Sashe 143
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Zo nan" jin kiran Angel yasa ta É—an saki fuskarta, ta soma tafiya tana tunkarar gadon ta, a bakin gadon ta tsaya tana kallonta"ba nan nace ki tsaya ba, dawo nan gefe na" tai maganar tana nuna mata gefen gadon, dawowa tai daga gefen gadon ta tsaya tana faman mutsustsuka rigar hannunta,
numfasawa tai tare da juyawa ta kalli majnun dake tsaye yana ta faman raba ido, hannayen shi biyu rufe da gabanshi, Parveen tace"Abanza, bayan ka gama nuna mana abun na ka shine yanzu zaka wani sa hannu ka rufe, kai ɗin nan ba ƙaramun shaƙiyi bane, ae wlh da ace nice zan maka wanka, da duk saina gurje farar fatarnan ta ka, aljani kawai" Tana magana tana jifarshi da harara idonshi akanta sai murguɗa mata baki ya ke yi.
"Zonan Majnun uban masu hankali" Angel ce ta kira shi, A hankali ya ke nufar inda take ba tare daya zame hannun shi daga gabanshi ba, a gefen gadon Ya tsaya dab da ita, Jamima tana a 6angaren dama shi yana a 6angaren hagu, kowa ya natsu yana jiran jin sasancin da Angel zata yi musu.
"Ku faÉ—amin meyasa kuka raina azeeza ne? Tsarar wasan ku ce ita? Daga taimako? Yau one week ba wanda ya kula da ba ku yi wanka ba, don ita ta taimaka zata yi muku shine kuke yi mata iya shege ko"! Tai maganar tana duban kowannansu,
Jamima ce tafara magana tana tsino baki
"Ae ni sai da nace mata, tabarnin inyi wankan ta ƙi bari inyi, bana son tayi min wanka, nafison su hanna su cuɗa min bayana ko ke...." tun kan ta ƙarasa maganar Angel tace"Oh saboda sune manya wanda suka isa dake, banda ita ko? Ɗaga mata kai tai alamar eh ta ƙara da cewa"azeeza fa ƴar ƙarama ce the same height as me, ta ya za'ai tayi min wanka."
Mamaki ne ya kama su Hannah, Kowa ya É—an zaro ido suna kallonta, Angel tace"Okey," kafin ta maida duban ta ga majnoon"what about u? Meyasa ka rainata"? da buÉ—ar bakinsa sai cewa yae"I don't want her to bathe me because she's so little, nafa girme ta, da ma ba ita ta ke yi min ba, Danish ne yanzu baya nan, Haris yana min da naufal"
Har cikin zuciyarta taji gabanta yaÉ—an faÉ—i saboda sunan Danish da majnon ya ambata, nan take taji wata irin kewarshi ta baibaye sassan jikinta, kasa magana tai, idanuwanta bakomai suke nuno mata ba face kyakkyawar fuskarshi, da sauri ta kwantar da kanta ta kifa fuskarta saman pillow, ganin hakan yasa suka fahimci dalilin shiga damuwarta, su kansu da Majnun Ya ambaci sunan Danish sai da zuciyoyinsu suka amsa.
Haris ne yaci gaba da yin magana yana duban su Jamima dake a tsaitsaye gefe da gefen na gadonta
"daga yanzu kada na kuskura na ƙara ganin wani a cikin ku ya raina azeeza, Ƴan ranin wayau, just because u saw her a little girl like u that's why ku ka raina ta, Let me tell you that even Angel, whom you respect, is younger than azeeza."
