Sashe 142
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daƙyar suka samu Angel ta je ta yi wanka, A cikon kwana na uku da aka tafi dashi, Hanna ce ta wanke mata uniform ɗinta, Dogon wandonta sabo da vest ɗinta, dama su ne ajikinta aranar da abun ya afku, Tsaffin kayanta ta maida ajikinta, yanzu ta daina kwana gefen gadonshi, Asaman gadon take kwanciya tasha kukanta, duk Idan dare ya nutsa tashi take ta zauna, tana yi masu addu'a shida batul, Da daddynta, Kwana ta ke yi a zaune tana kai kukanta wurin Allah, Da ga ita har Gabriel babu wanda ya ƙara tada zancen haura tagar nan saboda babu lafiya atattare dasu, baiwar Allah azeeza ita keta yin jinyar Gabriel, Yaji jiki sosai, Gashi ƴan uwa nasu haushinsa suke ji, gani suke kamar baya ƙaunar Danish ne shiyasa ya ke neman naƙasa musu ɗan uwansu, A kwana atashi ba wuya wurin Allah yau tsawon 2 weeks kenan Ba'a dawo da Danish ba, A lissafi na Batul ta shiga Cikin wata na biyu kenan ba'a dawo musu da ita ba, Haka zalika Unaiza ƴar gidan daddy, Yau ta cika sati Sati biyu da kwanaki ba'a dawo da ita ba..........
(Iya abunda ku ka samu yau kenan, Da babu ƙwara ba daɗi, Mu haɗu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya)
💔PRISONERS💔
Kwance ta ke asaman gadonshi, hannunta rungume da pillow ɗin sa ta ƙanƙame shi a ƙirjinta, bacci take yi amma sam babu kwanciyar hankali atattare da ita, sai jan numfashi ta ke yi ga cikinta da ke ta yin kukan yunwa, hatta ƙirjinta wani irin nauyi yai mata, zuciyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi, duk irin sanyin da yanayin ke da shi hakan bai hana zufa tsastsafo mata ba, saboda damuwa da kuma rashin cin abinci har rama ta yi fuskarta ta faɗa, sai uban hasken da ta yi, gashin kanta kuwa kamar na mahaukaciya, rabon da ta sharce shi tun lokacin da aka tafi da Danish, wankan ma sai in sun matsa mata ta ke yin shi akai akai, haka abinci sai sun mata dole sun tasa ta gaba tukunna take ɗan tsakurar kayan marmari tasha idan ta gama ta kora da ruwa, fruit kaɗai ta ke iya sha, duk ta takura kanta,Ta hana kanta sakat kamar wadda ta aikata zunubi, ga shi rayuwarta gaba ɗaya ta koma saman gadon Danish, idan kaga ta sauko to toilet zata shiga domin yin wani uziri amma bayan haka babu ruwanta da kowa, Saman gado take naɗewa ta addabi zuciyarta da tunane tunane na damuwa, depression tuni ya fara samun gur6i acikin zuciyarta, idan damuwa ta yi mata yawa kanta har sara mata ya ke yi da matsanancin ciwon kai, zuciyarta tai mata nauyi kamar an ɗaura mata dutse saman ƙirjinta haka ta ke ji, wani lokacin idan abun yai mata yawa har amai take yi, Rayuwar Angel ta zama abun tausayi, kowa tausayinta ya ke yi acikin su, sun damu da damuwarta, suna matuƙar jin takaicin halin da ta shiga kamar ba Angel ɗin su ba.................💔
Ƙasa ƙasa ta ke jin hayaniyarsu a cikin kunnanta, sai surutu su ke yi duk sun cika ɗakin, tana ta faman ƙoƙarin buɗe idanuwanta amma sunƙi bata haɗin kai baccin ne bai ishe ta ba, ga kuma matsiyaciyar yunwar da ta ke ji, A hankali take motsa la66anta tana karanto addu'ar tashi daga bacci, kafin daƙyar ta iya buɗe manyan idanuwan nata waɗanda suka raunata sosai saboda kukan da take yawan yi akowani dare na Allah, bismilla ta furta yayin da ta ke yunƙurin miƙewa zaune ta jingina bayanta jikin bango, old uniform trouser ɗinta ne a jikinta baƙi, Sai jar vest ɗinta data sanya, don tafi sha'awar kwanciya bacci da ita, buɗe baki tai sakamakon hammar da tazo mata ba shiri ta ɗaura hannunta saman bakin nata Tana ambaton Alhamdulillah.
