Sashe 71
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
bayan sun kammala Yi mata tambayoyin har bakin motarta suka rakota, ta buɗe ta shiga, suka yi mata godiya taja motar ta fuce daga Cikin gidan, Tana cikin yin driving saman titi Junaid Ya farka yana ta tsala kuka, a dole ta kashe motar daga gefe ɗaya ta rumgumo shi ajikinta tana lallashinshi, yace mata Yunwa yake Ji, ta bashi abinci yaci," tunawa da madararsa da ta ajiye mashi a backseat na motar yasa ta juya ta kai hannu ta ɗauko mashi ita, acikin bottle take, ta cire murfin ta kafa mashi abaki yana sha, yayin da ta shiga zurfin tunani, abun ya tsaya mata aranta, ita gaba ɗaya rayuwar duniyar tsoronta take ji, meya faru dasu uzair? Shiru ba labarinsu kusan shekara huɗu? Sannan ga wasu mutane suna Bibiyar rayuwarta da sunan jami'ae ne, Anya kuwa bazata gudu tabar ƙasar nan ba, na wani lokaci? Gani take kamar zata rasa ɗanta ne, kamar yadda ta rasa mutun ukun nan masu mahimmanci, tana cikin yin wannan xancen zucin junaid ya fashe da kuka yana faɗin"tasa mashi madara a hanci," da sauri takai idonta kanshi, fuskarshi ta 6aci da madarar, batasan ya akai ta janye robar daga bakinshi ba ta kwafa mashi a hancin shi, rufe bottle ɗin tayi tare da ajiyeta gefe ɗaya, ta zaro hanky cikin ƴar purse ɗinta ta shiga goge mashi madarar, bayan ta kammala ta maida hanky a cikin purse ɗin, Ta rungumeshi ajikinta tana lallashinshi, har saida yayi shiru lamo ajikinta tukunna ta tashi motar ta miƙi hanya ta nufi gida,
Lokacin da ta koma Gida, a palour ta taras da Mami da wasu ƙawayenta suna fira, sai da ta fara gaishe su, suka amsa mata, tare da miƙa mata hannu ta basu junaid, Ita kuma ta wuce cikin ɗakinta, tana shiga ta rage kayan jikinta ta faɗa toilet tayi wanka, ta fito waist ɗinta a ɗaure da towel tana kokarin zama saman mirror chair, alert ya shigo Cikin wayarta dake ajiye saman mattress, da sauri takai hannu ta ɗauki wayar, kamar a mafarki take ganin credit alert ɗin da aka turo mata via dollar account ɗinta, wanda a kuɗinmu na nigeria kuɗi ne bana wasa ba, har saida ta dafe ƙirjinta da hannu ɗaya, ta shiga ruɗu akan wannan kuɗin da aka turo mata, bayan ita ba wanda ta ba acct number ɗinta, Shi kanshi dollar account ɗin ta jima bata yi amfani dashi ba,
Komawa ta yi gefen gadonta ta zauna hannunta ruƙe da wayar tana kallonta, wani saƙonne ya kuma shigowa cikin wayarta, cikin harshen turanci aka rubuto shi, karantawa tayi kamar haka
_mun gode da haÉ—in kan da kika bamu_
Nan take ta gane cewa Jami'an nan ne suka Turo mata da kuɗin, ajiyar zuciya ta sauke tare da jefar da wayar saman pillow, Ta gyara kwanciyarta saman mattress ɗin, Yayin da idanuwanta ke fuskantar ceilling, zuciyarta a cunkushe take da tunani kala kala duk akan Jami'an nan, Su kuma ko daga ina suke? Waye ya sanya su bibiyar case ɗin su tajuddeen? amma tasha ruwan mamakin Irin Ƙirar jikinsu, especially wannan ɗayan daya zauna saman sofa wanda take tunanin shi ne team leader ɗinsu, Kamar shi ya ƙera kanshi, daga gani dai jami'ae ne su bana wasa ba, ita dai fatanta Allah ya tabbatar da alkhairi akan bincikensu dana su Uncle bash,
