← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 179

Sashe 76

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Angel tace"Ni dama nasan za'a rina, Mutanan nan raina mana wayau suke yi, Tsohuwa tayi mana ƙaryar cewa An kaisu treatment room inda za'a duba lafiyarsu, tsawon 2 weeks kenan, Ga shi yau an dawo dasu babu alamun sauƙi ajikin su, ga dukkan alamu ma wani sabon Ciwon aka jaza musu " rai amatuƙar 6ace angel tayi maganar tana huci, Mubeen yace"pls Mubi komai a hankali, ko dan saboda su Deeja, Ni inaga yakamata aje a sanarma tsohuwa tazo ta duba halin da suke aciki...."tun kafin mubeen yakai karshen maganar shi angel ta wurga mashi uwar harara, kamar zata rufe shi da bugu tace"Amma baka da hankali wlh, wai har yaushe ne zaku fahimci cewa matar nan Muguwace ba sonki take Yi ba, Kuma babbar maƙaryaciya ce! Tayi mana ƙaryar cewa A cikin satin da aka ɗauki su parveen za'a dawo dasu, Sai gashi yau tsawon 2 weeks kenan, Sannan bayan haka ta sanar damu cewa Su parveen sun samu lafiya harma suna tambayarmu, To yau gashi dai an dawo dasu Ba kamar yarda aka ɗauke su ba, kwata kwata babu cikakkiyar lafiya atare da su, ku baku lura da canzawar da su kayi bane? Muryarta a harzuƙe tayi maganar, Jijiyoyin wuyanta duk sun bayyana jikin fatarta saboda tsabar masifa, Kowa yayi shiru yana sauraronta, Cigaba da magana tayi"Kun maida kanku kamar gumaka, Ana cutarku baku ganewa, Yanzu ku kalli fuskokinsu deeja da la66ansu, wlh ko makaho ya shafa jikinsu sai yaji ajikinshi cewa basu da ƙoshin lafiya, Balle ku da kuke Mutane, Su parveen ba Maganin ciwonsu akayi musu ba, Ƙara musu wani ciwon akayi bisa wanda suke dashi"

Wannan bayanin Da angel ta kora musu Yasa sun fara Kokwanton Kalaman tsohuwa, Sun kuma fara yarda da ita,
Muryar hibba asanyaye tace"angel ae mu bamu san komai ba, Rayuwa kawai muke Yi acikin duhu, ba lallai mu iya fahimtarki ba," Haris Yace"Tun da kike atare damu ban ta6a Yarda dake ba, Saboda ina zargin ke ɗin Kamar babu gaskiya acikin lamurranki, Yau ce rana ta farko Da kika fara sanya mini kokwanton wani abu acikin raina, Sai dai bazan ta6a Yarda dake ba har sai kin bani kwakkwaran Hujja da zata tabbatar mani cewa Cutar da rayuwarmu ake Yi,' haris na kai karshen maganar shi, Batool tace"Muna goyan bayan haris, Idan har dagaske Ana Cutarmu a gidan kurkukun nan, To kiyi ƙoƙari ki bayyanar mana da kwakkwarar hujjar da zamu aminta dake, Ɗaya bayan ɗaya Angel ke binsu da kallo, wai wace irin hujja ce suke so Ta kawo musu? Bayan ga abu nan zahiri sun gani, acikin zuciyarta tayi tambayar, Tunawa da irin rayuwar da suka taso suna yi yasa ta Yi musu uziri, dole suna da ƙarancin fahimta, kansu Yana acikin duhun Jahilci, idan har bata lalubo hujjar da zasu Gasgata maganarta ba, to kuwa bazasu ta6a yarda da kalamanta ba, taya za'ae ta samo hujja bayan tsohuwa ta gargaɗe ta akan kada ta kuskura Tace zata Zurfafa bincike akan Gidan kurkukun, har ga Allah tana matuƙar fargabar Abunda zai biyo baya idan har tace zata Kawo musu hujja,

