← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 179

Sashe 166

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Dan Allah kada ku cutar mu, Ku ƙyale mu mu yi rayuwarmu, Lafin me mu ka aikata ma ku ne, da ku ke son ƙarar da mu....." Kafin Deeja ta ƙarasa maganar tsohuwa zafreen ta buga sanar hannunta, muryarta a kausashe tace"Ban baku iznin Yin magana ba, " tun da ta ambaci hakan babu wanda ya ƙara magana, A hankali ta ɗaura idanuwanta kan fuskar Angel ta soma magana yayin da take tunkararta

"ZA6I UKU ZAN BAKI! A CIKI DOLE KI ÆŠAUKI ÆŠAYA, SAKAMAKON RASHIN KUNYAR DA KIKA YI MINI"! runtse ido Angel ta yi Jikinta na kerma zuciyarta a tsorace ta ke da fargabar jin Za6in da Tsohuwa zafreen za ta furta mata.

A tsanake tsohuwa Zafreen Ta ci gaba da cewa" za6i na farko shi ne I will order the giants to do terrible things to your sisters while you watch, or I will kill two of your sisters. The last option is that you will no longer get healthy food. From now on, you will only have to eat leaves like animals, Sannan ruwan shan ku zai koma na zafi,"

Tsabar tashin da hankalin ta yai batasan sa'adda ta furta Innalillah wa'inna ilaihirraji'un! Muryarta adisashe .

Haƙiƙa ta yi danasanin maganar data gaya wa tsohuwa zafreen, Wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke fuskarta, Muryarta A raunace ta soma magana

"Idan har maganar dana faɗa maki ce tasa kika bani wannan za6in, ina neman alfarma a wurin ki, Ba dan hali na ba, zan zuƙunna akan gwiwowina dan in nemi yafiyarki, saboda ni na yi maki laifi bai kamata hukuncin da za ki yi mini ya shafi ƴan uwana ba.

Girgiza kai tsohuwa zafreen tayi tare da cewa"kin ƙara tabkar wani kuskuren, Ni Ba'ayi min jayayya, sannan idan na zartar da hukun ci, babu wanda ya isa yasa in canza, Bayan haka kina yi min magana idanuwanki a cikin nawa, Anya kuwa kinsan wacece tsohuwa zafreen? Ta yi tambayar da izza, Angel dai bata ce komai ba, Jikinta duk yai sanyi.

"Idan ba ki za6i É—aya daga cikin za6in dana lissafa ma ki ba, zan aiwatar da duka uku" fuskokin su Deeja tabi da kallo bayin Allah, Jikin su sai kerma ya ke yi, da yatsun hannayen su su ke yi mata nuna da ta É—auki za6i na uku, duk da basu san menene ganyan ba hankalin su yafi kwanciya da shi tunda abin ci ne.

Zuciyar Tsohuwa zafreen ta hasala sosai Jin yadda ta yi shiru bata amsa mata ba, har ta buɗe baki zata zartar da hukunci muryar Angel ta katse ta da cewa"Za6i na uku amma duk da haka ina baki haƙuri, akan ki cire ƴan uwana daga horon da zaki bani" Girgiza kai tsohuwa zafeen ta yi fuskarta babu sassauci rashin imani ne tsantsa,
Juyawa tayi tare da nufar Benan É—akin da sauri gaints É—in dake take mata baya su ka bi bayanta, atare su ka fuce daga cikin É—akin.

Zubewa Angel ta yi saman gwiwowinta, sosai ta fashe da matsanancin ku ka tamkar ranta zai fita, takaici duk ya ishe ta, ji ta ke kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu saboda baƙin cikin halin da ta jefa ƴan uwanta.

Tsananin tausayinta ne ya kama su Deeja, Jiki asanyaye su ka nufo wurinta hada su azeeza da ke a 6oye ƙarƙashin gado, A kewaye da Angel suka zuzzuƙunna suna lallashinta, Cikin shessheƙar kuka tace"Na tsani kaina, nayi danasani, zuciya ta ja mini na gaya mata magana, ga shi yanzu naja ma ku Cin ganye, Duk laifina ne, ni da ya kamata ace ina taimakon ku sai gashi ni nake ƙara jefa maku cikin matsala, " daƙyar ta ƙarasa maganar.

