Sashe 112
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin shessheƙar kuka angel take lallashin Furen, Batasan cewa Danish Yana tsaye bakin ƙopar toilet ɗin ya la6e yana kallonta, tsananin tausayinta ne ya kama shi, sai dai baijin zai iya zuwa ya lallashe ta, saboda alƙawarin daya ɗaukar mata, abunda baisani ba ita kanta, A halin yanzu a matuƙar ƙagare take da son su shirya da juna don ba ƙaramin azabtuwa take yi ba,
Shiru ta ɗanyi tana ƙarewa furen kallon, ganin Ya daina tsastsafo da ruwa ajikinshi, wani iko na Allah sai taga furen ya kwanta cikin ƙasar tukunyar, alamar mamallakin shi bacci yake yi, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, aranta ta raya cewa Batool taji lallashin da take yi mata shiyasa tayi shiru ta kwanta tana bacci, A hankali ta mayar da idanuwanta kan furen daddynta, tafi yarda dana batool akan nashi, saboda shi bata da tabbacin yana raye koya mutu, Jikin furen yayi kore shar dashi, kuma iccen yaɗan miƙe ba kamar lokacin farko da ya fito a lanƙwashe ba, Ziraran yatsun hannunta ta ɗaura asaman furen daddynta tare da shafa ganyen shi, a fili ta furta I wish kana araye daddyna, har yanzun kana nan acikin zuciyata, ba abinda ya sauya daga ƙaunar da nake yi maka, I luv u so much, zan cigaba dayi maka addu'a kaida batool ɗina da kuma ƴan uwana prisoners, Alƙawarine na ɗaukarwa kaina,"
murmushi tasaki tana faɗin"Har na tuna lokacin da na ƙala maka sharrin cewa kai ba mahaifina bane, ɗan yankar kaine, aranar kasha bugu wurin ƴan ƙato da gora, kuma duk da abunda nayi maka hakan baisa ka guje ni ba, saima ka ƙara ƙaunata, ashe babu rabon xamu ƙare rayuwarmu atare.....haka na dinga burin in zama house wife, ashe da rabon in zama prison wife, Gidan hutun da nake burin inyi aure, har ina faɗa ma aunty aneelerh zan auri hamshaƙin mai kuɗi saboda masu aiki su dinga yi mini hidima ina daga kwance, sai gashi na ƙare agidan kurkukun ƙaddara, wayyo Allah na, babu daddyna babu aunty aneelerh da uncle uzair, babu mommy adamana da uncle abdallah, babu makaranta, babu house wife, duk waɗannan burinkan sun tashi a tutar babu....."
daƙyar ta ƙarasa yin maganar saboda kukan da yafi karfinta, ta kifa kanta saman gwiwowinta taci gaba da kuka, tana fadin nayi danasani daddyna ka yafe mini, wlh ina matuƙar ƙaunarka, dama saida ka fada mini cewa bani da tamkarka a duniyar nan yanzu na shida hakan.....'
Duk wannan suratan da take yi akan kunnan Danish, Ya ɗan jingina kanshi jikin ƙopar toilet ɗin, Ya natsu yana sauraronta, Hakanan taji aranta kamar akwai mutun abayan ta, a hankali ta ɗan dago da kanta, tana ƙoƙarin juyawa ta kalli bayanta danish yai saurin fita daga Cikin toilet din ya tsaya daga waje, Yana faman sauke ajiyar zuciya,
Baiyi tsammanin ta biyo shi ba, Sai dai yaji ta ambaci sunan shi,
"Danish"! Kasa juyawa baya yae don ya kalleta, duk yabi ya kama kanshi,
"Shine kana ji inata kuka ko kazo ka lallashe ni" Yayi mamakin jin abunda ta ce, cije lips ɗinsa yae kafin yace"Saboda me zanzo in lallashe ki? Ko kin manta alƙawarin dana ɗaukar miki? Batare daya juyo ya kalleta ba, yayi maganar,
"Meyasa kake bibiyata? Nasan saboda ni kazo bakin ƙopar toilet din nan ka tsaya, Allah kaɗai yasan tun lokacin da kake kallona, kaga kuwa Alƙawarin Ya jima da karyewa,"
girgiza kanshi ya ɗan yi tare da cewa"bana sa6a alƙawari, idan kin manta bari in tuna maki, kin ce kada na kurkura na ƙara hada ido dake kinaso in nisanta kaina agare ki, Tabbas nazo bakin ƙopar toilet din kuma na kalle ki amma ban bari mun hada ido ba. Hope kin fahimta yanzu ban karya miki alƙawarinki ba, Tun da bamu haɗa ido da juna ba kuma banzo kusa dake ba,"
Harara ta shiga jefa ma bayan shi, kamar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa, wani irin kewarshi take ji kamar tae hauka, tayi danasanin sanya shi ya ɗaukar mata alƙawarin nan, ta manta cewa Prisoners basu Iya karya alƙawari ba, ta inda suka banbanta da mutanan dake rayuwa awaje kenan, majority dinsu basa ƙarya kuma basu Iya gulma ba, musamman DANISH!
