Sashe 29
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
tafi ƙarfin awa ɗaya a tsaye Tana Kallon hotonsu dake a manne Jikin bangon bedroom ɗinsu, Idanuwanta Sun Cicciko tab da ƙwalla, Har yau she ne wannan baƙin Cikin zai gushe acikin zuciyarta? taya zata Iya sakin jiki tayi rayuwa acikin duniyar nan batare da Ya'yanta ba? tabbas ta yi babban rashin, A kullum ta kali hoton su, sai ta zubar masu da hawaye, Almost 2 years kenan babu su babu labarin su, itace kullum Cikin zullumi da zarar wayarta tayi ringing, jikinta har 6ari ya ke yi don ta ɗauka taga ko Jami'an dake bincike kan case ɗin su tajuddeen ne suka kirata don su sanar da ita ko an gano inda suke,
Tun lokacin da suka dawo Seoul hajiya adama Bata ƙara samun kwanciyar hankali ba, Gangar jikinta gaba ɗaya tana a nigeria, Sunan tana zaune a korea ne, duk irin Sabon da tayi da ƙasar hakan baisa ta gundure ta ba, duk don saboda Abunda ya faru na 6acewarsu tajudden, Ita fa a ayanzu Tafi sha'awar su koma nigeria, Hankalinta sai yafi kwanciya koba komai Zata dinga ganin ƴan uwanta,
Tsadadden leshi ne a jikinta, launin silver yabi shape ɗin jikinta, Ta kashe ɗaurin ɗan kwali, Yayin da ta goya hannayenta a saman ƙirjinta,
Sam ta kasa janye idanuwanta daga Kallon hoton nasu da take yi, bakowa tafi ji ba, face Angle ƙaramar yarinyar da bata mallaki hankalinta ba, taso ace tuntuni rainon yarinyar ya dawo hanninta da yanzu suna atare, Sai dai kash Ƙaddara ta riga fata,
Ziraran hawaye ne suka soma saukowa kan kuncinta,
Muryar me aikinta ce Ajumma ta katse mata Tunanin nata
Cikin harshen su na korea take sanar da ita cewa Saƙon ta ya iso, Share hawayen fuskarta ta yi, kafin tace"A shigo mun da su ciki," itama da harshen nasu take magana, don tana ji ba laifi,
Turo ƙopar ɗakin ajumma tayi, Babbar macace ta kwana biyu aduniya tsufa ya fara kamata, fara ce sol gashin kanta iya kafaɗarta ya tsaya, Jikinta na sanye da ƴar riga da gajeran skirt, Faffaɗan tray ne a hannunta, Saman shi kwalaban Soju ne (Giya) sun kusa Uku, tare da glass cup guda ɗaya,
A saman Round table ɗin dake a kusa da gadon hajiya adama, ta ɗaura tray ɗin, Ta juya zata fita, har ta kusa kaiwa bakin ƙopar fita muryar hajiya adama ta katse ta"Idan mutun yana so ya bugu sosai, har ya manta wanene shi, kamar yaya ya kamata yasha" shiru ajumma tayi tana tuna gargaɗin da Abdallah ya yi mata akan karta kuskura ta ƙara ba matar shi soju tasha, idan ba haka sai ya kore ta daga aiki, Yau ɗunma don Abdalla baya a gari ne, Shiyasa ta kawo mata soju ɗin,
"Kin yi shiru baki amsa mun ba"? Muryar na kerma tace"Kwalba É—aya, Amma ran ki shidaÉ—e ina jin tsoro, kada yalla6ai ya ritsa ki a lokacin da kika sha kika bugu, Zai iya korata daga aiki"
