← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 179

Sashe 53

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga Can Cikin ɗakin kuwa, Hankalin batool yaƙi kwanciyar, tana so taje ta taimaka mata amma zuciyarta taƙi bata haɗin kai, Idan ma tayi motsi kamar zata sauko daga saman gadonta, sai haris ya dakatar da ita tare da cewa"duk wanda ya kuskura yaje da niyar taimakata, babu ruwan mu da shi," tunzurasu yake yi duk don saboda kada suje su taimaki angel

In taƙaice maku zance, A gajarcanshi Har dare yayi babu wanda ya motsa daga Cikin su, Sun bar angel acikin toilet ita kaɗai, tun tana kiran sunayensu har tagaji tadaina, baiwar Allah ta shiga mawuyacin hali, anan cikin cikin toilet ɗin ta kwanta saman floor ɗin, abu uku suka haɗe mata a lokaci ɗaya, Ciwon kai, raɗaɗi da Cikinta ke yi mata da kuma matsiyaciyar yunwar data addabe ta, yinin ranar ko ruwa bata kora ma maƙoshinta ba, ya bushe ƙamas har wani ƙaiƙayin azaba yake yi mata,

Kafin su kwanta bacci, sai da suka cinye abincin angel da batool ta ajiye masu ita da haris, Koda su ka kammala cin abincin, Zaman jiran dawowar Danish Suka tsaya yi, har saida tsohuwa ta fito daga Cikin ɗakinta ta same su a zazzaune saman gadajensu, ganin damuwa akan fuskokinsu yasa tace"Akan danish ne"? Har suna haɗa baki wurin amsa mata da eh, Shiru ta ɗanyi tana kallonsu kafin tace"ku ƙara haƙuri, danish bazai samu damar dawowa yau ba, jikin nashi yayi tsauri sakamon Illar da ƴar uwarku angel tayi mashi, akwai wani dafi a hannunta wanda ku baku sani ba, idan har ta yakushi mutun kota gartsa mashi cizo, ya ɗauki tsawon lokaci ba'a bashi emmergency treatment ba, Dafin yana Illata sassan jikin shi ne, kuskuren da mu kayi shi ne, da bamu yi gaggawar miƙa dashi zuwa treatment room ba, lokacim da Angel tayi mashi wannan jahilin bugun, Shiyasa har Dafin yayi mashi illa ajikinshi........." dakatawa ta yi da yin maganar fuskarta duk a harmutse duk don su yarda da abunda take faɗa masu, Cikin jin ƙunar rai haris yace " idan har ɗan uwanmu ya rasa ranshi saboda ita, bazamu ƙyale ta ba, ita ma sai mun kashe ta" yana rufe baki deeja tace"Ae dama ba son shi take yi ba, muguwa kawai, tun da tazo gidan kurkukun nan, ta ɗaura mashi karan tsana ni bansan me danish ya tsare mata ba, " takai kai karshen maganar tana huci,

Haris Yace" Yadda tayi ma danish Jahilin bugu, muma sai mun rama mashi, In yaso suyi jinyar atare"

Yasmin tace"ƙwarai kuwa, Muje mu same ta har inda take, mu nakaɗa mata bugu har sai ta kasa tashi,"

Tsohuwa ta fakaici idonsu ta saki wani irin kafin murmushi, hanya mafi sauƙi da zata koya ma angel hankali, saboda rashin kunyar da take yi mata,

Cikin sanyin murya batool tace"Bai kamata mu ce zamu bugeta ba, wannan ba dai dai bane, saboda ita ɗin yarinya ce duk mun girmeta, bugu bashi zaisa ta gane kuskurenta ba, idan muka daina shiga sabgarta ma ya wadatar, daga yanzu babu ruwanmu da ita, har sai danish yaji sauƙi ya dawo cikinmu tukunna zamu waiwayeta,"

Azeeza tace"na goyi bayan shawarar da batool ta bada," suma sauran su ka ce duk sun goyi bayanta, banda haris da deeja,

"Tsohuwa yanzu Sai yaushe kenan zamu sake ganin É—an uwanmi? Idanuwanmu sun yi maraicin rashin ganin shi" javed ne yayi maganar muryarshi a sanyaye,

