← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 179

Sashe 123

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya sunan mahaifinki? Kuma wanene shi"? Muryarta A disashe tace"Ae ni bansan real name nashi ba, na dai san ana kiran shi Jan wuya..." bata ƙarasa maganar ba angel ta katse ta da cewa"Ba ki ta6a zuwa school bane? Da wani suna kike amfani"? Ta bata amsa da cewa"ni tunda na taso ban ta6a zuwa school ba, daddyna bayaso ina shan wahala, A gida ake koya min karatu, yanzu ma don na kwallafa raine akan inason zuwa south korea karatu shine yace zai sani...."

Jinjina kai angel tae kafin tace"Amma awace ƙasa ku ke zaune duk da naji kina magana da yare biyu, hausa da turanci so na kasa gane wani jinsi kike"

Wannan karan tamkar zata fashe mata da kuka ta yi maganar don ta gaji da tsayuwa,

"My dad is from Nigeria and my mom is from England. I've never been to Nigeria, and I don't know my dad's hometown or his job, Ni da Mommyna ne kawai muke rayuwa a england sai Æ´an Aikin gidan mu, amma yana yawan zuwa kawo min ziyara daga Nigeria"

Hankalin angel ya ƙara tashi, daƙyar tace mata yanzu kiyi haƙuri kiyi wankan idan kin kammala zanyi maki bayanin komai" Girgiza kai tayi"ae bazan iya wanka awannan toilet din ba, saboda ba irin na gidanmu bane, ni nasaba acikin bathtub nake yi, kuma masu aikin gidan mu ne suke taimaka min wurin yin wankan"

Kallon ta kawai angel ke yi, Iya cutuwa dai an Cuci yarinyar nan, tama rasa taya zata fahimtar da ita cewa Nan kurkuku ne, ba high school ta ƙasar korea ba? Zaiyi wuya ta fahimce ta, babbar matsalar irinsu Suna da ƙarancin imani, sannan basu da tawakkali, Tana iya ta faɗa mata azo asamu matsala, Ya za tayi da ita?

Yayin da su Angel suke a sashen toilet dinsu ita da ƴar gidan daddy, Su kuma can ɗaki suna fama da wannan mahaukacin Yaron, abunda ya faru Suna ƙoƙarin zuwa suci abinci, Eve tace dasu,

"Wai nikam Ina Yaron nan yake ne"? Kafin wani ya buɗe baki ya bata amsa suka Ji ƙarar karyewar wani abu acikin kunnuwansu, Agigice suka kai idanuwansu wurin da suka Jiyo sautin ƙarar, ransu yae mutuƙar 6aci ganin Irin uwar 6arnar da Yaron yayi musu, Gaba ɗaya Ya kado da cake ɗinsu ƙasa, Table ɗin Ya 6alle, Cake ɗin ya ƙundumo kasa Ya tarwatse, hakan bai ishe shi ba, sai da ya hau saman Cake ɗin Ya dinga duma hannuwanshi aciki Yana Kwaso shi Yana turawa abakinsa, duk ya 6ata uniform ɗin jikin shi da cake ɗin, A ƙarshe ma sai ya hau saman Cake ɗin ya dinga burgima yana dariya, a fusace parveen ta nufi inda yake, Haris da Danish suna ta ƙoƙarin dakatar da ita akan kada ta buge shi, amma ina ko waiwayon su bata yi ba, wata irin damƙa takai ma wuyan rigar shi, ta ɗago dashi ta daddage ta buga kanshi a ƙasa, azabar zafi yasa shi fashewa da kuka mai tsiwar gaske, tana huci tace"Shege ashe kana jin bugu, ae nayi tunanin kurma ne kai" Sautin kukan yaron ne ya karaɗe kunnuwansu angel dake a sashen toilet ɗinsu, da gudu suka nufi ɗakin suna shugowa suka ci burki suna kallon Yaron dake ta kuka, Hatta gabriel dake kwance yana bacci shi da Sarah sai da suka farka saboda sautin kukan fitinannan Yaron, An rasa me lallashin shi acikin su, haushin shi suke Ji, Ya baƙanta musu rai, duk irin yadda suka ƙwalla fa ransu ga son cin cake ɗin nan ya tarwatsa komai, Farin Cikinsu Ya gushe, Har ga Allah basu Ji daɗin zuwan prisoners ɗin nan ba, Saboda mutun biyun nan dake acikinsu, Mahaukacin yaron nan da Angel ta sanyawa suna Majnun saboda Yaƙi faɗa musu sunanshi, Sai kuma Unaiza ƴar gidan daddy, A ranar Bayan Danish ya lallashi Yaron Yaje dashi toilet ya wanke mishi Jikin shi Da uniform ɗinshi da ya 6ata da cake, Ya shanya su saman igiyar toilet ɗinsu, ya ɗauko bargo Ya ƙudundune shi ajiki yakai shi Daki ya kwantar dashi saman gadon shi, Cikin ƙanƙani lokaci bacci yayi awon gaba dashi, Hankalinsu har ya kwanta, ashe ƙura bata lafa ba, Sun gama shan wahalar gyara ɗakin nasu da ya 6ata musu ya hargitsa komai, Suna ƙoƙarin zama su huta, Unaiza tace musu Yunwa take ji, Suka ce mata Ga abinci can saman dining carpet ɗinsu taje taci, Saboda damuwa ma yasa babu wanda ya waiwayi abinci acikin su, Sai wannan ƙaramar yarinyar jamimah ita kaɗai ta zauna tana ci.

