← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 179

Sashe 152

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba su kwanta da niyar yin bacci ba, saboda Angel ta hanasu yin baccin marece, saboda su samu damar tashi tsakar dare su dinga yin addu'o'insu, wani irin bacci ne mai daÉ—i ya É—auke su, hada masu yin min shari irinsu parveen aci ci mala ikun tauna.

Dare yana gab da yi, aka buɗe ƙopar ɗakin su, sautin bai farkar dasu daga bacci ba, A hankali Giant ɗin ke saukowa saman staircases, kafaɗarshi ɗauke da mutun, daga gani macace duba da irin shape ɗin ƙafafuwanta, uban gashin kanta ya sauko ta bayanshi inda kanta yake, ya lullu6e fuskarta, Ƴar rigar dake a jikinta guntuwa ce launin ja, daƙyar ta rufe mazannanta, hakan ya bayyana suffar fararen cinyoyinta, kamar ka ta6a jini ya ɗigo, Yanayin tafiyar Giant ɗin da ya ɗauko ta, ta banbanta da ta sauran Giants da suka saba zuwa kawo musu abinci, akwai natsuwa da kamala atattare da shi, jikinshi gaba ɗaya a rufe yake da baƙaƙen kaya, baka ganin koda yatsan hannun shi ne, bai nufi ko ina ba, sai saman gadon da ke ɗauke da no 3 a saman shi ya kwantar da ita a hankali, tare da janyo duvet ɗin dake a saman mattress ɗin Ya lullu6e mata jikinta dashi, a hankali yake ja da baya batare da ya juya ba, kamar yana kallon su, Har sai daya kai bakin benan tukunna ya juya da sauri ya haura benan ya fuce daga cikin ɗakin.......nima kuma na ajiye alƙalamina🤟

💋PRISONERS💋

A hankali yake ja da baya batare da ya juya ba, kamar yana kallon su, Har sai da ya kai bakin benan tukunna ya juya da sauri ya haura benan ya fuce daga cikin É—akin.

Ko sautin rufe ƙopar bai farkar da su ba, kamar matattu, yaushe rabon da su yi irin wannan baccin su kansu sun manta, tsawon lokaci babu wanda ya farka, har dare ya yi, Hasken ceilling ya ɗauke, Na floor lamps ya kunna kan shi.

Azeeza ce ta fara yin motsi zata farka, hannunta dafe da mararta, wani irin azababben fitsari ne ya matse ta, da kasala a jikinta ta yunƙura ta miƙe zaune saman shimfiɗarsu, idanuwanta biji biji bata iya ganin komai.

muryarta cikin shessheƙar kuka ta soma magana tana laluban Jikin Angel.

"Angel ki tashi ki raka ni toilet, fitsari ni ke ji ya matse ni sosai....pls Angel ki tashi kada in yi shi a wando,"

Ko motsi Angel ba ta yi ba, balle har ta sa ran za ta farka.

Jamimah ce ta jiyo muryar Azeeza da ke ta yin kuka, farkawarta kenan, ta zame jikinta daga na Angel, ta miƙe zaune tana mutsustsuka idanuwanta da yatsun hannayenta, fuskarta a ɗaure babu annuri.

Ƙura ido ta yi a kan fuskar azeeza Dake ta kerma tana kuka, Muryarta da alamun bacci bai isheta ta ambaci sunanta"Azeeza...' tana jin muryar jamimah tai saurin katse kukan nata tare da cewa"Jamimah fitsari nake ji, dan Allah ki taimaka ki raka ni toilet, ya matse ni" baki asake Jamimah ke kallonta,

"Toilet dinne saina raka ki? Ke baki iya zuwa? Ko tsoro kike ji ne"? ta yi tambayar tana binta da kallon rainin wayau.

Jamimah ba ta san cewa azeeza na fama da lalurar rashin gani ba, Muryarta na rawa tace"Jamimah bana gani, idan dare yayi, makauniyace ni...."

