Sashe 7
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
duk duniya babu wanda bata Jin tausayin shi Irin mahaifinta, azabtar da shi take Yi, Shi kuma Ya mutu akan sonta Bai iya rabuwa da ita ga shi ta tsani taga yana karatul Alqur'ani, da zarar Ya fara saita 6allo mashi aikin da zaisa ya ajiye karatun, kuma bai isa Yayi salla acikin gidan ba idan uziri ya hana shi zuwa masallaci, Kamar shaiÉ—aniya haka take, har malami aka dauko yayi mata addu'a Don a fidda aljanun da ake hasashen tana dasu, tun malamin na cikin yi mata rukiya ya dafa kanta, ta dinga buge mashi hannu tana faÉ—in dama ya daina wahalar dakanshi, Ita lafiyarta qalou
Bayan malamin ya kammala Yi mata ruƙiya, Ta sace takalmanshi ƴan madina, sai da ya tashi tafiya aka nemi takalma wayam an ɗauke su, su ka yi ta nema kasa ko sama babu su, bayan tafiyarshi ta fiddo takalman da ta 6oye a ƙarƙashin gadonsu taba Taj, wai gashi A maida mata su na yara daidai kafarta, haushi kamar Ya rufeta da bugu, yaji kunyar abun nan haka ya kwashi takalman yaje har gidan malamin Ya mayar mashi da abun sa,
Babban abunda zai baka mamaki da ita sam bata da tsoro, yasha farkawa tsakar dare Ya sameta zaune a falo tana kallon cartoon har ta Iya kunna kallo, tun abun na damunshi harya hakura ya kyaleta,
Akwai ranar da zaije gabatar da wani programme agidan radion su, Sai daya kammala shiri Yaji ƙopa a rufe, Tasa key ta rufeshi, dalilin da ya sa Ta yi ma shi haka shi ne, Kullum In zai tafi Evening duty, a mota yake ɗaukarta yakaita Gidan Amininsa Uzair, Ita kuma bata son zuwa gidan tafi son duk inda zai je ya tafi da ita, Wannan ne yasa a ranar Ta saci keyi din ɗakin shi bayan ya shiga wanka, Ta ɗauko kujera ta sanya Yadda tsawonta zai kai, Ta murɗa mashi key ta datse ɗakin Ƙarfin Hali,
Tun yana lallashinta ta buɗe ma shi ƙopa har yakai ga danƙara mata zagi kamar mai yin magana da babban mutun, Ya zazzageta Da masifa duk wannan baisa ta buɗe mashi ƙopa ba, har saida ya kira Uzair A waya ya sanar dashi cewa Angel Ta rufe shi a ɗaki, ya kawo mashi taimakon gaggawa batare da 6ata lokaci ba sai ga uzair Yazo gidan, A zaune Ya same ta saman Sofa tana kallo, aikuwa ya kar6e key din a hannunta Ya je ya buɗe ma shi ƙofa, koda ya fito baibi ta kanta ba Ya fuce daga falon yana huci, Uzair dai yaci dariya, shi ya ruƙo hannunta adole suka tafi da ita wurin aikin nasu,
Saboda bala'in angel Saida yakai ga kullum sai Taj Ya zubar mata da hawaye don ta dinga Jin tausayin shi, bawan Allah duk yayi duhu ya rame, ita kuwa Babyn tashi har kumatu ta yi saboda rayuwar Jin daÉ—i, yarinya fa kamar rainon turai fara sol da ita, gashi duk wanda yaji Labarin Halayyarta bai yarda, saboda kowa Mamakin shekarunta ya ke yi Just 5 years fa,
Duk irin ɗawainiyar da yake Yi mata sam bata Gani Shine girka mata abinci Yayi mata wanka ya wanke mata gashi Yayi mata kitson kalaba, har ƙunshi na jan lalle yake ƙunsa mata da kanshi, Amma yarinyar nan Idonta sun makance idan kana son Ganin Dariyar ta to ka tabbata ta ƙuntata ma Mahaifinta ne,
Lokacin da takai Shekara 7 a duniya, Ranar wata friday Ya shiryata zasu fita Gidan ɗaya daga Cikin abokanan aikinshi, mai suna Muhsin lokacin da suka je ba ƙaramin farin Ciki muhsin da matarshi sukayi ba, musamman da yazo masu da angel, yarinyar da kowa yake kwaɗayin Yin tozali da ita saboda kyanta, Allah yayita da farin Jini,
Tunda suka je gidan aka kawo masu kayan makwalashe, Taƙi ci da suka tambaye ta meyasa baza ta ci ba sai cewa tayi Daddynta ne Ya hanata cin abincin gidan mutane, a lokacim kasa magana taj yayi saboda baisan amsar da zai basu ba, ƙiri ƙiri ta yi mashi ƙarya, Muhsin ya roke shi akan yayi mata magana taci abincin, Sai taj ya sanya baki yana lallashinta akan taci, da buɗar bakin ta sai cewa tayi "Ai ko yace inci idan muka je gida buguna yake yi,"
Gaba ɗaya Angel ta kashe mashi baki, Muhsin kuwa ya nuna rashin jin daɗin shi akan maganar angel, har suka ta shi tafiya Bata Ci komai ba, tun lokacin yaci alwashin saiya yi mata fada in suka je gida, Ashe da zasu Baro gidan, Ta sace warin Takalmin matar gidan mai tsadar gaske, Babu wanda Ya lura sai bayan Da sukayi nisa da tafiya saman titi, Ta ɗago takalmin tana nuna mashi Wai yakai amayar mata dasu Na yara, Sun burgeta, hankali atashe Yayi parking ɗin motar, dama a ƙule Yake da ita wuyanta Ya shaƙo Ya jijjigata Ya hauta da masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, a karshe yace"Bana sonki kin fita araina, Ke ni ba mahaifin ki bane, bansanki ba ki fita arayuwata" Yayi waɗannan kalaman ne Cikin fushi, buɗe motar yayi tare da fitar da ita waje"Kije ki nemi wani uban"