"Angel Ki yi haƙuri ki daina zubar da hawayen ki, ki daina ɗaurawa kan ki laifi, Allah ya riga da ya ƙaddara faruwar hakan, pls kidana kuka bamu san ganin hawayen ki na zuba" Deeja ce ta yi maganar, Sarah tace"tun farko banso kika tanka mata ba, da duk hakan bata faru ba" idanuwanta jawur ta kalli fuskar Sarah da ta yi maganar ta mayar mata da martani"wlh zuciyace ta ɗebe ni, bansan ma na furta mata maganar ba, amma meyasa zata hukunta mu, mu duka bayan nice mai laifi"? Cikin ƙunar rai ta yi maganar, Batul tace"Saboda zalunci! Dama ai ba zata ɗauki mataki akan ki ke kaɗai ba , saboda kin nuna baki tsoronta, shiyasa ta haɗa damu don ta ƙuntata ki, kuma in sha Allah ba abunda zai faru damu, Ki kwantar da hankalin ki Angel, su ci gaba da kawo mana ganyen zamu ci, ruwa kuma ai muna da shi a cikin toilet sai mu koma muna shan na fanfo, ba dole sai wanda su ke kawo mana ba, '

Idanuwanta arauna ce ta ke bin su da kallo mai nuni da tsantsar tausayin su da ta ke ji, ta lura basu san me ganyen ya ke nufi ba shiyasa su ka aminci za su ci, duk da acikin za6in da tsohuwa zafreen ta bata shi ne mafi sauƙi agare su.

Muryarta asanyaye tace"Amma ae ba ku saba cin ganyen ba, ba mu san wani irin ganye zasu kawo mana ba, ina jin fargabar su kawo mana wanda zai cutar damu"

Cikin kwantar da murya Hanna ta soma magana" kada ki damu kan ki, Da daÉ—i da ba daÉ—i zamu ci"

Ta yi mamakin kalaman su agare ta, maimakon su ji haushin Abunda taja masu amma sai ga shi suna lallashinta.

A hankali ta ɗaura idanuwanta akan fuskokin su Azeeza da Jamimah da Parveen tun kafin ta yi masu magana parveen ta riga ta cewa "ba sai kin ce komai ba Angel, kwanciyar hankalin ki yafi mana komai, tabbas naji ba daɗi saboda ƙaunar da ke a tsakanina da abinci amma na haƙura tunda bamu da za6i, ƙaddarar mu ce tazo mana a haka, zamu jure muci ganye....." runtse ido Angel tayi yayin da hawaye ke cigaba da tsastsafo mata saman kuncin ta.

Cikin sanyin murya Azeeza tace"Nima bani da matsala Angel, zanci ganye da babu ƙwara ba daɗi, sannan duk runtsi duk wuya idan Allah yaso mu rayu ba wanda ya isa ya hana, nidai fata na shine Allah ya ba ki ikon ku6utar damu daga Cikin kurkukun ƙaddarar nan, wlh banaso in mutu acikin shi, " maganar Azeeza ta yi matuƙar ta6a zuciyoyin su, su kansu basu fatan suyi wulaƙantacciyar mutuwa a gidan kurkukun kamar yarda ƴar uwarsu Unaizah ta yi, idanuwan Angel jaga jaga da hawaye ta ke kallonsu ɗaya bayan ɗaya.

Muryar jamimah tamkar zata fashe da kuka tace"Nidai banason ganye, na saba da cin nama, amma in dai Genie ɗita zata daina kuka to nima zan haƙura inci ganyen" Murmushi ne ya bayyana akan fuskokinsu, Da sauri Angel ta miƙa hannu ta ruƙo Jamimah zuwa jikinta ta rungumeta sosai tamkar zata mayar da ita cikin cikinta.

"Nima bani da damuwa Angel, duk idan na tuna abunda kika faÉ—a mana dangane da irin tanadin da Allah yayiwa bayinsa salihai, waÉ—anda suka yi imani dashi sannan su kayi tawakkali, basu sa6a mashi ba, Sai inji daÉ—i araina, wahalar mu a gidan duniya ne, idan muka mutu zamu ji daÉ—i," sosai Angel ta kuma fashewa da wani kukan jin abunda Yasmin tace.

"Yana daga cikin rukunan Imani mutun yayi imani da ƙaddara mai kyau da mara kyau, kamar yarda kika koyar damu, don haka munyi imani da ƙaddararmu, zamu rungume ta hannu bibbiyu, har zuwa lokacin da Allah zai ɗauki ranmu mu huta, amma duk da haka bamu sare ba, sannan bamu fidda rai da rahamar ubangiji ba, wata rana zamuji daɗi sai dai bamu sani ba, jin daɗin namu daga gidan duniya zai fara ko kuwa sai mun koma gare shi Allah wa'alamu," eve ce ta yi maganar, hibba tace"ai ni tunda Angel ta faɗa mana cewa kowa zai mutu harda waɗanda suka cutar damu da waɗanda suka sadaukar da mu, wlh sai naji daɗi araina, tunda ba dawwama za mu yi acikin duniyar nan ba, dukkan mu zamu koma ga mahaliccinmu ne, Allah zai yi mana hisabi tsakanin mu dasu zaibi mana haƙƙin mu, aranar da basu isa su ƙwaci kansu ba, " Maganganun dasu ke yi sun yi matuƙar faranta ma junansu, Musamman Angel taji daɗi da su ka yi imani da ƙaddarar rayuwarsu, a shirye su ke da su fuskanci kowani irin ƙalubale da zai zo masu acikin arayuwarsu a mutu ko ayi arai.
Chapter 166 · 0% Book details