← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 179

Sashe 151

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Furennin duk sun bushe sun fita hayyacin su, hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, da sauri ta miƙe taje bakin fanfo ta cuko bokiti da ruwa ta dawo ta kwarara shi acikin tukunyar, bayan ta kammala ta juya ta kai bucket ɗin gefen fanfon ta ajiye shi, kamar ance ta waiwayo ta kalli furennin, unexpected idanuwanta suka sauka akan Sabbin tsiron furennin da suka cika tukunyar fulawar, A matuƙar ruɗe ta ke kallonsu, launuka daban daban daga cikin su akwai wani dogon fure wanda tsayin shi ya kere sauran, Lafiyayyan gaske, Ganyayyakinsa sun bubbuɗe launin punch pink ya ciza sosai.

Zazzare idanuwanta waje ta yi, Hannunta dafe da saitin ƙirjinta, don ba ƙaramin faɗuwa gabanta yai ba, walking slowly ta nufi tukunyar fulawar kamar wadda taga wani abun tsoro, duƙawa ta ɗanyi tana ƙare musu kallo, kusan guda takwas ne sabbin furennin, bakwai daga cikin su, ganyayyakin jikinsu sun ɗan bubbushe, akwai wani ɗan ƙarami fari fat irin na jikin aunty Aneelerh, sai dai wannan ganyayyakinsa kamar sun mutu, duk sun tsomare.

Tarasa tunanin me zata yi agame da waÉ—anann sabbin furennin da su ka yi tsiro, ta gaza fahimtar na wanene su? tunawa tai da maganar Danish, a inda yake faÉ—a mata cewa kowani fure yana É—auke da ran mutun, idan har dagaske ne, taya za'ae tasan ran wanene akansu? Ga biyu ma daga cikin furennin sunfi jigata.

Wani irin faɗuwar gaba taji, ba tare da sanin dalilin hakan ba, sai ta dinga ji aranta kamar Danish yana atare da ita cikin toilet ɗin, da sauri ta juya tana ƙarewa makewayin kallo, babu kowa a wuri.

Muryarta na É—an rawa ta furta sunanshi "DANISH"! cike da sa ran zai amsa mata, shiru ba'a amsa mata kiran nata ba, kusan sau uku tana ambaton sunanshi,

"Danish, are you here with me? Please answer my call. I really miss you my Man," she said, her voice on the verge of tears.

Sai faman wurwuga idanuwanta take yi acikin toilet É—in, duk da taga babu kowa amma ita ranta ya bata cewar Yana atare da ita.

"Danish Even if you can't speak, please make some kind of sound to let me know that you're here. I need to know if my suspicions are true, saboda a duk lokacin sa ka zo kusa dani, Inaji a jikina kuma na yarda da hakan,"

kamar mahaukaciya sai sambatu ta ke yi a cikin toilet.

Da ƙarfi ta ƙara furta sunan shi"Danish ka amsa min" karaf akan kunnuwansu Deeja dake zuƙunne cikin sashen, su azeeza har sun fito daga wankan, hibba da parveen sun shiga, ita kaɗaice bata fito ba,

"Kamar muryar Angel nake ji acikin toilet!" yasmin ce tai maganar, Deeja tace"kin riga ni faÉ—i, nima naji maganarta tana ambaton sunan Danish" hanna tace"Anya lafiyarta kuwa? Yakamata muje mu duba,"

Kusan atare suka miƙe, zuwa bakin ƙopar toilet ɗin, knocking deeja tayi mata tare da ɗaga murya tace"Angel! Lafiya mu ka ji kina kiran sunan Danish"?

Jin muryoyin su Yasa ta dakata da yin sambatun, idanuwanta acike tab da ƙwalla, ta nufi ƙopar, bata buɗe ba, magana tayi masu cikin sanyin murya

"Babu komai, banma san na ambaci sunanshi ba, nayi missing din shi ne"

"Shiyasa kike ta ƙwala mashi kira a cikin toilet, gaskiya Angel ba ƙaramin ƙaunar ɗan uwan nan namu ki ke yi ba, muna nan munata jiran ki ki fito, ashe kina nan kina ta sambatu halan ko wankan ba ki yi ba"?

