← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 179

Sashe 145

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sannu sister, Allah ya baki lafiya" acewar javed, Suma saura suka ƙara yi mata ya jiki, sam ta kasa motsa la66anta donta amsa musu, daƙyar tafara magana kamar ma sambatu ta ke yi musu tana ambaton sunan Danish da batul, miryar deeja ce tasa ta ƙoƙarin buɗe idanuwanta

"Angel ki daure kidaina sanya damuwa aranki, Idan kina yin hakan ba ƙaramin raunata mata zuciyoyin mu kike yi ba, ke da kika saba ƙarfafa mana gwiwa, amma yau kece kike neman zaucewa saboda rashin su, kowa ya jure amma kin gaza, Ya ki ke so muyi"? Idanuwanta acike tab da ƙwalla tayi mata maganar.

Cizon la66a ta ta yi ba tare data iya furta mata komai ba, ruwan hannun Azeeza ya kuma kar6a Ya kuskure mata bakinta dashi, tare da wanke mata fuskarta, Kafin ya miƙa ma Azeeza robar tasa hannu ta kar6a,

"Akwai sauran abinci"? Yai tambayar yana kallon su, har suna hada baki wurin rabka salati suna faÉ—in"Mun manta Bamu É—ebi abincin ba, gashi giants sun tafi dashi" Kamar zasu fashe da kuka.

Chinonsu dake sauraronsu shida jamima, jin suna neman abinci yasa Suka nufi ƙarƙashin gadon Batul atare suka ruƙo hannun kwandon, suka nufo wurinsu, tunkan su ƙaraso Ƴan uwan nasu suka ga uban tulun abincin da suka ajiye musu, Wani irin farin Cikine ya lullu6e su, Ba ƙaramin daɗi su ka ji ba, Bakin parveen washe da annuri tace"Kai ba dai kune ku ka ɗebi abincin nan ba"? Har suna haɗa baki wurin furta"Mune nan muka ajiye shi" with proud su kai maganar, suna ƙarasowa parveen ta kar6i kwandon daga hannunsu ta ruƙe shi, tace da Azeeza ta ɗauko Mayafi da zasu goge aman da Angel tay, ta masa mata da toh, ta juya ta nufi akwatin kayansu kafin ta dawo Gabriel yace ta miƙo ma shi abunda zai fara bata ta ci.

Zura hannu tayi cikin kwandon ta ɗauko meat balls ta miƙa mashi, ya kar6a ya soma bata abaki tana ci, ba ƙaramin daɗin shi su ka ji ba ganin yadda ta zaƙe tana ci.

Dawowa Azeeza tai hannunta ruƙe da ɗan mayafi ta shiga goge mashi aman da Angel ta yi a jikin vest dinsa, da saman laps ɗinsa, bayan ta kammala tace mashi ya curo mata taje ta wanke mashi, murmushi yaɗan saki tare da kallon ta yace"bakya gajiya da yi min wanki Azeeza, kibar shi zan wanke da da kaina" maƙe mashi kafaɗa tai alamar bazata bari ba, yace toh bari na ƙarasa bata abincin, sai na baki rigar,

sai da ya kammala bata ya kwantar da Angel kamar me bacci ta lumshe idanuwanta, hankalinsu ba ƙaramin kwanciya yai ba, Kowa ya nufi gadon shi ya zauna, parveen ta ɗauki kwandon taje ta ajiye musu a ƙarƙashin gado, miƙewa Gabriel yai daga gefen gadonta, Ya tu6e rigar jikin shi ya miƙa ma azeeza tasa hannu ta kar6a, ta nufi toilet shima yabi bayanta don ya watsa ruwa ma jikinsa.

Bacci mai daÉ—i ya É—auki Angel, Su majnun dake shirin yin wasa atsakar É—akinsu, parveen ta lalla6asu akan su yi shiru kada su tada Angel tunda sun ga bata da lafiya, suka amsa mata da toh, Kafin marece yai kowannansu na zaune, wasu sun É—an kishingiÉ—a da niyar bacci ya É—auke su, rabi da kwatansu idanuwansu arufe yake, duk don saboda Angel sunyi tsif babu mai magana, gudun kada su katse mata baccin ta.

