Sashe 23
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Malam Garba yace"Naga lokacin da uzair ya fita, har magana mun yi da shi, Abunda ya faru ina zaune saman benci ina sauraron radio, Sai ga Uzair ya fito daga Cikin gidan, Sai faman sauri yake yi, Ya buɗe mota ya shiga yayi mata key,Ya ƙaraso da motar Yana yi mun hon in buɗe mashi gate, Na taso Na buɗe mashi, har ina tambayarshi ko lafiya, naga zai fita a lokacin da bansaba ganin ya fita ba, ya ce mun babu komai, bazai jimaba yanzu zai dawo, Nayi ma shi Allah ya kiyaye hanya, wannan shine maganarmu ta ƙarshe da shi,'
Jinjina kai ipo yayi"bayan wannan ko akwai Wani wanda ke yawan zuwa gidajensu?
Har suna haÉ—a baki wurin cewa a'a,
Dco yace"Yanzu Idan munason ganawa da iyayen kowannansu taya zamu same su"? ya yi tambayar yana kallon aneelerh,
Cikin sanyin murya tace"surukaina basa ƙasar nan tun da jimawa suka tafi suwa south korea amma kwanan nan zasu dawo, Shi kuma taj Iyayen shi Suna zaune a Buzaye, Sun tsufa sosai, Ni aganina baikamata asanar dasu ba, Hankalin su zai tashi sosai,'
"Bazamu sanar dasu ba, Amma Shi taj ina matar shi? Ipo ne yayi mata tambayar,
Abie yace"ae shi Taj tunda matarshi ta haifi Æ´arshi ta fari, ta gudu tabar gidan, Kamar yadda aneelerh ta sanar dani, Acikin bathtub tabar mashi jinjirar,Itace ANGEL yarinyarshi,"
Dco yace"Okey, Shine Yake auran Æ´ar gidan tsohon gomna, Alhaji Ubaid Sani wadata" Jinjina kai abie yayi eh shine,
Ipo yace"Abunda za'ae yanzu, zamu fara bincikar wayar taj, wata'ƙil asamu wata shaida, Sannan zuwa gobe in Allah yakai mu, Zamu Kira Surukanki, don yakamata asanar dasu halin da ake Ciki, Shima Alhaji ubaid Zamu tuntu6e shi, Sannan Zamu Je gidan Radion da suke aiki, Dole mu binciki kowa dake atare dasu, idan Akayi sati ɗaya ba'aji ɗuriyarsu ba,Za'a Yaɗa labarin 6acewar su ta kafafan sada zumunta, Wata'ƙil adace"
Sun jima suna tattaunawa Da ƴan sandan kafin su tashi tafiya, Sai da suka ƙara kwantarma Aneelerh hankalinta, Sukayi mata alkawarin zasuyi iyakar bakin ƙoƙarinsu, sosai suka bata baki, kafin Ƴan sandan suka tafi, Ya rage gidan daga ita sai Abie sai su baba maigadi, Umarni abie Ya basu dasu Cigaba da kula da gidajen, Kafin a ƙare Binciken,
Ita kuma aneelerh yace Ta tashi su tafi gida, don bazai barta ita kaÉ—ai agidan ba, ba don taso ba tabi bayanshi, A motarshi suka tafi,drivern gidansu ne ke tukasu,
Tsawon One Week Ƴan sanda suna Bincike akan case ɗin, Basu samu komai ba,Har gidan radion su taj sukaje,Ɗaya bayan ɗaya Aka fiddo da ma'aikatan gidan radion suka yi masu tambayoyi,
A Ƙarshen Satin Cikin Weekend Uncle abdallah Ya dawo ƙasar tare da Hajiya adama, duk arana ɗaya Suka shigo garin tare da Alhaji ubaid,
Sun girgiza da jin abunda ya faru na 6acewar Su tajudeen Hajiya adama tasha kuka tamkar ranta zaifita, Haka Alhaji ubaid ya shiga matsananciyar damuwa Musamma da ya ji cewa tare da jikar shi Taj ya tafi adaren Ranar, yarinyar da yake gani tamkar ƴarsa benazir data gudu tabarshi tsawon shekaru, kasancewar shi babban mutun Wanda yasan mutane da dama, tun ranar daya shigo ƙasar Ya kira Cp(Commisioner Of Police)Sukayi zama na musamman Akan case ɗin 6acewar Su tajo,
Gaba É—aya Cp ya tattara Jami'an da suke akan aikin Binciken case É—in, don yaji bayani daga garesu, Bakomai yafi É—aure ma kowa kaiba, face Yadda aka rasa samun wata hujja da zata tona asirin abunda ya faru dasu adaren ranar,
Wayar Taj da suke tunanin zasu samu Wata shaida atare da ita, koda Akaba me gyaran waya ya canza screen ɗin, Cikin rashin sa'a suka samu komai na wayar Ya goge, Duk zurfin binciken da Jami'an sukayi, Basu samu koda motocinsu ba, Saƙo da lungu na garin da bayan garin dare da rana haka sukayi binciken amma basu samu wata shaida ba, A ƙarshe binciken ya koma CID,
Labarin 6acewar Su taj ya karaɗe social media, Ta ko'ina zancen 6acewarsu a keyi, Mafi rinjayen mutane sunfi tunanin An kashesu ne a 6oye, Tunda kowa yasan su da son fiddo da gaskiya, kota halin ƙaƙa, Wannan yasa mutane su ke Hasashen kodai an kashesu a 6oye ne Allah shine mafi sanin dai dai!!!
