← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 179

Sashe 122

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Danish ne yace da sauran"Idan kuna jin yunwa ga abinci nan, Idan zaku huta ga beds ɗinku nan, sannan......." bai ƙarasa ba yaɗan kalli ƙopar shiga sashen toilet ɗinsu yace"Game buƙatar watsa ruwa ko yin wani uziri wannan ƙopar zaku bi, Anan toilets ɗin mu su ke" Yana magana hankalin shi na akan Matashiyar yarinyar nan, dake ta kallon shi tana faman cizon pink lips ɗinta, ran angel idan yai dubu ya 6aci, bakomai yafi ƙona mata rai ba face ganin yadda take kallon Danish tana cizon le6e, tarasa gane me hakan ke nufi, to ko dai halittarta ce ahaka? Ko kuwa wani sabon salon iskancin ne"?

"Bana jin yunwa, I need to take bath, before in kwanta In huta" Ƴar gidan daddy ce tayi maganar tana ƙoƙarin sauke School bag ɗinta, Idon kowa na akanta, Miƙa ma Danish Backpack ɗin tai tare da cewa"Ka ajiye min ita, sannan ka raka ki toilet ɗin, bazan iya ganewa ba" Wani irin kallon harara angel take jefa ma Danish, duk yasha jinin jikin shi, Sam ya kasa kar6ar jakar Unaiza, Sai angel ce ta kar6e jakar tace"Zan ajiye maki ita, sannan zan raka ki toilet ɗin, idan ma kinaso har cuɗa maki baya zan Iya yi" Girgiza kai Unaiza tae tana fadin"No, bana so, ki dai ajiye min back pack ɗin, Shi sai ya raka ni toilet ɗin" mamaki ne ya kama angel, aranta tace"that's impossible, kinzo da bidi'a," Kar6ar jakar tayi daga hannun unaiza taje ta ajiye mata ita gefen donta mai ɗauke da no 16, juyowar da za ta yi, karaf idanuwanta suka sauka akan Unaiza da ke ƙoƙarin cire Coat ɗinta, Bakomai ne ya faɗar mata da gaba ba, face Ƙirjin Unaiza, Musamman da ta ƙarasa Cire rigar Hankalin Kowa Ya koma kansu, Kamar babu riga ajikinta saboda Yadda surar su ta bayyana ajikin vest din, Manya manya dasu kamar balan balan, shatun nipples ɗin sun fito sosai, kamar zasu huda ta, gata yarinya amma tubarkalla, Allah yayita da boobs, "

Kwanciyar hankali ya ƙarewa angel, Kishi ne ya addabi zuciyarta, kodan hada ƙarin ita bata da su ne, Oho dai,

Bayan Unaiza ta ɗebe Coat ɗin Ta miƙa ma Danish tace Ya ruƙe mata, Hannun shi na kerma ya ruƙeta, wani irin ƙamshi ne ke fita jikin coat ɗinta," hannayenta ta ɗaura saman gajeran skirt ɗinta, Waro ido angel tae baki a sake take kallon ikon Allah, Cire shi tae ya rage daga ita sai Short na mata, "

duk su naufal suna a tsaye suna kallon ikon Allah, Miƙe ma Danish Skirt ɗin ta yi"Ka ajiye min su" Kafin yai yunƙurin kar6ar skirt ɗin angel tai saurin komawa wurinsu ta sanya hannu ta kar6i skirt din ta kuma ƙwaci coat ɗin dake a hannun Danish, Fuskarta a ɗaure ta nufi akwatinsu ta sanya mata su a ciki, Kafin ta dawo ta tsaya agefen Danish,

"Muje ka raka ni toile ɗin" ta yi maganar tana ƙoƙarin ruƙo hannunshi, Angel tae saurin ka6e mata hannun"Ni zan raka ki," Bata jira amsar da unaiza zata bata ba, Taja hannunta, ta wuce da ita zuwa sashen toilet ɗinsu, sai bayan da suka shige, azeeza da parveen suka kalli juna, Alamar mamaki, sufa sunga abunda basu ta6a ganin irin shi ba, tun da ko tsohuwa nata azube suke kamar silifas, Cikinsu kuwa ba wadda ta ke da su irin na ƴar gidan daddy, har ƙwara waɗan da suka fara manyanta, Sune ya fara fito mawa, amma ita ko wannan ƴar shilan ƙirjinta sunfi ƙarfin jikinta da shekarunta.

