← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 179

Sashe 67

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A ƙa'idar wasan, Ba'a magana, idan na kama mutun yayi magana, kowa zaiyi mashi dunduna Biyu, sannan ya rasa abincin shi, Bayan wannan kuma Zai wanke mana uniform ɗinmu idan su ka yi ɗauɗa, zai kuma wanke toilets ɗinmu, Bayan wannan kuma ɗan wasa yana da damar da zai iya ta6a ko'ina ajikin sauran ƴan wasa domin ya samu damar canko wanda akace ya za6a, wannan ba laifi bane" alƙaliyar wasa ce ta kora masu wannan jawabin, tayi hakanne don tasan halin angel da shegen wayau, tana iya cewa zata yi ma danish raɗa don ya gano ta,

Cigaba da tafiya Danish Yayi yana ruƙo hannayensu, yana zuwa kan saitin angel ƴan hanjin cikinta suka kaɗa, kowa ya tsaresu da ido, jira kawai suke su ga idan danish zai iya gano ta,

Ruƙo hannunta na dama yayi da hannayenshi biyu, ya shafa su ya matsasu sosai, runtse idanuwanta ta yi jikinta na kerma, ba halin tace mashi itace, saboda idon kowa dake akansu,

Sakin hannunta ya yi, nan take su deeja suka soma Sakin murmushin mugunta, wani irin wahalallan yawu ta haɗiya, A wani slow danish Ya ɗaga ƙafarshi har zai wuce sai kuma ya ɗan dakata, kowa ya baza ido yana kallon ikon Allah,

Komawa ya yi gabanta ya tsaya tare da miƙa hannu tamkar zai kamo hannunta, sai kuma ya kauce hannunshi ya cafko sumar kanta, ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi, cikin sanyin murya yace"she's the one, am i right? Gaba ɗaya su Azeeza suka Daka sowa suna Tafa mashi hannu, hatta tsohuwa saida Ta ɗanyi murmushi duk da ba haka taso ba, amma Abunda ya burgeta kaifin basira irin na danish, yayi wayau, saboda yayi amfani da yanayin kakarwar da jikinta keyi, da ya ruƙo hannunta da farko ya fuskanci hakan, shiyasa ya sake dawowa ya kai hannu kamar zai damƙi hannunta, sai yayi wayan kaucewa ya damƙi gashin kanta, saboda yasan idan itace, zai samu gashin kanta har wurin qugunta, wato danish yayi amfani da kwakwalwarshi,

Wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya angel ta sauke, lokaci É—aya kuma ta fashe da wata irin mahaukaciyar dariya hada dafe ciki, Taji daÉ—i data tsalleke tarkonsu Haris da deeja, kamar su fashe da kuka saboda tsabar 6acin rai da takaici, plan É—insu ya rushe,

Sai da ta kammala shan dariyar, tukunna ta sanya hannayenta biyu ta warware ma danish É—aurin da akayi mashi akan fuska, bayan ta kammala ta xame rigar tare da wurga ma haris ita saman fuskarshi, rai a6ace haris ya ca6e rigarshi yana faman kumbura baki

Natsuwa tayi tana kallon danish dake ta faman ƙoƙarin bude idanuwanshi, eyes lashes ɗinshi sun cukurkuɗe sun hana shi buɗe ido, matsawa tayi kusa dashi sosai, ta sanya yatsun hannunta wurin buɗe mashi idanuwan, yadda zai gani da kawai,

Fuskarta É—auke da murmushi tace mashi"thank u so much danish, ka taimake ni, da yau an karya mini spinal cord É—i na, gaba É—aya suka saki dariya, banda haris da deeja,

Ruƙo hannunta danish yayi acikin na shi, ya jata suka koma gefe ɗaya, aka cigaba da buga wasa, juyawa tsohuwa tayi batare da kowa ya ganta ba, ta koma Cikin ɗakinta, taja ƙopa ta rufe,

Lokacin da suka kammala wasan, Saman gadajensu suka koma, waÉ—anda suka sha bugu sai faman jinyar kansu suke yi, rabi da kwatarsu ba'a É—auko tsawon lokaci ba suka kama baccin wahala,