Fuskarta a yamutse ta basu amsa da cewa"ban kai ga yi ba, na tsaya bama furenni ruwa ne, idan na fito zan nuna maku wani abun mamaki, amma yanzu ku koma ku zauna kunsa inata magana acikin toilet bayan babu kyau,' a ƙagare take da su tafi, jin shiru yasa ta fahimci cewa sun tafi, ajiyar zuciya ta ɗan sauke, ba tare da 6ata lokaci ba, ta yi wankan, suna a zaune sai gata ta fito, adai dai time ɗin da su parveen da hibba suma su ka fito daga wankan.

Kallon su ta yi gaba É—aya idanuwansu akanta, jira suke suji me zata faÉ—a musu

"Kunsan me ya faru"? Girgiza mata kai su ka yi alamar a'a tace"dana shiga toilet na ɗebo ruwa na zuba ma tukunyar fulawar nan, naje in ajiye bucket ɗin, Juyowar da zan yi idanuwana su ka yi tozali da sabbin furenni masu kyan gaske, dayawa fa nayi mamakin fitowar......." bata kai ga ƙarasa maganar ba, da gudu su deeja suka shige cikin toilet ɗin, a bakin tukunyar flower ɗin suka tsaitsaya cirko cirko suna kallon furennin, gwanin ban sha'awa, sunyi matuƙar burgesu, sai dai abun da ya ruɗarsu sun kasa gane furennin wanene, sun 6ata lokaci wurin kallonsu, kamar su cinye su, daga bisani ne suka bar wurin, sauran da basu yi wanka ba a cikinsu suka shige toilets.

Lokacin da Angel ta shiga É—akinsu, Jamima na nan yadda suka barta, zaune tana duba madubi, azeeza tana azaune saman shimfiÉ—ar sarah, tana sharce mata gashi, sai santin shi ta ke yi, saboda ita tsayin gashinta bai kai nasu ba,

"Sumar kan ki sak irin na Unaiza ne Æ´ar gidan daddy, banbancin kaÉ—an ne ita nata tsawo ne da shi ba yawa ke kuma naki yana da yawa kamar roba jikin shi"

"Allah sarki har kin tuna min da ita, ko yanzu tana awani hali, oho, " acewar parveen, ta yi maganar ne a yayin da ta ke ƙarasa shiga cikin ɗakin.

Angel tuni ta wuce gefen gadonta, parveen ce ta ɗauko mata comb donta gyara masu gashin kan su, atare da Sarah suka zauna zaman gyara masu sumar kan nasu, ɗaya bayan ɗaya suka yi ma kowan nan su bayan sun fito daga wankan, mutun ɗaya ta rage bata yi wanka ba, har magana azeeza ta yi mata akan tazo ta yi mata wanka tace ita bataso, Su ƙyale ta, haƙorinta ke ciwo, alhalin ƙarya ta ke yi babu wani ciwon haƙori da ta ke yi, wankan ne bata so, Dama angel neman hanyar da zasu shirya da ita take yi, aiko tana zaune saman gadonta, ba zato ba tsammani taji an ɗauketa, ta dinga kuka tana wuntsila ƴan ƙafafuwanta tana faɗin bata so ta sauke ta, hada ƙwala masu deeja kira tana faɗin bazasu zo su cece ta ba, suna ganin genie zata cutar da ita, dariya suka dinga yi mata babu wanda ya motsa.

A cikin toilet ta sauketa, da gudu ta nufi ƙopa zata fuce Angel tai saurin rigata isa ta datse ƙopar da jamlock, kallon kallo su ka shiga yi a tsakaninsu,

Nuna jamimah tai da yatsan hannunta tare da cewa"dama daga ganin ki ba ƙaramar fitinanniya bace, amma duk masifarki baki kai ni ba lokacin da ina ƙarama, kawai daga tsautsayi yasa na 6alle maki haƙori, shine zaki ɗaura min karan tsana, nifa ce Angel ɗin ki,' ta yi maganar tana marairaice mata fuska.