Ta6e baki jamima tayi mata tare da cewa"ƙarya ne, Ni zaki raina ma wayau? Idan da gaske baki gani to ya akai da rana kike gani? Nafa san me nake yi,"

Takaici ne ya ishi azeeza duk yadda taso ta fahimtar da jamima taƙi yarda cewa bata gani, hakan yasa ta miƙe a makance ta soma tafiya tana laluban hanya, jamimah sai kallon bayanta ta ke yi, abun ya ɗaure mata kai ganin yadda ta ke ta sanya hannu tana laluban hanya, cikin rashin sa'a Azeeza ta nufi bango gadan gadan duk a tunaninta ta ƙaraso bakin ƙopar shiga sashen toilet ɗin ne, ta daddage zata buga kanta, Jamimah ta kware murya tare da cewa"Bango ne fa ba ƙopa fa",

Ta yi maganar tare da miƙewa da gudu ta nufi in da Azeeza ta ke a tsaye jiki na kerma don ba ƙaramin firgita ta yi ba, da taji muryar jamimah tana faɗa mata cewa bango ne ba ƙopa ba.

ba ta yi tsammanin zata taimaka mata ba, sai jin hannunta ta yi a cikin nata, ta ruƙo ta tare da jan ta zuwa cikin sashen, kafin su ƙarasa toilet ɗin tuni ta fara sakin fitsarin a wando, Suna shiga ciki ta zame wandon jikinta, da sauri jamimah ta kawar da kanta gefe don kada taga tsiraicinta, bayan ta gama yin fitsarin, ta yi tsarki kafin ta maida wandon jikinta, ta kira sunan jamimah, ta taimaka mata a daddafe su ka nufi ƙopar fita.

"Amma dai idon ki a rufe ya ke lokacin da nake cikin yin fitsarin ko? Azeeza ce tai maganar, murmushi jamimah ta saki tare da cewa"naga komai, daga yanzu sai ki daina raina min wayau kina kira na Æ´ar yarinya, nima ae kina min wanka, kuma kina ganin nawa"

Shiru Azeeza ta yi ba tare da ta tanka mata ba.
A lokacin sun fito daga sashen toilet din
"Amma wai dagaske baki gani da daddare? To ya akai kike gani da rana? yamutsa fuska azeeza tai"ko nace maki eh, ba yarda za ki yi dani ba, ki bari idan Angel ta farka daga bacci ki tambaye ki ji, " ta amsa mata da toh.

A lokacin sun shiga cikin ɗakin nasu, har zasu nufi shimfiɗar da Angel ta yi musu, ba zato ba tsammani idanuwan Jamimah suka sauka akan Gado mai ɗauke da no 3, dakatawa ta yi da yin tafiyar, ta ƙurawa gadon ido ta hango mutun naɗe cikin bargo, tunani ta shiga yi wanene saman gadon? Saboda a iya saninta tunda aka kwashe mazan cikin su, babu mai kwana saman tsaffin gadajen su sai Angel! Ita kaɗaice ta ke kwana saman gadon Danish, da sauri jamimah ta juya ta kalli ɗayan 6angaren don taga ko wani daga cikin su Hibba ne Ya dawo saman gadon ya kwanta, sai dai ko da tabi gadajen su da kallo kowannan su yana nan,'

A firgice ta wurga eye balls ɗin ta kan shimfidar Angel don ta tabbatar idan Angel ɗin tana nan, lamarin ya yi matuƙar razana ta ganin Angel baje saman bargo sai sharar baccin ta ke yi.

Azeeza da ta gaji da tsayuwa jin taƙi motsawa su tafi, muryarta a kasalance tace"Jamimah! Ke fa nake jira naji kin dakata da tafiya, Me kike yi ne, dan Allah ki kaina saman shimfiɗarmu in kwanta,"

Hankalin Jamimah ba ƙaramin tashi yai ba, muryarta atsorace ta furta"Azeeza Genie a ɗakin mu, saman gado no 3" ta yi maganar tana zazzare idanuwanta.

duk da Azeeza bata iya gani hakan bai hanata zare idanuwanta ba, zuciyarta ta yi wani irin bugu tamkar zata faso kirjinta, Azeeza sarkin tsoro,

"Innallahi wa'inna ilaihirraji'un! Jamimah ki faɗa min gaskiya, ko dai ƙarya kike yi min, wani irin genie kuma a cikin ɗakin mu, ki dai duba da kyau,"

jamimah tace" kin san Allah dagaske na ke maki, kamar mutun ne saman gadon, kuma na dudduba su hibba mun cika mu goma sha É—aya, na saman gadon shine cikon na sha biyu."