In the night 🌌

Lokacin da dare yayi hasken ɗakin ya ɗauke, suka ɗauko fitilun ɗakin suka kunna su Saman Dining carpet ɗin su, Dakin yayi haske sosai, Kowa ya samu wuri saman Carpet ɗin ya zauna, Batool taje ƙarƙashin gadonta ta ɗauko masu Kingin Tsiren namansu, Ta rarraba masu Kowa Ya kar6a Yana ci, da suka kammala Suka ci snacks ɗinsu da Sauran kayan marmarinsu, Suna Ci suna fira gwanin ban sha'awa,

Bayan sun kammala Ci, Kowa ya kasa runtsawa, dama angel tayi tunanin daƙyar su iya yin bacci saboda baccin da suka sha A jiya, idanuwansu sunyi wuƙi wuƙi, babu alamun bacci,

Duk suna a zaune saman gadajensu, Tunani ta soma yi kodai taje toilet ta ƙara jaraba fasa glass window ɗin nan? Wata'ƙil idan ta dage kullum tana zuwa tana Bugun jikinshi, Allah ya taimaketa ya fara tsagewa, juyawa ta ɗanyi tare da kallonsu, kowa ya kishingiɗa saman gadon shi, kallon shimfiɗar danish tayi ya kifa kanshi saman Pillow, Aranta tace Allah yasa yayi bacci, kada yayi mini irin na jiya, don na lura akwai almatsutsai akanshi, ba shi kaɗai bane,

Zuro ƙafarta ƙasa tayi daga saman gadon, ganin sun rufe idanuwansu yasa ta lalla6a cikin sanɗa taje gaban Carpet ta ɗauki fitila, da sauri ta wuce ta shiga sashen toilet ɗinsu, Taja ƙopa ta garƙame ta, ajiyar zuciya ta sauke yayin da bayanta ke ajingine da ƙopar,

Glass window ɗin ta ƙurawa ido daga inda take a tsaye, tana ƙoƙarin motsawa da nufin taje ta fara aiwatar da aikin fasa shi, kwatsam Tajiyo shessheƙar kuka tare da Iface iface daga Can Cikin ɗakinsu, A matuƙar kiɗime ta juya takai hannu ɗaya ta Zare jam lock ɗin kopar, da gudun gaske ta faɗo Cikin Ɗakin, Tunkafin ta ƙarasa Ciki, Ta hango su batool da hanna, agaban gadon Deeja, su javed kuma suna a tsaitsaye gaban gadon parveen, ga kuma haris da danish agaban gadon Rubina, Hankalinta yayi matuƙar tashi, Iskokai ne suka tashi Ko kuwa menene? Karasawa ciki ta yi da sauri taci burki agaban Gadon Parveen, Idonta akanta, Ta daddafe Cikinta sai juyi take yi tana kuka tana fadin Cikinta Ciwo zata mutu su taimaka mata,

Arude ta kalli fuskokinsu Batool, Bakomai ta gani ba face tsantsar tashin hankali, sun rasa ya zasu yi mata, da sauri angel ta matsa gadon Deeja dake ta ihu tana fadin Cikinta ciwo yake yi mata, wuce wa tayi zuwa gadon rubina ta tsaya tana kallonta itama ta daddafe Ciki sai kuka take yi tana matse idanuwanta, fuskarta tayi jaga jaga da kwalla,

Kallon Su haris Tayi muryarta na kerma tace"MEKE FARU WA NE'?_

Fuskar Haris a hargitse ya bata amsa da cewa"mu ma bamu sani ba, muna a kwance muka Ji sautin kukansu, mun rasa ya zamuyi da su"

Shiru angel ta ɗanyi ta ruɗe ta rasa madafa, Komawa Tayi bakin gadon Parveen, su batool duk suna a tsaitsaye cirko cirko, a ƙasa ta sauke fitilar hannunta, kafin ta ɗago takai hannu ta janyo Parveen zuwa Jikinta, ƙanƙameta praveen ta yi sosai tana kuka tana faɗin" angel ki taimaka mun ciki na, bana jin daɗi, xafi yake yi mini raɗaɗi nake ji,

