← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 179

Sashe 108

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kwana atashi ba wuya wurin Allah, Yau tsawon Sati biyu kenan ba'a dawo musu da batool ba, babu ita babu alamarta, Kullum sai sun sanya ran zasu ga an shigo da ita amma sai suji shiru, hatta sababbin prisoners da suke tsammanin za'a kawo musu har yau ba azo dasu ba, rashin dawo musu da batool yafi komai ɗaga musu da hankali, ganin sun sanya damuwa sosai yasa angel ta faɗa musu maganar da suka ta6a yi ita da batool, a inda take ce mata, tana so su haɗa hannu wurin sama ma junan su farin Ciki koda kuwa babu wani acikinsu, wannan maganar tayi matuƙar karya musu zuciya, domin kuwa ranar da angel ta faɗa musu ita, kusan kwana su ka yi a zaune suna jimamin rashin ta, sunyi matuƙar yin kewar ƴan uwarsu fiye da tunanin mai tunani, a ƙarshe da suka rasa abunyi sai suka koma suna biye ma angel, atare da ita suka zuwa toilet wurin tukunyar fulawar nan don suga awani hali batool take aciki, tun da ta basu labarin Abunda danish ya faɗa mata na cewa batool ɗinsu ce a jikin Jan furen nan shi kuma koren Na daddynta ne, abun ka ga masu ƙarancin hankali ga kuma ƙuruciyar dake ɗawainiya dasu duk sai suka yarda da zancen danish, a rana sau uku suke zuwa wurin furannin nan domin su basu ruwa, da safe da rana da daddare, wani lokacin har tsakar dare suna zuwa duba furen suga a wani yanayi yake, idan suka samu furen batool yana tsastsafo da ruwa ajikinshi, haka zasu zauna sunata kuka suna lallashin furen amatsayin batool suna yi mashi magiya akan yayi haƙuri ya daina kuka, Suna atare dashi, Idan kuma suka samu furen ya kwanta cikin ƙasar dake a ruƙe dashi, sai su yi ta jin daɗi suna faɗin batool bacci take yi, kada su takura mata su tafi su barta ta huta, duk wannan haukan da suke yi danish yana kallonsu, Ya rasa gane wani irin kaine dasu, shi yayi abu don ya faranta ma angel rai, su kuma sun ɗauka dagaske ne, gashi har suna ƙoƙarin zautar da kansu akan furennin bogi.

A kowace rana idan dare yai kafin su kwanta bacci sai sunyi ma batool addu'a Akan Allah ya kare musu ita aduk inda take, tsawon kwanakin nan sunƙi sakewa da Danish suna atare dashi ne, badan sun yarda dashi ba, musamman angel ko kallo bai haɗa ta da shi, bawan Allah duk ya shiga damuwa daurewa kawai yake yi, amma rashin tanka mashi da take yi ba ƙaramin illata zuciyarshi take yi ba, yanzu takai ga ko wasa suke yi da zarar ya tsoma baki, to zata zame hannunta ne tace ta fasa, ƙiri ƙiri ta guje shi ta maida shi abokin gabanta, a ƙarshe daya gaji da irin wulaƙancin da take yi mishi, aikuwa ya janye jikin shi daga gare ta, Ya nisanta kanshi da duk wani abu da zai haɗa shi da ita, hakan ba ƙaramin takurata yai ba, itafa tafi son yai ta binta tana yakice shi, sai gashi reshe na neman ya juye da mujiya.

*PRISONERS❤*

A wata rana suna kwakkwance saman sabbin gadajen da suka gaje na baƙin prisoners sai sharar baccinsu suke yi, babu wanda ya farka acikin su, Gari tuni Ya jima da wayewa, A wannan lokacin ne motsun buɗe dakin tsohuwa Ya karaɗe Cikin ɗakin, A hankali ta buɗe ƙopar Hannunta ruƙe da sanda kamar kullum, fuskarta babu walwala, tsufanta ya fito sosai, jikinta na sanye Cikin rigar ta, Ta gado Launin Ja, Cigaba da dogara sandar tayi yayin da take tun karar Cikin dakin, Tayi mamakin ganinsu kwance saman sabbin gadajen da aka kawo maimakon ta gansu A saman nasu beds ɗin, Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, a fili tace"Zaman Prison yayi maku daɗi Jikokina, Kuna hutawarku Cikin walwala, Sai dai kun manta da Tsohuwa Tamira,"