Tsohuwa tace" A yadda mu ka tattauna da giant, Ya sanar dani cewa"Danish zai É—auki Tsawon kwana Biyar Kafin ya dawo cikin ku,"

Ransu ya ƙara 6aci jin cewa sai ya ɗauki tsawon kwana biyar kafin ya samu sauƙi, Kamar su ɗaura hannayensu saman kawunansu su fasa ihu, haka suke ji saboda tsabar takaici, tsanar da su kayi ma angel ta ƙara ninkuwa acikin zuciyarsu,

"Kowa ya je ya kwanta, Mu kwana lafiya Yara na" takai ƙarshen maganar tare da juyawa tana dogara sanda Ta nufi ɗakinta, ta shige tare da jan ƙopa ta datse,

Kallonsu batool tayi"Mu yi haƙuri muje mu kwanta," gyaɗa kai su kayi kowa Ya wuce zuwa saman gadon shi Ya kwanta,

Gaba ɗaya duk tattaunawar da su batool su kayi tare da tsohuwa akan kunnan angel, baiwar Allah da rarrafe ta fito daga Cikin toilet, ɗin abakin ƙopar shiga ɗakinsu, Ta zauna tare da jingina bayanta, saboda takasa ƙarasa tafiya cikin ɗakin, Kaf taji irin ƙalin sharrin da tsohuwa tayi mata, sai yanzu ta gane dalilin dayasa suka juya mata ba, Lokacin ta take ta kiransu acikin toilet don su kawo mata agaji, ashe sun jita suka ƙi zuwa, saboda tuggun da tsohuwa ta ƙulla mata,

Jikinta duk yayi sanyi, zuciyarta ta karaya, Don sun É—auki gaba da ita wannan ba damuwarta bace, ta yi masu uziri saboda jahilcin dake É—awainiya dasu, ita tausayinsu ma take ji, yadda ake ta juya masu tunaninsu, wanda da ace suna da wayau babu wanda ya isa yayi masu haka,

Abu uku ne yafi tsaya mata arai, na farko shine Batool, bata ta6a tsammanin batool zata Juya mata baya ba, Tunanowa tayi da maganarsu ta jiya da kanta take faɗa mata cewa"Koda ace kowa zai juya mata, Ita tana atare da ita, kuma a koda yaushe zata kasance a hannun damanta, amma sai gashi yau ba irin kiran sunan batool da batayi ba aka tazo ta taimake ta amma taƙi zuwa, Abu na Biyu kuwa meyasa tsohuwa take Yi masu ƘARYA? da girmanta tsofe tsofe da ita? ƙaryafa alamace dake nuna cewa mutun baida gaskiya, lallai wannan matar ba ƙaramar makira bace, abu na ƙarshe daya tsaya mata aranta shi ne DANISH! A wani hali yake ciki? Meke faruwa da shi? meyasa baza'a dawo da shi cikinsu ba? Jiyafa tsohuwa da kanta tace masu yau zai dawo, amma kuma yau sai gashi ta canza magana, meyasa❓❓❓

Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta,

A hankali ta kifa kanta saman gwiwowinta, yalwatacciyar sumar kanta ta yi mata rumfa tamkar hijabi, shessheƙar kuka taci gaba da yi ita kanɗai a cikin toilet area, tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, gaba ɗaya ta tsani Gidan Kurkukun ƙaddara, A yanzu bata ƙi ta samu hanyar da zata gudu daga Cikin shi ba koda kuwa ita kaɗai ce, tunda ta lura Yaran da take son taimaka ma rayuwarsu, Zaiyi wuya taci galaba akansu, saboda already an juye masu tunaninsu,

Dare yayi sosai, duhu ya mamaye Cikin idanuwanta, ƙasa ƙasa da murya take ambaton sunan daddynta, wata magana ce ta faɗo mata acikin ranta wanda daddynta ne ya ta6a faɗa mata ita