Murguɗa mata baki jamima tayi tare da juya mata ƙeya, Dariya angel ta saki tana kallon bayanta, Kamar kasanya ƙafa ka take ta saboda ƙarantarta, komai nata gwanin burgewa irin na azeeza, tana matuƙar jin tausayin su.

Jin shiru Angel din bata motsa ba yasa ta É—an waigo ta saci kallonta, suna haÉ—a ido ta wurga mata harara.

Dafe ƙirji Angel ta yi da hannu ɗaya

"Genie ɗin kika harara, aiko yanzun nan zan ƙarasa 6a66ake sauran haƙoran na bakin ki ki koma wawulo, " jin wannan maganar yasa Jamimah fashewa da wani sabon kukan.

matsawa Angel ta yi dab da ita, ta ɗan zuƙunna saman ƙafafuwanta, tare da ɗaura hannayenta biyu saman kafaɗar jamima ta juyo da ita, suna facing ɗin juna

Sassauta muryarta tayi Cikin sigar lallashi tace"its okey my little sis, stop crying, bakisan cewa hawayenki, tsada ne dasu ba, " zumbura mata ƙaramin bakinta ta yi, fuskarnan a tur6une, har wani hura hanci ta ke yi, shafa gefen fuskarta Angel ta yi da hannunta,

"Ƴar kyakkyawa da ke kamar Azeeza ta, idan muka fita daga cikin kurkukun nan, zamuje gidan daddyna, akwai suturar sanyawata da daddyna ya siya min tun ina ƴar ƙarama, nasan zasu yi maki, bayan haka ina da kayan wasa, irinsu teddy nasan baki san su ba, hada piano ɗina, duk zan baki su, sannan in sanya ki makaranta, kema ki yi karatu, kamar yarda sauran yara su ke yi, ko baki so" ta6e baki tayi don ita bata fahimci zancenta ba, amma taji an ambaci kayan wasa, Ɗaga mata gira tai"ina so," mirmushi Angel ta saki"amma fa sai mun shirya," hura hanci ta yi, tare da cewa "Ae mun shirya" dariya Angel ta saki, Tare da janyota jikinta, ta rungumeta sosai, kafin ta raba jikin su.

Wanka ta yi mata a cikin toilet É—in, ta kuma wanke mata gashin kanta, bayan ta gama ta goyota saman bayanta,

Suna shiga cikin ɗakin, su parveen suka dinga sowa suna tafa musu hannu, Ganin sun shirya da juna, ba ƙaramin daɗi su ka ji ba, A saman gadonta ta zaunar da ita, ta ɗauko comb ta sharce mata sumar kanta, bayan ta gama, Kalaba ta yi mata guda biyu, sun sauko gefe da gefen kafaɗarta, ta zura mata ribbon ɗinta jikin wutsiyar kalaba ɗaya, ba ƙaramin kyau ta yi ba.

Lokacin da marece ya nutsa kingin abincin su na safe da su ka ajiye, Hannah ta É—auko musu, asaman dining carpet É—insu suka zazzauna, Suna ci saboda gatanci abaki Angel ta dinga ba jamimah, ran azeeza ya 6aci musamman da ta dinga yi mata gwalo, yarinyar ta rainata, kishi ya rufeta, ganin yadda azeeza ke É—aure fuskarta, yasa Angel ta koma tana basu abincin su biyu ita da Jamima, idan ta basu abaki su ka ci, itama sai taci, a haka har suka kammala.

Saman gadajensu suka haye tare da kwantawa, a ƙasa Angel ta shimfiɗa bargonta, su uku suka kwanta asaman shimfiɗar, ita da Jamima da Azeeza, sarakan kishi, duk abunda jamimah tayi sai azeeza tayi, suna a kwance saman shimfiɗar, jamima ta rungume Angel, itama azeeza ta baya ta rungumeta, sai dariya take yi, abin ba ƙaramin nishaɗi yake sanyata ba.
Chapter 151 · 0% Book details