Sashe 102
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin harshen turanci yaci gaba da cewa "Angel, kinga abunda kika ja ma kanki ko? Yanzu da ace banzo ba ya zaki yi? Kalli yadda kika raunata kanki, ta ko'ina babu lafiya a jikinki, saboda kafiya irin taki na gargaɗe ki amma kika ƙi jin magana ta, saboda baki ɗauke ni abakin komai ba, kin ɗauka cewa shiga cikin prison abune mai sauƙi, yanzu gashi nan kin ja ma kanki yin jinya, nasan ko gobe aka nuna maki hanya fita ba zaki ƙara gigin binta ba" shi kaɗai yake ta sambatun shi, baiwar Allah, sai nishi take yi, ita kaɗai tasan irin raɗaɗin da take ji ajikinta,
Haɗe fuskokinsu yai wuri ɗaya, ya mayar da hands ɗinshi Tsakanin sumar kanta da wuyanta, harshen shi ya ɗaura saman fuskarta, a hankali ya soma lashe jinin dake zuba, har sai da yaga babu sauran jinin dake ɗiga tukunna ya zame tongue ɗinshi, idanuwanta sai rurrufewa suke Yi, biji biji take ganin shi, tun tana yin numfashi daƙyar daƙyar har ta kai ga sumewa saman jikinshi, da dabara ya samu ya zame wandon unform ɗinta daga saman laps ɗin shi, Ya damƙo dogayen ƙafafuwanta, Ya shiga kiciniyar sanya mata shi, daƙyar ya zura mata wandon yaja shi har saman waist ɗinta, bayan ya kammala, Ya ɗaɗɗago da ita, ya yarfata saman kafaɗarshi Ya miƙe Ya juya Ya nufi hanyar komawa ɗakin su, sai dai da alama danish bata taga ya koma Cikin ɗakinsu ba, 6acewa yai ya faɗo Cikin toilet ɗinsu ɗauke da ita a hannunshi, a lokacin Har ya gyara ɗaukar da ya yi mata, ya sauko ta daga saman kafaɗar shi, Ya yi mata irin ɗaukar da ake yi ma jariri, Yana kan hanyar fitowa daga Cikin toilet ɗin, Yaji motsin mutun Yana tunkaro ɗakin Da wani irin sauri Ya faɗo bakin ƙopar sashensu, Kunji yadda akai danish Ya ɗauko angel,
*PRISONERS💔*
hankalinsu yaƙi kwanciya, Ganin irin raunatar da angel tayi, masu karyayyiyar zuciya acikinsu tuni sun fashe da kuka, Hibba tace"wannan wata irin rayuwace, daga wannan sai wannan, yau dai bata yi mana daɗi ba, muna fama da azeeza data sume ga kuma Angel itama asume jikinta duk ciwuka, wai dan Allah meya faru da ita ne? Tana rufe baki hanna tace"pls danish ka faɗa mana a ina kaga angel, can fa nabarta a zaune, Yanzu kuma sai gashi ka shigo da ita daga Cikin toilet, yaushe ta shiga ciki? A matuƙar ruɗe tayi mashi tambayar, haris yace"Allah yasa ba wani mugun abun ka yi mata ba, Wama ya sani ko bugunta ka yi don ka huce haushin abunda muka yi maka," da sauri danish ya ɗago da idanuwanshi ya ɗaurasu kan fuskar haris da ya yi maganar, wani irin raɗaɗi yake ji acikin zuciyar shi, ƴan uwanshi suna yi mishi kallon mugu mara tausayi mara imani, duk sai yaji ya tsani kanshi, sam ya kasa furta komai, duk da ya ɗago ne da niyar ya mayar mishi da martanin maganar shi amma sai ya kasa,
"Yakamata muyi ƙoƙarin wurin ceto rayuwan ƴan uwanmu bawai mu tsaya muna surutu mara amfani ba" Acewar Mubeen,
Cikin fushi haris yace"Ka faÉ—a mana me ka yi ma angel da har ta suma? Hawaye ne suka cika idanuwanshi, Cikin sanyin murya yace"ka bari tafarka sai ka tambaye ta me nayi mata, idan har ni na zalunce ta, kuna da right da xaku iya rama mata, amma bai kamata ace kuna tuhumata ba"
