Sashe 85
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read
Azeeza tace"Saura ɗaki ɗaya ya rage, wa za'a bamawa" angel tace"Na daddyna ne idan Allah yasa yana araye, ko ince daddynmu" gaba ɗaya suka saki murmushin farin ciki, parveen tace"amma kina ganin daddynki zai so mu," angel tace sosai ma, In ma daddyn nawa baya araye, zamu zauna wurin auntyna adama ne, Ko gidansu aunty aneelerh na, zasu ɗauki nauyin duk wani abu da zamu buƙata, Cin mu shan mu da suturarmu, kuma zamu yi rayuwar ƴanci, Zamu je inda muke so, Muje shan ice cream, muje cinema kallo, hada shopping mall zamu dinga zuwa kowa ya za6i abunda yake so, " parveen na murmushi tace"Zamu dinga samun abinci akai akai"? Dariya angel tayi tare da cewa"Sau uku arana, za'a bamu breakfast, lunch and dinner, Idan ma kinga dama tsakar dare kika farga da yunwa zaki Iya zuwa kitchen ki girka abunda ranki yayi maki, " Gaba ɗaya suka sanya ihu suna murna jin tace zasu Iya girki da kansu, Ga kuma abinci available, A lokacin jikin angel yayi mugun sanyi, ganin yadda suke ta farin Ciki, gani take kamar bazasu rayu ba, balle aje ga maganar fita daga Cikin wannan Kurman kurkukun ƙaddarar,
Batool tace"wlh angel baki ji irin daɗin da naji ba, sai naji dama ace yau mu fita daga kurkukun nan, muje gidanku, kinga shikenan mun rabu da giants, bazasu ƙara zuwa su ɗauki wani acikin mu ba, balle har su cutar dashi,"
Azeeza tace"Nima na ƙosa inga ranar da zamu fita daga prison ɗin nan, wlh Ina so inyi rayuwa irin wadda ki kayi tare da daddynki, ae kince mana zai so mu, muma zai maida mu kamar ya'yanshi, zai dinga zuwa damu yawo yakaimu wuraren da kika bamu labari ko"? Angel tace"Eh, kuma koda ace babu daddyna, akwai sauran dangina duk zasu so ku, kuma zasu gatanta ku kamar ya'yansu ku," acikin zuciyarta tace"sai dai fitar ce keda wuya, bansan ya zamuyi ba, gidan kurkukun nan yafi ƙarfi na, sai dai bai fi ƙarfin mahaliccin mu ba,
Har dare Yayi suna fira Gwanin ban sha'awa, ta faranta musu sosai, Bayin Allah sun ƙwallafa rai da son yin irin rayuwar da tayi, wato rayuwar ƴan ci, yanzu a shirye suke da zarar sun samu hanyar fita zasu bita ne, hmmmmmm
*â¤â¤â¤PRISONERSâ¤â¤â¤*
Saboda daɗin fira yasa suka dawo bakin gadon angel kowa ya samu wuri a gefe da gefen gadon suka zauna waɗanda basu samu wuri ba daga ƙasa suka zauna, Javed hada ƙoƙarin ɗauko fitilun ɗakin guda uku Ya kunna a ƙasa ya ajiye su, ɗakin ya yi haske, sun ɗauki tsawon lokaci, sai da angel taga sun fara gyangyaɗin bacci, ta Katse masu firar tare da cewa"its time to sleep, Kowa Yaje ya kwanta, gobe in Allah ya kai mu da rai da lafiya zan ƙarasa baku labarin" suka amsa mata da toh, ɗaya bayan ɗaya kowa Ya miƙe suna tafiya suna bangaje juna a haka suka nufi gadajen su, har sun kwakkwanta Muryar angel suka ji yo tana cewa"Su yi addu'a kafin su kwanta" suka amsa mata da toh,
Danish yana lafe saman gadonshi, ya lumshe idanuwanshi, amma babu alamun bacci yake yi, Gyara kwanciyarta ta yi, yau bata ju ya ma shi baya ba, suna fuskantar Juna,
Ganin yana mutsu mutsun buɗe idanuwanshi yasa tayi saurin Fuskantar ceilling, tare da rufe idanuwanta, Sam bata ji lokacin daya sauko daga saman gadonshi ba, sai dai taji hucin numfashin mutun yana kokawa da Nata numfashin, da sauri ta buɗe idanuwanta, Tsabar firgitar da ta yi ne yasa ta zare ido, Ganin fuskarshi a kusa da ta ta, Saman gadonta Ya hau Ya yi mata rumfa da ƙirjinshi, ƙiris Ya rage tsinin hancin shi ya gogi nata, Tsananin mamaki ne Ya kamata, Tuni ta shiga ruɗanin kome zai yi mata, Gashi ya tsareta da idanuwanshi ko ƙyaftawa babu, muryarta na inda inda tace"La..fi..ya"!? Yace"haƙuri nazo na baki, ki daina fushi dani, tun jiya baki yi mini magana ba, Idan muka haɗa ido sai ki ta harare na," daƙyar yakai ƙarshen maganar throat dinsa na moving kamar yana swallowing ɗin wani abu, yana ganin ta fara yunƙurin motsa la66anta alamar zata yi magana da sauri ya ɗaura dogon yatsan shi saman ƙaramin bakinta, Cikin sanyin murya yace"Pls don't shout at me, Idan kinsan ba me daɗi zaki faɗa mini ba, Kiyi shiru kawai, nafa baki haƙuri, Kuma na gane kuskure na,"