"Kada ki damu, Bazan faɗa ma shi cewa ke kika kawo mun giyar ba, Zance ni na fita na siyo ta, hakan yayi maki" jinjina kai ajumma tayi kafin ta ruƙe handle ɗin ƙopar ta fuce,
Zama Hajiya adama tayi a gefen katafaren gadonta, takai hannu ta Ɗauki kwalbar Soju Ta cire mufin, Abaki ta kwafata Cikin ƙanƙanin Lokaci ta shanye duka, wani irin biji biji tafara gani a cikin idanuwanta, Ajiye kwalbar tayi, tare da kai hannu ta ƙara ɗaukar wata kwalbar ta shanye duka, sauke kwalbar tayi saman table, Ta yunƙura zata miƙe duniyar ta soma juya mata, sha tara sha takwas ta dinga gani acikin idanuwanta, wani irin nauyi Jikinta yayi mata, Tangal tangal ta soma yi tana tafiya ta nufi hoton dake manne jikin bangon ɗakinsu, Ta curo hoton ta ƙura mashi ido tana kallon shi, har wani girgiza kai take yi,
Can dai ta rushe da wata irin mahaukaciyar dariya tamkar zararra, muryarta ashaƙe ta soma magana"Duniya juyi juyi, wohoho Kai ya ɗau zafi, In ban da ta6ara da ɗamsil basira Ta ya za'ace mutun ya 6ace tun 1960 Amma An gaza gano inda yake? Ƴan sandan nan basu san ciwon kansu ba, Gashin Hammata ma yafi su Amfani, Nayi fushi Allah Ni da kaina zan nemo abuna ahe, Ku zuba ido ku gani yanzun nan zan gano su,' takai ƙarshen maganar tare da ajiye hoton ƙasa, tattare Zanin leshin jikinta tayi, ta zuƙunna ƙasa tana rarrafe, Saƙo da lungu na ɗakin ta shiga Bi tana sambatu Tana faɗin"Gasu Can sun 6oye, kamo su nan kamaso Sunan, Zo nan ɗan ɗana Uzairu Yaron mamansa, kaima zo Tajuddeen ɗina, Kai na manta da Angela ta Yarinyata zonan in raira maki waƙa, Wacece Kumatu Angel ce kumatu, kumatutu kumatu, kumatutun mama, kumatutun baba......" tana raira waƙar tana kuka, zama tayi tare da cewa"Yauwa, Ga abinci Nan Shekaran jiya na girka maku shi, nasan kuna jin yunwa, banda wawaso, duk wanda ka samu rabon ka ne,," gaba ɗaya ta haukace ita kaɗai take ta sambatu, giya takai mata karo, ita fa ala dole su take gani acikin idanuwanta, tana magana tana sakin gyatsa,
Yunƙurawa tayi ta miƙe tsaye tana faɗin"Zan Binciko ku duk inda kuka 6oye ja'iran yaran, harni zan girka maku abinci ku ƙi ci? Kai tajo hada cewa ba daɗi? Ni da ku ne" hannu tasa ta zuge zip ɗin rigarta, Ta cire rigar tare da yin wurgi da ita ƙasa, Ta warware zanin shima ta jefar da shi ƙasa, ya rage daga ita sai undy, Ƴar duma duma da ita, ga uban tumbi, wurgi tayi da kallabi leshin kanta, Ta koma mahaukaciyar ƙarfi da yaji, dambe ta shiga yi ita kaɗai, sai da ta Tarwatsa komai na ɗakin, da sunan tana neman Su Uzairu, itace har cikin toilet, gaban toilet seat taje tana leƙawa, Hankali Ya gushe,
A karshe ta zube ƙasa tana birgima tana faɗin"Ya Allah kota sama ne, A jeho mini su, Nasan kasan inda su ke, tunda kai kana ganin komai, ko karkashin ƙasa mutun ya 6oye......."
