Sashe 165
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A ranar ina zaune tsakiyar gado, ina ta kuka ina ambaton sunyen ku, ina faɗin ni na gaji amaidani wurin ƴan uwana, idan ba haka ba zan haɗiyi zuciya in mutu, saboda na gaji da maraicin ku gani na ke kamar mutuwa zanyi, Angel shiru babu wanda yazo gare ni, hakan ya ƙara hasala zuciyata, Dama akwai wata ƙaramar wuƙa ta fruit da aka sako min cikin kayan abinci, sai nayi tunanin in ɗauke ta in yi kamar zan kashe kaina wata'ƙil asamu wani yazo gare ni tunda suna ganin komai da na ke yi, na sauko daga saman gadon na ɗauki wuƙar tare da buɗe murya ina faɗin"ko dai su zo su maidani wurin ƴan uwana ko in kashe kaina, kowa ya huta," ina kammala yin maganar Na watsa da gudu na shige toilet ɗin ɗakin naja ƙopa na rufe, ina jiran ganin ko zasu zo gare ni, jin shiru yasa nayi tunanin in ɗan yanka hannuna Jini Ya fito ko sun gani su zo, Ina ƙoƙari ɗaura wuƙar saman hannuna da niyar in yanka, ba zato ba tsammani kunnuwana su ka soma jiyo min takun tafiyar mutun a cikin toilet ɗin, a tsananin tsorace na ɗago don inga wanene ya shigo bayan na rufe ƙopa, Tsabar tsoro Yasa na jefar da wuƙar dake a hannuna Yayin da nake kallon Shi, Giant ne sanye Cikin baƙaƙen Kaya, dogo ne yana da faffaɗan ƙirji sai dai tafiyar shi ta banbanta dana sauran Gaints da su ke kawo mana abinci, kuma shi wannan Yana magana Don har ce min yai yazo ne ya taimake ni ya maidani cikin ƴan uwana idan inaso" cikin shessheƙar kuka nace mashi kada ka cutar dani, idan har dagaske za ka iya taimaka mini, ka nuna min hanyar da zan bi in koma wurin su, ko ka ɗauke ni ka kaini."
Tun da na ambaci hakan sai naji wani irin bacci acikin idanuwana, daga nan ban ƙara sanin me ya faru dani ba, sai dai na farka na ji kin rungume ni.
Ajiyar zuciya Angel ta dinga saukewa, Hankalinta ya kwanta sosai, jin cewa ba su yi mata irin na Unaiza ba, sai dai akwai wani abu da ya É—aure mata kai dangane da labarin da batul ta bata, shin meyasa ita basu yi sex da ita ba kamar yadda su ka yi da Unaiza? Kuma har abinci su ke bata lafiyayye, basu cutar da ita ba ko kaÉ—an, Iya jinin al'adarta ne su ka tsotse, after that Angel ta yi mamakin Giant É—in daya taimaki batul ya dawo da ita cikin su, a iya saninta Giant basa magana, sai dai ko tsakaninsu da manyan su zai iya yiwuwa suna magana, Amma ita Batul Giant É—in ya yi mata magana har ya nemi taimakonta!! lamarin ya É—aure mata kai.
Ta yi zurfi acikin tunaninta, muryar Batul ta katseta da cewa"Rabin raina, Me ki ke tunani ne? Allah yasa labarin dana baki bai É—aga maki hankalin ki ba, dama saida nayi fagabar hakan"
Girgiza kai Angel Ta yi"a'a hankalina bai tashi ba, just na ɗanyi mamakin wasu abubuwa ne, Yanzu dai nuna min Jan tabon da ke a saman ƙirjin ki inaso na gani" da sauri batul ta sanya hannu ta soma nannaɗe ƙasan rigar da ke a jikinta har zuwa saman ƙirjinta, daga ƙasan boobs ɗinta da suka fara tasawa, Angel ta yi tozali da Jan tabon da ke a wurin, kasancewarta fara sosai, fatar wurin ta yi jawur.