Sai da tabi kowani gado ɗaya bayan ɗaya tana binsu da kallo, tun daga kan gadon haris da deeja, zuwa nasu Javed da rubina, a bakin gadon da angel take kwance ta ɗan dakata tana kallonta, ganin wani irin sabon salon kwanciya, ta wawware ƙafafuwanta, har sun sauko daga ƙasan gadon, gashin kanta duk ya tarwatse ya barbazo saman mattress ɗinta, fuskar tsohuwa asake tace"Unaisah mutuniyata sarkin tsiwa Ina matuƙar yinki," tana ambaton hakan taɗan ja da baya kaɗan, ta daddage ta buga sandar hannunta a ƙasa, Nan take ta bada wani irin sauti kamar fashewar bomb, agigice suka farka suna faman zazzare idanuwansu, saboda tsabar ruɗu parveen da rubina suka sauko daga saman gadajensu, Da gudun gaske suka nufi toilet zasu shige su 6oye, azeeza da tafi kowa jin tsoro tuni ta jima da shigewa ƙarƙashin gadonta, tsohuwa ta rikitar dasu, babu wanda ya lura da ita, sai da suka gama tsorata, Tukunna Ta soma Yi musu gyaran murya, Nan fa Hankalin kowa Ya dawo kanta, sai faman mutsustsuka idanuwansu suke yi, Na cikin toilet da suka 6oye sai gasu sun fito hannunsu ruƙe cikin na juna, azeeza ta leƙo daga ƙarƙashin gado don ta ga wanene yai musu gyaran murya tana yin tozali da fuskar tsohuwa sai gata ta fito tana faman sauke ajiyar zuciya,

Da alama ta nishaɗantu da abunda ta yi musu, Sai tiƙar dariya take Yi, su kuwa sai faman sauke ajiyar zuciya suke yi hada masu dafe ƙirjinsu, hanna tace"Tsohuwa kin bamu tsoro, ƙiris ya rage in saki fitsari a wando,"

Dakatawa ta ɗanyi da yin dariyar da take yi, Ta dago tana kallonsu tace" Naji daɗin ganin ku cikin ƙoshin lafiya, Ina fata baku da wata damuwa"? Tai tambayar tana jiran amsarsu, atare suka haɗa baki wurin cewa"Ƴar uwarmu batool ba a dawo mana da ita ba, almost 2 weeks kenan, bamu san awani hali take ciki ba," shiru tsohuwa ta ɗanyi na wani lokaci kafin tace"ku ƙara haƙuri idan da rabon za'a dawo da ita, to za ku ganta ne, amma abunda nake so daku, ku daina sanya damuwa aranku" tsohuwa na rufe baki muryar Danish ta ratsa kunnanta,

"Long time, ba mu ganki ba, kin daina zuwa wurin mu" Murmushi tayi tare da nuna shi da sandar hannunta tace"Shikaɗai ya damu dani, dama nasan babu wanda zaiyi kewata acikin ku idan bashi ɗin ba, maimakon da kuka ganni ku tambayeni lafiya na ɗauki tsawon lokaci banzo wurinku ba, amma babu wanda yae tunanin hakan," ta karasa maganar tana kwa6e fuskarta, hada jefa musu harara tana murguɗa musu baki, gaba ɗaya suka kama tiƙar dariya ganin yadda take murmura idanuwanta yadda kasan na gwaggwon buri, da alama yau wasa tazo tayi musu,

"Kodan bani da amfani awurinku ne shiyasa kuka ƙi damuwa da rashina" shiru suka ɗanyi, angel dai tana zaune ta jingina bayanta jikin bango,

