Sashe 21
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba su ƙyasta lighter ɗin ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna ya ƙyasta ya jefe saman ciyayin dake a kewaye da shi. Da gudu wutar ta shiga cinye ciyayin har ta hau saman jikinsa. A lokacin sun shige cikin motocinsu, da gudu suka fisge su tare da barin cikin dajin. Cikin ƙanƙanin lokaci, wutar tacinye shi ƙurmus.
*To Jama'a Zaku ga nasanya Farkon labarin nayi hakan ne don in tariyo maku daga inda zamu tashi fatan an waye ni*
*waɗan da su ka shirya yin payment zasu iya farawa, 08103884440 cikin wata mai zuwa free pages book one zai ƙare, Ina yi ma kowa fatan alkhairi, sai mun haɗu a next page in Allah yakai mu da rai da lafiya*
*💋Boss Batureâœï¸ðŸ’‹**💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
_daga alÆ™alamin Boss Batureâœï¸_
*Dedicated To Aunty Kubraâ¤*
*E8*
Hasken rana ne ya haske fuskarta, sakamakon windown bedroom ɗinta da ta bari a buɗe, dogon numfashi ta ja tare da buɗe kumburarrun idanuwanta waɗanda suka yi luhu-luhu da su sun ƙanƙance saboda kukan da ta sha a daren Jiya. Kwance take a saman gadonsu, jikinta duk ya yi nauyi sam ta kasa motsawa, gefe da gefe na gadon ta kalla don ta ga ko Uzair ya dawo. Ras ta ji gabanta ya faɗi ganin still bai dawo gidan ba, hankali a tashe ta yunƙura ta miƙe zaune tare da wurga idanuwanta kan agogon bangon, ƙarfe tara na safe ko sallar Asubahi ba ta samu ta yi ba, saboda nauyin barcin da ya ɗauke ta.
Siraran hawaye ne suka gangaro daga cikin kwarmin idanuwanta har izuwa saman kuncinta, masu É—umi, harshenta ta sanya ta É—an lashi gefen bakinta inda ruwan hawayen ya gifta.
Daƙyar ta samu ta lalla6a ta sauko daga saman gadon, still riga da wandon jiya ne a jikinta, kanta babu mayafi, sumar kanta ce da ta zubo mata ta ko'ina ta yamutse.
A hankali take tafiya harta shige toilet, after some minutes ta fito daga cikin toilet É—inta, da alama alwala ta yi, lemar ruwa ce a fuskarta da hannayenta.
Cikin wani irin yanayi na jin faduwar gaba, da tsinkewar zuciya, ta nufi closet É—in kayan su, buÉ—ewa ta yi tare da zura hannu ta É—auki hijab É—inta, ta sanya a jikinta.
Saman dardumar dake shimfiÉ—e ta tsaya, a tsanake ta kabbara sallah, cikin nutsuwa ta soma yin ibadarta.
Bayan ta kammala, zama tayi saman dardumar tare da ɗaga hannayenta Cikin harshen larabci ta soma yin addu'o'inta daga ƙarshe ta rushe da matsanancin kuka tana faɗin. "Ya Allah Ka dawo mun da mijina lafiya,Ya Allah ka karemun shi aduk inda yake! inaji araina kamar wani mummunan abu ne ya faru da shi, Uzair bai ta6a tafiya batare da sanina ba. Amma jiya ya tafi ya barni in the midnight without my knowledge," Sosai take yin kukan ta jima, kafin ta yanke shawarar zuwa Wurin taj donta tambaye shi idan Sunyi waya da Uzair."
Miƙewa tayi da sauri, ta fito daga Cikin bedroom ɗinta, ta nufi hanyar fita daga falon, a bakin gate ta samu maigadin gidanta zaune saman benci yana sauraron radio.
Tunda ya hango ta ya yi saurin ajiye radio É—in saman bencin ya mike ya tunkare ta, "Barka da safiya hajiya, kun tashi lafiya."Ba ta amsa mashi sallamarshi ba, saboda ba ta acikin natsuwarta,
"Inaso zanje wurin taj ne, may be sunyi waya da uzair, wlh nadamu sosai nakasa samun natsuwa baba, inaji kamar wani abu ya faru da shi," Tana magana hawaye na fita daga cikin idanuwanta.