Ta yi zurfi acikin tunaninta, tajiyo muryar baby junaid yana faɗin"Mommy kizo inji mami, " daga kwancen da take ta juya tana kallonshi, ya ruƙe qugu abakin ƙopar ɗakin, yana ta faman zumbura baki yace"Bake kika sanya mun madara a hanci ba, ae na faɗa mata, tace zata rama mini"
Yadda yayi maganar ne ya bata dariya, har fararen haƙoranta suka bayyana, Miƙa mashi hannu tayi"zo nan My baby boy" maƙe kafa ɗa yayi"Ae baki sona, Tunda kika sanya mun madara a hanci," saukowa tayi daga saman gadon ta wuce wurin closet ɗinta, Jallabiya ta ɗauko ta zura ta ajikinta, kafin ta dawo ta nufi inda yake a tsaye, ta zuqunna agabanshi tare da kai hannu tana shafa sumar kanshi tace"My baby boy, nifa mommynka ce, ni na haife ka, bani da tamkarka aduniyar nan inasonka fiye da kaina, jinka nake kamar bugun zuciyata,' takarasa maganar tare da sanya hannu ta ɗauke shi, kafin ta mike ta wuce cikin falon,
A lokacin ƙawayen Mami sun tafi, A zaune ta same ta saman Sofa, Riga bubu ce a jikinta, idonta na akan plasma tv, tashar arewa 24 take kallo
Takun tafiyar aneelerh ne ya janyo hankalinta, ta juyo tare da kallonta, fuskarta asake tace"My daughter Kinyi mana laifi, Junaid ya faÉ—a mini abunda kika yi mashi acikin mota, ashe dama shirin kashe shi ki kayi"? cikin zolaya tayi maganar, Fuskar aneelerh É—auke da murmushi tace"Kuskure ne mami bansan nayi mashi haka ba, kuma fa har hakuri na bashi amma shine bai kar6i uzirina ba," takai karshen maganar a yayin da take zama saman Sofa tare da junaid, Ya manne ma jikinta,
Kallon shi mami tayi"ka yafe mata ko in rama maka"? Ashagwa6e yace"nayi mata amma idan ta ƙara, afaɗa ma uncle bash ya sanya gun ya harbe mata kai," gaba ɗaya suka kwashe da dariya aneelerh tace"amma baka da mutunci junaid, uwar taka zaka sa a harba da bindinga? Idan na mutu ya zaka yi"? Watsa hannu yayi tare da cewa"Shikenan, sai aje kasuwa asiyo wata uwar" tuntsirewa su kayi da dariya, mami tace"Aku sarkin ɗumi, Kwanan nan xan sanyaka makaranta, tun da bakinka ya buɗe, ga surutu" Aneelerh tace"nima tunanin da nake yi kenan, ko islamiyace a fara sanya shi yana zuwa kafin asanya shi ta bokan," fira suka cigaba da yi har baby junaid yayi bacci a jikinta, aneelerh bata fada ma mami game da abunda ya faru da ita ba, kamar yadda jami'an suka gargaɗeta akan ta manta da komai nasu ta ɗauka tamkar mafarki tayi shiyasa taja bakinta tayi shiru gudun kada taja ma kanta,
*Back to Prison*
After One Day👌
Wani irin narkakken Jini ne mai kauri da ƙarni yake gangarowa ta cikin ƙoramar ruwan dake Gudana, Sassan Jikin mutun ta gani gunduwa gunduwa tsulundum acikin Jinin, Hannu tasa ta dafe kanta tare da fashewa da matsancin kuka na fitar hayyaci,
