← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 179

Sashe 45

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokaci ɗaya taji mummunar faɗuwar gaba ras! Tamkar ƙirjinta zai dare biyu, bugun zuciyarta ya ƙaru, Jiki na rawa ta sauko daga Saman gadon muryarta na kerma take ambaton sunan Junaid,

Da gudun gaske Ta faɗo Cikin Falon, Tana ɗaura kanta saman Sofa ɗin data kwantar da junaid, taga wayam babu shi sai dai towel ɗin data nannaɗe shi aciki, A ƙasa aka jefar da shi,

Kamar afarmaki take ganin lamarin, Tsabar ruɗi tarasa me zatayi, Tsananin tsoro ne bayyane akan fuskarta, Ƙarasawa tayi gaban sofa ɗin ta sanya hannu tana shafa Saman kujerarar, ta tabbatar cewa an ɗauke Mata Yaronta, tunani tayi kodai Musa ya shigo ya ɗauke shi ne? da gudu ta zabura Ta fito daga cikin falon, Har ta kusa kaiwa Bakin gate ta juyo kukan baby junaid ɗinta, a matuƙar gigice ta juya ta koma Cikin gidan, duk inda ta nufa sai taga babu shi, Rushewa tayi da matsanancin kuka tana faɗin"Innallalahi wa'innna ilaihirraji'un! Wayyo Allah na! dan Allah wanene ya shigo? kada ku cutar mun da yarona na roƙe ku, ku ƙyale mun shi, ' tana Cikin maganar nan tajiyo takun tafiyar mutun a firgice ta juya bayanta, gifcin shi ta gani koma wanene yana a sanye Cikin bakaken Kaya, Fuskar shi tana sanye da face mask, Hannunshi na ruƙe da Baby Junaid, Da gudun gaske Aneeelerh tabi bayanshi, sai dai kafin ta ƙarasa tuni ya 6ace ma ganinta,
Gaba É—aya ta haukace Jikinta sai tsuma yake yi ga wata uwar zufa data tsastsafo mata, ita ba kanta take ji mawa ba, ÆŠanta take jimawa ba, shida bai mallaki hankalin shi ba,
"Dan Allah na roƙe ka ka dawo mun da ɗana, Kome kakeso zan baka, Amma kada ka cutar mun shi, idan ma ni kakeso ka dauke ni ka ƙyale mun shi pls," cikin shessheƙar kuka tayi maganar,

Motsi ta kuma Ji daga can saman stairs ɗin gidan, A hautsine ta ɗaga ido tana kallon mutun dake atsaye, Hannun shi ruƙe da baby junaid, ƙarfin hali hada ɗaura shi saman kafadarshi, yana shafa bayanshi, kuma yaron yayi shiru,