Sautin kukan Azeeza ne Ya jawo hankulansu, kusan atare suka Waiwaya baya suna kallonta, Har ta sauko daga saman gadonta, Sai faman laluban hanya take Yi tana faÉ—in" Wai bakowa ne akusa, Ni baza'a nuna mini su parveenar mu ba, dagaske an dawo mana dasu? Ina ta magana tun É—azu babu mai ji na,"

Kallon Naufal Haris yayi tare da cewa"Kaje ka ruƙo ta kada ta faɗi" Naufal ya amsa mashi da toh, Da hanzari Ya tunkari parveen, Yana ƙarasawa gabanta, Ya ruƙo hannunta acikin nashi, Ya janyota zuwa inda suke abakin benan, "to ina su parveenar suke Ae ban ganinsu" Tsoki Haris Ya ɗan ja"kefa matsalarki kenan abu kaɗan sai kuka, Kamar kinfi kowa baki, Ki barmu muji da abunda Ya ishe mu," a ƙule yayi maganar, cikin sanyin murya danish yace"haris ka bi ta a hankali, banaso kana yi mata magana irin haka" jinjina kai haris yayi tare da cewa na daina, kawai bana son yawan kukanta ne,"

"Ni dai ku nuna mini Su, kuma kuka bazan daina ba, Yanzu na fara sai dai ka buge ni" rai a6ace azeeza tayi maganar, mutumin dake fama da kanshi, kwata kwata bata iya ganin fuskokinsu, Biji biji take gani,

Matsar da ita naufal Yayi zuwa gabansu deeja da suka ƙame Sai shessheƙar kuka suke yi, ko gajiya basa yi,

"Gasu nan Agabanki Kiyi musu magana" naufal ne yae maganar, Hannayenta ta ɗaura asaman kirjin deeja tana shafata, Harta samu ta ruƙo hannunta ta ɗago shi zuwa saitin hancinta ta shinshina shi, duk suna kallonta, farin Ciki ne ya bayyana akan fuskarta, rungumeta tayi tana faɗin"Deeja Ashe kune dagaske, Nayi farin Ciki da aka dawo mana da ku, yanzu shikenan kunji sauƙi baza'a ƙara raba mu daku ba, Ni dai na roƙe ku kada ku ƙara Yin rashin lafiya, Kodan saboda kada araba mu daku, Saboda bamu jin daɗin rashin ganinku acikinmu" ita kaɗai take ta sambatunta, Javed ya kira sunanta"Azeeza Kiyi hakuri ki ƙyaleta, Basu son ana ta6a su, Har yanzu da sauran Jikin nasu" Cikin shessheƙar kuka tace"meyasa toh basu son ana ta6a su? Basuyi farin Ciki da dawowa Cikin mu bane? Duk irin kewarsu da muka Yi," babu alamun zata fahimce su, angel ce tace"Javed ka barta, tun da naga yanzu Deeja bata Yi ƙara ba kamar yarda tayi ɗazu da batool ta ruƙota," Eve tace"Nima na lura da hakan"

"Nidai kuyi mini magana, Wai sai kace baku Ji na, ko fushi kuke Yi damu ne"? matsawa tayi gaban Rubina Ta ruƙo hannayenta takaisu saitin hancinta ta shinshinasu, kafin ta faɗa jikinta ta rungumeta tana faɗin rubina, Kema bazaki Yi mini magana ba? Duk kun shareni," jin shiru bata amsa mata ba, yasa ta janye jikinta daga na rubuna, da alama Jikinta yayi sanyi, Ruƙo hannun Parveen Tayi, batare data shinshina shi ba tace"parveen, Ke ma ba za kiyi mini magana ba? Meyasa bakwa farin ciki da dawowarku Cikinmu ne? Duk irin kewarku damu kayi, Munji raɗaɗin rashinku acikinmu, Tun ranar da Giants suka zo suka tafi daku, Kusan kullum ne sai Mun ajiye maku abinci, amma abanza yake lalacewa, mun yi maraicinku sosai" takai kai karshen maganar tare da ɗaura kanta saman kirjin parveen, hada ƙoƙarin zagayo da hannayenta zuwa bayan parveen ta ƙanƙameta,