Ita ko Unaiza Æ´ar gidan daddy ta ce musu ba zata ci ba saboda a gidansu saman dining table ake jera mata abinci kala goma sha biyar, sai ta za6a ta darje, hatta abincin ma abaki masu aikin gidansu suke bata tana ci" gaba É—aya ta rikita su da maganganunta, sun gaza gane inda ta dosa,

Duk yadda suka so su lallasheta akan taci abinci taƙi ci, tace musu dole a kira kukun da suke girƙa abinci a makarantar ta, don ta faɗa musu kalar wanda ake girka mata agidan daddynta, idan har suna son zaman lafiya, idan ba haka ba zata yi magana da shugaban makarantar yayi musu magana, " Su angel sun sha dariya kamar zautattu jin wani sokiburutsi na Unaiza, Sun maida ta mahaukaciya, ta zamar musu tamkar Comedy, kuma ita har ga Allah dagaske take basu Umarni, Rashin sani yafi dare duhu.

Lokacin da dare Ya tsala, Babu wanda Ya runtsa acikinsu daga su har sabbin prisoners ɗin saboda rigimar Mahaukacin yaron nan MAJNUN! ya addabi rayuwarsu tun da ya farka daga bacci, Ya dinga Tsalle tsalle har saman gadajen su, Ya hanasu sakat, Su azeeza sun sha kuka saboda ƙululun baƙin cikin daya dasa musu, Har bugunshi suka so suyi amma Danish ya hana su, ya basu haƙuri akan kada su ta6a shi yaro ne, ba dan sun so ba suka Haƙura suka ƙyale shi, Taimakon da Allah yayi musu yaron baison duhu, Sun gane hakan ne lokacin da Danish Ya sauko daga saman gadonshi yaje ya kashe floor lamps ɗin ɗakin, Duhu ya gauraye ko'ina, ai kuwa ya birkice musu ya dinga kuka yana fadin su taimaka mashi, dodo zai cinye shi, angel tace munafuki ai kaine dodon daka addabi rayuwarmu ashe kana magana, nayi tunanin kurma ne kai.

Daƙyar Danish Ya ruƙo hannun shi Cikin duhu Ya kai shi saman gadonshi ya haye Yana faman sauke ajiyar zuciya, ganin ya samu natsuwa ne, ya tambaye shi ya sunanshi, Muryarshi adisashe ya ce"CHINONSO" jinjina kai Danish yai kafin ya miƙe ya rufa mishi bargo saman Jikin shi.

