Sashe 56
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Farko dai ke doguwace, fara sol son kowa ƙin wanda ya rasa, idanuwanki Dara dara dasu manya farare ƙyal launin su brown colour, ga dogon hanci, tausasan la66anki brownish colour ne yadda kasan yankan tumatur saboda tsabar kyansu, ke fa ɗin kyakkyawa ce ajin farko, tun da angel ta soma magana batool ta saki baki galala tana kallonta, Tsabar farin Ciki ya hana ta furta komai, Daɗi take Ji ana zayyana mata irin kyanta,
Wani abu da angel bata sani ba, tun lokacin da Ta soma zayyana kyan fuskar Batool, Gaba ɗaya su Hanna dasu azeeza, rubina Hibba, eve, yasmin, da deeja da parveen Kaf ɗinsu Suna a zuƙunna kewaye dasu, Jira suke ta kammala Zayyana ma Batool kyawun fuskarta suma ta faɗa masu Ya nasu Kyan yake, Tofa angel ta zama Mirror,
Baƙaramin wahalar da ita su ka yi ba, Sai da tagama da matan sai ga Javed da mubeen, hada naufal suma suka tasa ta gaba sai ta faɗa masu Ya kyawun fuskarsu yake, har wani jiri take gani acikin idanuwanta saboda tsabar gajiya, Ga gunwa tana ji sunƙi bari ko toilet ta shiga ta watsa ruwa ajikinta, sai daɗi suke ji an faɗa masu cewa su kyawawane, Sai da ta kammala Javed Yace"Yanzu ki faɗa mana waye yafi kowa kyau acikin mu"? Suka tsareta da ido suna jira su ji amsar da zata basu, Kowa sai gyara sumar kanshi yake yi don ta ce shine yafi kyau,
"Zan fada maku tsakani da Allah, wanda yafi kowa kyau acikin ku, Baya atare daku yanzu haka," gaba É—aya taga sun kwashe da dariya, Da mamaki akan fuskarta tace"meya baku dariya" Mubeen yace"saboda Kin canka dai dai, Wannan wanda baya atare damu shine yafi kowa kyau acikin mu,"
Murmushin gefen fuska angel tasaki tare da É—aura idonta kan batool tace"Amma duk da kyanshi, Batool itace zata zo na É—aya saboda Ita macace, bayan batool kuma sai Azeeza kodan saboda wannan kyakkyawan murmushin nata, Daga azeeza kuma sai Javed...." duk wanda ta ambaci sunanshi sai taga yanata washe baki
"To ki faÉ—a mana wanene Yafi kowa muni Acikin mu"?
Batare data yanke shawara da zuciyarta ta basu amsa da cewa"Haris ne, Cikin mata Kuma deeja ce"
Deeja dake atsaye Ta ruƙe qugu tuni ta tur6une fuska, jin an kirata da mummuna, dama a ƙule take da angel ganin yadda sauran Ƴan uwanta duk suka Saki jiki da ita, bayan irin Ƙarairakin da tayi masu, ita kanta angel tayi mamakin zuwan da su ka yi wurinta, bayan Irin juya mata bayan da su kayi amma yau sai gashi sun sake da ita, duk da tasan Zaiyi wuya ayanzu su yarda da ita, kamar yadda suka yarda da ita a lokacin Baya,
Duk wannan abun dake faruwa Haris Baya acikin É—akin bai jima da farkawa ba, Ya wuce Toilet, baisan wainar da suke toyawa ba,
"Kowa ya ta shi yaje ya shiga wanka, ya tsarkake jikin shi, kafin giants su kawo mana breakfast É—in mu," batool ce tayi masu magana, É—aya bayan É—aya kowa ya mike Ya nufi Toilet,
Lokacin da suka kammala Yin wanka, bada jimawa ba, Giants Suka kawo masu Abinci, Yau Hada Chocolate Cake aka kawo masu Kowa ɗaya, ba ƙaramin dadi suka ji ba, Saboda suna matuƙar son cake,