"Yana yi maki zafi"? Angel ce ta yi maga tambayar, batul tace"A'a, bana jin zafi," jinjina kai Angel ta yi"zan yi maki addu'a, in tofa maki saman fatar wurin a yanzu, sannan da Anjima kafin mu kwanta zan ƙara yi ma ki, don inaji araina cewa Jan tabon nan ba alkhairi bane, dole akwai wani abu da ya ke nufi" ba tare da 6ata lokaci ba Angel ta karanto addu'o'i tare da tottafa mata saman fatar wurin, bayan ta kammala yin addu'ar ta ɗago su ka kalli juna.
"Allah ya tsare min ke ya kare min ke tare da sauran ƴan uwana daga sharrin waɗannan azzaluman mutanan" fuskar Batul ɗauke da murmushi ta amsa mata da ameen, ruƙo hannunta Angel ta yi acikin nata"taso mu koma Ɗaki, kada ajimu shiru, "
A tare su ka miƙa tare da nufar ƙopar fita daga cikin toilet ɗin, sam ta manta da zancen ainihin abunda ya kawota Cikin toilet ɗin.
Shigar su ɗakin keda wuya, kunnuwan su su ka soma Jiyo masu motsin buɗe ƙopa, ras! gaban su ya faɗi, Azeeza da jamimah jiki na kerma su ka sauko daga saman gadagen su, atare su ka shige ƙarƙashin gado, Hankalin su sarah ba ƙaramin tashi yai ba, Kowan nan su Zuciyar shi ta hau harbawa da ƙarfi da ƙarfi, Deeja da ke kwance saman gadon Haris tuni ta zabura ra miƙe zaune, Gaba ɗaya idanuwansu na akan Matakalar benan, A bakin ƙopar fitowa daga sashen toilet ɗinsu Batul da Angel su ka dakata da yin tafiya Hannunsu ruƙe Cikin Na juna, Kowa Jira ya ke yaga wanene zaya shigo.
Jin takun tafiyar ta yasa hankalin su ya ƙara tashi, A hankali ta ke saukowa daga saman matakalar benan hannunta a ruƙe da sandarta, Kamar kullum Cikin jar shiga ta doguwar riga, Takunkumin da ke akan fuskarta Iya saman tsinin hancinta Ya tsaya, blue eyes ɗin ta, sai ɗaukar ido su ke Yi, Daga bayanta Giants ne masu take mata baya, Majiya ƙarfi dogaye masu ƙirar dakarun Yaƙi, Tuni kowan nan su yasha Jinin jikin shi.
A tsakiyar Ɗakin nasu tsohuwa zafreen Taci burki, tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, Babu wanda yai tunanin ya gaishe ta a cikin su saboda tsoratar da su ka yi, a ƙalla ta ɗauki mintuna tana ƙare masu kallo, kafin ta soma magana da kakkausar murya
"Ba ku Iya gaisuwa bane? Ko jira ku ke yi ni in fara gaishe da ku"? Muryoyin su na rawa su ka soma gaishe da ita, banda mutun ɗaya Angel da su azeeza waɗanda su ka 6oye a ƙarƙashin gado ita da jamamah, sun rungume juna jiki na kerma saboda tsoron da ke gare su.
"Ba haka nake so ku gaisar dani ba, saukowa za ku yi daga saman gadajen ku, Ku russina min," da sauri Sarah dasu hibba da ke zaune saman shimfiɗa su ka miƙe tsaye su Deeja su ka sauko saman gadajensu ita da parveen, a tsananin tsoroce su ka ƙarasa gabanta, Da niyar su zuƙunna mata kamar yarda ta buƙata, muryar Angel ce ta katse su
"Karku kuskura ku russina mata! Ae ita ba Allah bace, banga dalilin da zaisa mu girmama ki ba, because you don't deserve it!"
A firgice su Deeja ke kallon Angel da ta yi maganar cikin ƙwarin gwiwa, tsabar mamaki ne yasa tsohuwa zafreen Saurin wurga ƙwayar idanuwanta kan fuskar Angel tamkar zasu faɗo ƙasa, Tun da take arayuwarta wani mahaluƙi bai ta6a yi mata katsalandan ba kamar yarda Angel ta yi mata ayanzu ɗin nan, Sam ta kasa magana sai kallonta ta ke yi haɗi da jinjina kanta.
