Sashe 103
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga gefen gadon angel ya zauna, Yana binta da kallo, sai yaji sam baya son ya tada ta daga bacci, saboda sanin tsiwarta, Its better ya ƙyale ta zuwa wani lokaci, A hankali Ya ajiye robar ruwan daga ƙasa, ya haura saman gadon, ya sanya hannayen shi biyu ya damƙi ƙafafuwanta, A tsanake Yake daddana mata su, Yana yi mata tausarsu, duk inda ya ta6a sai kaji ya bata sauti ƙass, daga bisa ni ya ruƙo yatsun hannayenta, Ya dinga jansu, bayan ya kammala, Ya kwanta daga gefenta, idanuwanshi akan fuskarta,
"Idan tana bacci tafi kyau, da sanya zuciya natsuwa, amma idan tafarka, tsiwarta tafi komai É—aga hankali," da wannan zancen zucin bacci yayi awon gaba dashi,
Daƙin yai tsit, Ba ka Jin sautin komai saina minsharinsu,
Bayan wani lokaci, Hasken fitilun saman É—akinsu Ya gaure ko'ina, wanda ke nuni da cewa gari ya waye, babu alamun masu bacci zasu farka,
Motsin buɗe ƙopa ne Ya karaɗe kunnuwan danish, A hankali Ya ɗan ware sexy eyes ɗinshi, ya yunƙura ya miƙe daga zaune ya jingina bayan shi da bango, Angel na a kwance gefenshi, idanuwanshi sai faman lumshewa suke Yi, da alama baccin bai ishe shi ba, jikinshi duk ba daɗi, A buƙace yake da son Yin wanka, gaba ɗaya hankalin shi ya koma kan staircases jin Sautin tafiyar mutane.
Giants ne suke shigowa hannayensu ɗauke da sabbin gadaje kalar nasu, duk mutun ɗaya yana ruƙe da gado ɗaya, A jere suke saukowa daga saman benan, kusan su Goma sha biyar, Kaitsaye suka wuce can Cikin ɗakin, 6angaren da gadajensu danish suke fuskanta, A nan suka jera sabbin metal beds ɗin da suka shigo dasu,
Duk akan idonshi, Bayan sun kammala jera gadajen, Sai ga Wani giant ɗin Ya shigo Hannun shi ruƙe da doguwar ledar kaya, mai ɗauke da sunan Prison, Bargunane acikinta tare da bedsheets da kuma pillow, Yana ƙarasowa Ciki, Batare da 6ata Lokaci ba, suka curo da zannuwan gadon suka shimfiɗa ma kowani gado, daga bisani suka ɗaura bargunan, tare da pillow, Bayan sun Kammala A jere suka Juya suka fuce daga Cikin ɗakin,
Mamaki ne ya kama danish, yayin da yake saukowa daga saman gadonshi, Ya nufi inda gadajen suke a jere, Yana ƙare musu kallo,
aranshi yace sabbin prisoners za'a kawo mana, Har mutun goma sha biyar? Mun cika talatin kenan," ta6e baki ya ɗanyi, Shi dai fatan shi Allah yasa kar akawo musu masu ɗan banzan surutu da tsiwa, Sai da yabi kowani gado ya ƙare ma numbobin jikinsu kallo, sun fara daga no16 har izuwa No30, Jinji na kai yai kafin Ya juya ya nufi gadon angel, daga gefe ya zauna, tare da kai hannu daga ƙasa gefen gadon, Ya ruƙo bottle water ɗin daya ajiye, har ya tarba hannu zai ɗibi ruwa ya watsa mata, Yaji motsin buɗe ƙopa, dakatawa ya ɗanyi yana jiran ganin wanene zai shigo, Yayi tsammanin xaiga new prisoners ɗin da za'a kawo musu, amma sai yaga Giants suna shigowa, Ukun farkon masu kawo musu abinci ne, Hannayensu ruƙe da wooden trays, Na bayansu kuma su biyu ne hannayensu ruƙe da wasu jibga jibgan akwatuna kusan guda biyu masu girma, Suna da tayoyi daga ƙasan su, daga bayan masu ruƙe da akwaitin, akwai wani Giant ɗin kuma hannun shi ruƙe da Floor laps Masu girma, daga gani zasu yi haske sosai idan aka kunnasu, Danish dai ya zubawa sarautar Allah ido, sai kallonsu yake yi,