💔PRISONERS💔

Kunnuwansu ne suka soma jiyo musu motsin buɗe ɗakin su, Ras gabansu Ya faɗi ba tare da sanin dalilin hakan ba, kusan atare kowannansu Ya buɗe idanuwanshi Hankalinsu gaba ɗaya ya koma Kan staircases ɗin, Jira suke suga waye zai shigo ko wani ne za'a dawo musu dashi tunda an riga an kawo musu abinci, Yadda suke zazzare idanuwansu akan ƙafafuwan masu shigowa tamkar ƙwayar idanuwansu zasu faɗo ƙasa,

Bakowa bace face tsohuwa Zafreen Hannunta ruƙe da sanda cikin shigarta ta jajayen kaya, Rabin fuskarta rufe yake, Iya idanuwanta ne awaje, Hankalin su ba ƙaramin tashi yai ba, Abayanta Wasu Gabza gabzan Giants ne Su biyu garada masu ɗauke da Star 2 agaban baƙar rigar jikinsu, Takun tafiyarsu yadda kasan na wani namun dawa.

Wahalallan yawu kowannansu Ya haɗiya, hakanan suka dinga jin bugun zuciyarsu na hauhawa, Chinonso dake ta tsalle tsalle ganinsu yasa shi yin saurin nufar gadon parveen ya haye ya zauna gefenta hada ɗaura kanshi saman kafaɗar ta, Azeeza kuwa cikin sanɗa ta duro daga saman gadon ta faɗa ƙarƙashinsa ta la6e jikinta nata kerma, ganin ta 6oye yasa jamima lalla6awa itama ta sauko daga saman gadonta, ta shige ƙarƙashi. sauran kuwa ba wanda ya motsa kowa yasha jinin jikinsa.

Lokacin da mai girma tsohuwa Zafreen ta ƙaraso Tsakiyar ɗakin nasu, Sai kowannansu ya sadda kanshi ƙasa ba tare da sun furta komai ba, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, duk sun kame kansu.

"Fatan na same ku lafiya" tai tambayar tana kallon fuskokinsu, wasu daga cikinsu ne suka samu damar amsa mata da cewa"Muna lafiya" tace"tsawon lokaci banzo na duba jikokina ba, saboda uzurirrika da suka yi min yawa, sai yau na samu damar leƙo wa, hope you're happy to see me"

kamar waɗanda aka ma dole haka suka furta mata"eh" Jinjina kai ta ɗanyi yayin da take cigaba da binsu da kallo kafin ta tsayar da idanuwanta akan fuskar haris Ya ɗaure fuskarshi sosai, Idonshi na kallon ƙas

"Zuwan nawa ba lallai bane yayi maku daÉ—i ba, domin kuwa nazo ne na raba ku da zaratan samarin dake a cikin ku" a firgice suka É—ago suna kallonta la66ansu na kerma ba tare da wani ya iya furta wani abu.

"Haris, Mubeen, Naufal, Javed, and Gabriel, A kan ku nake magana, Ba'a ta6a zuwa an ɗauke ku ba, wannan karan kurkukun ƙaddara ya buƙace ku, Don haka ba tare da 6ata lokaci ba, kowannan ku ya sauko daga saman gadon shi, A jere zaku tafi," A matuƙar ruɗe su parveen ke kallonsu, wani iko na Allah babu wanda ya musa acikinsu, Kamar yadda ta basu umarni haka suka sauko a jere suka nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, Sai waiwayon ƴan uwansu suke yi, idanuwan kowannansu cike tab da kwalla kai daga gani bada son ransu suke yin tafiyar ba, Sarrafa su aka yi, Hankalin Deeja idan ya yi duba toh ya tashi, Ba ita kaɗai ba hatta sauran matan da ke acikin su, Gashi sun gaza ɗaga koda yatsan su, Sai hawayen da ke gangarowa ta cikin idanuwansu.