Hawayen da ta gani kwance a cikin fararen idanuwanshi ne yasa taji zuciyarta ta karaya, sai ma taji tausayin shi yakamata, Shi dai haka rayuwarshi take, Yana da matuƙar saukin kai, ga haƙuri matsalar shi ɗaya ragwanci, hannu tasa ta kawar da yatsanshi daga saman bakinta,
Sai da ta fara jefa mashi harara, kafin tace"Zan yafe maka amma sai ka yi mini alƙawarin wani abu" yace"komene ne zanyi" ɗan ta6a baki tayi tare da cewa"kada ka ƙara bari a ɗauki wani daga Cikin mu, Saboda nasan kana da ƙarfin da zaka Iya hana wa" tunkafin ta karasa maganar, Yae saurin girgiza kai yana faɗin"That's impossible, ki fahimce ni, Ni ba kowa bane face prisoner, bani da ƙarfin da zan Iya yin fighting da giants, sunfi ƙarfina, idan ba so kike in rasa raina ba"
tsoki taja"hmmm dama nasan haka zaka ce, Idan har dagaske baka da ƙarfi, to ta ya akai ka ke Iya shiga toilet bayan na datse ƙopa ta Ciki? Kuma ya akai ka iya 6a66ako glass door ɗin dake acikin toilet, tun daga tushen shi, taya zan yarda da maganganunka? Ta yi tambayar tana kallon cikin idanuwanshi, Har lokacin yana a yadda yake bai ɗago ba,
Runtse idanuwanshi ya yi, tare da biting lower lip ɗinshi, A hankali ya ɗan ware su akan fuskarta, Muryar shi arauna ce ya soma magana"Bansan ya zanyi in fahimtar dake ba Angel, Ni kaina bansan Ya akai nake iya shiga wurin dake a rufe ba, Also ƙarfin da yazo mini time dana cire glashin nan yanzu babu shi ajikinta...." kawar da kanta gefe tayi tare da cewa"Ban yarda dakai ba, danish Ina zargin kai ma Giant ne, kamai da mu shashasha kana 6oye mana ainihin wanene kai, Sannan kuma kasan Komai game da kurkukun nan, Amma kaƙi ka sanar damu, kafi so mu yi ta shan wahala har mu rasa rayukan mu, Kana ji kana gani ana cutar da rayuwar ƴan uwan mu amma kai hankalin ka kwance, Ko ajikinka.....' Kafin ta rufe bakinta, Taji saukar ɗigon ruwan acikinsu, da sauri ta kalle shi, Hawayen shi ne suka sauka cikin bakin ta, Yana girgiza kai yace"angel stop accusing me, am not a giant, Bana jin daɗin maganganun da kike gaya mini, its hurting my heart," Daƙyar Ya kai karshen maganar, wani irin raɗadi zuciyarshi ke Yi mishi, idan akwai abunda ya tsana Ya biyo bayan Giant, Yaji zafin Kalaman angel fiye da zafin marin da ta yi mi shi, ita kanta angel da ta yi maganar sai daga baya ta yi danasanin furta mashi zargin da take yi akanshi, bata ta6a ganin fushi akan fuskar danish ba, sai yau, Jikin shi har kerma yake Yi, wurin saukowa daga saman gadonta, da sauri ta mike xaune tana kallon shi, Ji take kamar ta kira shi ta lallashe shi, girman kai ya hana tayi hakan, Ta yi tsammanin zai kwanta asaman gadon shi ne, amma sai taga ya ɗauki pillown shi tare da bargonshi, bai nufi ko'ina ba sai cikin toilet area ɗinsu, duk sai taji ba daɗi, Ya rasa ina zai kwanta sai cikin toilet, In da madaddalar shaiɗanu suke? Dama Ya lafiyar giwa, har ta koma ta kwanta da niyar tayi bacci amma sai ta gaza runtsawa, Damuwa duk ta cika ta, a ƙarshe dai ta ji bazata Iya jurewa ba, ta miƙe Ta sauko daga saman gadonta, sai da ta fara zuwa gaban table ta ɗauko fitila ta nufi cikin sashen toilet ɗin, Tana zura ƙafarta Ciki, ta same shi a kwance saman shimfidar da yayi, hawaye ta ko'ina asaman face ɗinshi, ya lumshe idanuwan shi jin motsin mutun yasa shi ɗan buɗe idanuwan da suka canza launi, koda ya yi arba da ita sai ya ju ya mata baya, A ƙasa ta ajiye fitilar ta zauna gefen shimfiɗar tashi, Kusan mintuna tana kallon gefen fuskarshi, Daƙyar ta iya buɗe baki ta soma magana,
"Danish fushi ka ke yi dani? nayi nadama, da nasan kalamaina zasu 6ata maka ranka, da ban furta maka su ba, nima na faɗi ne kawai badan ina nufin hakan ba, " Babu irin lallashin da bata yi mishi ba, amma ɗan tahalikin nan yaƙi tanka mata, Muryarta a karye tace"Nagaji da lallashinka, Kaga Idan ma bazaka haƙura ba, to ka tashi mu koma ɗaki ka kwanta, Amma kwana a wurin toilet ɗin nan sam bai dace ba, Akwai shaiɗanun aljanu zasu iya cutar dakai,' sai lokacin yace"Meye damuwarki idan sun cutar dani? Jikin ki ko nawa"? Ta bashi amsa da cewa"Namu, saboda na damu dakai, dani dakai abu ɗaya ne, jinin dake yawo ajikin ka shi yake yawo ajikina, taya ɗan uwa zai share ɗan uwansa? Duk da nasan laifina ne amma na gane kuskure na na yin fushi dakai bazan ƙara ba," Bai ƙara tanka mata ba,