Ta jima tana sambatu, kafin Allah ya kawo bacci ya yi awon gaba da ita, Lokacin da Uncle abdallah ya shigo Cikin gidan, Jikinshi sanye Cikin Suit sun zauna ma shi,
Tun a palour suka yi kici6us da Ajumma, Sam ba ta yi tsammanin Aranar zasu dawo ba, A tsorace ta gaishe dashi muryarta na kerma, Kota kanta bai bi, kaitsaye ya nufi bedroom ɗinsu Ya tura ƙopar ya shiga, tun daga kan Kayan Hajiya adama data tube ya fara Cin karo da su yashe a ƙasan tiles, Ko'ina na ɗakin ta hargitsa shi, tsayar da idanuwan shi yayi akan hajiya adama da ke kwance ƙasa ta baje sai sharar bacci take yi hada minshari, Ga kwalaban Soju ɗin da tasha nan Ajiye saman table,
"YA SALAM" rai a6ace ya ambaci hakan, kutsa kai yae cikin ɗakin A ƙasa yayi toxali da hotonsu Uzair, wanda hajiya adama ta jefar ƙasa, zuƙunnawa yayi tare dakai hannu ya ɗauki hoton nasu yana kallo,
Nan take ya gane dalilin shan giyar nata, in har zata cigaba da kallon hotonsu uzair, to kuwa bazata ta6a daina shaye shaye ba, ba irin faɗan da baiyi mata ba akan tadaina amma taƙiya,
Takawa yayi zuwa jikin bangon ya liƙa hoton, kafin Ya nufi inda take a kwance ya zuƙunna, ya jima yana kallonta, hannu yakai saman ƙafarta yaɗan bubbuga, Shiru bata farka ba, Sai da yayi dagaske Sannan Ta buɗe idanuwanta waɗanda sukayi jawur dasu, Tana kallon shi,
"Get up, Ina son magana da ke" da alama har yanzu wine ɗin bata sake ta ba, daƙyar ta lalla6a ta miƙe zaune tana faman yin hamma,
"Waya kawo wannan abun Cikin gidan nan"? Ya yi tambayar yana nuna kwalaban Soju É—in da ta sha, fuskar shi a murtuke,
"Ni na kawo su, don su É—ebe mini kewa,"
"Narasa gane meke damunki? Meyasa kullum burinki ki 6atamun rai? Kin manta sharuɗɗan da dr park ya gindaya maki akan lafiyarki? Kina tunanin shan wine ɗin da kike yi shi ne mafita agare ki? Yakai ƙarshen maganar yana kallonta,
Sai faman lumshe ido take yi,"magana fa nake yi maki? Harara ta wurga mashi"To Ubana Alhaji Adamu, Zaka fara faɗan naka ko? nasan bai wuci kace haramin bane shan giya, Zan illata lafiyata, bayan shi sai kuma me"? A harzuƙe tayi maganar tana kallon shi, har saida gabanshi ya faɗi ras! Saboda yadda ta rufe ido tana gaya mashi magana, lallai har yanzu bata dawo Cikin hayyacin ta ba,
Sassauta muryarshi yae, Cikin sigar lallashi yace"Allah ya huci zuciyarki, ni ba faÉ—a nace zanyi maki ba, Amma dan Allah kidaina shaye shayen nan baida amfani, idan damuwa ce tayi maki yawa Ki É—auko qur'ani ki karanta mana"
"Ka yanke shawara game da komawarmu nigeria? nifa na lura kamar baka damu da 6acewarsu ba, harkokin kasuwancinka kawai kasa agaba, NikaÉ—ai ce nasanya damuwa akansu, almost 2 years ban ta6a ganin ka tashi tsakar dare kayi Nafila a kansu ba,
Jinjina kanshi yae"Adama kenan, Ae duk cikakken musulmi wanda yayi imani da Allah, ya kuma yi imani da ƙaddara mai kyau ko mara kyau, Bazai ta6a zama ya ƙuntata kan shi ba don Allah ya jarabce shi, Nasan cewa aduk inda suke Allah yana atare dasu, Kuma inayi masu addu'a, wannan ma ya wadatar ba dole saina tashi tsakar dare ba, bansani ba ko so kike in ajiye harkokin kasuwancina, In sanya damuwa araina a ƙarshe Nima in koma ɗan giya,' hannu tasa ta dafe gefen kanta, hawaye masu ɗumi suka soma shararowa mata,
Ruƙo hannayenta ya yi Cikin nashi"Ki faɗamun kome kike so zanyi maki, Amma dan Allah kidaina shaye shayen nan kodan saboda lafiyarki, bana so kema in rasa ki kamar yadda narasa iyaye na, da kuma ya'yana," cikin shessheƙar kuka tace"Mu koma Nigeri, Nagaji da zama a ƙasar nan, ƙwara idan ina acan zanfi samun kwanciyar hankali,"
"Shikenan, Zanyi abunda kike so amma ki É—an bani lokaci, In kammala wani aiki da nake yi, da zarar na gama zamu koma can É—in kamar yadda kikeso,"
Gyaɗa kai tayi"wannan karan idan har baka Cika min alƙawarina ba, sai dai kawai kaji labarin Na tafi,"
"In sha Allah hakan bazata faruwa," sosai ya kwantar mata da hankalinta, Har ya samu Ta shiga toilet tayi wanka ta canza kaya, Da kanshi ya gyara masu É—akin, ya tattara kwalaban Soju É—in ya fita yaje ya jefar dasu, Sannan hankalin shi ya kwanta,