Rayuwar Aneelerh gwanin ban tausayi baiwar Allah, Ta jigata sosai, ta shiga mawuyacin hali na rayuwa, ta rame sosai ta ƙanjame hatta aiki Abie ya hanata zuwa tunda ba ƙoshin lafiya gareta ba, Rashin Uzair da taj da kuma ANGEL ba ƙaramin nakasa rayuwarta yayi ba,Tayi kewarsu sosai,a kullum addu'arta Allah ya bayyanar dasu aduk inda suke, saboda su takan tashi tsakar dare tayi nafilfili, tayi masu addu'a Tana kuka,Haka rayuwarta taci gaba da kasancewa, Abinci kanshi sai abie da mami sun tasata gaba tukunna take Cinshi, a karshe da ciwon nata yayi yawa, Dr ya duba ta, Ashe hada laulayin Ciki, Allahu akhbar Abunda suka jima suna rokon Allah ya basu ita da uzair, Ga shi Yau Allah ya kar6i addu'arsu a lokacin da shi uzair ɗin Bayanan, Allah sarki rayuwa kenan.
A 6angarensu Hajiya adama kuwa, basu koma south korea ba, Anan suka Ci gaba da zama, saboda halin da ake Ciki na 6atan Ya'yansu ,kullum Cikin zullumi suke,
Akwana Atashi Yau wata ɗaya cuff da 6atansu tajuddeen, A lokacin Kowa ya fara sarewa, Tuni ƴan sanda sun sallami su baba maigadi, makullan gidajensu Yana a hannun jami'an CID, sun ruƙe su har zuwa lokacin da zasu kammala bincikensu,
Tun Uncle abdallah Yana 6oye wa Mutanan Buzaye game da 6atansu Tajo, harya yanke shawarar zuwa buzaye don ya sanar dasu halin da ake Ciki,
A ranar da suka shirya tafiya tare da hajiya adama suka Bi jirgin asubahi zuwa katsina state, A hotel suka sauka, A washe gari su ka wuce zuwa buzaye, Lokacin da suka isa garin da safe, a ƙopar gidansu Malam zahiru suka risƙi mutane zazzaune saman tabarma, nan fa hankalinsu ya tashi, Sunzo da mummunan labari Sun riski labarin dayafi nasu ɗaga hankali .
