← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 179

Sashe 47

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin shessheƙar kuka tace"Idan ka ta shi ka kashe ni dan Allah, kada ka barni da rai na, meyasa zai ce na ɗauki wuƙa? Ina ruwan shi? Idan har bai shiga hurumina ba ni zan shiga nashi ne"? Ta yi tambayar a ƙule,
Batool tace"ban goyi bayan wani a cikin ku ba, Amma laifin danish nafi gani, meyasa za ka tona mata asiri don ta ɗauki wuƙa? Menene naka aciki? Juyawa ta yi kan angel'ke kuma angel baki kyauta ba, kalli yadda kika raunta shi, sai kace ba ɗan uwanki ba...."tunkafin takai ƙarshen maganar angel tace"danish bazai ta6a zama ɗan uwana ba, bana son shi bana ƙaunar ganin shi,"
Jinjina kai batool ta yi"its okey, daga yanzu zan shiga tsakanin ku, kada wanda ya ƙara shiga hurumin wani ina fata hakan ya yi,"
Javed yace"idan ma suka ƙara ni da kaina zan sanar ma tsohuwa a ɗauki mataki akansu,"
daga haka Haris da su mubeen suka kama hannun danish su kayi mashi jagora zuwa saman gadonshi, kwanciya saman gadon ya yi bawan Allah har wani jiri yake gani acikin idanuwanshi, shifa bakomai yasa ya tona ma angel a sirin ta ɗauki wuƙa ba, face sanin irin tsanar da tayi mashi, tsoron shi kada ace shi zata yanka da wuƙar wannan dalilin ne yasa shi tona mata asiri, ashe da rabon yaci na jaki a hannunta,
Miƙa mata hannu azeeza ta yi"ki tashi muke ki kwanta, ki huta" sai da ta ɗanyi jim kafin ta ruƙo hannun azeeza ta miƙe, saman gado ta koma ta zauna, hawaye sha6a sha6a akan fuskarta, danish ya tarwatsa mata plan ɗinta, taji takaici kamar ta sanya pillow ta taushe ma shi fuska haka take ji,
"Angel me zaki yi da wuƙa"? batool ce ta yi mata tambayar, ɗagowa angel ta yi tare da kallonta, tana a tsaye gefen gadonta,
Girgiza kai ta É—anyi"babu komai, kawai inaso na mallake ta ne," É—an zaro ido batool ta yi"karfa ace wani kike harin kashewa a cikin mu" cikin zolaya ta yi mata maganar,
Cikin sanyin murya angel tace"a'a batool bazan iya kisan kai ba, ni kawai naso ace na mallaki wuƙar,"
"Da ace kina shiri da danish, da ya aro maki wuƙar shi," da mamaki angel ta kalle ta tare da cewa"yana da wuƙa"? Jinjina mata kai ta yi eh, akwai wata ƙaramar wuƙa da yake amfani da ita wurin datse gashin kan shi, tsohuwa ce ta bashi wuƙar lokacin da ya ta6a tambayarta yana so ya rage tsayin sumar kanshi, shi ne ta ba shi wuƙar to bai mayar mata da ita ba, har yau tana nan a wurin shi,"
Dafe kai angel ta yi tare da satar kallon danish dake a kwance saman gadonshi, da alama bacci ya yi awon gaba dashi, yadai sha wahala,
"Ga samu ga rashi" ta ambaci hakan acikin azuciyarta, tasan koda me take yawo danish bazai ta6a ara mata wuƙar shi ba
Kallon batool ta yi"kinsan inda yake 6oye wuƙar" kallon sama batool ta ɗanyi da alama tunani take yi, can tace"a ƙarƙashin katifar gadonshi naga yana 6oye ta,
Angel tace"ki taimaka kice ya ara maki ita a matsayin ke zakiyi amfani da ita,
Ɗan zaro ido batool ta yi"ae bai yadda ya fiddo da wuƙar nan, kaifi ne da ita tana da haɗarin gaske, kona tambaye shi bazai bani ba, saboda yasan ba abun da zan yi da ita,"
Jinjina kai angel ta yi"shikenan na haƙura" daga haka bata kuma cewa komai ba, ta koma ta kwanta amma fa bawai ta haƙura bane, a can cikin zuciyarta tana shirya yadda zata sace wuƙar danish batare da sanin shi ba, da wannan tunanin ta yini da shi kuma ta kwana,

