Sashe 34
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 6 min read
Yinin ranar angel a galabaice ta yi shi, sai da takai ga bata gane komai idanuwanta sun rufe saboda tsabar jin yunwa, ga raÉ—aÉ—in da zuciyarta ke yi mata, wani irin matsanancin ciwon kai ne ya far mata, a nan saman benan ta zube rai hannun Allah,
lokacin da dare ya yi, hasken ɗakin da kan shi ya ɗauke, dama ƙa'ida ne idan dare ya yi gaba ɗaya hasken wurin yake kashe kan shi, sai dai mutun in yana buƙatar haske ya yi amfani da fitilun da ke ajiye saman table,
Duhu ya mamaye idanuwanta, ta ƙuntata sosai ji ta ke kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu, wannan wata irin rayuwa ce me cike da ruɗa ni? taya zata ci gaba da rayuwa acikin kurkukun nan? ta gaza gane sarƙaƙiyar da ke acikin rayuwarta, shin wanene a cikin danginta ya kawo ta cikin gidan kurkuku da sunan araine ta? Anya kuwa wannan ba ƙanzon kurege bane? tabbas akwai mata maƙarƙashi a cikin gidan kurkukun nan,
A cikin zuciyarta take wannan tunane tunanen,
Saboda tsabar yunwa ko yatsanta, bata iya É—agawa,
Batool sam ta kasa runtsawa saboda halin da yarinyar take ciki, ta damu da ita sosai ga shi ita kuma bata so ta kusanto ta, kowa ya yi bacci ban da ita,
Saukowa ta yi daga saman gadonta cikin duhu ta shiga laluban inda fitilun suke, har Allah yasa ta gano table ɗin takai hannu ta ruƙe handle ɗin fitilar bayan ta kunnata, tafiya ta soma yi Cikin ɗakin har zuwa saman benan anan ta samu angel cikin mawuyacin hali, zuƙunnawa ta yi agabanta, muryarta ƙasa ƙasa tace"Yar uwa" angel bata iya amsa mata ba, domin kuwa takai mataki na ƙarshe wanda ko la66anta bata iya motsawa, a lokacin jikinta ya yi mugun yin sanyi ta fidda rai da rayuwa, cikin zuciya ta dinga yi furta kalmar"ruwa! ƙishi nake ji! A taimaka mun," batool batasan me take cewa ba, saboda a cikin zuciya ta yi maganar, Allah dai ne kawai ya taimake ta, batool ta yi tunanin ko tana buƙatar ruwa, dama ɗazu ta 6oye mata chicken wraps ɗinta, tun ɗazu taso ta bata taci sai dai taƙi bata fuska, shiyasa ta ajiye mata zuwa lokacin da zata neme ta,
Miƙewa ta yi da sauri ta nufi ƙarƙashin gadonta inda take ajiyar ruwa acikin bottle water, ta zuƙunna tana haskawa da fitilar hannunta, kwando ne ajiye a karkashin gadon, a cikin shi take 6oye abinci idan ta rage saboda gudun yunwa, zura hannu tayi ciki ta ɗauko Chicken wrap ɗin, Ta tura cikin aljihunta, sannan ta ɗauki robar ruwan ta ruƙo a hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma yana a ruƙe da fitila, da sauri ta koma saman benan saitin inda angel take ta zuƙunna, ta sauke fitilar ƙasa, tare da bottle ɗin, hannu tasa ta tallabo kan angel ta jingina shi gefen shoulder ɗinta,
Sannan ta É—auki bottle din ta buÉ—e murfin ta kafa mata bakin robar,
yadda kasan mafaraucin da yayi rashin ruwan sha na tsawon sati ɗaya haka angel ta shiga ɗaɗɗakar ruwan, maƙoshinta har wani sauti yake badawa, kwat kwat!