"Yanzu ya zamuyi da su? nifa nagaji da tsayuwa ƙafafuwana har sun fara Yi mini zogi, Yakamata Mu koma Cikin ɗaki Mu xauna, yasmin ce tayi maganar,

Kallonsu Deeja Angel ta yi tare da cewa"Ku zo mu shiga Cikin ɗaki, Nasan Kuma kun gaji da tsayuwa" pls ku wuce mu tafi dare yayi sosai" ta karasa maganar tare da nuna musu Hanya, sai lokacin deeja ta iya buɗe baki tace dasu"Ni bazan Iya tafiya ba, ƙafafuwana zafi suke Yi mini," Kallon Juna su ka yi, Hatta muryarta ta canza, kamar ba deeja da suka sani ba, Muryar parveen na rawa tace"Nima Bazan Iya tafiya ba, raɗaɗi nake Ji," daƙyar tayi maganar saboda raɗaɗin da bakinta ke Yi mata, wanda shi ya hana su yin magana tun ɗazu amma duk suna jin me suke cewa kuma suna fahimta,

Rubina tace"nima bazan Iya ba," lamarin yayi matuƙar ɗaure musu kai, Haris yace abunda za'ae yanzu, Zan Goya deeja abayana, danish ka goya rubina ita kuma angel ta goya parveen kai kuma naufal Ka taimaka Ma Azeeza ku shigo ciki, Zuƙunnawa su ka yi agabansu Deeja, Suka haye saman bayansu, Atare suka miƙe suka nufi Cikin ɗakin dasu, Sauran ƴan uwan nasu duk suna abiye dasu, A saman gadajensu suka sauke su, angel ta tambayesu ko suna jin yunwa, suka ce mata a'a, bacci suke so suyi sun gaji," acikin zuciyarta ta kudiri aniyar idan Suka farka gobe zata Tambaye su game da abunda ya faru dasu, duk da tasan zaiyi wuya su iya tunawa,
Basu kwanta bacci ba har sai da suka Ci abincin da giants suka kawo musu, bayan sun kammala ci suka koma saman gadajensu suka kwanta zuciyar kowannan su acukunshe take Da tunanin halin da suka riski Æ´an uwansu,

A daren ranar bayan kowa Ya koma saman gadonshi Ya kwanta, Angel tabi su ɗaya bayan ɗaya Ta tottofe su da addu'a, Ta lullu6e musu jikinsu da bargunansu, Wani abu daya ƙara ɗaure mata kai, A lokacin harta koma saman gadonta ta zauna ta ɗaga hannayenta sama tana Yin addu'o'i kamar yadda ta saba, Kwatsam Taji shessheƙar kukan Deeja, ga dukkan alamu mafarki take Yi, da hanzari angel ta sauko daga saman gadonta taje bakin gadon deeja ta ɗan ranƙwafa tare da kasa kunne tana sauraron me take cewa, Kuka take Yi tana faɗin bana so ku daina kuna cutar dani, zafi nake ji, kashe ni kuke Yi, Ni ku ƙyaleni ku rabu dani" Ciccije la66ata tayi tare da kai hannayenta saman mattress ɗinta tana damkar jikin katifar, Idanuwanta na fitar da ruwan hawaye, Can kuma sai taga deeja ta kai hannu tana sosa gaban wandonta, tana faɗin ƙaiƙayi take ji, zafi yake yi mata, mutuwa zatayi," Daga bisani ne Deeja tadaina sambatun da take Yi, taci gaba da yin baccinta

Haƙika angel tayi matuƙar girgiza duk da bata Iya gano komai game da sambatun deeja ba, amma Jikinta yayi mugun yin sanyi, tabbas tana hasashen An yi masu wani mugun abunne kuma agabansu a Kayi musu, tun da gashi nan ta gani da idonta deeja na sosa wurin tana faɗin cewa ƙaiƙayi yake Yi mata,

Ikon Allah kenan, An juya musu tunaninsu don kada su Iya tuna komai Da akayi musu, Amma sai gashi Allah Ya haska mata wani abu ta cikin mafarkin da deeja ta yi, yanzu ya rage nata tayi ƙoƙari ta gano me akayi musu,
Chapter 76 · 0% Book details