← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 179

Sashe 155

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kanta batul ɗin saida ta ɗan murmusa, a hankali ta yunƙura ta miƙe, itama azeeza ta miƙe zaune saman mattress ɗin, Saukowa ta yi daga saman gadon taci gaba da tafiya tana bin ɗakin nasu da kallo, ganin irin sauye sauyen da a ka yi mashi, gaba ɗaya suka bi bayanta suna tafiya atare da ita, dakatawa tayi da yin tafiyar tare da juyowa ta kallesu tace"Jiya na tambaye ku amma ba ku bani amsa ba, ina Danish dasu haris su ke ne"? Deeja ce tai ƙarfin halin faɗa mata cewa anzo an tafi dasu almost one week, An riga tafiya da Danish," iya abunda ta sanar da ita kenan, bata faɗa mata awani hali aka tafi da shi ba, jinjina kanta ta yi ba tare da tace komai ba, sai dai fuskarta ta nuna alamun damuwa, kuma idanuwanta hawaye ne acike dasu.

"An kawo mana sabbin prisoners ne? Jiya kamar naso inga wata ƙaramar yarinya," tai tambayar tana kallonsu "naga kuma sabbin gadaje, kusan goma sha biyar" yasmin ce ta bata amsa dacewa"Eh, bayan tafiyarki aka kawo su, Amma mutun biyar ne prisoners ɗin, sai dai daga cikinsu Giants sun tafi da mutun uku, yanzu biyune atare damu. jamimah itace ƙaramar sai Sarah," ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa"ku bani labari mana, dame dame ya faru bayan bana nan"? A taƙaice Angel ta sanar da ita duk wani abu da ya faru bayan bata nan sai dai bata faɗa mata wanda zai sanyata damuwa ba.

"Mu koma mu zauna batul," yasmin ce tai mata maganar, ganin sai yawo su ke yi cikin ɗakin, ga shi daga gani jikin nata babu ƙwari, ga ƴar guntuwar rigar dake a jikinta sai ɗagewa ta ke yi.

"Kina jin yunwa" parveen ce tai mata tambayar, ɗaga mata kai ta yi alamar eh, langwa6e kai parveen"wayyo Allah, ga shi babu abinci sai giants sun kawo mana" ƴar dariya Batul ta saki kafin tace"Ki kwantar da hankalin ki, kallon ku da na ke yasa naji na ƙoshi, babu wani yunwa atare dani,"

"Batul baki bamu labarin ina aka kai ki ba tsawon wata uku? Sannan waye ya dawo mana dake ko giant ne, mun ga kin canza mana sosai, kin rame kamar babu ƙoshin lafiya atare da ke" rubina ce tayi maganar,

Shiru ta É—anyi kamar bazata amsa mata tambayoyin ta ba, duk su ka tsareta da ido suna kallonta, tun kafin ta fara magana Angel ta raya aranta cewa batul baza ta faÉ—a masu gaskiyar abunda ya faru da ita ba, ko dan kada ta sanya su damuwa.

A tsanake ta soma magana"bakomai ne zan iya tunawa ba, tun time da aka tafi dani, na dai san ba a cutar dani ba, ramar da ku ka gani a jikina bata komai bace face rashin ku atare dani, na tsinci kaina acikin wani É—aki ina rayuwa ni kaÉ—ai, ban rasa ci da sha ba, ana kawo min lafiyayyen abinci, ina yin wanka har ma in kwanta in yi bacci, mafi yawancin lokutta, ina yawan yin kukan rashin ku, in dinga ihu ina ambaton sunayen ku don kuzo ku É—auke ni sai dai shiru babu mai jina........." iya abinda ta faÉ—a masu kenan, kuma sun yarda da maganarta, banda Angel, don koda tana basu labarin idonta akan Angel don tasan bazata yarda da ita ba, abunda yasa su deeja suka yarda da labarin da ta basu, saboda an dawo masu da ita ba kamar yarda aka saba dawowa dasu ba, Cikin mawuyacin hali, wasu ma basa a cikin hayyacin su.

