← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 179

Sashe 137

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

ruƙo hannun Majnun mubeen yai tare da jan shi zuwa gaban Danish da ke zaune gefen gadonsa, Yace"yanzu faɗa min tsakanin haris da Danish wanene fari"? Jin muryarsu yasa Danish kawar da idon shi daga kan fuskar Angel, ya dawo da dubanshi akan fuskar chinonso daya ƙura mishi ido, har wani kashe ido ɗaya yake yi.

"Idan har ya kasa banbance waye fari acikin su, to kuwa dole mu zubda chinonsu Cikin Kwandon shara, don banga amfanin shi acikin mu ba, abincin da yake ci ma ya tashi abanza," parveen ce tai maganar, kowannan su ya saki murmushi, Angel tace"da alama ƙarya ta ƙare, Ya tasa Danish gaba sai kallon shi ya ke yi, yaƙi magana"

"Kai muke jira" acewar mubeen, girgiza kai chinonsu yai fuskarshi a hargitsa ya kalli mubeen'"to..ae na kasa ganewa, shima haris ɗin ya dawo gefen shi ya zauna, sai in banbance" Miƙewa haris yai tare da komawa gefen Danish ya zauna, Suka tasa chinonso gaba Akan saiya gano musu wanene fari acikin su, shifa bilhaƙƙi Haris fari ne, Ya dai ce musu Danish yafi kyau, matsalar shi ɗaya Baƙi ne wulik, Shiyasa Haris yafi shi kyau, wannan maganar ba ƙaramar dariya ta basu ba, Ga dukkan alamu bayan ta6in hankali da yake dashi Chinonso yana fama da matsalar Gani, yau sun tabbatar da hakan, tun da gashi ya tabbatar musu da cewa Danish yafi kyau, sai dai baƙi ne, har tambayarshi su ka yi shi fa wani kala ne, yace musu shima baƙi ne

Mutumin da ya ke albino, hasken ma ya wuce na lafiya, Amma yana kiran kan shi da baƙi, kusan mutun uku fararen Cikin su, su ka tambaye shi ya faɗa musu wani kala ne su, yace musu duk baƙaƙe ne. Ba ƙaramin nishaɗi su ka yi ba a ranar, Lokacin da dare yai, Kowannansu Ya canza kayan shi zuwa tsoffinsu, Wanda suka maida na bacci, Kafin suka haura saman gadajensu suka kakkwanta.

Gabriel ya kasa runtsawa Yana zaune tsakiyar gadon shi, Sarai Angel ta lura dashi, hakan yasa itama taƙi kwantawa tayi baccin, Haka zalika, Danishi yaƙi runtse idanuwanshi, Ga bacci yana ji amma yaƙi bari ya ɗauke shi, Saukowa tai daga saman gadonta, zumbur Danish Ya mike zauna, tare da kallon ta yace

"Angel where're u going, ba zaki bacci ba" yatsina fuska ta ɗanyi tare da kallon shi" Addu'a nake so inyi maku kafin in kwanta...." tunkan ta ƙarasa maganar taga ya sauko daga saman gadon shi, Ya ruƙo hannunta acikin nashi tare da cewa"Nima zan ta ya ki, mu yi musu addu'ar a tare" dariyar yaƙe ta sakar mashi"kai da baka iya ba, taya zaka iya taya ni mu yi musu addu'ar?

"Ni dai muje," duk yadda taso ta yi mashi wayau don ya koma ya kwanta ita kuma ta samu damar zantawa da Gabriel Ya hana hakan faruwa, Atare su ka bi gadajen su Hannu tana karanta musu addu'o'i tana tottofa musu saman bargunan su, hatta sarah da ke a kwance ƙasa sai da ta zuƙunna ta yi mata addu'a, kafin ta miƙe bayan ta kammala, ta tsaya a Tsaye tana satar kallon Gabriel da ya hana idon shi bacci tasan duk don saboda ita ne, Ganin tana kallon shi yasa Danish damƙar hannunta yaja ta har zuwa saman gadonta, fuskarshi a ɗaure yace"ki kwanta ki yi bacci," ba tare da ta yi mishi musu ba, ta hau saman mattress ɗin ta kwanta, tare da ɗaura kanta saman pillow, ' ta yi tsammanin zai haura nashi gadon ya kwanta amma sai taga ya zauna gefen gadonta, Ya tsareta da waɗannan kyawawan idanuwanshi nashi

