← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 179

Sashe 138

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gabriel why, ba ka taimake ta ba! Ae da ka sani ka taho da ita, Batul ce fa ƴar uwar mu" Shima aruɗe yace mata"Angel ni bansan cewa ƴar uwar ku bace, tun da bansan ta ba, naso na taimake ta, sai dai tsoro ya hana in ƙarasa wurinta, cos stairs ɗin dake kewaye da ground floor ɗin naga suna motsi kamar masu rai, that's the reason why na rikice, cos abunda ban saba gani ba ne....." shessheƙar kukanta ne ya katse mashi maganar tashi, ya zuba mata ido yana kallonta, sassauta muryarsa ya ɗanyi"Ki daina kuka, Danish zai iya jin sautin kukan ki ya farka, Yakamata mu tattauna akan abunda ya dace mu yi," cikin matsananciyar damuwa tace"ae wlh Saina je na ɗauko ta, koda zan rasa raina ne, komai zai faru sai dai ya faru, amma bazan runtsa acikin daren nan ba, dole naje!!!'

tana ƙarasa maganar ta nufi toilet ɗin da tagar take da sauri Gabriel yabi bayanta yana fadin"ki tsaya Angel, kada mu yi gaggawa, yanzu dare ne, why ba zamu bari sai gobe ba"? Ba tare da ta juyo ta kalle shi ba tace"In bari sai gobe, salon sai wani abu ya cutar da ita, Ina ji araina Allah ne ya taimaki batul ta gudu daga wurin su, shiyasa ta ke neman hanyar da zata dawo cikin mu, wannan munafukin ginin bazai bari ta iya gane komai ba, wahala zata sha ƙarshe ma ta rasa ranta,'

Ba ƙaramin daɗi Gabriel yaji aranshi ba, dama abunda yake so kenan, Su je atare da ita su nemo ƴan uwansu, dama koda yace mata kada su yi gaggawar yin hakan ya faɗi ne kawai ba don yana nufin hakan ba.

"Amma angel kina ganin zamu iya shiga lafiya lou? Na fahimci cewa ginin yana da rikitarwa, ga ban tsoro.

"zan roƙi Allah ya kare ni daga sharrinsu, in sha Allah zamu je mu dawo lafiya ba tare da wani abu ya same mu ba" da ƙwarin gwiwa ta bashi amsa da alama ta manta abunda ya faru da ita, saboda amakance take burinta kawai taje ta nemo batul,.

"Amma Baki tunanin Danish zai iya hana mu? Suna tafiya suna magana har ta isa bakin tagar, ta bashi amsa da cewa"Shi da yake bacci, koda ace ya farka, bai isa ya hanamu ba, Akan batul ba abunda bazan Iya yi ba" tana magana tana jan majina.

Ganin tsayinta bai kai wa yasa Gabriel matsawa bakin tagar, tun da yana da tsayi, Ya soma ƙoƙarin cire glass ɗin.

"Idan muka ga sister ɗinki, Nima zaki taimaka min in gano ƴar uwarta Gabriella, " ta amsa mashi da eh," ajiyar zuciya ya sauke, yayin da yake cigaba da ƙoƙarin cire glass ɗin, Lokaci ɗaya taji gabanta ya yi wani irin mugun bugu, nan take ranta ya bata cewar, Danish Ya iso inda suke, Kafin tayi yunƙuri Juyawa, Muryarshi ta ratsa kunnuwansu

"Bazan ta6a bari ku haura tagar nan ba! " da sauri Gabriel ya zame hannun shi daga saman glass ɗin, kusan atare suka juya baya suna kallon shi, Ya ɗaure fuskarshi sosai, tare da goya hannayen shi saman ƙirjin shi, mamaki ne akan fuskar Gabriel, Taya akai ya farka har yazo inda suke yaji abunda suke Shirin yi?

Anya kuwa wannan cikakken mutun ne? Muryar angel tamkar zata fashe da kuka tace"wlh Danish bazan saurare ka ba, dole nabi shi mu haura tagar nan, da kanshi ya faÉ—amin cewa ya bi ta cikinta jiya, har ya ga wata yarinya tana gudu a hawa na uku, tana neman taimakon shi, kuma a yadda ya suffanta min ita, sak batul ce"

matsawa tai kusa dashi, ta sassauta muryarta"pls Danish, ka bamu haɗin kai, muje mu ɗauko batool, kana da damar da zaka iya taimaka mana dan Allah, Ni idan ma kayi min alƙawarin zaka je ka dauko min ita, sai in koma ɗaki in jira ka....." cikin shessheƙar kuka ta ƙasa maganar, hawaye ta ko'ina saman fuskarta.

Idon Danish akan fuskar Gabriel, wani irin haushinsa yake ji, saboda shine silar komai, cikin kakkausar murya yace"Ba gaskiya ya fada maki ba, yarinyar daya gani ba batul bace, cos babu yarda za'ae batul ta iya fitowa daga inda aka killace ta, shin ko kin manta ranar da kika dira window din abunda ya faru dake? Let me remind u, Kin ga daddynki, alhalin bashi bane, idanuwanki ne suke nuna maki hakan, that mean shima Gabriel abunda idon shi su ka gane mashi ba gaskiya bane........" tunkan Danish ya rufe bakinsa gabriel yace"Dama na lura da kai tuntuni kaƙi bani dama in yi magana da Angel, saboda kai ɗin munafuki ne, baka son gaskiya, shiyasa zaka ƙaryata abunda idanuwana suka nuna min, Angel karki ce zaki yarda da kalamansa, kada hakan yasa kice kin fasa bina mu shiga cikin kurkukun, Ki tuna halin da ƴar uwarki take aciki, zata iya rasa ranta.....