"Albino, Follow their back" tai maganar ba tare da ta juya ta kalli inda chinonso yake zaune gefen parveen, Jikinshi nata kerma ya sauko daga saman gadon idon parveen akanshi, Yana tafiya yana waiwayonta kamar zaiyi tuntu6e, ahaka harya haura saman starcases É—in Yabi bayansu Haris, Tashin hankalin da ba'a sama shi date! Kaf an kwashe mazansu, Cikin su 20 yanzu saura mutun goma sha É—aya, Shin Ina za'a kai su haris?

Tsayar da idanuwanta ta yi akan gadon Angel dake ta sharar bacci, babu alamun zata farka,

"Ba'a san ƙaddarar kurkuku da rauni ba, tana bacci gwanin ban sha'awa, nan badajimawa ba, zamu buƙace ki" Tayi maganar tare da matsawa dab da gadon Angel Ta ɗaura sandarta asaman ƙafarta, Nan take angel tayi wani irin juyi ta fuskanci ceilling ba tare data farka daga baccin ba, A saman ƙirjinta zafreen ta ɗaura sandar hannunta Saitin zuciyarta, Wani irin numfashi Angel ta shiga fitarwa ahargitse, Su Deeja dake kallon abunda ke faruwa kamar su ɗaura hannu aka su fasa ihu, Sai dai kash babu mai iya motsawa a cikinsu, Sai da Angel tagama banƙarewa kamar zata koma zombie, tukunna tsohuwa zafreen ta sauke sandar daga saman ƙirjinta.

💋PRISONERS💋

A hankali ta ɗauke idanuwanta daga kan fuskarta Angel, ta mayar dasu kan fuskokinsu Parveen da suka jiƙe sharkaf da hawaye, La66ansu sai kerma suke yi kamar waɗanda sanyi ya kama.

"Tun da ku ka taso a gidan kurkukun nan ba ku ta6a gabza faɗa a tsakanin ku ba, kullum kuna a cikin farin ciki, ba'a ta6a samun prisoners masu ƴanci irin ku ba, Prison ta gatanta ku, Sai dai kash a dokar gidan kurkukun ƙaddara prisoners basu da ƴan cin kansu, bamu amince ma wani daga cikin ku ya ji daɗin rayuwar shi ba, yakamata ace a yanzu kun yi bankwana da farin ciki, fatan an fahimce ni" tai maganar tana binsu da shu'umin kallo.

kamar ta yi magana da duwatsu, babu wanda ya tanka mata, Wata ƴar iskar dariya zafreen ta saki tare da cewa"Dama na sani ba za ku Iya magana ba, saboda ban baku iznin yin ta ba," Ta ƙarasa maganar tare da juyawa Giants ɗin da ke abayanta suka take mata baya, Tana tafiya Cikin ƙasaita, sai da ta kai bakin matakalar benan ta ɗan dakata da yin tafiyar suma Giants ɗin suka tsaya da yin tafiyar, magana ta soma yi masu ba tare da ta juyo ta kalle su ba.

"Idan ƴar uwar ku ta farka, ku isar min da saƙon gaisuwata agare ta, nabarku lafiya" tana ƙarasa yin maganar tasa kai ta fuce daga cikin ɗakin tare da masu take mata baya.

Fitar su keda Wuya! Sautin rufe ƙopar ya fargar dasu, a firgice su ke kallon kallo a tsakanin su, fuskokin su ɗauke da matsananciyar damuwa, kukan ma yaƙi zuwa masu sai hawayen da ke ta wanke fuskokin su, tsananin tausayin kansu ne ya kama su, wannan wata irin rayuwace suna ji suna gani anyi masu yankar ƙauna An rabasu da ƴan uwansu, babu mai iya magana acikinsu, saboda tsabar takaici da baƙin cikin da su ke ji,

Azeeza da ke la6e ƙarƙashin gado, tasha kuka kamar ranta zai fita, ta ƙanƙame jikinta da ke ta kerma tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, itama jamima tana nan ƙarƙashin gadonta bata motsa ba, ta dai ji duk maganganun da tsohuwa zafreen tayi acikin ɗakin su, sai faman zare idanuwanta ta ke yi.
Chapter 145 · 0% Book details