Zuba ma shi ido tayi tana kallon shi batare da ƙyaftawar ido ba, Koma wanene wannan mutumin ba ƙaramin karkarfa bane, Yana da tsayi da kuma faffaɗan Ƙirji, ta ko'ina ya rufe jikin shi, ta yadda mutun bazai iya shaida shi ba,
Muryarta na kerma tace"Dan Allah kada ka cutar mun da shi, kome kakeso zan baka," ta yi maganar tana kallon shi, zufa ta ko'ina saman fuskarta,
Gani take kamar zai jefo shi ta saman bene ne ya faÉ—o kasa kanshi ya fashe,
Fashewa ta kuma yi da wani sabon Kukan, Tunawa tayi da musa driver da gudu ta juya ta nufi hanyar fita don taje ta sanar da shi abunda ke faru,
Harta ruƙe handle ɗin ƙopar, Muryar mutumin ta ratsa kunnnuwanta,
Cikin harshen Turanci yace"idan kika kuskura kika fita, zan wurgo da shi ƙasa," Ras Taji gabanta ya faɗi, Kamar gunƙi haka ta ƙame, zuciyarta a cunkushe Ta juyo tana kallon shi, Har lokacin Yana a can sama,
Muryarta na kerma tace"Na fasa bazanje ba, wlh bazanje ba, dan Allah ka bani ɗana, wlh nayi maka alƙawari bazan ƙara zuwa gidan ba,"
Dawowa cikin Falon Ta yi, A bakin stairs É—in ta tsaya, fuskarta jaga jaga da hawaye, Bata ta6a ganin tashin hankali ba irin na yau, Ko wanene wannan mutumin? Taya akai ya shigo Cikin gidan? Bayan makullan gidan Suna a hannun jami'an Æ´an sanda? Anya kuwa mutunne kodai ta bango ya ratsa Ya shigo?
"Ka faÉ—amun ko nawa kakeso zan baka ina da kuÉ—i, Ni dai kawai burina ka bani Yarona,"
Tana magana tana taka staircases É—in, a kokarin ta nata haura inda yake,
"Hajiya" Muryar Musa driver ce, A firgice aneelerh ta juya tana kallon musa, Ai koda musa yayi arba da mutumin dake A can saman stairs sanye da bakaken kaya, Nan take jikin shi ya hau yin kerma, Ya shiga ambaton"Ƙalu Innallahi wa'inna ilaihirraji'un hajiya wannan kuma daga ina"?
Cikin muryar kuka aneelerh tace"Nima bansani ba, Daga shiga Cikin ɗaki na dawo na taras ya dauke mun baby junaid ɗina, dan Allah kataimaka ka sanya baki mu bashi haƙuri ya bamu junaid mu tafi mubar masa gidan,"
Kallon shi musa Ya kuma yi"Bawan Allah, Don son da kake ma iyayenka Ka taimaka ka bamu yaron nan, Wlh tsautsayi da ƙaddara ne ya kawo mu Cikin gidan nan, dama saida na gargaɗi hajiya nace mata kada mu zo, Amma ta sanya naci akan sai mun zo yanzu ga irinta nan"
Roƙonshi suka dinga yi ko tanka masu baiyi ba, tamkar baijin me suke cewa, Ya ƙanƙame Yaro a hannunshi sai shafa sumar kanshi yake yi,