"Gabriel, banji kace komai ba"? Danish ne yae mishi magana ganin yayi tsaye bai motsa ba shi da sauran Æ´an uwan nashi, Cikin sanyin murya yace"Inaso na kwanta, saboda kaina ciwo yake yi min" Nuna mashi gadonshi danish yae da hannu, Yace mashi thanks kafin Ya nufi gadon, Sai da ya fara cire coat É—insa, Ya É—aura ta gefe, Sannan ya haye gadon ya kwanta,

Kallon Jamima su kayi ƴar ƙaramar yarinyar nan, parveen ta raya aranta cewa"Wannan dai rainonta zamuyi da alama" Haris ne yace da ita"Kefa? Zaki kwanta ko xaki ci abinci" Ta6e baki ta ɗanyi kafin tace"Yunwa nake ji," Deeja tace"amma ke kike yin wanka da kanki"? Ɗaga mata kai tayi"Eh, inayi yanzu, amma sai ana cuta min bayana saboda hannu na bai kai wa" Murmushine ya bayyana akan fuskokinsu, don ba ƙaramin burgesu tayi ba, gata ƴar kyakkyawa da ita, Hibba tace"idan ma kinaso har wankan sai muyi maki," dariya tasaki tare da sanya tafin hannayenta ta rufe fuskarta, alamar taji kunya.

Ruƙo hannunta Haris yae acikin nashi yace"muje muci abinci ko"? Tace mishi eh, " mubeen yace"to itafa Wannan bamu ji ra'ayinta ba, " yae maganar yana nuna Sarah dake atsaye Ta ruƙe qugu, Yatsina fuska Ta ɗanyi can kuma saita ƙaƙaro murmushi tace"Nima bana Jin yunwa, zan kwanta na huta ne" tae maganar tare da juya ta nufi gadajensu, Ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, a sukwane Ta juyo ta kalle su Deeja tace"wai a ina zata kwanta ne"?

Nan take su ka fahimci cewa Ta raino gadon ne, Wato yayi mata ƙanƙanta, Hannah tace"Acan inda kuka Baro, a saman Ina ki ke kwana ne"? ta6e baki Sarah ta yi Ba tare da ta bata amsa ba, Ta maida idonta kan gadon, Ta curo bargon saman shi, Ta shimfiɗashi a ƙasa, ta ɗauko pillow ta jefa, Kafin ta cire coat ɗin Jikinta ta ɗaura a ƙasa, Ta faɗa sama gadon ta kwanta.

A bunda ya faru bayan Angel ta raka Æ´ar gidan daddy toilet, suna shiga ciki taja burki ta tsaya Tana faman zazzare blue eyes É—inta haÉ—i da yatsina fuska, Angel tace"Ni xan Koma, ayi wanka lafiya" har zata juya muryar Unaiza ta dakatar da ita

