado ta killace su,
Har yanzu babu wanda Ya tuna da Angel a cikin su, bacci ne ya fara ɗaukar su Javed, cikin ƙanƙanin lokaci baccin yai awon gaba dasu, ganin sun samu bacci yasa hankalin su Batul ya ƙara kwanciya. Kamar sun samu tv haka suka tasa su agaba suna kallon su yayin da su ke yin bacci,
Farin Cikin su ragagge ne, Abu Biyu ya tsaya masu aransu, Na farko Meyasa ba a dawo da Danish ba, Bayan An riga tafiya dashi? Na biyu me aka yi masu na tsawon watannin nan? basu da amsar tambayoyinsu.
"Allah sarki Danish ɗinmu shi ba'a dawo mana dashi ba, Na yi tsammanin dukan su zamu gansu" Batul ce tayi maganar, Deeja tace"saboda mugun nufin su akan shi sunƙi dawo mana da ɗan uwanmu, Nafi damuwa dashi saboda halin da aka tafi dashi, "
Da alama ransu ya 6aci sosai na rashin dawo masu da Danish, tsawon Awanni Sunyi zugudum babu mai Magana a cikinsu, Wuraren marece Mubeen Ya farka daga bacci, A matuƙar firgice ya zabura ya miƙe zaune Yana haki Gaba ɗaya idanuwan su akan fuskar shi, Kafin su yi yunƙurin tunkarar shi Ya duro daga saman gadon shi kafar shi kamar zata 6alle A haka ya dinga janta ya nufi Sashen toilet ɗinsu, Da gudu Hannah dasu Yasmin suka bi bayan shi, A cikin toilet suka tarar dashi Ya zuƙunna gaban fanfo Yana kwara amai, Wani irin Farin abu mai yauƙi yauƙi ya ke fitowa daga bakin shi har ta hancin shi ya dinga gangarowa, Wa'iya zubillahi! Zuciyoyin su sun karaya da ganin yadda Mubeen ke kwara aman fargabar su kada ya mutu kamar yadda unaiza ta tafi tabarsu, Tuna wannan yasa hawaye wanke fuskokinsu, A gaban shi suka zuƙunna suna kallon fuskar shi, Sai nishi yake yi Yana jan numfashi a wahalce,
"Mubeen dan Allah ka jure, bamu so wani abu ya same ka, Kaga Muna ƙaunar ka sosai" a hankali ya ɗago da idon shi kan fuskar Parveen da tayi maganar, Girgiza kanshi ya yi yana faman cizon la66an shi ya soma magana "Kada ku tada hankalin ku akaina, lafiyata qalou," tun daga kan yarda yai maganar zai ƙara tabbatar maka da Babu lafiya a jikin shi, ya faɗi hakan ne kawai don ya kwantar masu hankalin su,
"Wlh baka da lafiya Mubeen, Kalli yadda idanuwan ka suka canza launi, kamar ba mubeen ɗin mu ba", murmushi ya ƙakalo akan fuskar shi Yayin da ya ke kallon Hanna da ta yi maganar,
"Nifa lafiyata qalou, Nagode da kulawar ku agare ni, nayi missing ɗinku sosai," Cikin sanyin murya ya furta hakan, A hanzarce Batul ta miƙa hannu ta kunna fanfo ruwa ya soma zubowa, tarba tafin hannayen ta tayi Ruwa ya taru a cikinsu ta wanke mashi fuskar shi tare da zuba mashi ruwan a bakin shi Ya kuskure shi, Bayan ta kammala ta ruƙo hannun shi "Mu koma ɗaki Mubeen" Sai da suka taimaka mashi tukunna Ya iya miƙewa, fitowa su ka yi daga Cikin toilet zuwa ɗaki, A saman gadon Shi Ya kwanta Yana faman sauke ajiyar zuciya, kewaye da gadon shi suka tsaya suna tottafa mashi addu'o'i, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mashi ba, bayan sun samu komai ya lafa suna shirin komawa su zauna Kwatsam Gabriel Ya farka Hananyen shi biyu daddafe da kanshi Ya fasa wata irin gigitacciyar ƙara da ta janyo hankulan su Gare shi, Jikin shi sai kerma yake yi musamman la66ansa, Sambatu ya ke yi na fitar hayyaci, A hankali Su ka soma tafiya suna tunkarar gadon shi, A kewaye da gadon shi suka ja burki suna ambaton sunan shi Muryoyin su a tsorace
"Gabriel! Meke damun ka? Faɗa mana ina ke yi maka ciwo," Shiru bai tanka masu ba, Hankalin Azeeza duk yafi tashi don tuni tafara sharar ƙwalla, tsananin tausayin shi ne ya kama su, musamman da ya daddafe kanshi sai ya tuna masu da Danish, duk idan ciwon shi ya tashi haka ya ke yi masu ya dinga fasa ƙara,