Takaici ne ya isheta, Can dai tace"Idan nace na fasa alƙawarin fa"? Danish ya bata amsa da cewa"Idan kin fasa Ni bansa fa, bazai ta6a yiyuwa ba" yana faɗin hakan Ya wuce cikin dakinsu yabarta a tsaye tana faman cizon le6enta,
Daga bisani ta gyaÉ—a kai tare da wuce wa ta nufi cikin dakin, a kwance ta same shi saman gadon shi ya rungume pillow, ta6e baki tayi kafi ta nufi nata gadon ta haye ta zauna daga tsakiyarshi ta É—aga hannayenta sama tana jera addu'o'i, Cikin harshen larabci,
ta ɗauki tsawon lokaci daga bisani ta shafa hannayenta saman fuskarta, kafin ta gyara kwanciyarta, Sai da ta lumshe idanuwanta, Zuciyarta ta soma tariyo mata maganganun da tsohuwa ta faɗa musu kafin tafiyarta, tabbas akwai wasu kalamai da tayi aciki waɗanda suka ɗaure mata kanta, ta kasa fahimtar inda suka dosa, Duk irin kaifin basirarta, ta gaza gano menene tsohuwa take nufi, da tace musu su dauka cewa su makullaine da zasu Iya buɗewa kansu ƙopar farin ciki, tayaya kenan? daƙyar ta samu bacci ya ɗauketa a daren ranar,!
Ko a washe garin ranar babu wanda ya sanya sabon uniform ɗinshi acikinsu, damuwar rashin tsohuwa ta hanasu sukuni, ga fargabar zuwan tsohuwa Zafreen, da kuma new prisoners, daga Sunji motsin ƙopa a firgice suke kallon ƙopar, don suga wanane, a ƙarshe sai su ga bakowa, Kunnuwansu ne kawai suke Jiyo musu hakan, sakamakon sanya rai da suka yi, wasa wasa yau har tsawon 2 weeks da tafiyar tsohuwa babu wani sabon Labari, ta ko'ina shiru kake ji, su kaɗai suke rayuwarsu, hankalinsu har ya ɗan kwanta don a tunaninsu, An ƙyalesu ne su yi rayuwarsu su kaɗai, Bakomai yafi ɗaga musu hankali ba, face rashin batool don a lissafinsu yau Wata ɗaya kenan babu Ƴar uwarsu acikinsu, Ba'a dawo musu da ita, har sun fara fidda rai da sake ganinta 🥺
*PRISONERS💔*
Yau tun da sassafe Angel da hanna suka taimaka ma ƴan uwansu mata wurin gyara sumar kansu, gwanin ban sha'awa kowa saida suka wanke mashi sumar kanshi, suka gyara musu ita, su kansu ba ƙaramin daɗi suka ji ba, ganin yadda sumar kansu tayi kyau ga laushi da kyan gani a ido, ga wani irin ƙamshi da gashin nasu yake fitarwa mai daɗin shaƙa, Bayan Sun kammala gyara ma su azeeza, Hanna da angel suke koma toilet, saboda su wanke nasu gashin kan, sai da angel ta kammala wanke ma hanna, ya rage saura ita, duk yadda hanna taso ta wanke mata gashin kanta, hakan ya faskara, saboda uban yawan dake gare shi, Gashi ya nannaɗe yadda kasan taliyar indomi, Tun tana nish tana ƙoƙarin tattaro gashin kan Angel, kamar hannunta zasu 6alle, a ƙarshe data ga abun yafi ƙarfinta, sai ta fita tabar angel acikin toilet ɗin, sai gasu sun shigo kusan su Shida hada su javed da naufal, wai sun zo wanke mata