← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 179

Sashe 139

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

faɗa ya kaure a tsakanin Danish da Gabriel, Yadda kasan dawakai suna kokawa, dunƙule hannu Gabriel yai ya dinga naushin cikin Danish, Don ya sakar mashi wuyanshi daya shaƙe mashi amma yaƙi saki, duk da irin jahilin naushin da yake kaima Cikin shi, ko girgiza baiyi ba tamkar baisan ma ya na yi mata, ganin dagaske so yake ya kashe shi yasa Gabriel daddagewa Ya sauke mashi naushi saman idon shi na hagu, nan take Danish ya saki wuyan Gabriel Gaba ɗaya ya faɗi ƙasa hannun shi dafe da idonshi, kamar zaiyi hauka, shi kanshi Gabriel da ya yi silar jefa shi cikin halin da yake ciki sai da gabanshi ya faɗi, ganin Jini yana gangarowa ta cikin idon nashi daya nausa, wata irin gigitacciyar ƙara Angel ta saki, A matuƙar razane ta miƙe daga kwancen da take akasa ta watsa da gudu ta zube sama gwiwowinta agaban Danish, Hannu biyi ta sanya wurin ɗago dashi ta ƙanƙame shi ajikinta, Sai kuka take yi tamkar ranta zai fita, Gaba ɗaya tabi ta gigice, ta ruɗe ganin yadda idon shi ke fitar da jini jawur dashi,

"INNALALLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN! Gabriel ka kashe mishi idonshi, Ka kashe min Danish ɗina! wayyo Allah na! nashiga uku na bani na lalace!!" Hankalin Gabriel idan yai dubu to ya tashi, Kamar ya ɗaura hannu akai ya fasa ihu haka yake ji, la66ansa sai kerma suke yi, ya haɗa uban gumi, Muryarshi aruɗe yake faɗin"Angel bada son raina na aikata mishi hakan ba, shine ya shaƙe min wuyana! sosai ta ƙanƙame Danish ajikinta, Jikinshi yai wani irin mahaukacin zafi na fitar hayyacin, ko ina kerma yake yi, ga wani irin nishi da ya ke fitarwa.

hannunta data ɗaura saman nashi hannun daya rufe idon da ke bleeding dashi, tuni ya jima da jiƙewa sharkaf da jininsa, wa'iya zubillahi, Lamarin tamkar a mafarki yake faruwa, sun yi fatan ace mafarki ne su ke yi ba agaske ya faru ba, ta yi Danasanin Biye ma Gabriel da tai da duk hakan bata faru ba, da tasan Danish zai rasa idonshi silar yunƙurinsu na haura taga da bata yi gigin yin hakan ba, Yanzu gashi dare ɗaya sun ja mashi bala'e, Gabriel ya naƙasa shi, akan abunda bai taka kara ya karya shi ba, duk wannan koke koken da suke yi na cikin ɗaki basu farka daga baccin da suke yi ba, kamar waɗanda suka sha sleeping pills, tana kuka tana faɗin Gabriel ya zamuyi Dashi kada ya mutu, jinin shi sai zuba ya ke yi, Ya Allah kasa mafarki ne nake yi, bazan iya jure ganin danish cikin mawuyacin halin nan ba! Bazan ta6a yafe ma kaina ba, da kai kanka Gabriel kaine silar komai, Ga shi zan rasa ɗan uwana....

