← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 179

Sashe 2

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsiyace suka kwararo da gudu cikin dajin da ya shigo da motar, ai ko da jin sautin shigowarsu, bai san lokacin da ya fisgi ƙafarsa ba, ya ɗago da ita daga jikin ƙarfen, jini ya dinga kwaranya. A haka ya dinga jan ƙafar har ya karaso daidai wani uban rami mai zurfi wanda kasansa tafkeken ruwa ne ke gudana, tsayawa ya yi zuciyarsa na raya masa cewar ya jefar da Angel cikin ruwan, ya ƙwammace ta mutu a cikin ruwan da ta yi mutuwar wulakanta a hannun mutanen da suka biyo su, don babu ɗigon imani a kansu, in suka kama mutun fetur suke zazzaga masa su ƙona shi har lahira. Ya yi zurfi a cikin tunanin Angel sai kuka take yi, sautin motocin miyagun da suka biyo shi ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa, Allah Sarki yana ji yana gani haka ya ɗaga Angel sama ya yi wurgi da ita, tsulundum ta faɗa cikin tafkeken ruwan mai zurfin gaske yana jiyo sautin kururuwarta.

Ba ƙaramin tashin hankali ba ne zai sa uba ya yi silar mutuwar ɗiyarsa.

Saboda tsabar kuka jikinsa har jijjiga yake yi, duk ya ji ya tsani kansa. Don tuni ya fitar da rai da rayuwa a cikin duniyar nan, domin kuwa Angel tamkar numfashi take a gare shi, jiki a mace ya zube saman guiwowinsa a gaban ramin wani irin jiri ne ya soma kwasar shi, nan take ya yanke jiki ya faÉ—i a mace.

A daidai lokacin suka ƙaraso da motocinsu, bayan sun yi parking sun kewaye shi, wasu gabza-gabzan samari ne suka fito, ƙirar Samudawa, baƙake wulik! Babu ɗigon imani a kan fuskokinsu, sun yi shigar bakaken kaya da alama bodyguards ne, a tare suka buɗe wa iyayen gidan nasu murfin motocin don su fito.

Abin ban mamaki, manyan mutanane dattawa, suna sanye cikin shiga ta mutunci wato shigar Hausawa, shadda har da malun-malun kai ka ce mutanen arziƙi ne. Koda fitowar su, ba su dora idonsu a kan komai ba sai a kan gawar Taj dake yashe cikin ciyayi.

Guntun tsaki É—aya daga cikinsu ya ja, "Mala'ika ya riga mu É—aukar ransa, ba haka na so ba."

Na gefensa ya ce, "Ban so ya yi salahar mutuwa irin wannan ba, amma duk da haka ba mu makaro ba, tun a nan za mu fara azabtar da shi kafin mu mika shi hannun Munkar da Nakir."

Tuntsirewa suka yi da wata irin mahaukaciyar dariya, lokaci guda kuma suka ɗaure fuskokinsu. Ɗaya daga cikin manyan mutanen ne ya juya tare da kallan ɗaya daga cikin miyagun da suka zo da su, cike da ba da umarni ya ce, "Miƙo mini galon ɗin fetur tare da lighter." A hanzarce wanda ya yi wa magana ya nufi motocinsu.

"Maganin masu kunnen kashi ke nan, an gaya musu shiga gonarmu abu ne mai sauƙi." Bai kai ƙarshen maganar ba, aka miƙo masa galon din fetur yasa hannu ya kar6a, cire murfin ya yi tare da zazzage masa fetur ɗin a jikin rigarsa, sharkaf suka wanke shi.
Dalilin da yasa za mu ƙona shi, saboda gudun mu bar wata hujja da zai sa a zarge mu.

Ba su ƙyasta lighter ɗin ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna ya ƙyasta ya jefe saman ciyayin dake a kewaye da shi. Da gudu wutar ta shiga cinye ciyayin har ta hau saman jikinsa. A lokacin sun shige cikin motocinsu, da gudu suka fisge su tare da barin cikin dajin. Cikin ƙanƙanin lokaci, wutar tacinye shi ƙurmus

*Boss Bature ✍️*

dedicated to Aunty kubra😘

*E2*

_Kamar yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata'ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al'ummar Annabi ba.✍️_

GargarÉ—i

_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!👌_

The Begining Of The Story,(Farkon Labari)

ƙasa ƙasa Cikin baccinsa ya soma Jin sautin kukan Jariri acikin kunnuwan shi, tun abun bai damun shi har kukan Ya fara addabar shi, ya hana shi sakat wanda Hakan Yayi silar farkawar shi daga bacci, a hankali ya ɗan ware manyan idanuwan shi masu ɗauke da Bacci don da alama bai gaji da baccin ba, Ceilling Ya ƙurawa ido kamar mai karanto wani abu, a ƙoƙarin shi naya tariyo abunda kunnuwanshi ke jiyo mashi wanda Yayi silar farkawar sa daga Bacci,

Yana ƙoƙarin tunanowa Kwatsam Yaji kukan Jaririn Inya inya, mai sautin gaske, Zumbur ya ƙarasa Janye Blacket ɗin daya Lullu6a dashi Yayi wurgi dashi gefe ɗaya, kayan Bacci ne Ajikinshi Brown Colour Riga da wando, yayi mamakin ganin babu ita asaman gadon, ko ina taje ne? sauko da ƙafafun shi ya yi ƙasa ya yi, Cike da fargaba Ya miƙe yana mai tunanin Inda aka samu Kukan Jariri Acikin Gidansa, Shi dai A iya sanin shi Matar shi bata haihu ba,duk da cikinta nata yakai wata tara,