A daren yau ta kammala shirya yadda zata ɗauke wuƙar, kowa ya yi bacci saman gadonshi, duk sun lullu6e da bargunansu, angel ce kaɗai idonta biyu tana kwance idonta na fuskantar ceilling duk da duhu babu wadataccen haske saina fitilun ɗakinsu da suka kunna,

"Lokaci ya yi da zan tashi inje saman gadon danish in ɗauke wuƙar sa," acikin zuciyarta ta yi maganar, tana ƙoƙarin miƙewa tajiyo takun tafiyar mutun acikin ɗakin nasu, da sauri ta koma ta kwanta cike da fargabar wanene a dai dai wannan lokacin ya faɗo masu ɗaki,
Ƙyalla ido ta yi daga kwancen da take tana satar kallon inda take jiyo sautin tafiyar, kaskon turaren wuta ta hango a hannun mutumin dake zarya cikin ɗakin nasu, wani irin baƙin hayaki ke tashi daga cikin kaskon, kamar ana turara turaren wuta,
Mutumin dake ruƙe da kaskon turaren wutar, jikin shi na a sanye cikin doguwar riga me hula launin ja, rigar har ja take ƙasa,
Kasa kunne angel tayi tana sauraron muryar mutumin dake magana, kamar muryar tsohuwa sai dai bata iya tantance da wani yare ake magana ba, wani irin gu6ataccem yare mara daÉ—in ji,
Nan fa hankalin angel ya É—an tashi, xufa ta wanke fuskarta, duk ta sha jinin jikinta, tsoro take ji kada ace wani mugun ne yazo cutar da su,
Bata kai ƙarshen zancem zucin nata ba, ta hango mutun yana tafiya a bakin gadajen su Hannah, yana tafiya yana hura masu hayaƙin zuwa saman jikin su,
Da sauri angel taja bargo ta lullu6e fuskarta, acikin zuciyarta tana ambaton la'ila ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalamin," lokacin da mutumin yazo saitin gadonta, da sauri ta sanya tafin hannayenta duka biyun ta toshe bakinta da hancinta, duk don saboda kada hayaƙin ya samu damar shiga jikin ta,
Tana jiyo takun tafiyar mutumin yadda kasan takun tafiyar jaki,
Lokaci ɗaya tadaina jin takun tafiyar da kuma surutan da mutumin ya ke yi, da sauri ta ya ye bargonta, tabi ko'ina da kallo bata ga kowa ba, alamar mutumin ya tafi, sai dai hayaƙin daya turara masu har yanzu bai gushe ba,
Saukowa angel tayi daga saman gadonta, Zuciyarta cike da ruɗani, ko wanene mutun nan daya zo masu a tsakiyar dare, sanye da jajayen kaya? Turaren menene yake hayaƙa masu a cikin ɗakinsu da kuma saman jikin su? sam bata yadda da hayaƙin nan ba, tafi tunanin wani mugun abunne aka turara masu,
Tunawa ta yi da surori da kuma addu'o'in da malaminsu na makatantar islamiyya ya ta6a koya masu yace su yawaita karansu domin neman kariya daga sharrin mutun sharrin aljan da duk wani abun cutarwa,
"Zan tai taimaka masu, saboda basu da maiyi masu addu'a, a kullum in na kwanta ina bacci, daddyna yana yi mun addu'a, su kuwa basu da iyayen da zasu yi masu addu'a" acikin ranta tayi maganar
Kamar yadda mutumin nan yabi ko'ina na ɗakin yana turara Masu baƙin hayaƙin nan, itama haka ta soma bin kowace kusurwa ta ɗakin nasu tana karanta Ayatul kursiyyu, da amanar rasuli, Suratul mulk, Suratul kafiroon, Suratul ikhlas, falaqi da nasi, duk in ta karanta kowannan su Saita maimaita, daga bisani tabi kowani gado tana tottofa masu addu'oin saman bargunan da suka lullu6a da shi, daga kan gadon hanna ta faro xuwa gadon mubeen har zuwa gadajen su batool, tana zuwa kan gadon danish taja guntun tsoki zata wuce, sai kuma taji aranta kamar bata kyauta ba, don me zata yi ma kowannan su addu'a amma shi ta kasa yi ma shi saboda me? Lafin me ya yi mata? shiru ta yi tana tunani, menene ribar ta idan taƙi yi mashi addu'a,