Gaba daya sun rikita mata tunaninta, kowa yana ƙoƙarin jan ra'ayinta, ta rasa wa zata bi acikin su, domin kuwa sun raba hankalinta gida biyu, zuciyarta na raya mata cewar tabi Danish su koma ɗaki, saboda akwai ƙamshin gaskiya a maganarshi, zai iya yiwuwa ba batul bace Gabriel ya gani, anyi amfani da matashiyar ne don a tsoratar da shi, kamar yarda itama a ka yi mata amfani da daddynta, yayin da awani sashen na zuciyarta yana raya mata cewar, tabbas Gabriel baiyi mata ƙarya ma, Ƴar uwarsu ce ya gani, kada Tabi Danish azo asamu matsala idan ya kasance dagaske Ita dince, tana fargabar halin da zata shiga, ita kaɗai acikin prison, zaifa iya yiwuwa Danish Yasan gaskiya Gabriel yake faɗi, Tun da baison dama tana dira tagar shiyasa zai kafe akan cewa ƙarya ya ke yi mata.

Ta yi zurfi acikin tunaninta, taji an damƙi hannunta, da sauri ta kalli hannun wanda ya ruƙeta, Danish ne ke ƙoƙarin fusgarta don su koma ɗaki, rai a matuƙar 6ace, Gabriel Ya damƙi ɗayan hannun nata yana huci, Zuciyar kowannansu takai wuya, A shirye suke da su farmaki junansu.

"Ka sakar mata hannu tunkafin ranka ya 6aci!" Danish ne yai maganar fuskarshi a murtuke, tsoki Gabriel yaja

"bazan saki ba, saboda ba hannunka na ruƙe ba,"

"Bana so ka yi danasani, tun wuri ka ajiye makaman yaƙin ka, kazo mu koma ɗaki, mu sasanta kanmu, amma idan ka nace akan sai ka ƙwaci hannun Angel ta ƙarfi don kuje ku dirar tagar can, Zanyi maka abun da ba ka ta6a tunani ba" Gabriel na huci yace"kai duk abunda kaga dama, bazan ta6a sakin hannunta ba, saboda ba mallakin ka bane, ni ban ta6a ganin mutun mai ƙarfin hali irin naka ba, Yarinyar nan fa ba dangin ka ba ce, Zaman Prison ne ya haɗa ka da ita, we're all prisoners babu wata alaƙa ta jini, don haka yadda ka ke taƙama da ita, nima haka nake taƙama da ita........"

zaro eye balls É—insa yai jin abunda
Gabriel ke faɗa masa, maganar ta ƙona masa rai, wato har yana da bakin da zai ce Hannun Angel ba mallakinsa bane? To na wanene idan ba nashi ba? sannan yace bai da alaƙar komai da ita, me hakan ke nufi,? Shima yana da iko akanta kamar yadda yake dashi? Ta ya hakan zai yiwu! Girgiza kai ya somayi yana huci ya furta"Kada ka kuskura ka maimaita kalaman da ka yi min Ayanzu, Domin kuwa Angel tawace ni kaɗai, ba wani mahaluƙin da ya isa ya shiga tsakanina da ita...." yana ƙarasa maganar Ya fusgi hannun Angel, ta fashe musu da kuka saboda raɗadin da taji, An rasa wanda zai haƙura yabarma wani, shima Gabriel yaƙi sakin hannunta, suka dinga janta kamar wata ɗiyar roba, Har cikin zuciyarshi yake jin kukan nata sai dai ba yadda zaiyi ya lallasheta, don bai jin zai iya haƙura yabar wa Gabriel ita donsu haura taga, duk a bunda ya ke yi yana yi don ita ne baison abunda zai cutar da ita, A ƙarshe da ta gaji ta fasa ƙara mai tsiwar gaske, Ta zame hannayenta daga cikin na kowannansu, tana kuka tace"ya isa haka! Ya isa, Ni ku ƙyale ni inji da abunda ke damuna, so ku ke ku kashe ni ne! " cikin sanyin murya Danish yace"Am sorry angel, laifinsa ne, kizo mu koma ɗaki," harara ta wurga mashi da idanuwanta wadanda suka rune zuwa ja,

"Ni banzan bika ba danish, dole inje in ɗauko batul ɗinmu, idan har kai bazaka iya zuwa ka ɗauko min ita ba, to ka ƙyale ni inbi Gabriel mu je" Muryarshi araunace yace"Angel ki fahince ni, ba gaskiya bane abunda ya gaya maki, bana so ne ku yi danasani,"

Harara Gabriel ya watsa mashi tare da cewa"idan har dagaske ƙarya na ke yi akan abunda na faɗa mata, to ka bari muje tare da ita mu duba, idan har bamu ganta ba, shi ne ka ke da damar da za ka iya ƙaryata ni,"

rai a6ace Danish ya nuna shi da yatsa

"Ka yi min shiru! Bana so na ƙara jin maganarka, wawa kawai, kaine silar komai, kuma bazan ƙyale ka ba,"

Gabriel ya daki ƙirjinshi da hannu tare da cewa nima bana so ka ƙyale ni, Ɗan rainin wayau, dama daga ganin fuskarka ba mutumin kirki bane, wama yasani ko ɗan leƙen asiri ne kai acikin mu......."

Ɗaya daga Cikin abunda Danish ya tsani Ya ji an faɗa mashi kenan, aiko ranshi yayi mugun 6aci har baisan time daya damƙi wuyan Gabriel da hannu biyu ba, ya tura shi zuwa jikin bango ya matse shi, Da gudu Angel ta nufe su da niyar ta dakatar dashi, sai dai kafin ta isa, tai tuntu6e ta kife ƙasa, Kafin ta yi wani yunƙurin ɗagowa
Chapter 138 · 0% Book details