A washe garin ranar da aka kawo musu sabbin prisoners, lokacin Da Giants suka zo kawo musu Abinci, Sun ga haukan da basu ta6a gani ba, wato unaiza ce ta tsare giants tana zazzaga musu masifa akan su bi tsarinta, na gidan daddynta, hada ƙoƙarin ɗauko jotter acikin school bag ɗinta tare da biro ta rubuta musu list na abunda take so adinga girka mata tana ci, bayan ta gama ta je gaban su ta miƙa musu paper ɗin data yago cikin jotter din, tace dasu su kar6a, Kamar gumaka babu wanda ya motsa a cikin su,
Su haris suna ta ƙoƙarin fahimtar da ita akan ta matsa daga gabansu basa magana, amma taƙi sauraransu, ba don Allah yasa Naufal Yaje ya janyeta ba, da ranar ta yabawa aya zaƙinta, don wlh mazga zata sha awurin su, don basa ɗaukar raini.

A taƙaice Cikin kwana uku sai da suka fita hayyacinsu, Akan mutun biyun nan Unaiza ƴar gidan daddy da kuma Majnun Chinonso,

Wata sabuwar rigima ta unaiza, ta faɗa musu cewa ita fa Ta saba agidansu masu aiki suna yi mata tausa, don haka suma dole suyi mata, Kuma idan zata kwanta bacci, Da pillow uku take kwana saman gadonta, ta saba duk in zata kwanta, tana ɗaura kanta saman pillow, ɗaya kuma A tsakankanin ƙafafuwanta, Cikon na Ukun A ƙirji take rungume shi, Ba tare da sun yi mata musu ba, Su Parveen su ka yi mata tausa, Lokacin da dare ya yi Danish da Mubeen suka bata pillows ɗin su don ta kwanta kamar yadda ta saba yi agidansu, Idan fa tace su yi mata abu su ka ƙi yi mata, Kamar ƙaramar yarinya haka zata zauna tana raira musu kuka, waya ga shagwa6a66a

Haris yace"Su ƙyaleta Ai wadda tafita iya masifa tazo kuma ta miƙa wuya sun yi rayuwa da daɗi da ba daɗi balle kuma ita, " Wato yana magana akan angel, sai dai fa akwai banbanci sosai tsakanin Angel da Unaizah.

Ranar da haƙurinta ya ƙare, ganin anƙi yi mata abunda take so, Tace musu zata kashe kanta, a lokacin sun ɗauka wasa take Yi ashe dagaske take, dama irinsu basu Cika imani ba, basu da tawakkalli, gata dai da sunan musulmai amma babu musuluncin acikin zuciyarta,

Suna zazzaune acikin ɗakinsu kamar masu zaman makoki, ba zato ba tsammani suka soma Jin Ihunta Acikin Toilet, Da gudun gaske suka faɗa Sashen makewayin nasu, sai dai koda suka isa ta datse ƙopa, Suka dinga bugu taƙi buɗe musu, Danish ne ya bugi ƙopar da hannayenshi nan take ta buɗe, Suna Shiga Ciki suka same ta kwance Ƙasa Tana burgima, gefenta ledar detergent ce da tasha duk don ta kashe kanta, Rai a6ace Danish yasa hannu ya damƙo damtse hannunta, ya ɗago da ita, tana ta faman shessheƙar kuka, Da gwiwar hannun shi ya daki bayanta, gaba ɗaya saida ta amayar da abunda tasha kaf ɗinsa, cikinta kamar zai 6alle saboda ɗamewar da yayi, Idanuwanta su kayi luhu luhu, Saboda tsabar kuka hada majina ta hanci ta baki,

Angel ce ta taimaka mata wurin wanke mata fuskarta, ta kuskure bakinta, kafin ta ruƙota ita da hanna suka shigo da ita Cikin ɗakin a saman gadonta suka kwantar da ita, sai nishi take yi, launin idanuwanta sun ciza, daga gani tana acikin mawuyacin hali, zazza6i ya rufe jikinta ta ko'ina, A kewaye da gadon Su angel suka zazzauna tare da Danish, Sauran Ƴan uwan nasu suna atsaye suna kallonta,
Chapter 123 · 0% Book details