A saman dining Carpet ɗinsu, Giants ɗin suka sauke kayan breakfast ɗin nasu, waɗanda ke a ruƙe da akwatin nan, a tsakiyar ɗakin suka ajiyesu, Saura Giant ɗin dake ɗauke da floor lamps a hannun shi, Daga ƙasa Ya ɗaura su, Atare suka juya hada masu kawo musu abincin suka fuce daga Cikin ɗakin, Fitarsu keda wuya, Danish ya soma Jin takun tafiyar wani kuma again yana saukowa daga saman benan, da sauri yakai idonshi kan me shigowa, Gaba ɗaya Jajayen kayane ajikin mutumin, doguwar riga ce bazai Iya tantance macace ko Namiji ba, gaban rigarsa taurari ne guda uku, hannunshi na dama yana a ruƙe da sanda Golden colour, daga gani tsohone, hatta takalmin shi jajaye ne, a bayanshi wasu Giants ne su Huɗu, kowanne hannayenshi na a ruƙe da kayan amfani na toilet, A tsakiyar ɗakin Mai sanye da jajayen kayan ya tsaya, Ganin haka yasa danish ya miƙe ya ɗan sara mashi, Da hannu yai mishi alamar Jinjina, kafin Ya juya ya kalli giants da suka zo atare, Da hannu yayi musu nuni da sashen shiga toilet ɗinsu, suka nufi Ciki suka shige, kusan Minti talatin Suna aciki, Kafin daga bisani suka shigo cikin ɗakin, Babu kayan da suka zo dasu a hannunsu, sun barsu acikin makewayin nasu,
Tamkar sojoji haka suke ƙame abayan Wannan ɗan tahalikin mai sanye da jajayen kaya,
Danish Yana a tsaye yana binsu da kallon mamaki,
Ware ido yayi ganin mutumin ya É—aga hannun shi É—aya ya É—aura shi saman fuskarshi, nan take ya zame mask É—in da ya 6oye ainihin fuskarshi, dattijuwace fara tass, launin idanuwanta blue ne, daga gani baturiyace, tana da dogon hanci, gaban kanta hurhurace,
Ƙayataccen murmushi tasakar ma danish tare da cewa"Ƴan uwan naka bacci suke Yi? Muryarshi na ɗan rawa yace"eh" lumshe idanuwanta tayi yayin da take kallonsu tace"gwanin ban sha'awa, tunkafin in fara zama acikin ku har naji kun kwanta mini araina,
aÉ—an ruÉ—e danish yake kallonta, kai daga ganinta kasan babu wasa atare da ita, Sam batayi kama da masu Imani ba.
"Zan tafi but I will come back. When they wake up, tell them that their new guardian has come to visit them," fuskarta asake tayi maganar,
Ya amsa mata da toh, Har ta ɗaga ƙafa zata juya sai kuma ta dan dakata, yayin da idanuwanta suka sauka akan Angel dake kwance saman gadonta, Shu'umin murmushi ne ya bayyana akan fuskarta tsohuwar, A hankali ta furta sunan ta
*Unaisa zaheer tajudeen Our destiny*
Ta ambaci hakan tare da juyawa ta nufi hanyar fita daga Cikin dakin,da sauri Giants ɗin suka Bi bayanta, bayan tafiyarsu danish ya maimaita kalmar ƙarshe da tsohuwar ta furta *Our destiny* kalmar ta tsaya mashi arai, yayi mamakin jinta, shin meyasa ta kalli angel ta ambaci sunanta a amtsayin ƙaddararsu? ta6e lips ɗinshi ya ɗanyi tare da komawa saman gadon angel ya zauna, A tsanake yake kallon fine face ɗinta, soft lips ɗinta sun bushe sosai, robar ruwan dake a hannun shi ya kai saitin bakinsa ya kur6i ruwan tare da watsa mata shi saman fuskarta..................