Yayi tunanin zata saduda ta bashi haƙuri, Amma sai yaga ta watsa da gudu Ta nufi Cikin wata ƴar kasuwa mai tarin jama'a, fitowa yayi daga Cikin motar yabi bayanta, yana faman ƙwala mata kira Koda Ta lura yana binta saita Ƙwala Ihu tana faɗin "Wayyo Allah taimako wani mutun zai sace ta, ɗan yankar kaine ataimaka A mayar da ita wurin iyayenta, kafin kace me Tuni mutane sunyi dandazo akansu, Ganin mutane sun taru hada ƴan ƙato da gora, Aikuwa Ta fashe da kuka ta faki idon mutane ta sanya hannu ta daki hancinta batare da kowa Ya ankara ba, Ya soma bleeding duk don mutane su ɗauki abun serious sosai tadinga kuka tana Faɗa masu cewa"Ba mahaifinta bane sace ta ya yi yana gana mata azaba, Yanzu ma gudowa tayi tana neman iyayenta, dan Allah Hukuma su dauki mataki akanshi, Jin wannan maganar yasa ran mutane Ya 6aci, Musamman ƴan ƙato da gorar nan sun fusata sosai, Kamar jira su ke yi dama a harzuƙe suke, Gaba ɗaya suka rufar mashi da bugu kamar sun samu jaki ita kuwa ko ajikinta, har rantsuwa ya dinga yi masu akan cewa Ƴarsa ce ba satarta yayi ba, Amma suka ƙi yadda saboda bata yi masu kama da jinsin baƙar fata ba, tafi kama da ƴa'yan larabawa da turawa, shi kuma yana da ɗan duhun fata ga kuma Launin idonta ba kalar nashi ba
Ba don Allah yasa an samu wani bawan Allah ya kira ƴan sanda ba, da tuni ƴan ƙato da goran nan sun jima da halaka Tajuddeen, daƙyar suka ƙwace shi a hannunsu, Sunyi ma shi jina jina, rashin sani yafi dare duhu dayawa mutanan da suka rufar mashi da bugu sun san shi, saboda sanannan Ɗan jaridane a garin, babbar matsalar da aka samu, mafi akasarin su Fuskarshice dayawa basu sani ba muryar shi kawai suka sani, A wannan lokacin kuma ba wanda ya an kara kuma ba su ba shi damar da zai yi masu bayani ba.
Police station suka wuce dashi, A cikin Cell suka tura shi, tare da garƙame shi, Sam baya acikin hayyacinshi, Ya galabaita sosai,
A Yayin da Taj ke acikin Cell kulle cikin mawuyacin Hali, Angel tana Office ɗin Dpo tana shan A.c ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya,
Ganin yarinyar tana da wayau yasa dpo ya soma tambayarta Ya sunanta, Tace mashi sunanta Angel, ya kuma tambayarta ko zata Iya tuna wani abu game da mai satar Yaran da aka kama ya sace ta? da budar bakinta sai cewa tayi ae bashi kaÉ—ai bane mai satar Yaran ba, Akwai abokin aikin shi Uzairu, atare suke sace ya'yan mutane,
A lokacin taj ya dawo hayyacinshi, Suna magana da wani inspector Ya nemi alfarmar su taimaka su ba shi waya Ya kira aminin shi da matar sa zasu bada shaida akan shi,Babu musu inspector É—in ya bashi damar Yin waya, Nan ya kira uzair Ya kwashe duk abunda Ya faru ya sanar mashi,
Bawan Allah uzair ashe da rabon Yaci na jaki, Saboda tsabar sauri Ko aneelerh bai jira ba, yaja mota Ya nufi station din da taj ya yi mashi kwatance.
Bayan yayi parking ɗin motar, Ya fito ya shiga Ciki da azama, Kamar jira suke Uzairu Ya ƙaraso suka Tallabi ƙeyar shi zuwa cell ɗin da aka rufe Taj, Suka Hankaɗa shi ciki Lokacin daya Kalli tajuddeen dake ta faman Nishi Fuskar shi duk Sahun naushin mutane, bakinshi da hancinshi duk sun fashe, baisan Lokacin daya fashe da kuka ba kamar ƙaramin yaro, rungumeshi yayi ajikinshi, sosai, Gwanin ban tausayi,
Har kiran Angel a kayi daga office din Dpo, Aka nuna mata uzair suka tambayeta shi ne, Tace Eh shi ne.
Sun sha wahala a hannun ƴan sandan, Yinin ranar har dare ya yi ana Bincike a kan su, Daƙyar suka samu a kayi masu alfarmar su kira wani da zai bada shaida akansu, Anan ne Uzair Ya kira Aneelerh, Ya bata address ɗin Ps din da zata same su,
Ba'a ɗauki Lokaci ba Motar Aneelerh Ta ƙaraso Cikin harabar station ɗin, hankalin ta duk Yabi ya tashi Jin suna a hannun police, bayan Tayi parking ɗin motar, Ta fito sanye Cikin doguwar riga ta yafa mayafi akanta a hanzar ce ta nufi cikin station ɗin, Lokacin da ta shiga Ciki, ƴan sandan suka Yi mata jagwaro zuwa cell din da aka rufe su, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba Ganin Yadda aka raunata Taj, duk ya fita hayyacin shi kamar wanda yayi hatsarin mota, Saboda jigatar da yayi.