"Hajiya wannan mutumin fa, ba bamu yaron nan zaiyi ba, Kizo muyi ta kanmu kawai, Allah zai baki wani É—an, idan ba haka ba mu duka zamu rasa ranmu,"
"Wlh ba inda Zanje sai ya bani yarona, saboda bakasan ciwon haihuwa ba shiyasa zaka ce mu tafi mubar ma shi yaro a hannu, " rai a6ace takai ƙarshen maganar, Duk yana atsaye yana sauraron su,
Suna Cikin yin maganar nan, gaba É—aya hasken gidan ya É—auke, duhu ya mamaye ko'ina,
Aneelerh ta shiga matsanancin tashin hankali, Cikin duhu taci gaba da tattaka matattakalar benan, Tana jiyo muryar musa yana kwala mata kira, amma ina kota kanshi bata bi ba, lokacin da ta ƙarasa hawa benan, Muryarta na rawa take faɗin"Bawan Allah, ka bani yaro na in tafi, nasan kana jina, dan Allah kada ka cutar mun shi," tana magana tana lalube Cikin duhu,
Motsin shi ta dinga Ji acikin kunnuwanta, alamun yana a kusa da ita, Kamar ma zagayeta yake yi, Jikinta sai kerma yake yi, ga wata uwar zufa dake tsastsafo mata, mugun tsoro take ji, amma saboda soyayyar dake a tsakanin uwa da É—a, ta kasa guduwa ta kwammace komai zai faru ya faru, koda zata rasa É—anta ne,
Wani irin daddaɗan ƙamshin turare ta soma shaƙa Cikin hancinta, koma wanene wannan Ba 6arawo bane, Kuma ba da niyar mugunta yazo ba, Lamarin ya rikitar da ita,
Cikin sanyin murya tace"Dan Allah ka bani shi in tafi, wlh bazan faÉ—i ma kowa naga mutun acikin gidan ba,"
Hannunta taji ya ruƙo, ras taji gabanta ya faɗi, ɗaura mata baby junaid yayi asaman ƙirjinta, da sauri ta tallebe shi, ta rungume abunta ajikinta, Natsuwa tayi tana jiran jin ya furta wata magana sai dai baice komai ba,
Lokacin da ta daina jin motsinshi a kusa da ita, a dai dai wannan lokacin hasken Gidan Ya dawo gaba É—aya ya gauraye ko'ina,
Nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, tare da ɗaura idanuwanta kan baby junaid dake ta sharar bacci, saman ƙirjinta,
Ƙara ƙanƙame shi tayi ajikinta, kamar zata mayar dashi Cikin cikinta, Yau da ace ɗan tahalinkin nan ya kashe mata shi, da kuwa har ranta zata iya rasawa,
"Hajiya zamu iya tafiya yanzu"? Musa ne yayi maganar jikinshi sai kerma yake yi, yana daga can down stairs, Harara ta wurga mashi,
"Ka bani key É—in motar, ka kama gabanka, Sakaran Namiji kawai, hada cewa in bar mashi yarona in Zo mu tafi, ban ta6a ganin ragwon namiji irin ka ba, duk macan da ta aure ka tayi asara, " zuru musa yayi mata da ido,"
Saukowa down stairs tayi tare da miƙa mashi hannu"bani key ɗin motar"
Cikin sanyin murya yace"ayi haƙuri hajiya ruɗu ne ya jawo hakan"
A fadace tace"dalla ni bani key,"
Zaro key ɗin motar yayi daga Cikin aljihun shi ya miƙa mata, tasa hannu ta fusge shi, Cikin fushi ta fuce daga cikin falon,
Da gudu musa yabi bayanta yana lallashinta.
Bayan ta rufe gidan da key ta buÉ—e mota zata shiga driver seat, da sauri musa Yayi hanzarin cewa"Dan Allah aunty aneelerh kiyi hakuri wlh bana Cikin hayyacina ne, su6ul da baka nayi wurin furta maganar, ban kaiga tace ta ba,"
Daƙyar musa ya samu aneelerh ta haƙura ta miƙa mashi key din motar, ta shiga passenger front seat ta zauna shi kuma ya zauna a driver seat,"
Da gudun gaske ya fusgi motar, kafin su ƙarasa gida saida ta gargaɗe shi akan karya kuskura ya faɗa ma su abie dangane da mutumin da suka gani Cikin gidan, yaja bakin shi yayi shiru tun da bai cutar dasu ba, su ɗauka tamkar mafarki su kayi, Yace mata toh,

Lokacin da suka ƙaraso Cikin gidan, A parking space Musa ya yi parking ɗin motar, ya fito ya zagaya ta other side ɗin ya buɗe ma Aneelerh mota,
Fitowa tayi hannunta rungume da baby junaid, Har lokacin Jikinta kerma yake yi, ta tsorata sosai da wannan tahalikin da ya kai masu farmaki,
Kallon musa tayi shima kallon nata yake yi, harara ta jefa mashi ya sunnar da kan shi ƙasa, Ni zan wuce ciki, "
"To hajiya sai Allah yakaimu, Allah ya kyauta gaba," bata amsa ma shi ba ta nufi Cikin gidan,
Da alama duk sunyi bacci, bata nufi ko'ina ba, Sai Cikin Bedroom É—inta, a saman gado ta kwantar da junaid, sai baccin shi yake yi hankali kwance,

Rage kayan jikinta ta yi, ta shiga toilet domin yin wanka, after 15 mins ta fito waist É—inta É—aure da towel fari,
Walking slowly ta nufi Saman mirror chair ta zauna, tare da É—aura gwiwar hannunta gaban madubin, ta zabga uban ta gumi,
Zuciyarta a cike take da tunanin mutumin nan, ko wanene shi? Taya akai ya samu damar shiga Cikin gidan dake a garƙame? Kodai bayan shigarsu ciki shima Ya samu damar shiga Cikin gidan? Shin me yaje yi acikin gidan, gaba ɗaya ta burkita ma kanta lissafi, kusan raba dare ta yi azaune tana tunani akan shi, bata iya gano komai ba, a ƙarshe ta miƙe taje gaban closet, ta buɗe ta curo kayan baccinta, Ta sanya su ajikinta,
Chapter 45 · 0% Book details