"Why danish? What's going on? Why don't you go to bed? You're bothering me." A hasale tai maganar tana jifar shi da harara, cikin sanyin murya yace"idan kina so in yi bacci to ki fara yi, if not sai dai mu kwana idon mu biyu," muryarta a takure tace"hakan ma bazata faru ba," runtse idanuwanta ta yi, zuciyarta nata saƙa mata yarda zata yi mashi wayau, yayin da shi kuma Man ɗin Ya jingina bayanshi da bango idonshi akan Gabriel, Dake zaune tsakiyar bed nasa.

A hankali ta ɗan buɗe idanuwanta, ta saci kallon fuskar Danish, miƙewa tayi zaune, Jin motsinta yasa shi kallon ta

Yamutsa fuska ta ɗanyi tare da cewa"Zan shiga toilet ne," ruƙo hannunta yai acikin nashi"muje in raka ki" fusge hannunta tai fuskarta a ɗaure tace"Banaso, Ka zauna anan inje in dawo," bai damu ba, tun da yasan ita kaɗai zata shiga, zai zauna ne ya tsare Gabriel kada ya motsa, Saukowa tai daga saman gadonta ta nufi sashen toilet ɗinsu, tana jiyo muryar Shi yana bata umarnin kada ta daɗe acikin toilet ɗin, idan ba haka ba zai biyo bayanta.

ta amsa mashi da toh, tana shiga ƙopar sashen toilet ɗin, ta juyo tana leƙen Gabriel, Dama abunda ya kai ta kenan, tun kafin ta shiga ran shi ya bashi cewar ba wani abu zatai acikin toilet ɗin ba, za ta je ne don ta samu damar yin magana dashi, Satar kallon Danish yai, ganin ya ɗan lumshe idanuwanshi yasa shi yin saurin kallon ƙopar shiga sashen toilet ɗin, cikin sa'a ya hango angel tana ɗaga mashi hannu, A hankali ya janyo pillow ɗinsa da ya jingina bayanshi da shi, Ya rungume shi a ƙirjinshi, Ya sanya hannu yana ta6a zip ɗin jikin shi, ta ɗauki tsawon lokacin kafin ta fahimci abinda ya ke son nuna mata, buɗe ido Danish yai tare da saukowa daga saman gadon shi, Ya nufi sashen toilet ɗin, da sauri Gabriel yai mata alamar gashi nan zuwa, kamar walkiya ta buɗe toilet ta shige, Yana shigowa wurin, ya soma kiran sunanta"Angel! Angel!" buɗe ƙopar tai tare da fitowa tana yarfa hannunta data wanko shi da ruwa, Kallon shi tai aranta tace"Jarababbe kawai" a fili kuma tace"lafiya"?

"Na jira ne baki fito ba, shine nazo in duba ki" harara ta wurga mashi, kafin taja hannun shi, suka koma É—akin, tace mashi"ka hau gadon ka, ka kwanta nima in kwanta a nawa, in yaso sai mu fuskanci juna" Ya amsa mata da toh, bayan kowannan su ya haura saman gadonshi, suka ci gaba da kallon juna, tun yana ganinta biji biji, har ya kai ga rufe eyes É—inshi, tsawon mintuna ta fahimci cewa bacci ne yai awon gaba dashi.