Har ta kusa wuce gadon shi taja da baya ta koma tare da shiga daga gefen gadon, ranƙwafawa ta ɗanyi saitin fuskarshi ta soma karanto addu'o'in bayan ta kamalla ta tottofa mashi saman fuskarshi, kamar daga sama taji an damƙi hannunta, a razane ta kalle shi ashe ya farka, muryar shi a disashe yace"tsanar takai har ki zo kan gadona kina tofa mun miyau asaman fuskata"? Zuba ma shi ido angel ta yi batare da tace Furta komai ba, tama rasa bakin magana, yadda ya yi mata maganar ita kanta ta yi mamaki sai kace ba wannan mai jin shakkartata ba, bakomai yake jima tsoro ba, face wannan kalmar da take faɗi na cewa zata tofa ma mutun charman dudu Cikin shi ya kumbura, tuna wannan yasa shi ƙara tsorata, shi kanshi baisan yana da ƙwarin gwiwar yi mata magana irin haka ba,
tsawa ya ɗanyi mata tare da cewa"Ba ki ji ina magana ba"? Still ta yi ma shi shiru saboda bata jin zata iya faɗa mashi cewa addu'a take yi mashi, don ma kada yaji kamar tana ƙaunarsa ne,
Ganin ta yi mashi shiru ya ƙara har zuƙa, A tsananin tsorace Ya damƙo ƙasan rigarta da ƙarfi da niyar ya goge abunda ta tofa ma shi asaman fuskar shi, Cikin rashin sa'a ya janyota gaba ɗaya ta faɗa saman jikin shi..................🥱

*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*

dukkan ilahirin jikin shi rawa yake yi, kusan suman kwance ya yi saboda tsabar tsoratar da ya yi jin Angel saman jikin shi ɗungurugum, zuciyarta har wani tafarfasa take yi saboda tsabar fusata, a rayuwarta ta tsani jikinta ya haɗu dana ɗa namijin da ba daddynta ba, kamar ta haɗiyi zuciya take ji, tayi Niyar idan ta ɗago ta kwashe shi da zazzafan mari, Sai dai wani yanayi da ta tsinkaye shi a ciki ya yi silar dakatar da ita, lokacin da jikinta ya haɗe da nashi wani irin zafi taji rau tamkar hucin garwashin wuta, lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai, ta fahimci cewa baida ƙoshin lafiya, da alamun zazza6i attare dashi numfashinsa kanshi da hucin zafi yake fita, gaba ɗaya jikin nashi a raunace yake, Ga fargabar angel dake a kwance saman shi, yasha jinin jikinshi a tsorace yake da tsiwatarwa, baiso ta tayar mashi da lalurarshi

daddagewa tayi tare da yunƙurawa ta ɗago daga jikin shi, tarwatsastsiyar sumar kanta ta sauka har saman wuyan shi, a raunace ta kalli kyakkyawar fuskarshi, sama sama yake numfashi ya lumshe sexy eyes ɗin shi bai kai ga datse su ba, shima ɗin ita yake kallo, farar fatar wuyan shi tabi da kallo, ta ko'ina Jan tabon yakushin da ta yi ma shi ne,

Sun ɗauki tsawon lokaci A saman gadon Batare da wani ya furta wata kalma ba, idanuwansu acikin na juna, Jira yake ya ga wani Irin hukunci zata yanke mashi don yasan ba ƙyale shi za ta yi ba, tana iya cewa xata karanta mashi charman dudu, Cikin shi ya kumbura,
Chapter 47 · 0% Book details