"Nifa ban fahimta ba, Ina bathtub yake ne? tana nufin (kwamin wanka) Wannan wani irin toilet ne kamar na Marasa galihu" Tsabar mamaki yasa angel sakin baki kamar sakarya tana kallonta, Daƙyar ta iya buɗe baki tace"ba mu da bathtub, Iya a bunda idonki suka gane maki acikin toilet din su muke dasu, Ga Shower nan, Sai kuma bokiti, can kuma Soso ne da sabulu," aruɗe unaiza tace"that's Impossible, ae ni bana sharing soson wanka, Kuma bana wanka in ba a cikin bathtub ba, I can't stay here i wanna go home, cos daddy ba haka Ya kwatanta min school ɗin ba, Yace min fa komai irin na Gidan mu ne, but why naga banbanci"? tamkar zata fashe da kuka tayi maganar, har saida gaban angel ya faɗi jin abunda tace, Wato ita duk a tunaninta School ce aka kawota batasan cewa Prison bane, To me hakan ke nufi? Kodai mahaifinta ne ya yi mata ƙarya kan cewa za'a kawo ta makaranta! Tashin hankali Sai lokacin angel ta tuna da irin uniform ɗinta na gayu, dama ta yi mamakin ganinta da haɗaɗɗun takalma ƴan ƙwaras ƙwaras, Ga gajeran skirt na gayu, Ga kuma ƙatuwar School bag Ta goyo, Tabɗijancan, In dai a bunda take hasashe ya tabbata to kuwa Iyayenta sun Cuce ta, Mamaki Ya hana angel cewa komai, taya akai basu gusar mata da hankalinta ba? Kamar yarda aka yi ma Gabriel? Ko kuwa sihirin ne bai kama Jikinta ba?

ta yi zurfi acikin tunaninta muryar unaiza ta katse ta"Pls talk to me! Ni ban fahimci komai ba, game da school din nan," tashin hankali ne Ya bayyana ƙarara akan fuskar angel, miryarta na ɗan rawa tace da unaiza"wacece ke? Dama ke ba rainon Kurkuku bace"? Waro ido tae tare da maimaita sunan prison da angel ta faɗi, Ba don ta fahimci me hakan ke nufi ba,

"Ban fahimce ki ba, Naji kince prison, Nifa daddyna yace dani xai sanya ni a high school Na south korea, saboda inason kallon drama ɗin su komai nasu yana ƙayatar dani, Daddyna yana yi min komai nake so, shi ne Da kanshi, Ya sama min admission a school ɗin nan, a gida aka kawo min uniform na sanya ajiki na......" unaiza bata ƙarasa maganarta ba, Angel ta ɗaura hannunta akai,! Irin ta shiga ukun nan, fito wa ta yi daga Cikin toilet ɗin Ta tsaya daga waje tana ambaton"Innallahi wa'inna ilaihirraji'un"! da sauri ƴar gidan daddy ta biyo bayan angel, baiwar Allah duk ta ruɗe ta rasa gane me angel ke nufi,

"Pls tell me the truth Ko ba school bane nan ɗin? I ave to know" wani irin kallon tausayi angel ke binta dashi, muryarta kamar ta mashayin giya tace"Zaki iya tuna Ta ina aka kawo ki Nan" girgiza kai tayi"I can't remember, Ni dai nasan time da masu aikin gidan mu, suka taimaka min nayi wanka na sanya uniform da daddyna ya bani, so bayan nan sun rakoni zuwa wurin da motocin bodyguards ɗina su ke, sun buɗe min mota, Na shiga Ciki na zauna, ina ta farin ciki, duk na qagara mu ƙarasa Airport sai bacci ya ɗauke ni, daga nan ban ƙara tuna komai ba, sai dai na ganni Acikin School ɗin nan tare da sauran students din da muka zo da su" Tana magana tana yatsina fuska daga gani ɗabi'arta ce yin hakan,

Jinjina kai angel tae yayin da take kallonta, haƙika ta yi mamakin da basu canza mata tunaninta ba, tun da har ta iya faɗin yadda aka kawota Cikinsu, tabbas kowanene Ubanta ba ƙaramin Mugu bane, Azzalumi, Wato shi wayau yayi mata ya fake da cewa za'a kaita Sk don ta yi karatu batasan cewa Sadaukar da ita ya yi ba zuwa Gidan Kurkukun ƙaddara, don biyan wata buƙata tashi, Rayuwarta abun tausayi baiwar Allah, Sai da aka gama sangartata, Daga gani an gama jiyar da ita duk wani daɗi na duniyar nan kafin aka tsamota daga aljannar duniya aka kawota gidan kurkukun ƙaddara,

Ganin irin kallon da angel take binta dashi ne yasa tace"Pls Ke nake jira ki bani amsa," A ƙagare tayi maganar,
Chapter 122 · 0% Book details