A firgice ta farka daga baccin da take yi sakamakon bugun ƙafarta da aka yi, wata irin Zabura Ta yi tare da miƙe wa zaune, Tana binsu Da Kallo, ɗaya Bayan ɗaya, Suna a kewaye da gadonta, Batool Hanna hibba, Azeeza, yasmin, eve, javed Sai kiran sunanta suke Yi suna tambayarta lafiya? Me take ma kuka? Abunda ya faru suna a kwance saman gadajensu suka soma Jin shessheƙar kukan angel, Hakan yasa suka yi gaggawar zuwa gaban gadonta don suji dalilin yin kukan nata,
"Angel meya faru ne? Duk kin bi kin ruÉ—e? ko kinyi mummunan mafarki ne"? batool ce ta jefa mata tambayoyin,
Ƙanƙame Jikinta Ta yi da hannayenta, wata irin zufa Ce ke tsastsafo mata ajikin fatarta, Sai faman zazzare Manyan idanuwanta take Yi, gaba ɗaya bata Acikin hayyacinta, tayi matuƙar tsorata da mafarkin da tayi, muryarta na kerma ta soma Magana"Ina parveen? ina rubina da Deeja an dawo dasu? Ko kuwa har yanzu? Takai ƙarshen maganar tana kallonsu Batool,
*â¤â¤â¤PRISONERSâ¤â¤â¤*
"Angel Still ba'a dawo dasu ba, Abincin da muka rage musu tun jiya ya riga da ya lalace, da mun sani mun cinye shi," Hanna ce ta bata amsa, Azeeza tace"Yanzu shikenan baza adawo mana da su Parveenar mu ba? sun tafi kenan"? Muryarta a sanyaye tayi maganar, Hibba tace"Pls Azeeza stop sayin that bana jin daɗi, kuna karya mana zuciya, Tsohuwa fa tace za'a dawo dasu da zarar Sun samu lafiya," Eve ce ta kalli Hibba da tayi maganar tace"Hib kin manta lokacin baya? Ƴan uwanmu da muke atare dasu? Wasu in an ɗauke su ba'a dawowa dasu sun tafi kenan"? Idon angel akansu tana sauraronsu, kwata kwata bata acikin natsuwarta, tana matuƙar jin tsoron ta yi mummunan mafarki, saboda Xaiyi wuya mafarkinta yaƙi xama gaskiya, kafin zuwanta gidan kurkukun ƙaddara saida tafara mafarkin kasancewa acikin shi kuma sai ga shi ta tabbata, ta tsinci kanta acikin shi,
"Yakamata mu daina wannan maganar, Muna ƙara tayar wa junan mu hankali, Idan muka kwantar da hankalin mu, za'a dawo dasu ne," acewar Javed, yasmin tace"Yanzu me zamuyi toh? Ni nagaji da zama zugudum, " fuskarta a yamutse Tayi maganar,
Azeeza tace"Muna da abunyi mana, Angel zata Wanke mana gashin kanmu, ta kuma gyara mana shi, " tunkan takai karshen maganar, yasmin ta harare ta"Kefa matsalarki kenan, Sai ana magana ta hankali ki wani soko wa mutane Shiririta aciki," zum6ura baki Azeeza Ta yi tare da murguÉ—awa mata shi tace"To me kike so Muyi? Wanka ko motsa Jiki? Ko kuma bacci? Ko giants xamu Jira su kawo mana abinci"?
Banza yasmin tayi da ita, Zama batool tayi a gefen gadon angel, ta ruƙo hannun angel acikin nata tace"Sister, na lura sam bakya acikin hayyacin ki, Ki faɗa mini, me kika gani acikin baccin ki wanda ya tsoratar dake"? Idanuwan angel cike tab da ƙwalla ta ɗago ta kalli fuskar batool, bazata Iya faɗa mata ainihin abunda ta gani acikin mafarkin ta ba, Saboda Bata son ta tayar mata da hankali, Kuma faɗin baida amfani, sannan ma babu kyau mutun yayi mummunan mafarki ya faɗi ma wasu,
Don haka tace mata"bakomai batool Just bana Jin daÉ—in Jikina ne,"