Da gudu Gabriel Ya nufi igiyar shanyarsu ganin mayafin azeeza da ta manta Tun ranar da akazo aka tafi ƴar gidan daddy, Angel ta shanya shi don ya bushe bayan ta kammala sanyaya mata jikin ta dashi, aranar suka barshi saman igiyar, ɗaukowa Gabriel yai jiki na 6ari garin sauri hada tuntu6e ya ƙarasa inda Angel take a zuƙunne ta ƙanƙame shi ajikinta, daƙyar Gabriel ya iya 6an6aro kanshi daga saman ƙirjin Angel, ya dawo dashi saman jikin shi, ya sanya mashi mayafin ya tamke mashi idanuwanshi dashi, sai nishi ya ke yi yana yarfa dogayen yatsun hannayenshi, Bawan Allah shi kaɗai yasan irin raɗaɗin azabar da yake ji acikin idonshi, jijiyoyin hannanyenshi dana wuyanshi shatunsu yafito ruɗu ruɗu saman fatarshi, hatta saman goshinsa jijiyoyinne, gwanin ban tsoro, sosai Gabriel ya ɗaure mashi mayafin duk don jinin ya dakata da zuba, haƙiƙa na yi baƙin Cikin ganin kakkyawar fuskar Danish da jini ya wanke ta, har saman wuyan shi, Gabriel na gama daure mashi idon nashi, angel ta sanya hannu biyu ta dawo dashi jikinta, ta ƙanƙame shi tana cigaba da yin kuka mai cin rai, tana faɗin"ɗan uwana rabin raina dan Allah kada ka mutu kabarni Danish ɗina, na gane kuskure na, ban da wayau, ga shi naja maka ka rasa idanuwanka, duk laifina ne, namanta cewa duk abunda ka ke yi kana yi ne don ka kare ni daga faɗawa halaka amma saboda taurin kai irin nawa nagaza fahimtar hakan, mun cuce ka Danish mune silar komai!!........ Sosai ta fashe da kuka, Shima Gabriel ɗin kukan yake yi tamkar ranshi zai fita, tashin hankalin da ba'a sama shi date!!

Mexai faru da danish? Ga ido yana ta bleeding zai mutune ko zai rayu a matsayin makaho mara ido ɗaya? Wani irin hukunci su haris zasu ɗauka idan suka gane cewa Gabriel ne silar da Danish ɗinsu Ya makance? Wani hali zasu tsinci kansu? Alƙamina Ya tsaya Cak! sai mun haɗu next page in Allah yakaimu da rai da lafiya, amma fa ga dukkan alamu Danish ɗinku saiya leƙa treatment room! Daga nan kuma.6arna zata auku, Don angel bazata juri zama babu shi ba, dama shine mai tsawatar mata akan karta haura taga, inaga idan babu shi........😳 hasashe na ne kawai🥱

💋PRISONERS💋

Saboda tsabar yadda jinin ke fita hatta Mayafin da Gabriel ya ɗaure mashi idon nashi ya jiƙe sharkaf da jininsa, Lamarin ya yi matuƙar gigitasu, Sautin muryarta har ya fara disashe wa saboda tsabar kukan da tasha, Gabriel da ke a zuƙunne ƙasa gabanshi sai yarfa hannayen shi ya ke yi, Yarasa uwar ubanshi zuciyarshi sai bugawa ta ke da ƙarfi da ƙarfi duk ya firgice tsoranshi kada Danish ya rasa ranshi silar naushin da yai mashi.

Jikinta ba ƙaramin zafi yai ba, har time ɗin hannayenta biyu na ƙanƙame da kanshi a ƙirjinta, Jikin shi ya saki sosai shi kaɗai yasan zogin azabar da ya ke ji a cikin idon shi. Sama sama numfashin sa ke fita, maƙoshin shi ya bushe, ta ko'ina babu sauƙi a jikin shi, addu'oi ta dinga karantowa tana tottofa mashi samar sumar kanshi,

Cikin fitar hayyaci ya ke yamutsa vest ɗin jikinta da hannayenshi masu dogayen akaifu, duk ya faffasa mata fatar bayanta, amma ko kaɗan bata ji zafi ba, batasan ma yana yi ba, damuwarta gaba ɗaya akanshi ne, Da ace tana da halin da zata iya ɗauke mashi ciwon ta maida shi akanta da tuni ta yi hakan, Zaifi mata sauƙi akan taga Danish acikin mawuyacin hali.

la66anta na rawa ta soma ambaton sunan shi tana faɗin dan Allah Danish kada ka mutu kabarni, kada ka daina motsi, ni ko idona ne ma zan iya badawa asanya ma ka, Ya Allah ka kawo mishi ɗauki, Wannan wata irin baƙar rana ce, Sosai take kuka, idanuwanta sun yi jaga jaga da hawaye ta rasa ya zata yi dashi ga jinin yaƙi daina bleeding, Gabriel da ya gama rikicewa Sai magiya ya ke yi ma Angel akan ta cire idon shi ɗaya ta sanya ma Danish tun da shi ne silar rasa idon nashi.