Mutanan da suka samu a ƙopar gidan, Ƴan zaman makoki ne, Allah ya yi ma iyayen tajuddeen rasuwa su duka Biyun, Malam Zahiru ne Ya fara Rasuwa sakamakon Hatsarin Da yayi, Yana Cikin tafiya gefen titi ya dawo daga gona zashi gida, Wata mota ƙirar dab,Ta biyo ta titin da gudun gaske kaitsaye tabi takanshi, Ashe burkin motar ne Ya samu matsala, Duk yadda drivern dake tuƙa ta yaso Ya yi control ɗinta abun Yaci tura,Gaba ɗayansu suka mutu a wannan lokacin,
Tunda labarin mutuwar shi ta riski Yahanasu mahaifiyar tajuddeen taji mummunar mutuwar da Mijinta yayi,nan take Zuciyarta ta buga ko shurawa batayi ba, innalallahi'wa'inna ilahirraji'un!!!Uncle abdallah yaji mutuwar ɗan uwansa,duk yadda yaso ya jure hakan ya faskara tamkar ƙaramin yaro haka ya dinga kuka,mutane suna lallashinshi,
Hajiya adama saboda tsabar kiɗima har suma saida tayi, Ciwo gadan gadan Ya taso mata, A nan gidan deeje suka xauna mahaifiyarsu Uncle abdallah, ita kanta deeje batasan inda kanta yake ba Tun bayan rasuwar malam Zahiru Ta kamu da ciwon paralyse, Laraba ƙanwar yahana su Ce ke yin jinyarta, da wasu daga cikin ƴan uwansu na nan buzayen, Kafin Barin su uncle abdallah buzaye, Itama deeje Allah yayi mata rasu wa, Wa'iyazubillah Babu wanda bai tausaya ma Uncle abdallah ba, lokaci ɗaya ya rasa ya'yan shi da suka 6ace,Ya rasa ya'yan shi da matar sa yanzu kuma Yayi babban rashi na mahaifiyarsu deeje, Lamarin dai babu daɗin ji!
Kusan wata É—aya su ka yi A buzaye kafin suka tattara yanasu yanasu suka koma Jos,
Zaman ƙasar gaba ɗaya ya gagaresu, Babu wani Labari me daɗi, a ƙarshe suka tattara suka koma south korea, Cike da zullumin Me zai biyo baya, Don sunyi magana da Ipo, ya yi masu alƙwarin duk halin da ake Ciki game da bincikensu taj zai kira su awaya ya sanar dasu, Shima Alhaji Ubaid, Sun ƙare magana da Jami'an dake bincike a kan case ɗinsu Tajuddeen, sun yi mashi alƙwarin zasu yi iyakar bakin ƙoƙarinsu,wurin Bincikar ainihin abunda ya faru da su,kuma zasu binciko su aduk inda suke muddin suna a doron duniyar nan!,kuma duk halin da ake aciki zasu dunga tuntu6arshi akai kai,
A 6angaren Aneelerh kuwa,Komai Ya hargitse mata baiwar Allah, Ga rashin da ta yi Ga kuma Laulayin Ciki da take fama dashi, kullum cikin yin kuka take, tsananin tausayinta ya kama su Abie, Kowa lallashinta yake yi, Akan tayi hakuri tabarma Allah komai, tun daga wannan lokacin ta hana idonta bacci,Takan tashi tsakar dare tayi nafilfili duk don saboda su Angel,idan tafara nafilfili har sai kafafunta sun fara yi mata zogi tukunna take dakatawa, idan kaga aneelerh tayi bacci to da rana ne, domin kuwa ta maida dare lokacin yin ibadarta, kullum rana ta Allah sai ta yi masu sadaka, bayan haka ta yi magana da abie akan A nemo manyan malamai su taya su da addu'a kuma ayi masu sauka, batare da 6ata lokaci ba, Abie Ya aiwatar da duk wani abu da Aneelerh ta bashi shawara akai,
Ƴan sanda Sun Dage damtse wurin Yin Bincike,Yayin da malamai suka Bada himma Wurin taya su addu'a da kuma yi masu sauka, Haka zalika su aneelerh Sun taka rawa wurin Yi masu addu'a, da sadaka, akan Allah ya bayyanar dasu,wannan kenan..
Shin ya rayuwar Angel ta ƙare a cikin ruwan da mahaifinta ya jefa ta? Ta rayu ko ta mutu?
Bayan wasu ƴan kwanaki da Tajuddeen ya jefa ta a cikin ruwa, hadari ne Ya haɗu bakikkirin a sararin samaniya, kafin wani lokaci yayyafi Ya soma sauka a doran ƙasa. Daji ne mai manya manyan bishiyoyi da tsirrai, kowane ganye ka kalla yayi kore shar da shi, gwanin ban sha'awa, musamman ciyayin da ke cikin dajin masu tsayi da cukowa, a daidai wannan lokacin garken shanu suka shigo cikin dajin. Aƙalla sun kai talatin da biyar, suna tafe suna Cin ciyawa.