Haris ne yai ƙoƙarin cewa"taya za'ae mu ƙi yin kewarki tsohuwa? ae munji daɗin irin taimakon da kika yi ma deeja, gashi ta samu sauƙi sosai ta wartsake," yakai karshen maganar tare da ɗan juyawa yana kallon deeja dake zaune gefen gadonta dake kusa da nashi, muryarta aɗan disashe tace"Nima inata so inyi maki godiya amma ban samu damar ganin ki ba, ranar da aka ɗauki batool, azeeza ta sume muka rasa ya zamuyi da ita, mun yayyafa mata ruwa ajikinta amma bata farka ba, Har ƙopar ɗakinki muka ƙwanƙwasa don kizo ki duba jikinta baki buɗe ba, shiyasa muka yi tsammanin ko baki nan ne,"

Jinjina kai ta ɗanyi tare da cewa"Hakane na ɗanyi nisan kiwo, Yanzu ma zuwa nayi don In duba ku ko akwai wani abu da kuke buƙata kafin in tafi" Basu fahimci me take nufi ba

"Mu ba abunda muke buƙata, Batool kawai muke so a dawo mana da ita" acewarsu parveen,

Tsohuwa tace"zata dawo ne, yanzu dai ku faÉ—a mini me ku ke so kafin in tafi, inji idan zan Iya yi maku shi"

Ta6e baki angel tai tare da cewa"kamar dagaske, nasan ko mun nemi taimako awurinki bazaki Iya yi mana shi ba" Kallonta tsohuwa tay, kafin tace"Me ki ke so Unaisah"? Yadda tayi maganar ba bu wasa akan fuskarta,

"Ki nuna mana hanyar da zamu fita daga Cikin kurkukun nan" shi ne abunda muke so" maimakon tsohuwa ta bata amsa saita fashe da dariya tana ɗan girgiza kai, daga bisani da ta tsagaita da yin dariyar tace"Kin buƙaci abunda bazan Iya yi maku shi ba, saboda yafi ƙarfina, Abunda nake so ki fahimta shine, Ni bakowa bace a gidan kurkukun nan, tun ban mallaki hankalina ba nake acikinsa, tsawon shekara da shekaru na rayu acikin kurkukun nan a matsayin prisoner kamar dai ku din nan, Nima tun ina ƙarama na taso acikinsa, Na jure duk wata gwagwarmayar dake acikinsa kafin na kawo wannan matsayin da nake dashi acikin kurkukun, ba lallai bane ku yarda dani ba, amma zan fada muku gaskiyata, Ni ban ta6a fita daga Cikinsa ba, Anan aka haifeni anan na rayu acikinsa nayi aure har na hayayyafa, akwai ya'yana da jikokina acikin kurkukun nan suna rayuwa". Tunda ta soma kora musu jawabi, angel take binta da wani irin kallon rainin wayau har sai da takai ƙarshen maganarta, sannan angel ta soma magana

"Idan har dagaske bakisan Hanyar fita daga Cikin kurkukun nan ba, to taya akai kikasan tarihin rayuwata? Kinsan komai agame dani, bayan haka ke da kanki kika faɗa mini cewa Mashine ko mota bazasu ta6a Iya kawo mutun Cikin kurkukun nan ba, kenan ƙarya kike yi mini"?

Dogon numfashi tsohuwa taja kafin tace"banyi maki ƙarya ba, tabbas hakane, Duk da bana fita daga cikinsa amma ina iya sanin meke wakana awajen kurkukun nan," lamarin yayi matuƙar ɗaurema angel kai, Wannan wata irin baƙar ƙaddarace? Kenan itama tsohuwa tun tana kamarsu ta ke rayuwa agidan kurkuku matsayin prisoner? Itama batasan kowa nata ba? anya kuwa zata Yadda da maganarta? Kafin angel tayi yunƙurin ƙara tambayarta wani abu, muryar naufal ta katse mata hanzarinta,

"Tsohuwa mun ga canji sosai, ga sabbin gadaje an kawo ga kuma akwatuna guda biyu, bayan haka kuma acikin toilets É—inmu an zuba kayan amfani acikinsu, mun yi mamakin ganin sauye sauyen nan, kamar zamu dawwama acikin farin ciki ne "
Chapter 108 · 0% Book details