kai, ashe bayan da hannah ta fita daga cikin toilet ɗin, ɗakinsu ta shiga taje ta kira su, donsu taimaka mata, mamaki Ya kama angel, ganin sun shigo suna nannaɗe hannuwan rigunansu, Kusan dambe akayi acikin toilet din, tana faɗin ita bata so su barshi ta haƙura da wanke gashin, Su kuma suka ce bata isa ba, Yadda aka wanke ma kowa gashi, Itama sai sun wanke mata nata, ko tana ko bata so, A lokacin Danish Yana la6e bakin ƙopar toilet din yana kallonsu, don ba ƙaramin nishaɗi ya samu ba, ganin yadda suke ta yawo acikin toilet din sai zagaye shi suke yi, Ita tana gudu su kuma suna bin bayanta hannayensu ruƙe da shower gel da comb, da sauran abubuwan da zasu yi amfani dasu wurin wanke mata gashin su gyara mata shi, Sai da kowannansu Ya gama galabaita, tukunna suka samu ta basu haɗin kai, Su shida suka wanke mata gashin kanta, tadaici azaba, har wani jiri take gani acikin idanuwanta, saboda yadda suke ja mata gashin, Bayan sun kammala wanke mata shi, waɗanda ke ruƙe da combs, suka soma sharce mata shi, daga bisani suka bi da mayukan gyaran gashi suka shasshafa mata, ' Lokacin da suka kammala, Sunyi mamaki Ganin irin yadda gashin kanta ke ta ɗaukar ido, yayi dark brown dashi ya warware tamkar hijabi yayi mata abayanta, ta yi farin Ciki sosai da suka taimaka mata wurin gyara mata gashin kanta, ta ƙara jin ƙaunarsu acikin zuciyarta,
Kafin marece ya doso, ɗaya bayan ɗaya suka soma shiga toilet suna Yin wanka, saboda yau sun shirya canza Uniform dinsu, sai ɗauki suke Yi zasu sanya sabbin kaya, Bayan sun kammala Yin wankan, Ya rage saura Danish Yaƙi zuwa yai wanka, Hatta mazan sun wanke sumar kansu, amma shi duk ya takure kanshi, Ya hana kanshi sukuni acikinsu, duk da ayanzu babu wanda yake nuna mishi wariya, tun ranar da tsohuwa tayi musu faɗa akan su daina ware shi acikinsu, tun daga ranar suka daina gaba da shi, Shi ɗin ne dai kamar baison suna kusanto shi, Kuma bakowa yaja hakan ba face Angel, ita ɗin dai ce da baya son ya karya mata alƙawari.
Ganin baida niyar tsohuwa ya wanke sumar kanshi Yasa haris zuwa har saman gadonshi, Ya damƙo hannun shi ya janyoshi, Har saida ya sauko daga saman gadonshi suka nufi toilet, Yana fadin Allah idan bakai wanka ba, Ni zanyi maka da kaina, kowa yana nishaɗi sai kai kaɗai duk kabi ka takura rayuwarka sai kace wani bare, Idanma don abunda ya faru ne ae mun yafe maka komai ya wuce mana, tun da ya riga daya faru," Kamar wani ubanshi haka haris ya dage yana tayi mishi faɗa, har suka shiga cikin toilet din, bawan Allah yai shiru bai tanka mishi ba, haris bai fito daga cikin toilet din ba sai da ya taimaka mashi ya wanke sumar kanshi, Kafin Ya fito yabarshi aciki, don yayi wankan,