Ƙura ido angel tayi tana kallon ɗigon Jinin dake ajikin wandon Parveen Nan take ta gane cewa Jinin al'ada ne, a karo na farko kenan da ta ta6a ganin sunyi jini, ta jima tana mamakin ya akai basu fara ba, saboda a shekarunsu ya isa ace sun fara Shi tuntuni saboda sun girmeta, abun ya ɗaure mata kai,' shessheƙar kukan Parveen ne Ya dawo da ita Cikin hayyacin ta,

Ɗago da kanta tayi daga Jikinta, ta dafa kafaɗunta"Kiyi haƙuri kiyi shiru parveen zanje in faɗa ma tsohuwa," takai ƙarshen maganar tare da saukowa daga saman gadon, ta kalli su batool dake atsaye Cikin yanayi na damuwa,

"Ku kula da su, Bari nayi mata magana tazo ta duba su, in yaso sai tayi maku bayanin Abunda ke damun su," amsa mata su kayi da toh, da sauri ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa takai hannu ta bubbuga ƙopar, almost 3 times tana knocking ƙopar, Kafin tajiyo motsinta,

Buɗe ƙopar tayi tare da fitowa Hannunta ruƙe da sanda,

"Meke faruwa ne nake Jin koke koke" tayi tambayar tana kallon Wurin gadajensu,

Muryar angel na rawa ta bata amsa da cewa"ciwon Ciki suke yi Ina tunanin menstruation ne, suna buƙatar magani da kuma pads ɗin da zasu sanya"

Maimakon taga damuwa akan fuskar tsohuwa sai taga ta duƙar dakai ƙasa tana sakin wani irin shu'umin murmushi, ran angel ya 6aci sosai,

"Magana fa nake yi maki akan lalurar dake damunsu, don me xaki 6uge da yi mun murmushi? Maimakon Inga damuwa akan fuskarki? Kina ji suna kuka suna ihu amma ke ko ajikin ki? Ba zaki je ki duba lafiyar Jikin su ba"?

Ɗagowa tsohuwa tayi tare da kallonta, da wannan Shaƙaƙƙiyar muryartata ta tsoffi ta soma magana

"I ave no responsibility to check their health, the giants will come and take them to the treatment room" har saida angel ta zabura jin abunda tace, Can kuma ta wurga mata harara,

"Amma dai baki da Tausayi kuma baki da Imani, taya zaki ce za'a zo a ɗauke su? bayan kina da halin da zaki iya duba su da kanki? Kenan Giants su zasu duba Lafiyar su, Ke fa yakamata ace Kin duba su, Ba wani ƙato ba," zuciyarta a harzuƙe takai ƙarshen maganar, Kafin tsohuwa ta mayar mata da martani, Suka Soma Jin motsi buɗe ƙopa daga can saman benan.........................

*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*

A matuƙar kiɗime angel ta juya tana kallon stairs ɗin, hatta su Batool a ruɗe suka kai idanuwansu kan benan, tunkafin ma su ƙarasa saukowa sautin takalmansu ya karaɗe kunnuwansu, Cikin takun nan nasu na majiya ƙarfi suke tafiya bakowa bane face GIANTS, a jere suka sauko daga saman Stair cases ɗin, haƙiƙa hankalin angel yayi matuƙar ta shi, Jikinta har tsuma yake yi, juyawa tayi tare da kallon tsohuwa, Cikin karyayyiyar murya tace" na roƙe ki dan Allah Ki taimaka, kada ki bari a tafi dasu parveen, abar mana su acikin mu, Ni nayi alƙawarin zan kula dasu," idanuwanta cike tab da ƙwalla takai ƙarshen maganar,

Girgiza kai tsohuwa ta yi babu alamun sassauci akan fuskarta tace"Ba hurumina bane shiga abunda ba ruwana, Dokar Prison ce, Wadda bani na tsarata ba, duk wani mara lafiya za'a zo a ɗauke shi akai shi inda za'a duba lafiyar shi, idan kinga na duba mutun to ciwon bai yi tsauri bane, Giants da ki ke gani basa sauraron kowa, Koda kuwa nice, saboda ba a ƙarƙashina suke ba, dukan mu Ma'akaita ne dake aiki gidan kurkukun ƙaddara, Kuma a ƙa'ida wani baya shiga hurumin wani........."
Chapter 67 · 0% Book details