Naufal yace"zamu zuba ido mu gani har zuwa lokacin da zata farka wlh idan har ta fada mana cewa kaine silar halin da tashi ga, to ka kwana da sanin cewa ba zamu ƙyale ka ba," Yana magana yana galla mishi harara, Girgiza kai danish ya ɗanyi batare daya tanka ma naufal ba, ya lura gaba ɗaya shi suke zargi akan halin da angel ta shiga, basu son cewa itace ta ja ma kanta ba,
"Ina azeeza take"? Yayi tambayar yana bin fuskokinsu da kallo, kusan atare suka haÉ—a baki wurin cewa"Ina ruwanka da ita? Ka damu dasu ne"? Girgixa kai ya É—anyi tare da cewa'taya bazan damu dasu ba, Æ´an uwanane su, baku isa ku hanani tambayarsu ba"
Javed yace"Har kana da bakin cewa su ɗin ƴan uwanka ne? Mugu dakai saboda rashin imani ka damƙi hannun batool ka miƙa ma wani ƙato ya ɗauke ta don aje acutar da ita, a haka har kake kiransu da ƴan uwan ka"? Tuni idanuwanshi sun cicciko tab da kwalla, tunawa da rashin imanin da ɗan uwansu danish yayi musu, jikin shi duk yayi sanyi, har lokacin yana zaune gefen gadon angel, daƙyar yake kallonsu saboda nauyin haɗa ido da su ya ke ji.
"Ka faÉ—a mana wanene kai!" har saida gabanshi ya faÉ—i jin tambayar da haris ya jefa mishi, muryarshi na kerma yace"wha..what u mean? Haris ni kake tambaya wanene Ni"? jinjina kai haris yai tare da cewa"Eh, so nake insan wanene kai! Danish bani kaÉ—ai ba gaba É—ayan mu nan zargin ka muke Yi, Kawai ka faÉ—a mana gaskiyar wanene kai, meyasa kake atare damu" a ruÉ—e danish yake kallonsu,
Naufal yace"bana tunanin danish cikakken mutun ne, Saboda babu zuciya a ƙarjinshi, Haba rashin imanin yayi yawa, ka duba kaga yau tsawon shekara nawa, danish yana atare da batool, tun kafin mu mallaki hankalin mu yake atare da ita, baida wani makusancin daya wuce ita, in ka cire haris, amma yau rana ɗaya ka gaza ceton rayuwarta, sai ma ka taimaka wurin miƙa ta ga azzaluman da zasu azabtar da rayuwarta......" wani irin kukane yazo ma naufal ba arxiƙi ya katse maganar, hawaye suka soma bin fuskarshi,
Haris ya ɗaura da cewa"ba zamu ta6a mantawa da wannan ranar ba, danish ka cika butulu, mara imani da tausayi, Yarinyar nan babu irin ciwon kan da batayi ba akanmu, tana matuƙar son ƴan uwanta, idan wani baya lafiya acikinmu, batool ko bacci bata iya yi har sai yaji sauƙi, ka cuce mu danish, kuma ka karya mata zuciya, nasan batul bazata ƙara yarda dakai ba, saboda kaine silar duk wani hali da zata tsinci kanta,"
Tun da suka soma yi mishi magana, yayi shiru yana binsu da kallo bai ko tanka musu ba, duk yadda zaiyi musu bayani yasan ba lallaine su fahimce shi ba, amma yafi su jin raɗaɗin rabuwa da batool, shi kaɗai yasan irin ƙuncin daya shiga lokacin daya janyota ya miƙa ma giant,
Sun tasa shi gaba suna jiran jin amsar dai basu, bai bi ta kansu na, ya miƙa ya tunkari inda su deeja suke zuƙunne, yana yunƙurin zuƙunnawa don ya duba lafiyar azeeza, naufal ya damƙi hannun shi tare da cewa"kada ka kuskura ka ta6a ta, babu ruwanka da rayuwarmu" murmushin takaici danish ya sakar mashi, batare daya mayar da martanin maganar shi ba, ya fusge hannun shi daga ruƙon da yae mishi, Ya zuƙunna agabansu deeja, wani irin haushin shi take ji kamar ta shaƙe wuyan shi, Tun da ya zuƙunna take ta aika mishi da harara kamar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa, wanda ake yin hararar domin shi baima san tana Yi ba, hankalin shi gaba ɗaya yana akan azeeza, dake rungume jikin deeja,