Tsananin tausayinta ya kama baba maigadi, tunda yake bai ta6a ganin hawayen Aneelerh ba, sai a daren jiya da kuma yau, ya lura da tashin hankalin dake akan fuskarta.
Cikin sanyin murya yace"Kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, in sha Allah uzair yana cikin ƙoshin lafiya, babu abin da zai faru da shi."
Gyaɗa mashi kai ta yi tare da wuce shi ta nufi gate ɗin, Hannu tasa ta buɗe ƙopar jikin shi ta fuce daga cikin gidan.
Girgiza kai maigadi ya yi ji yake da a ce yana da halin da zai iya taimakon Aneelerh a yau daya taimaketa, abin da ciwo ka ga mutumin daya saba kyautata maka a cikin wani ƙunci na rayuwa kuma baka da yadda za ka iya taimakon shi, komawa yayi jiki asanyaye ya zauna saman bencin.
Bayan fitar Aneelerh, kai tsaye ta nufi gidan Taj dake a jikin gidansu, tun abakin gate ta hango maigadin gidanshi a tsaye ya jingina bayan shi jikin gate É—in, fuskar shi duk a harmutse da alamun damuwa atattare da shi, hakanan taji gabanta yayi wani irin mugun bugu ras!
Ƙarasawa inda yake tsaye tayi muryarta da fargaba atattare da ita ta ce, "Assalamu alaikum"
Tunkan takai ƙarshen maganar taga ya ɗan firgita, sai daya kalleta tukunna Yaɗan saki fuskarshi yace"wa'alaikum salam, malama Aneelerh, in ce ko lafiya?''
Hawaye ne suka sake wanke fuskarta, cikin shessheƙar kuka ta ce, "Har yanzu uzair bai dawo ba, yanzu ma zuwa nayi wurin taj, don inji idan ya kira shi awaya," Tana kai ƙarshen maganarta baba maigadi ya ce, "Innallahi Wa'inna Ilaihir raji'un!"
A ruɗe ta ce, "Baba lafiya?" Cikin tashin hankali ya ce, "ƴar nan tun jiya na gaza samun kwanciya hankali, ko runtsawa ban yi ba, saboda damuwa, jiya bayan kin zo neman Taj, kin tafi na shiga daga Cikin ɗakina na kwanta, har bacci na fara bacci sama sama, can cikin dare wuraren ƙarfe ɗaya da rabi, ina kwance na ji fitar mota daga cikin gidan nan. A firgice na farka na fito daga ɗakina, koda na fito naga gate a wangale, na leƙe banga komai ba, na dawo na duba naga babu motar taj da yake yawan fita da ita, a nan na gane cewa shine ya fita cikin motarshi."
Tunda ya soma magana Aneelerh ta dafe ƙirjinta da tafin hannunta, ta zazzare ido tana kallon shi,
"Na yi mamakin ina Taj ya tafi batare daya sanar dani ba! domin kuwa tunda nake aiki a ƙarkashin shi bai ta6a lekawa koda ƙofar gida batare da sanina ba, amma sai gashi jiya tsakar dare ya fuce, kuma abun da ya ɗaure mun kai, ba shi kaɗai ya tafi ba. Hada ANGEL!" A gigice Aneelerh ta shiga ambaton Innallahi Wa'inna Ilahir raji'in! Na shiga Uku! Wai meke faruwa ne? Wayyo Allahna!" Gabaɗaya ta bi ta ruɗe, shi kan shi baba maigadi da ya sanar mata, sai da yayi danasani ganin yadda ta daura hannayenta a saman kanta tana zabga salati.
Juyawa tayi da gudun gaske Ta koma Cikin gidanta, A lokacin malam Garba maigadinta Yana zaune saman bencin yaga shigowarta a guje, har yana tambayarta lafiya, amma bata saurare shi ba.
Hankalinshi ya ƙi kwanciya, Miƙewa ya yi da nufin yaje su yi magana da tajo,yana ƙokarin fita daga cikin gidan, baba maigadin gidan Tajo, ya tura kofar gate ɗin, suka yi kicibus da juna.