_Ki sama ranki cewa ko babu ni zaki iya rayuwa, nasan cewa ƴata jaruma ce, mutane suna yabonki saboda ƙwarin gwiwar dake gare ki, Angel bana so rashina yayi silar canzawarki_ a lokacin da taj yayi mata wannan maganar saita fashe da kuka tana faɗin"Nidai daddy kada kayi mun maganar mutuwa bana so," murmushi taj yayi idanuwanshi cike tab da kwalla yace"daughter mutuwa dole ce, ni dai kawai alƙawarin da nake so kiyi mini, shi ne, ki kasance a yadda kike ko bayan raina, kada ki bari wani abu ya canzaki, kada kiyi tunanin idan kika rasa ni xaki rasa gatanki, Domin kuwa Allah yana atare dake, kuma shine gatan kowani bawa, idan kika shiga hali na ƙunci Allah zaki kaima kukanki, In sha Allah zaki samu mafita_

Sosai angel ta fashe da kuka tunawa da wannan maganar ta mahaifinta, wani irin yanayi ta shiga mara misaltuwa, kusan raba dare Tayi acikin toilet area É—insu, batare da ta motsa ba Jikinta duk yayi tsami babu daÉ—i, ga kaÉ—aici dake damunta, ga yunwa da ciwon da take fama dashi duk ita kaÉ—ai,

Ɗagowa ta yi da fuskarta wadda ta kumbura suntum tayi jawur, Tsinin hancinta yayi Ja, saboda matsar daya sha, Idanuwanta sun kumbura sun ƙanƙance, daƙyar take iya buɗe su, dogayen yatsun Hannayenta sai kerma suke Yi, wani irin matsanancin sanyi ne ya mamaye Jikinta, ta ko'ina babu sauƙi,

Daƙyar ta samu ta lalla6a Jikinta, Ta buɗe kofar da rarrafe Ta shiga Cikin ɗakin, tana tafiya tana kallon gadajensu duk sun kwanta sun lullu6e da bargo, hankalinsu kwance sai sharar bacci suke yi, adai dai bakin gadonta, Ta yunƙura ta miƙe ta haye sama ta kwanta, ta janyo bargo ta ƙudundune jikinta,

Acikin Ƴan kwanakin Nan angel ta fuskanci Mawuyacin Hali, saboda juya mata bayan da su kayi, Haris Ya samu damar fanshe haushin shi akanta saboda sunga bata da ƙoshin lafiya, wani sabon wulaƙancin, Sai haris yaga tana bacci, Ya je toilet ya Ciko bokiti da ruwa ya sheƙa mata ajikinta, Idan aka kawo masu abinci tana bacci, babu me tashinta daga Bacci, Haɗuwa suke su cinye mata abincinta, Sai da ta jera kwana Uku bata Ci abinci ba, Ta rame ta ƙanjame, Ta zama abun tausayi, ko magana daƙyar take iya furtata, yanzu takai ga ita ke ji shakkarsu, saboda Rashin lafiyar da take ɗawainiya da ita, bata son abunda suke Yi mata, duk Cikinsu mutun uku ne basu ta6a yi mata wulakanci ba, Batool Azeeza da Javed, basu atare da ita amma kuma ko kallon banza bai ta6a haɗa su da ita ba, kawai dai sun janye jikinsu daga nata ne, ita kanta angel ta lura da wani abu agame dasu, Sam wani abun bada son ransu suke yi ba, kamar ana tunzurasu ne, Shiyasa take Yi masu uziri, Duk wani plan ɗinta a yanzu ya tarwatse, Saboda juya mata bayan da su ka yi, Yanzu takaiga Ko sunan Allah da suke fadi sun daina, taya zata fahimtar dasu Cewa Akwai wanda ya halicce su, Bayan Sun ƙureta akan sai ta Kira masu Allah yazo sun ganshi tukunna zasuyi Imani dashi? Wa'iyazubillahi, Tsohuwa ta gama da rayuwar bayin Allahn nan, suna A cikin duhun jahilci, zaiyi wuya ta shawo kansu Cikin sauƙi, Saboda tsanarta da su kayi ayanzu tafi sha'awar zama Cikin toilet, akan ta zauna Cikin ɗakinsu suna yi mata gal6anci da rashin wayau ba, Sun kasa banbance tsakanin gaskiya da ƙarya, Duk da ba laifin su bane,

*Boss Bature🌷✍️*

Runtse idanuwanta ta É—anyi tare da buÉ—e su, ita kaÉ—ai zaune Cikin duhu, Ta gaza runtsawa,
Chapter 53 · 0% Book details