Yanzu sun saba da zarar Sun kammala Cin abinci, Sai a haɗu a motsa Jiki, Bayan sun gama, Kowa zai zauna ya huta ne, Yau fa tun da aka ta shi basu ga walwalar haris ba, Hatta angel tayi mamakin halin daya shiga yau, ya saba kullum sai ya ƙunsa mata baƙin Ciki, amma Yau kota kanta baibi ba, ko abincin shi bai ci ba, kamar wanda ɗan kanoma Ya kama haka ya dinga yi masu safa da marwa acikin ɗakin, idan ya gaji da yin zarya ƙafafuwanshi suka soma yi ma shi raɗaɗi sai ya koma saman gadonshi ya kwanta ya kalli ceilling, damuwace ta ishe shi ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji daɗi, Ya gaza samun kwanciyar hankali, kowa ya kasa gane kanshi,
A lokacin suna zazzaune Saman gadajen su suna hutawa, Haris Ya sauko daga saman nashi gadon, Buguzun buguzun yake tafiya har zuwa bakin kopar ɗakin tsohuwa yaci burki ya tsaya tare da kai hannu ya kwankwasa ƙopar, Duk suka zuba mashi ido suna kallon shi, kusan sau uku yana buga kopar kafin, Ya soma jin alamun ana buɗe kopar ta Ciki,
Tsohuwa Ce ta fito hannu ruƙe da sanda, tun daga kan yanayin yadda ta ganshi ta tabbatar da cewar ba a hayyacin shi yake ba, ya haɗe rai zuciyarshi har wani tafarfasa take Yi,
"Harisu Lafiya ka ke buga mun ƙopa"? Yana huci yace"Nagaji da jiran dawowar danish, So nake naganshi, ko bai warke ba adawo mana shi cikin mu mu cigaba da yin jinyarshi, hankalin mu sai yafi kwanciya," tunkan haris yakai ƙarshen maganarshi, Sauran ƴan uwan nashi duk suka sauko daga sama beds ɗinsu suka nufi inda tsohuwa da haris suke atsaye, banda angel dake hakimce saman gadonta, tana kallonsu,
Marairaice mata fuska Azeeza ta yi, Cikin sanyin murya ta wanda ya karaya tace"Idan har dagaske Kina son Mu, adawo mana da danish É—inmu mu cigaba da yin jinyarshi acikin mu, mun yi maraicin rashin shi acikin mu,"
Ɗaya bayan ɗaya suka shiga Yi mata magiya akan adawo masu da danish ɗinsu, Su suke Yi mata magana amma idonta na akan angel, dake kallonta fuskarta ɗauke da kayataccen murmushi, aranta tace"nasan yanzu zata ƙara jin haushina saboda sun fara tuhumarta akan bazata dawo masu da ɗan uwansu ba, Yanzu ya rage naki tsohuwa kodai ki dawo da danish ko kuwa sufara zarginki,"
Gyaɗa kai tsohuwa tayi fuskarta a tur6une tace"Ku kwantar da hankalin ku, Yau danish zai dawo Cikin ku, Kuje ku xauna," Takai ƙarshen Maganar tare da juyawa ta shige Cikin ɗakinta,
A bakin ƙopar ɗakinta, suka Zazzauna don yau sunci alwashin indai Danish bai dawo ba anan zasu kwana, angel dai na can kwance daman gadonta bata motsa ba, ta zuba ido tana jira taga ta wace ƙopa za'a shigo masu da danish, Dagaske zai dawo yau ko kuwa? Lumshe idanuwanta ta ɗanyi tana jin bacci sama sama,
Har wuraren marece ba'a dawo masu da É—an uwansu danish ba, sai da kowa ya fidda rai da dawowarshi aranar
Kwatsam Ba zato ba tsammani, suna zazaune a bakin kopar ɗakin tsohuwa wasu har sun fara gyangyaɗin Bacci, Suka soma Jin motsi buɗe ƙopa, zumbur kowan nan su Ya miƙe Cike da sa ran Ganin danish, sun tabbatar shi ne saboda yanzu ba lokacin kawo masu abinci bane sun riga sunci tun ɗazu da safe,