Gaba ɗaya ya ruɗe Yama rasa Ta ina zai ga Jinjirin dake kuka, Domin kuwa sautin ya karaɗe Ɗakin nashi,zukunnawa Ya yi tare da leƙa ƙarƙashin gado, wayam baiga komai ba miƙe wa ya yi da sauri ya nufi wardrobe Ya buɗe ya zazzago da kayan dake acikinta, duk a ƙoƙarin shi naya gano inda aka samu kukan Jariri aɗakinsa, Tuni ya haɗa uban gumi ajikinshi, aran shi harya fara tunanin kodai Aljanune!? abu kamar wasa idan jaririn yayi kuka sai ya lafa ƙasa ƙasa,wannan karan Yanayin kukan tamkar Ana zare Ranshi ne, har wani jan kukan akeyi inyaaaaaaa,

"Ka duba toilet"?zuciyar shi ce tayi mashi tambayar, shiru ya É—anyi kamar me tunanin wani abu,tun da yake arayuwar shi wani abu bai ta6a tsorata shi ba irin na yau, kukan jaririn duk ya firgitar da shi,har wani gumi ya haÉ—a,

Ja da baya da baya yayi a hanzar ce Ya juya gaban Faskeken Madubin É—akin, Wayar shi ya É—auko yana dannawa Call logs Ya shiga, missed calls Ya tarar Na Uzair, babban amininsa

Calling Layin yayi tana fara ringing, uzair ya É—aga kiran ko sallama baiyi ba ya soma magana"Uzair Akwai matsala Cikin gidan nan fa!" muryarshi na kerma yayi maganar,

On the other hand Uzair yace"Wata irin matsala kenan?
  "Kukan jariri ne Ya tashe ni daga bacci,Bansan a ina aka samo kukan ba, kuma na tashi banga benazir ba"

"Ka kwantar da hankalin ka, Gani nan zuwa"
  "Yawwa,dan Allah kayi sauri" rejecting call ɗin yayi kafin Ya ajiye wayar saman bedside drawer,

Walking Slowly Ya nufi hanyar toilet ɗin Cike da fargabar abunda zai taras, cikin sanɗa yake yin tafiyar, jikinshi na kerma,a hankali ya ruƙe Handle ɗin ƙopar ya buɗeta

  Haɗadɗen toilet ne Ko'ina Na Cikinshi Fari ƙal atsaftace ba ƙazanta, kamar ance Ya kalli ƙasan tiles,Ba zato ba tsammani Yaga ɗigon jini, Gaban shi ne Yayi wani irin mugun bugu ji kake daram! a firgice Ya ɗago da idanuwan shi yana kallon Cikin toilet ɗin,Wani irin tsoro ne Ya kama shi lokacin daya hango Jikin Bathtub(kwamin wanka) jaga jaga da Jini kamar an yanka ɗan akuya, a ruɗe ya soma ambaton Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un, kamkar a mafarki yake kallon Lamarin, Cike da fargaba ya ƙarasa shiga cikin toilet ɗin don ya gane wa idanuwanshi, a dai dai bakin kwamin wankan Ya tsara turus, Yana Kallon Jinjirin dake Acikinsa kwance,duk jini Ya wanke jikinshi Sai tsanyara kuka Yake yi,
   Lokaci guda gabanshi Ya faɗi rass tunawa da wasu maganganu da suka tsaya mashi aranshi tun shekaran jiya
 
  Tuni ya karaya hakan na nufin a daren Jiya ta haihu acikin toilet, saboda ƙarfin hali irin nata har ta iya haihuwa da kanta ta kuma Gudu duk da irin Jinin da ta Zubar, abun yayi mugun ɗaure mashi kai, ga wani irin ƙunci da yake Ji acan ƙasan Zuciyarshi, Tuni hawaye sun wanke fuskarshi, sam bazai juri ganin jaririn shi a cikin mawuyacin hali ba, sosai ya fashe da kuka tare da kai hannayenshi cikin bathtub ɗin Ya ɗauko Jaririn, bai damu da kayanshi su 6ace ba ahaka ya ƙanƙameshi ajikinshi yana shar6ar hawaye,

"Taj!taj!! muryar amininsa ce da alama sun shigo cikin gidan, Atare suka faɗo Cikin ɗakin nashi a fujajen, Su Biyu ne shida Matarshi wadda ke sanye Cikin Jallabiya baƙa, Ta yafa mayafi akanta, farace tass doguwa,Shi kuma Uxair din, Jallabiyace ajikinshi brown color

Shigarsu keda Wuya Sai gashi Ya fito rungume da jaririn a ƙirjinshi,

AruÉ—e suke kallonshi, murya na kerma Aneelarh tace"Ta haihu ne"?
Tunkafin ta rufe baki Uzair ya kar6e da cewa"Meya ke faruwane taj?wannan Jaririn fa?Kodai ta sauka ne"?
  Daƙyar ya iya daidaita natsuwarshi ya soma magana"Ita ce tabar mun shi, nima bansan meya faru ba, kawai naji kukan jariri, shine ma Ya tashe ni daga bacci,a toilet na sameshi cikin bathtub"
  Atare suka haɗa baki suna salati, Kafin Aneelarh ta kar6i Jinjirin Tabi ta gefenshi ta nufi toilet don ta gyara mashi jikinshi,

Uzair kuma Yaja Hannun Taj suka fito falo, tsayawa Sukayi suna fuskantar Juna, ran kowannan su a6ace,
  "Amma dai matar nan anyi ƴar akuya, dama can Ni bata kwantamun araina ba, In banda daƙiƙanci taya laifin ka zai shafi abunda ke cikinta"?
Chapter 2 · 0% Book details