"Batul yakamata kije ki yi wanka, akwai sabbin kaya da muka fada maki tsohuwa tamira ta bamu zamu ɗauko maki naki ki sanya, sannan muna so zamu gyara maki gashin kan ki" fuskarta ɗauke da murmushi tace masu toh, Eve tace"wai ina Uniform ɗin ki su ke ne? Ya akai aka sanya maki wannan guntuwar rigar launin Ja"? Muryarta da en ina tace"am..in..nima bansani ba, bansan waye ya canza min ita ba, kawai rana ɗaya na farka na ganni da ita a jikina" wani irin kallo Angel take binta dashi, kallon ban yarda da maganar ki ba, sai faman wurwurga ƙwayar idanuwanta ta ke yi, da zarar sun haɗa ido da Angel saita kawar da kanta gefe.

Ganin hakan yasa Angel ta ruƙo hannunta a cikin nata sosai ta damƙe shi tare da cewa"Muje na taimaka maki kiyi wankan" da sauri ta girgiza kai tare da cewa"Zan iya Angel, ki bari zanje nayi da kaina" a ruɗe tayi maganar, hakan ya ƙara tabbatar ma Angel abunda ta ke hasashe akanta, ta 6oye masu abunda ya faru da ita.

GyaÉ—a kai Angel tayi"Its ok, amma mu fara shiga toilet É—in, mu wanke maki kanki, In yaso daga bisani saimu fito mu barki ki yi wankan" muryarta adarare ta amsa mata da toh.

Mutun uku ne suka haɗu wurin wanke mata gashin kanta saboda yawanshi, Angel da Hanna sai Seeja, Sosai suka murje gashin kan nata, Bayan sun kammala wanke mata kan, suka barta cikin toilet din don tayi wanka, Angel fa jikinta duk ya yi sanyi, a ƙagare take da su samu damar da zasu ke6e da ita don suyi magana, sai dai ga dukkan alamu ita batul ɗin bata son su yi magana, shiyasa take kakkauce mata, Bayan wasu ƴan mintuna, Batul ta fito daga wakan, dama tun kafin fitowarta Angel ta ɗauko mata sabbin kayanta, ba tare da 6ata lokaci ba, ta zura uniform din a jikinta, Masha Allah, zayyana irin kyan da batul tayi a cikin kayan nata 6ata baki ne, abunka ga fara sol, Sun ƙara fiddo mata da kyanta, don ma ta ɗanyi rama.

daga ciki ta sanya red vest dinta, sama ta É—aura wrap coat dinta, kafin ta sanya black trouser din, Angel ce ta taimaka mata wurin É—aure igiyar coat É—in, ta É—aura mata Cotton scarves É—inta saman wuyanta, Bayan ta kammala gyara mata su tsaf a jikinta.

Su Parveen sai santin kyanta su ke yi, Hannu biyu angel ta sanya wurin janyota a jikinta, sosai ta rungumeta, tana ɗan bubbuga bayanta, in a low voice ta furta mata"Ina son magana da ke, amma na lura kamar baki so why"? Muryarta na ɗan rawa tace"Angel, banason tuna abunda ya faru dani, pls kada ki matsa min kada ki tambaye ni komai, na roƙe ki, kuma bana so hakan ya 6ata maki rai" suna yin maganar ne ba tare da sun raba jikinsu daga na juna ba.

"Shikenan batul, bazan tambaye ki ba, ni kaina bana son na takura maki, zan jira ki har zuwa time da kika ji zaki iya sanar dani sai ki faÉ—a min" ta amsa mata da toh," Deeja dake ta kallonsu manne da juna ta fahimci cewa magana su ke yi, bayan sun raba jikinsu, ta dinga bin su azeeza tana rungume su a jikinta tana faÉ—a masu irin kewarsu da ta yi, Deeja kuma taja hannun Angel su ka koma gefe É—aya,

Tambayarta ta yi me suka tattauna da batul, ta sanar da ita cewa ta tambaye ta ne game da abunda ya faru da ita amma bata faɗa mata komai ba, Deeja tace"kada mu takura mata, tunda ta nuna bata son mu sani, mu ƙyale ta kawai, wata kil hakan zaifi mana kwanciyar hankali," Angel ta gamsu da maganar deeja.