A matuƙar ruɗe Jamimah da majnoon suka kalli haris suna faman zare ido, Mamaki ƙarara akan fuskarsu, Hatta Gabriel da Sarah sai da suka jinjina maganarshi don basu ta6a sanin hakan ba, sai da ya faɗi yanzu,
Cigaba da magana haris yai,"Angel itace ƙaramar cikin mu kafin zuwan ku, tafi kowa ƙananun shekaru, ƴar azeezar nan da kuke rainawa yayarku ce,......." muryar Jamima da kokwanto ta furta"amma ae ƴar ƙaramace ko, meyasa ita bata yi tsawon Angel ɗin mu ba"? Hada ruƙe qugu tana magana.
Kafin haris yabata amsa deeja ta kar6e da cewa"Saboda haka Allah ya halicce ta, baki ga banbancin da ke a tsakanin kowannan mu bane? Wani yana da tsawo wani Jiki wani mara ƙiba, ahaka kowa da shekarunsa" da alama jamima bata fahimci me take nufi ba, Majnun sarkin mahaukata yace"to itama taje Allah ya ƙara mata tsawon mana sai ta koma kamar Angel" bismilla parveen tai tare da yunƙurawa ta sauko daga saman gadonta, ta rarumi pilow, majnun na ganin ta yi hakan ranshi ya bashi cewar shi zata buga, aiko da gudu ya nufi sashen toilet ɗinsu yana dariya, Sai da tafara zuwa ta kar6i kayanshi da azeeza ta jefar ƙasa ta ruƙo su da hannu ɗaya, yayin ɗayan hannun ke ruƙe da pillown data ɗauko Tabi bayan shi Cikin sashen toilet ɗin, Bata jima da shiga ba suka jiyo sautin kukan shi yana zazzaga mata masifa.
Murmushi kowannan su ya saki, har lokacin Azeeza na zuƙunne ƙasa kanta saman gwiwarta, Saukowa daga saman gado Gabriel yai tare da nufar inda take, har ya kusa ya isa muryar haris ta katse shi"me zaka mata" Kallon shi Gabriel yai ba tare daya bashi amsa ba, Ya cigana da tafiya
"Kada ka kuskure kace zaka yi mata magana, shisshigin yayi yawa, wannan fa ba ƴar uwarka ba ce, yakamata kadaina manne mata" rai 6ace haris ke yi mashi magana, ko ta kanshi Gabriel baibi ba, damuwarshi akan Azeeza ne, baya son yaga tana kuka, saboda ƙaunar da ta ke yi mishi, zuƙunna yai agabanta tare da kai hannu ya ɗago da kanta fuskar nan sharkaf da hawaye ta ɗaura idonta akan nashi
"Its okey azeeza, stop shedding ur tears, i don't know why ki ke son zubar da hawayen ki, akan abunda bai kai ya kawo ba," hannayen shi ya É—aura saman fuskarta yana goge mata hawayen, duk sun zuba ido suna kallon su banda Angel da ke ta shan kukanta ba tare da sauti na fita ba, An fama mata ciwon dake damun zuciyarta.
Ganin yaƙi jin maganar shi hada share mata hawaye hakan yasa haris yunƙura ya miƙe zai nufe su, Muryar azeeza na kerma tace"dan Allah haris ka ƙyale shi, ni bansan meyasa ku ka ɗaura mashi karan tsana ba, koda ace Gabriel shine silar abunda ya faru da Danish, bai kamata kuna mishi haka ba, tunda ya nemi yafiyarmu ya gane kuskurenshi, shi kanshi fa bada son ranshi hakan ya faru ba, Angel ta riga ta yi mana bayanin komai......"