Murmushi batool ta saki ba ƙaramin daɗi taji ba ganin yadda take shan ruwan,, Yarinya taji ƙamshin mutuwa,
Sai da ta shanye ruwan nan tass tamkar xata haÉ—a da robar ruwan duka ta shanye,
Janye bottle É—in ruwan ta yi daga bakinta, ta ajiye ta saman matakalar, ta mayar da murfin a mazauninsa,
Hannu ta zura cikin aljihun ta, ta ciro chicken wrap ɗin duk ta rugurguje, a haka ta dinga tura mata abaki, la66anta har kerma suke yi wurin ci, kuma har lokacin kanta yana asaman ƙirjin batool, sai da ta cinye tass ta soma jin wani irin tashin zuciya, yunƙurin amai ta soma yi, a ruɗe batool ta shiga bubbuga bayanta tana faɗin"Sorry sis, bari na raka ki toilet" kafin batool ta miƙe ta yi yunkurin tallabota, tuni Ta saki aman anan saman benan, ta dinga kwararo shi gaba ɗaya ya 6ata hada jikin rigarta, baiwar Allah taji jiki, saboda tsabar tausayinta da batool take ji, batasan lokacin da ta fashe da kuka ba, duka chicken wrap ɗin da taci sai da ta amayar da ita, tun ruwa na fita abakin ta, har yakai ga babu komai sai dai kawai kakarin aman da take yi,
Ganin mawuyacin halin da ta shiga ne yasa batool ta miƙe tare da ɗaukar fitilar, ta ruga da gudu zuwa ƙopar ɗakin tsohuwa, knocking ƙopar ta soma yi tamkar zata 6alleta,
Mutun uku dake bacci saida su ka farka, Danish da ya kasance baisan hayaniya ko misƙala zarratin, Sai hanna da kuma Haris, Har suna haɗa baki wurin tambayar Batool lafiya take neman tsohuwa, ko ta kansu bata bi ba, har saida tsohuwa ta buɗe ƙopar, Hannunta ruƙe da sanda ta fito, batool na kokarin buɗe baki ta yi mata jawabi, tariga ta cewa"Kada ki damu, ki koma wurinta zata dawo dai dai, nayi mata addu'a daga cikin ɗaki," tana faɗin hakan ta juya ta koma cikin ɗakinta, tare da jan ƙopa ta rufe,
Jikinta asanyaye ta juya sam ba haka taso ba, taso ace tsohuwa tazo ta duba jikinta, saboda halin da yarinyar take ciki, muryar Haris ce ta ratsa kunnanta"Just because her duk kin damu kanki, kin hana idonki bacci, meye alaƙarki da ita"?
Hanna tace"tambayar da nake so na yi mata kenan, shi dai danish baice komai ba, bacci ne dai an hana shi yi, ya takure saman gadon shi, sai faman lumshe ido yake yi,
Batool ku wa Ko kallo basu ishe ta ba, lokacin da ta koma wurin angel, wani abun mamaki a zaune ta same ta, ta jingina kanta jikin bango, shanyayyun idanuwanta a buÉ—e sun kaÉ—a sunyi jawur, Sumar kanta duk ta barbazo mata har saman fuskarta, la66anta na kerma take ambaton"rabbi yassir wala tu'asir watammim bil khairi" wani irin farin ciki ne ya lullu6e batool, har batasan lokacin da ta saki murmushi ba, maganar tsohuwa ta tabbata ga shi ta farka har tana magana, duk da batasan me take cewa ba,
"Yar uwa" ta ambaci sunanta, idanuwanta Jiƙe sharkaf da hawaye ta ɗago ta kalle ta, wato duk irin korar da take yi mata hakan baisa ta guje taba, lallai ba ƙaramin so take yi mata ba, batool ba tayi tsammanin zatayi mata magana ba, sai ji tayi tace"Ina so in wanke jiki na, bana jin daɗi,"
Miƙa mata hannu batool tayi"ki taso na raka ki toilet" miƙa mata hannu angel tayi, ta ruƙo nata daƙyar ta samu ta miƙe, ita kanta ta yi mamakin yadda ta rayu don ba ƙaramar azaba tasha ba, taji jiki sosai, amma yanzu ko yunwa bata ji, jikinta ba wani ciwo, sai dai ciwon dake a cikin zuciyarta dake tafarfasa,
Har toilet batool ta rakata, da yake babu wadataccen haske bata iya kallace shi da kyau, A bakin fanfo suka tsaya ta wanke mata gaban rigarta daya 6aci da kuma wandonta, wani irin sanyi jikinta, tuni ta soma kerma,
Fitowa su ka yi daga Cikin toilet ɗin hannunsu cikin na juna, batool ta kai ta har saman gadonta mai ɗauke da no 1 kusa dana danish na shi no 2 ne, sai na batool no 3, hawa saman gadon ta yi batool ta lullu6a mata bargo asaman jikinta, sosai ta ƙudundune,
Komawa batool tayi ta gyara inda angel ta 6ata da aman, ta goge ko'ina duk ita kadai baiwar Allah, bayan ta kammala ta dawo Cikin ɗakin ta ajiye fitilar saman table ɗin, ta kukkuna sauran fitilun ɗakin ya yi haske, danish da bai koma bacci ba ya lafe saman mattress ɗinshi, yana fuskantar angel dake ƙudundune cikin bargo, babu tazara tsakanin gadajensu gab su ke da juna, idan har mutun zai iya miƙa hannu to xai iya ta6o gadon dake a kusa da nashi, shi dai hakanan sam yarinyar bata kwanta ma shi ba, ji yake kamar an kawo masu monster acikin ɗakin su, bargo yasa ya lullu6e fuskarshi,