takun Tafiyar Giant suka Jiyo daga Can kusurwar Benan, Jiki na Rawa suka Watsa da gudu Xuwa bakin stairs É—in Kowa Ya ci burki yana faman Baza Idanuwanshi, Tuni Giant É—in daya kawo shi Ya juya ya fuce Ya datse door,
Tun daga ƙasa suka soma Kallon shi, doguwar ƙafarshi sai kerma take yatsun ƙafar duk sun manne ma juna, jikin shi sai rawa yake yi idanuwanshi sun zazzaro tamkar ƙwayar idonshi zata faɗo ƙasa, jijiyoyin wuyanshi duk sun fito ruɗu ruɗu saman farar fatarshi,
Kayan jikinshi duk sunyi uban squeezing, sumar kanshi ta hargitse duk ta cukuikuiye
Lamarin ya yi matuƙar ta6a zuciyoyinsu, Duk sun gaza yi mashi magana, haris ne ya yi ƙoƙarin furta sunan shi"DANISH lafiyarka kuwa? Ko har yanzu jikin ne"? Ya yi tambayar yana ƙoƙarin matsawa kusa danish,
Dafe kai suka ga yayi da hannuwanshi, Ya fasa wata irin gigitacciyar ƙara, wadda ta razanar dasu, Angel dake niyar nutsawa Cikin baccin ta, Sautin ƙarar danish ya farkar da ita, a firgice ta ware idanuwanta tare da kallon inda suke a tsaitsaye Cirko cirko abakin Benan, Da sauri ta sauko daga saman gadon Jikinta har 6ari yake yi, ta cikinsu ta ratsa ta tsaya Dab dashi tana kallon shi,
Ya ƙanƙame Jikinshi yana Girgiza masu kai, la66anshi na kerma ya soma faɗin kada su matso kusa da shi, baison ganin kowa, ya tsani kowa" yana kai ƙarshe maganar shi, da gudun gaske ya bi ta tsakiyarsu ya bangaje su bai nufi ko'ina ba sai Cikin toilet area ɗinsu Ya shige ɗaya daga Cikin toilet ɗin Yaja ƙopa ya datse yadda baza su iya shiga ba,
Fashewa da kuka Aziza tayi saboda tsoran da taji,
Da gudu suka ɗunguma zuwa bakin ƙopar ta farko, Haris ne ya shiga bin ƙofofin toilets ɗin yana kwala mashi kira"Danish! danish! Baka ji ina kiran ka? Wai meke faru ne? Pls ka buɗe mana ƙopa, Munyi kewarka sosai," a ƙopar toilet na ƙarshe yaje ya bubbuga ta yaji ta a garƙame alamar Nan ciki danish ya shiga,
A ruÉ—e rubina tace"Bari naje na faÉ—a ma tsohuwa tazo taga halin da É—an uwanmu yake ciki, kada mu rasa shi" ta yi maganar tare da juyawa da gudu ta fuce,
Cikin shessheƙar kuka aziza tace"Wayyo Allah danish meya ke faru dakai ne? Dan Allah ka buɗe ƙopar,"
Hawaye ne acike da idanuwansu Javed, Eve tace"Ban ta6a ganin shi cikin wannan mawuyacin halin ba, sam danish baya a hayyacin shi," tana rufe baki deeja tace"Ai duk laifin Angel ne, itace sila da ace bata ta6a lafiyar jikin shi ba, da duk hakanbata faru ba,"
Cike da takaici Angel tace"Nifa bani ce silar shigar shi cikin halin nan ba, koda ace ni ce amma ae an kai shi treatment room ko? meyasa daya dawo babu sauƙi ajikin shi? Kenan ba duba lafiyar jikin shi akayi ba, Wani abunne daban su ka yi mashi........"tsawa Haris ya daka mata"Idan har Danish ya rasa ranshi, ke ma ki shirya binshi, ƙafarshi kafarki, muguwa kawai,"
Fashewa angel tayi da matsanancin kuka tana faÉ—in ita ba ita bace sila,
Faɗo wa cikin wurin rubina tayi har suna haɗa baki wurin tambayarta ina tsohuwar take, idonta cike tab da kwalla tace"Na kwankwasa ƙofar ɗakinta, bata buɗe ba"
Guntun tsoki Haris yaja, Yaci gaba da bugun ƙopar yana kiran sunan danish amma shiru bai amsa masu ba,
Gaba ɗaya sun taru agaban toilet ɗin Sai faman ƙwala mashi kira suke yi ya yi shiru babu magana,