bayan ta sauke hannun ta ɗaura su saman pillow, kafin ta tsayar da idanuwanta kan ma su yin Surutun, kusan su Biyar, Zazzaune a ƙasa saman shimfiɗar Sarah, Hannah da Yasmin tare da Hibba da kuma rubina, sai Eve hada mai shimfidar Sarah, Hannunta ruƙe da nail cutter, Ita kuma Hanna tana ruƙe da nail filer, suna fira Sarah na yanke musu akaifa, idan tagama yi ma mutun ɗaya sai Hanna ta kankare mashi akaifar ta gyara mashi ita, idan ka gan su ahaka sai ka yi tsammanin basu da wata damuwa alhalin nan kuwa zuciyarsu a cunkushe take da matsananciyar damuwa.
tun da ta ɗaura idanuwanta akansu bata ɗauke ba, bakomai yake burgeta dasu ba, face yarda suke matuƙar ƙaunar junan su, Suna da kyakkyawar mu'amala a tsakanin su, Sau dayawa basu jin komai don su yi ma ɗan uwansu hidima, sa6anin wasu mutanan da zaka ga ƙashi ya hana su taimaki junan su, amma su waɗannan bayin Allahn suna da haɗin kai, tun da ta fara rashin lafiya basu ta6a bari ta wanke koda uniform ɗinta ba, hatta kayan marmarin da ta ke sha su ne suke kawo mata su har saman gadonta don ta sha, shiyasa take matuƙar ƙaunarsu.
Ɗauke idanuwanta tai daga kansu sarah, ta shiga bin kowani gado da Kallo, Parveen tana ƙudundune saman gadonta, bata farka daga bacci ba, sai juyi take yi saman mattress ɗinta kamar zata faɗo ƙasa, Sauran gadajensu Deeja tabi da kallo, Da alama idonta biyu, ta ƙurawa ceilling ido fuskarta ɗauke da damuwa, Haris ma Yana a zaune gefen gadon shi Ya zabga uban tagumi, gwiwowin hannayenshi asaman na ƙafafun shi, tasan bai wuci damuwar rashin ɗan uwansa bane, bawan Allah duk da irin juriyar shi hakan bai hana shi yin rama ba, sauran mazan duk suna a kwance saman gadon su basu farka daga bacci ba.
Tana cikin bin gadajen su da kallo, ta soma jiyo sautin dariyar Azeeza ta cikin sashen toilet ɗin su, Da sauri takai idonta kan ƙopar, Majnun ne ya fito babu kaya ajikin shi sai gudu ya ke yi jikinsa duk lemar ruwan wankan da ta yi mashi, Gaba ɗaya su Hanna suka ɗago Suna kallon su, Lamarin ya ɗaure musu kai ganin yadda yadda ya fito babu kaya yana ta gudu acikin ɗakin su, hauka tuburan yana ta tiƙar dariya ko kunya bai ji ko da ya ke ina yasanta.