Robar ruwan da haris ya ajiye a ƙasa, Danish Ya miƙa hannu ya ɗauko ta, A baki ya kur6i ruwan, duk suna a tsaye suna kallonshi, A saman fuskar azeeza ya watsa ruwan, Wani iko na Allah nan ta ke azeeza taja dogon numfashi, Jikinta ya soma kakarwa, Cike da mamaki suka dinga kallon danish da kuma azeeza, ganin yadda yai nasarar watsa mata ruwa ta farfaɗo,
Hannayenshi biyu ya sanya ya tallabo fuskar azeeza yana kallonta, muryarta adisashe take faÉ—in dan Alah kada ku bari su É—auke ni, wlh mutuwa zanyi, ni bazan bi su ba, "
"Azeeza"! Muryar danish ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, ta ɗan buɗe idanuwanta tana kallon shi biji biji saboda matsalar idanuwanta, da sauri su haris dasu hanna duk suka zuƙunno agabanta, suna ambaton sunanta, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, badan tana gane su ba, yayin da idanuwanta ke lumshewa, muryarta na ɗan rawa tace"Dagaske ba'a tafi dani ba, ina atare da ƴan uwana"? Atare suka haɗa baki wurin bata amsa da cewa"Eh, muna atare dake" har xatayi murmushi sai kuma ta fasa, tunawa da batool, nan da nan walwalar fuskarta ta ɗauke. A tsorace tace dasu"Ina Batool take" nan fa kowa yai shiru, hakan yasa ta fahimci cewa An ɗauke batool, shessheƙar kuka ta fara yi musu, Danish yace"its okey azeeza, ba lafiya gare ki ba, kina buƙatar ki huta" girgixa mashi kai tayi hawaye ta ko'ina akan fuskarta tace"Yanzu shikenan an ɗauke mana batool dinmu, an tafi da ita, baiwar Allah, nayi danasanin cizon ta da nayi, dame xata ji"? Fashewa tayi da kuka, Cikin sanyin murya haris yace"Pls azeeza stop shedding ur tears, Ya riga daya faru babu wanda ya isa ya dawo dashi baya, abunda nake so daku shine muyi haƙuri mu rungumi ƙaddararmu, idan da rabon za'a dawo mana da batool, Ko min daran daɗewa, ƴar uwarmu zata dawo cikinmu ne"
Sosai haris ya shiga kwantar musu da hankalinsu, sai gashi kowa daga Cikinsu yaja baki yae shiru, danish yace"Yakamata kuje ku kwanta....." daƙyar ya ƙarasa maganar, ganin irin kallon da suke watsa mishi, Haris yace"Itafa angel? Kaƙi faɗa mana meya faru da ita, a ina ka ɗauko ta? Me kuma ya haɗa ka da ita da har kayi mata wancan jahilin bugun,"
"Haris, bani da amsar da zan baka, amma idan tafarka, zaka Iya tambayarta, " yana kai karshen maganar, Ya miƙe tare da ɗaukar robar ruwan Ya nufi gadon angel, Bai kai ga ƙarasawa ba, Ya ɗan dakata da yin tafiyar, Batare daya juyo ya kalle su ba, da wata irin kakkausar murya yace"ku wuce ku je ku kwanta," Tun da ya ambaci hakan suka fara Jin wani irin matsiyacin bacci yana niyar dauƙarsu, A daddafe kowannansu Ya miƙe Deeja ta ruko hannun azeeza a saman gadonta suka kwanta su biyu ta rungumeta ajikinta, Cikin ƙanƙanin lokaci ɗakin yai tsit Baka jin hayaniyar komai bacci duk yae awon gaba dasu,
Ajiyar zuciya yaÉ—an sauke, Aranshi yace"nasan da hakanan nace su kwanta bazasu bi umarni na ba"