Tunkan ta ƙarasa maganarta, deeja ta katse ta da cewa"Azeeza kina da matsala! Tausayin ki bazai ta6a bari ki ga laifin shi ba, ke kowa naki ne, dame gaskiya da mara gaskiya, yanzu dik irin abunda Gabriel yai ma ɗan uwan mu Danish ke baki gani ba? Cikin mu ba wanda bai yi zazzza6in rashin Danish ba, wannan ƙaton Ya haddasa mana baƙin Ciki acikin zuciyar mu, ya naƙasa mana ɗan uwan mu, amma ahaka kike biye mashi, har wankin kayan shi ke kike yi kamar baiwarsa, kamar fa kina ƙara bashi damar da zai cigaba da cutar da mu ne" cikin nuna 6acin rai Deeja ta yi maganar, Dama sun fi kowa tsanar Gabriel ita da Haris, Su biyun nan sun zame mashi ciwon kai da masassara, Deeja da haris tamkar abu ɗayane, Kusan halinsu ɗaya, Idan suka tsani mutun sai ya ji kamar ya haɗiyi zuciya, kamar dai lokacin da Aka kawo Angel da suka addabe ta kafin asasanta, Zafin zuciya ne dasu, suna da wuyar sha'ani sai dai duk da hakan suna da kyakkyawar zuciya.
Ranshi bai ta6a 6aci ba irin na yau, Zame hannayenshi yai daga saman fuskar azeeza da yake share ma hawaye, Ya miƙe tare da juyawa yana kallon haris dake a tsaye yana jifar shi da kallon tsana.
"Bafa tsoron ku nake ji ba, sannan ba ƙarfi kuka fi ni ba, duk abunda ku ke yi min na ƙyale ku ne saboda nasan laifina ne, na rasa gane ku wasu irin mutane ne, sai kace ba kusan tsautsayi ba, nifa bada son raina na aikata mashi hakan ba! yadda ku ka ji zafi acikin zuciyarku bai kai kwatankwacin wanda naji ba, a lokacin dana naushi idonshi, ga Angel nan ku tambayeta irin tashin hankalin dana shiga ae ita tasa komai, har cewa nayi ta cire idona ta sanya mashi duk don saboda tausayin shi da naji........." kasa ƙarasa maganar yai, idanuwanshi cike tab da kwalla, jikinsu Hanna ba ƙaramin sanyi yayi ba, saboda akwai ƙamshin gaskiya a kalaman shi,
shigowa cikin ɗakin parveen tayi hannunta ruƙe dana majnun da ta sanyawa kaya, har sun shirya, Ganin Gabriel dake tsaye ido ya canza launi ga kuma haris agabanshi, hakan yasa ta dan dakata da yin tafiyar tana kallonsu,
"kuna ɗaukata tamkar wani maƙiyin ku, nifa ba bare bane acikin ku, kawai don bamu arayu atare bane sai daga baya na tsinci kaina acikin, da ku da ni duka prisoners ne da ƙaddara ta haɗa mu rayu a wuri ɗaya, akan me zan cuci wani acikin ku? Babu wanda yafi wani fa acikin mu! Bana jin daɗin juyamin baya da ku ke yi, nifa mutunne ba dutse ba, ina da zuciya a ƙirjina, dole in ji zafin ƙiyayyar da ku ke nuna min, meyasa nima baza ku soni ba ku ƙaunace kamar yadda kukeson junan ku? Yai tambayar cikin ƙunar rai yayin da ya ke bin kowannansu da kallo.
"Hatta azeeza da take ƙarama acikin ku tafi hankali, ita da Angel, sune waɗanda nasan ba za su ta6a juyamin baya ba, kuma ɗin rashin fahimta ne, a bun da baku sani ba, Danish shine silar da hakan ta faru, mun samu sa6ani dashi, ya sanya hannu ya shaƙe min wuyana, nayi nayi ya saki yaƙi saki kamar zan mutun a lokacin koda ace wani daga cikin ku ne yaji an shaƙe mashi wuya za'a kashe shi cikin fitar hayyaci zai iya yin komai donya ƙwaci kanshi, to nima shine abunda nayi at end nazo ina danasani, da ace da son raina na aikata mashi hakan ai baza ku ganni ina jinya ba,"
Haƙiƙa kalaman Gabriel sun yi matuƙar yin tasiri acikin zukatansu, duk sai su ka ji ba daɗi irin wariyar da suka nuna mashi.