Duk da halin da ya ke ciki hakan bai hana shi ƙoƙarin motsa red lips ɗinsa da su ka jiƙe sharkaf da jinin da ke ta gangarowa ta cikin ƙarƙashin mayafin da Gabriel ya ɗaure mashi ido da shi, magana ya ke so yai mata amma ya kasa, la66ansa sun ƙi bashi haɗin kai, Jikin shi gaba ɗaya ba sauƙi, Yanke shawarar fita tai don ta sanar ma sauran ƴan uwansu ƙwara kowa ya sani, don su nemi mafita atare, Tana kuka tana ƙoƙarin 6an6are shi daga jikinta sai dai yaƙi bari ta raba jikinta da nashi, idanuwanta cike tab da ƙwalla ta kalli Gabriel muryarta na kerma tace

"Ka... ruƙe shi, Zan je na faɗa ma su haris," duk yadda gabriel yaso ya raba Angel da Danish abun ya faskara, mugun ruƙo yai mata bana wasa ba, Kallon Gabriel din tai"kaje ka yi musu magana kowa ya tashi su zo, " hawaye ta ko'ina a fuskarshi yace"Angel Pls kada ki faɗa musu cewa ni ne silar rasa idon shi......" tun kan ya ƙarasa maganar ta rufe ido tana zazzaga mashi masifa

"Har kana da bakin da za ka ce kada na faɗa mu su? Dole su san cewa kaine silar komai, mugu kawai ai bansan haka ka ke ba da tun farko ban biye maka ba.....hada zagi ta haɗa mashi, Jiki duk ba ƙwari Gabriel ya miƙe har wani jiri yake gani acikin idanuwanshi ga ciwon mai raɗaɗi da ya addabe shi, a haka ya fuce daga Cikin toilet din, bai shiga ɗakin ba a bakin ƙopar ya tsaya yana matse kwalla.

Fitar Gabriel ke da wuya, ta soma jin muryarshi ƙasa ƙasa yana yi mata magana, da sauri ta ɗaura kunnanta saman la66ansa don ta samu damar jin me ya ke son faɗa mata.

Angel ki daina zubar da hawayen ki saboda ni, lafiyata qalou, ba abunda ya sami idona....."

Cikin muryar ku ka tace "ƙarya ka ke yi min Danish nasan ka faɗamin hakan ne don ka kwantar min da hankali na...." ku ka yaƙi bari ta ƙarasa maganar, Sassauta ruƙon da yai mata ya yi tare da ɗagowa da kanshi fuskar ta 6aci sosai da jiki, kasa tsayar da kan nashi yai, Sai dai ya kwantar da shi saman wuyanta, jikinta yai mugun sanyi, saboda ƙarfin hali irin nashi a haka ya cigaba da yi mata magana cikin raunin murya ta wanda ya gama galabaita.

_Angel, za'azo atafi dani, babu tabbacin zan dawo cikin ku, that doesn't mean that I'll die. Even if I'm not around, ki yi min alƙawarin ba za ki haura tagar nan ba_

cikin shessheƙar kuka tace"damuwar ka kenan Danish Ni yanzu bata wannan nake ba, lafiyarka nake so, kuma ni bazan juri rashin ka atare dani ba, wlh bazan iya zama babu batul sannan babu kai a tare dani ba....." kwantar da kanta tai gefen wuyanshi. Sun ɗauki tsawon lokaci a haka sai shesseƙar ku ke ta ke yi, muryarshi ce ta ƙara katse mata kukan nata daƙyar yake iya furta maganar

"Angel, ki tashi mu shiga ɗaki, ki ruƙe ni mu tafi, inaso inga ƴan uwana kafin atafi dani, nasan yanzu haka suna akan hanyar zuwa ɗauka na" Jin wannan maganar tashi yasa ta ɗaga murya ta ƙwala ma Gabriel kira, Jin sautin muryarta yasa shi yin saurin buɗe ƙopa ya faɗo toilet ɗin

Muryarta asanyaye tace mashi

"Ka taimaka mini mu shiga da shi É—aki"
Chapter 139 · 0% Book details