Hankalin su Deeja idan yai dubu to ya tashi, muryoyin su na rawa su ka soma ambaton sunan Angel suna bata haƙuri akan ta daina magana karta ja masu bala'e.
Dogon tsoki Angel taja mai sautin gaske, Tare da cewa"Ku ku ke jin tsoronta, Ni bana tsoron kowa sai Allahn da ya halicce ni shi nake tsoro, amma ba wani bawa ba, mai hannu biyu irin nawa mai ƙafafuwa biyu, wanda in mutuwa tazo ɗaukar shi bai isa ya kubce mata ba"! Idanuwan zafreen azazzare ta ke ƙarewa Angel kallo tun daga ƙasa har sama, Giants ɗin da ke a bayanta Har sun yunƙura zasu motsa tsohuwa zafreen ta dakatar da su ta hanyar ɗaga masu hannu.
"Angel dan Allah ki rufa mana asiri, Mu za ki jamawa ki yi shiru ki daina magana, Na roƙe ki badan halin mu ba," Batul ce ta yi mata maganar
Atare su Hibba su ka haɗa baki suna yi mata magiya akan ta yi shiru, ita kanta Angel ɗin ƙarfin haline kawai amma can cikin zuciyarta a tsorace take, sai dai bakinta yaƙi mutuwa, tana ƙoƙarin cigaba da yin magana Batul ta sanya hannu ta toshe mata bakinta, hannu ta sanya tana kiciniyar 6an6are hannayen Batul.
Ido cikin Ido Su ke kallon Juna ita da tsohuwa Zafreen, Abunda wani bai ta6a gigin yi mata ba, ba'ayi mata magana ana kallon Cikin idanuwanta, Yau sai ga wata ƴar ƙaramar cikin prisoners tana yi mata fitsara da rashin kunya akan idonta.
A hankali tsohuwa Zafreen ta ɗaura hannunta ɗa ya saman fuskarta, tare da zame takunkumin da ya rufe fuskarta, Kowa yasha jinin jikin shi, muryarsu na kerma suka zuƙunna saman gwiwowinsu agabanta suna roƙonta akan ta yi haƙuri kada ta cutar masu da Angel ɗin su.
Tuntsirewa tsohuwa zafreen ta yi da dariya tamkar bakinta zai 6are, duk su ka bi su ka ruÉ—e, a lokacin Angel Ta samu damar 6an6are hannun Batul data toshe mata baki da shi, Sai faman haki ta ke yi tana zare ido.
"Well done Unaiserh!" ta ambaci hakan tare da yi mata alamar jinjina da hannunta É—aya.
"Dole in yaba ma ki, saboda Ke ce prisoner ta farko da kika fara gaya mini magana ido cikin ido, ba tare da jin shakkata ba, sannan ke ce mutun na farko da kika fara furta min kalmar cewa ni baiwa ce kamar kowa, sa'an nan baki jin tsoro na" Bazawarin murmushi tsohuwa zafreen tasakar mata, kafin ta ɗaura da cewa"Wuyan ki Ya isa yanka, tun da har kika iya gaya mini magana, Ina jinjina maki, kin kafa tarihi a zuciyar tsohuwa Zafreen" ta ƙarasa maganar fuskarta ɗauke da shu'umin murmushin nan nata mai wuyar fassaruwa.
"Ni bana hukunta mutumin da ya nuna baya jin tsorona, sai dai in ta6a zuciyarshi, ta hanyar cutar da wanda ya mutu akan ƙaunarsa"! ras gaban Angel ya faɗi, Hankalinta Ya tashi, ta zazzaro idanuwanta akan fuskar zafreen, saboda ta fahimci me ta ke nufi, hatta su Deeja sun gane me ta ke nufi, gwiwowin su a sage, su ka mimmiƙe tsaye suna ja da baya, yayin da hawaye ke bin fuskokin su.