Ajiyar zuciya ta sauke, a hankali ta miƙe ta ɗauki pillow ɗinta, ta zuge zip ɗin ta curo ƴar takardar da Gabriel ya ajiye mata, ta buɗe ta cike da fargabar kada Ya farka, Saukowa tai daga saman gadonta ta nufi tsakiyar ɗakin nasu tana karanta wasiƙar, yayin da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi, wani irin ruɗani ne ya bayyana akan fuskarta, Takasa yarda da abunda Gabriel ya rubuta mata, Shin dagaske ne ya haura tagar nan ya shiga cikin prison ba tare da wani abu ya same shi ba? To ya akai ita ta kasa shiga? Can kuma ta koma tunanin yarinyar da ya ce mata ya gani tana neman taimakon shi, Anya kuwa Gabriel ba ƙarya ya ke faɗa mata ba? Sai dai kuma abunda zai sa ta iya yarda da maganar da ya rubuta mata, na farko bai yi kama da maƙaryaci ba, sa'annan idan har dagaske ƙarya yake yi mata to taya akai yasan da Tagar da aka cire glass ɗinta, nannaɗe takardar tayi tare da ɗagowa ta kalli shimfiɗar Gabriel, Har yanzu bai kwanta ba idanuwanshi na akanta, sai da ta fara juyawa ta kalli Danish da ke bacci, taga bai motsa ba, kafin ta maida dubanta ga Gabriel, Saukowa yai daga saman gadon shi ya tunkareta, hannunta ya ruƙo acikin nashi, Yaja ta suka shiga sashen toilet ɗin su, saboda su samu damar tattaunawa da juna ba tare da Danish Ya farka ba.

Ba acikin toilet su ka shiga ba, acikin sashen suka tsaya, muryarta da alamun mamaki tace"Abun da na karanta acikin wasiƙar nan taka dagaske ne? Jinjina mata kai yai"tabbas dagaske ne angel, naso tun time dana haura tagar na dawo ciki in sanar da ke amma Danish ya hanani yin hakan, Nasan ke kaɗai ce zaki iya taimaka min wurin nemo ƴar uwata tun da kema kina nema taki ƴar uwar, kuma naji awurin ƴan uwanki cewa, kina da burin fita daga Cikin kurkukun nan, shiyasa na ƙara samin ƙwarin gwiwar tunkarar ki in faɗa maki,' Tun da ya soma magana Angel ta ke binshi da kallo mai tattare da tsantsar mamaki da al'ajabi, Shi dai gashi ba musulmi ba, amma wani iko na Allah, ya samu damar shiga prison ba tare daya fuskanci irin matsalar daga fuskanta ba, a lokacin da ta dira tagar, ta wani 6angaren kuma ba ƙaramin daɗi taji ba, atlease ta samu wani mai ra'ayin son guduwa daga prison, idan su ka haɗa hannu dashi zasu iya sama ma kansu mafita.

"Angel kin yi shiru bai kamata muna 6ata lokaci ba, wannan ce damar da mu ke da ita, ta taimakon yarinyar nan, ita ka É—ai sai garari take yi acikin prison" fuskarshi da alamun damuwa yai mata maganar.

"Gabriel, ina kokwanto fa, zai yi wuya ace mutunce ita, may be barazana aka yi maka da ita don a tsorata ka, Nima time dana fita an tsoratar dani ta hanyar nuna min daddyna wasu haluttu munana suna cin naman jikin shi, aranar nasha wahala, ba don Allah yasa Danish yaje ya ɗauko ni ba, da shikenan tawa ta ƙare" girgiza mata kai Gabriel yai"Bana tunanin cewa anyi min barazana da itane, mutunce ita Angel I saw her from the top of the third floor. She was running, looking for help. fara ce kamar ke, tana da yawan sumar kai kalar naki, itama nata, Nannaɗaɗɗe ne harma yaso yafi naki yawa da nannaɗewa.......'

Tun da ya suffanta mata matashiyar yarinyar, Hankalinta yai matuƙar tashi, Ta zazzaro idanuwanta waje, La66anta na kerma ta furta sunan"BATOOL" domin kuwa a bayanin da ya yi mata kaf irin suffar batul ne,

"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un! Wlh inaji araina Æ´ar uwatace batul," tuni hawaye sun wanke mata fuskarta, jikinta ya kama kerma.
Chapter 137 · 0% Book details