"Wai meke faruwane É—an ladi"malam garbane yayi mashi tambayar fuskarshi a yamutse.
Baba maigadi ya ce, "Tun É—azu naso in zo mu yi magana. Amma damuwa ta hana ni, lamarin dai babu daÉ—in ji." Nan ya kwashe duk abin da ya faru na tafiyar Tajo tsakar dare ya sanar da shi."
Malam Garba ya hauyin sallallami, hankalinshi duk ya tashi a rude ya ce, "Indai kuwa haka ne akwai matsala. Ya kamata a sanar ma Ƴan sanda don a san abin yi tun kafin lokaci ya ƙure mana"!!
Jinjina kai baba maigadi ya yi" ni ma abun da nake tunani kenan, amma mu ɗan ƙara jira kaɗan zuwa anjima"
"Shikenan zan koma bakin aikina, zuwa anjima idan ba wani labari game dasu sai muje police station É—in" a cewar É—an ladi, daga haka suka yi sallama da juna. Ya koma gidan da sauri don ya barshi a buÉ—e bakowa
Aneelerh kuwa bayan shigarta Cikin gidan. Afujajen ta nufi bedroom É—inta ta shige, jikinta na kerma ta É—auki wayarta dake ajiye saman bedside drawer,
Call logs ta shiga ta dannawa numbar da tayi saving da Abie kira,Tana fara Ringing, Aka ɗaga wayar, muryar babban mutuncine mai cike da kamala Ta karade kunnuwanta, "Assslamu Alaikum daughter..." Tun kafin ya kai ƙarshen maganar, Aneelerh ta rushe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita..."
Muryar Abie a ruÉ—e ya shiga kwala mata kira." Aneelerh lafiya kike kuka meya faru? Waya ta6a mun ke? ki buÉ—e baki ki yi mun magana!"
Sai da ta yi kukan mai isarta, sannan ta soma magana cikin shessheƙar kuka"a...Abie..Uzair da Taj.." katse ta ya yi da cewa."me ya faru dasu? Wani ya rasu ne'
"A'a, tun daren jiya Uzair ya bar gida wuraren ƙarfe tara, shi kuma Taj ya bar gidansa karfe ɗaya da rabi na dare, kuma ya tafi tare da Angel. Babu wanda yasan meya faru dasu, kuma dukansu layinkan wayoyinsu akashe, Abie ina cikin matsanancin tashin hankali."
Lamarin ya girgiza abie sosai,"
Muryarshi cikin sigar lallashi ya ce, "ki kwantar da hankalin ki aneelerh, In sha Allah babu abun da ya faru da su, yanzu zan yi waya da uncle ɗinki, ki ɗan ƙara haƙuri." Cikin shessheƙar kuka ta ce"To Daddy, saina jika "ya ce" ki daure ki ci abinci, na san ba ki ci komai ba" Amsa mashi ta yi da to kafin suka yi sallama ta kashe wayar. Saman gado ta koma ta zauna zugudun cikin zullumi, salla kadai ke tada ta.
Wuraren ƙarfe huɗu na marece, tana kwance magashiyan fuskarta ta kumbura tayi suntum, tunda tayi sallar la'asar bata cire hijabin jikinta ba,
jiniyar motor Æ´an sanda tajiyo daga waje Wii! wiii! ras! taji gabanta ya faÉ—i, fargabarta kada ace gawar Uzair kota taj suka kawo Cikin gidan,
A hanzarce ta miƙe, da gudu ta fito daga cikin bedroom tana sauko ƙafarta cikin falon, adai dai wannan Lokacin mahaifinta Alhaji Muhammad falgore ya doko sallama, Yana sanye Cikin shiga ta alfarma, Shaddace fara tass taji guga, tare da malun malun, kanshi Na sanye Cikin hula, Bayan shi kuma Ƴan sanda ne su huɗu sanye cikin kakin su, ɗaya daga Cikinsu Uncle dinta ne kaninta mahaifinta me ruƙe da muƙamin dco(Divisional Crime Officer),Atare dashi akwai Ic (inspector crime) sai kuma Ipo(Investigation Police Officers) Su biyu ne ɗaya mace ɗaya Namiji masu tsayi da jiki ba laifi a launin fata baƙake ne,