Azeeza ce Ta biyo bayanshi hannunta ruƙe da uniform ɗin shi, Sai zagaye cikin ɗakin nasu su ke yi tana ta Ƙwala mashi kiran tana faɗin"Wai ba zaka tsaya in sanya maka kayan ka ba? Salon sai ka faɗi ko, don ma ka samu na yi maka wanka shine ka ke min wulaƙanci, ba don zuciyar imani ba Allah da bazan yi maka wankan ba ƙazami kawai, mutun jiki duk ciwo, har tsoron ta6a fatar shi nake yi kamar zata fashe saboda haske........" Su hanna sai dariya su ke yi musu, ita kanta Angel sai da ta ɗan murmusa ganin yadda take ta faman bin shi yana yi mata yawo da hankali, da ga ita har shi Sai ka rasa gane wanene babba acikin su, shiyasa duk suka rainata,
kamar sun samu tv haka suka dinga binsu da kallo, babu wanda ya lura da Angel ta farka da tuni sunzo wurinta.
Fitowa daga Cikin ƙopar sashen toilet ɗin su Jamima ta yi, hannunta ruƙe da rigar uniform ɗinta, daga ita sai ɗan wandonta ja, fuskarnan a murtuƙe ta sha mur, ƴan kumatuntu sun yi suntum dasu saboda tsabar fusata, Gashin kanta da aka ɗaure mata da ribbom Ya cika bayanta, kamar na ɗiyar roba, sai baƙin rai ta ke yi,
Hayaniyarsu Ce ta farkar da sauran da suke rage suna bacci, hatta haris daya zabga uban ta gumi da deeja dake kallon ceilling saida suka dawo da dubansu akan Majnun da Azeeza.
"Azeeza!" haris ne ya kira sunanta, hakan yasa ta tsaya tana haki, Ta waigo tana kallon shi.
Tun kafin ya soma yi mata magana, ta É—an É—aure fuskarta, muryarta tamkar za fashe da kuka ta soma magana
"Na gaji da raina min wayau da su ke yi, don sun ga na damu dasu, shiyasa suke yi min wulaƙanci dashi da waccan mai fuskar tumaturin, tsawon one week ba wanda yai tunanin yayi musu wanka, da yake ba hankali ne dasu ba, ko tsamin jikin su basa ji, a tunani na yi musu gwaninta, yau da safe na tada dasu daga bacci naja su muka shiga toilet na datse ƙopa don inyi musu wanka, nasa su ka fara yin brush, bayan sun gama nace toh su tu6e kaya in yi musu wanka, ba ku ga irin wulaƙancin da su ka yi min ba, Jamima hada ce min wai ita bazata tu6e kaya inyi mata wanka ba, saboda tsarata ce ita, ban fita da komai ba, daƙyar na samu shi majnun nayi mashi wanka ahaka ma saida ya dinga watsa min kumfa a ido ina wanke wa, ita kuma jamima kusan dambe mu ka yi da ita, taƙi yarda inyi mata wankan, hada cewa sai dai inyi mata da wando a jikinta don kada in gan mata jiki............kasa ƙarasa maganar ta yi idanuwanta cike tab da ƙwalla, sai kace ba ita bace ta gama shan dariya tana bin majnun da gudu ba, ita babban baƙin cikinta, Jamima da take yi mata kallon tsararta, ta raina mata wayau, da ga ita har majunun sun raina azeeza saboda ƙarantarta, duk a tunaninsu tsararsu ce basu san cewa ta girmesu nesa ba kusa ba.
Dariya suka dinga yi mata, musamman parveen da bata jima da farkawa ba, Hada gabriel dake kishingiÉ—e saman gadonshi, farkawarshi kenan yaji azeeza tana kora jawabi.
Ganin yadda su ke ta yi mata dariya yasa ta bubbuga ƙafafuwanta ƙasa, ta zuƙunna tana kuka, Muryar Angel ce ta katse musu dariyar tasu da wani irin kasala take magana da busassun la66anta
"Ku daina mata dariya kuna ƙara 6ata mata rai, Azeeza ki daina kuka, yanzu fa ki ka gama shan dariya, ke kanki sun baki nishaɗi, sai kina yi musu uziri, kinga ke yayarsu ce, su kuma ƙannanki, dole sai ana haƙuri da juna.....' ta kai ƙarshen maganar tare da ɗan juyawa ta kalli jamimah dake ta faman ɗaure fuska tana tsino ƙaramin bakinta.