*â¤â¤â¤PRISONERSâ¤â¤â¤*
Ruwan na sauka saman fuskarta, awani irin firgice ta farfaɗo ta zabura zata miƙe, ga6o6in jikinta suka ƙi bata haɗin kai, wani irin raɗaɗin azaba taji a jikin ta, ba arziƙi Ta koma ta kwanta, Cikin shessheƙar ku ka take ambaton sunan daddynta bakomai idanuwanta su ke hango mata ba face waɗannan halittun da ta gani suna cuzgar naman Jikin daddayn, abun ya tsaya mata aranta, daƙyar ma sautin muryar ke fita saboda raunatar da la66anta suka yi, ga maƙoshinta dake abushe ƙamas tana cikin buƙatar ruwan sha, jikinta sai kerma yakeyi, a hankali danish ya ajiye bottle water ɗin daga ƙasa gadon, rumfa ya yi mata da ƙirjinshi yana jiran ta ƙarasa dawowa cikin hayyacinta, yana ganin ta fara ƙoƙarin buɗe idanuwanta, ya yi saurin sanya tafin hannun shi ya toshe mata ƙaramin bakinta, saboda gudun tsiwarta, yasan muddin ta haɗa ido dashi sai ta zazzaga mishi masifa, jin hannun mutun saman fuskarta yasa ta ƙara firgita, da ƙarfi ta buɗe idanuwanta tana faman zazzare su, launin gray ɗinsu ya ciza, eye lashes ɗin sun cukurkuɗe Cikin juna, kaitsaye eye balls ɗinta suka sauka akan fuskar danish, biji biji take iya ganin shi,
Muryarshi na É—an rawa ya fara yi mata magana
"Angel.....ki natsu ba ki da ƙoshin lafiya" a dabarbarce yayi maganar ganin irin kallon da take watsa mishi, wanda ke nuni da tsantsar ƙiyayyarshi da take ji,
Sassauta muryar shi yai batare da ya zame tafin hannun shi daga saman fuskarta ba, yaci gaba da cewa"Nasan yanzu bani da sauran mutunci a wurin ki, kin gaya mini cewa kin tsane ni, baki son gani na, Angel Ni mai laifi ne a wurinki, duk yadda xanyi maki bayani ba lallai ne ki fahimce ni ba, Amma bazan takura maki ba, idan har da akwai abunda za ki yi mini wanda zaisa ki huce haushinki a kaina, Ni na amince ki yi mini shi, amma kada kice xaki ƙaurace mini, zuciyata zata iya bugawa........" bai kai ga ƙarasa yin maganar ba, Sakamakon damƙar hannun shi da angel tayi, Cikin fushi ta janye shi daga saman bakinta, batare da ta tanka mishi ba, da yasan yadda take jin tsanar shi a halin yanzu da bai wahalar da kanshi ba wurin neman yafiya agare ta, ji take kamar ta shaƙe wuyanshi ta jijjiga shi ta buga kanshi jikin bango har sai ya sheƙe tukunna ta ƙyale shi, Ba don Allah yasa jikin nata ba isasshen lafiyace dashi ba, da ba abunda zai hana yau ta Illata shi,
Tuni yasha jinin jikinshi, domin kuwa yana ji a jikin shi irin tsanar shi da take Ji, wasu irin zafafan hawaye ne suka cika idanuwan shi, muryar shi tamkar zai fashe da kuka yace"Ki bani dama ta ƙarshe xan gyara kuskure na," lumshe idanuwanta ta yi, Yayin da maƙoshinta ke motsi tamkar tana haɗiyar wani abu, sam bata jin zata Iya tanka mishi gani take kamar in yaji muryarta zai ji sanyi acikin zuciyarshi, that's the reason why taƙi yi mishi magana, tafi son Yaji a jikin shi irin halin da ya jefasu, har abada baxata ta6a mantawa da abunda ya faru Jiya ba, duk irin alƙawarin da ta ɗaukar wa batul akan zata taimaki rayuwarta, bazata ta6a bari a cutar da ita ba. Yanzu ya tashi abanza kenan? taya hankalin ta zai kwanta? Bayan batasan awani hali batool take aciki ba, tana can hannun waɗannan azzaluman mutanan da deeja ta bata labarin ta gansu akanta, suna Cutar da rayuwarta, Sai ta dinga imagining ga batul can itama sun danneta tana ta kuka tana buge buge.
Lokaci ɗaya angel ta fashe da kuka mai sautin gaske, Hankalin danish ya tashi matuƙa, duk yabi ya ruɗe, yana so ya lallashe ta, Sai dai yana jin shakkar ta6ata,