Badajimawa ba, Giants suka kawo masu lafiyayyan abinci, Saboda tsabar ƙauna, a baki suka dinga ba batul tana ci, sunƙi bari ta sanya hannunta taci, hakan ba ƙaramin karya mata zuciya yayi ba, tabbas an zalunce ta da aka raba ta da ƴan uwanta, amma yanzu Alhamdulillah tunda gata a cikinsu, da ranta da lafiyarta.

Bayan sun kammala Cin abincin, Giants suka tattara Farantan suka tafi dasu, A saman shimfidar sarah, suka zazzauna suna fira tare da batul, Angel tana zuƙunne gaban akwatinansu, Ta buɗe ta ɗauko Nail cutter da nail filler tare da madubi, ta dawo ta miƙe ma Sarah tace gashi ta gyara ma ƴar uwarsu akaifa, Murmushi sarah tasaki, tare da sanya hannu ta kar6a, Kafin su fara gyaran akaifar, Angel tace ta ɗan dakata, tana so su kalli faces ɗinsu a cikin madubi, ita da ƴar uwarta batul, Gefen batul ta zauna tare da ɗaga madubin, Ta haɗa fuskokinsu wuri ɗaya, Suka natsu suna kallon juna, hakanan Angel ta dinga jin faɗuwar gaba a yayin da take kallon fuskar batul ta cikin mirror, su azeeza sai faman leƙo da fuskokinsu suke yi suna kallon su.

"An ta6a faÉ—a maku cewa, Kuna bala'en kama da juna" Sarah ce tai maganar, parveen tace"wlh kuwa nima saida ki ka yi maganar nan tukunna na lura da hakan, Angel da batul suna kama sosai, musamman ta wurin shape É—in bakinsu, duk da ba launi É—aya bane, da kuma hasken fatarsu, gashin kansu ma Ya yi shige, hatta tsawonsu iri É—aya,"

Deeja tace"ae hatta Yatsun hannuwansu dana ƙafafuwansu iri ɗaya ne sak babu bambanci, najima da sanin wannan ban ta6a faɗi bane" sarah tace"to kodai ƴan gida ɗaya ne"? Girgiza kai Yasmin tai tare da cewa"A labarin da Angel ta bamu, ita kaɗaice Awurin daddynta, mommynta ma, tun tana yarinya ta gudu tabarta, bata da ƴar uwa mace tun da ta taso a rayuwarta,"

Sarah tace"hmmm adai yi shiru kawai amma fa ni akwai abunda nake zargi, ina da wata baiwa da ku ba ku sani ba, tun kasancewa ta a prison, nake wannan hasashen, nasha ganin masu kama da juna wanda su basu lura da hakan ba, sai dai ina tunanin zaman tare ne yasa muke kamanceceniya da juna, yanzu a cikin ku nan, kaf ɗinku Naga kamanceceniya atsakaninku da junan ku, Hatta wannan yarinyar da aka kawo mu tare da ita, Me take da suna....." Eve ce ta ƙarasa mata maganar da cewa"Kina nufin Ƴar gidan daddy" jinjina kai tayi "eh ita nake nufi, akwai kamanceceniyarta da wani acikin ku, amma bazan faɗi ba" tana ƴar dariya ta yi maganar,

"Ko kina nufin azeeza? Don kinga kalar gashinsu yayi shige da launin fatarsu," girgiza kai tayi"a'a, ba azeeza ba, bana so na faÉ—i maku ne"
Chapter 155 · 0% Book details