Girgiza kai azeeza tai jiki nata 6ari tace"jamimah bargo ne da pillow ba mutun ba, ni dai mu je mu kwanta, " ta yi maganar tana ƙoƙarin jan hannunta, duk tabi ta tsorata kanta.

"Ni dai sai naje na duba gadon inga wanene, ke ki ke je ki kwanta"

Ran Azeeza ba ƙaramin 6aci yai ba, zuƙunnawa ta yi ƙasa tana rarrafawa don ta gano inda shimfiɗar Angel ta ke.

A hankali jamimah ke tafiya tana tunkarar gadon, ga tsoro tana ji amma ta nace sai taga wanene, tana ƙarasawa bakin gadon, ta ɗan dakata, tare da miƙa hannunta yatsunta nata yin kerma ta ruƙo bargon, wani irin tsorone ya ziyarci zuciyarta, a hankali ta yaye bargo, a gigice ta runtse idanuwanta ta daddage ta fasa wata irin firgitacciyar ƙara wadda ta yi silar farkawar masu yin bacci.

A matuƙar ruɗe Azeeza ta faɗa saman jikin Angel da ke kwance, Allah yaso ta isa ga shimfiɗar da kuwa zuciyarta ta buga silar ƙarar da jamimah ta fasa.

Bakomai ne ya tsoratar da ita ba face Sumar kan matashiyar dake akwance saman gadon, dama can a tsoroce take shiyasa bata iya tantance gashine ko ba gashi ba, ita dai taga abu kamar hauka, Mai uban yawan gaske ya nanannaɗe, idanuwanta ne suka dinga nuna nata kamar gashin yana motsi, aiko ta rushe da kuka da gudun gaske tabar bakin gadon har tana tuntu6e garin gudu, hankalin su Deeja ba ƙaramin tashi yai ba, ganin yadda jamimah ta furgice tana kuka, bata nufi ko'ina ba, sai saman jikin Angel ta faɗa mata, suka ƙanƙameta ita da azeeza, sun tada mata hankali, ko motsi sun hana tayi tun da tafarka, duk sunbi sun furgice.

Babu wanda ya lura da abunda ya tsoratar dasu.

"Me ke faruwa ne? Wanene ke yi mana kwaratsi a cikin É—aki"? Parveen ce ta yi maganar fuskarta a yamutse, deeja tace"Jamimah ce, bansan me suke ma ihu ba" ta yi maganar tare da saukowa daga saman gadonta, tare da nufar shimfiÉ—ar Angel.

Su yasmin duk suna zazzaune saman gadonsu basu motsa ba, idanuwansu akansu Jamimah.

Zuƙunnawa Deeja ta yi agabansu tare da ambaton sunayensu

"Jamimah! Azeeza! Lafiya ku ke yin ku ka? Wani abu ya faru ne"? Bakin Angel ya mutun, takasa magana, saboda faÉ—uwar da gabanta ke yi.

Cikin shessheƙar kuka Jamima tace"Ge..nie a ɗakin mu, ga ta can kwance saman gado number 3"

Jin ta ambaci bed no 3 yasa kowan nan su yin saurin kai idanuwan shi kan gadon, ganin kamar mutun ne yasa su ka soma kallon junan su, a ƙoƙarin su na su gano wanene acikin su yaje ya kwanta gadon, Ɗaya bayan ɗaya suka dinga saukowa daga saman gadajen su, tun daga kan Eve yasmin hibba hannah rubina, Sarah, kaf ɗinsu, A tsananin tsoroce su ke ƙarewa gadon kallo sai faman zazzare idanuwansu su ke yi.
Chapter 152 · 0% Book details