← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 179

Sashe 30

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 6 min read

*UAE*

HaÉ—aÉ—diyar Daular Larabawa

Abu dhabi,

Alhaji Ubaid ne zaune A cikin Hamshaƙin falon gidansa, Wanda yaji Hadaddun furniture tsadaddun gaske, ga wani sanyin A.c dake ratsa sassan Jikin mutun,
Ya ɗau wankan Shadda, Ya hakimce saman 3 seater, Hannun shi na ruƙe da jarida, A gaban shi table ne mai ɗauke da mug na coffee,
Ya natsu yana Karanta Jaridar, kamar daga sama yaji An fisgeta, kafin ya É—ago ya kalli wanda ya kwaci jaridar daga hannun shi, tuni tayi tearing É—inta into pieces,
Bakowa bace face Laila, Mahaifiyar Benazir, doguwar balarabiya tasha wankan Abaya launin royal blue, yalwataccen gashin kanta har tsakiyar bayanta, Ƙafafunta na sanye da High heels,
Zuba mata ido yayi batare daya ce mata ƙala ba,
"Idan har zaka cigaba da kallon waɗannan gantalallun Ni kuma bazan gaji da yage duk wata jarida da zaka kawo A cikin gidan nan ba, tunda na lura bakasan ciwon kanka ba, Menene alaƙarka da su? Ga ƴarka ta cikin ka da ta 6ata shekara da shekaru Baka damu da ita ba, sai wasu can rainon talauci," rai a6ace takai ƙarshen maganar, tare da juyawa ta nufi bedroom ɗinta, Sai gata ta dawo hannunta ruƙe da newspaper me ɗauke da sunan khaleej times, ta wurga mashi saman fuskar shi"Ita ce jaridar dana amince maka ka karanta, tun da karantun jaridar ya zamar maka dole"
Hannu yasa ya janye jaridar daga saman fuskar shi, still idonshi na akan fuskarta,
"Mutanan da kika kira da gantalallu, Sunfi ki daraja da ƙima a idona, dake da ƴar taki, Saboda bakusan ciwon kanku ba, in banda rashin ɗa'a, da rashin sanin darajar miji har kin isa Ina karanta abu kinzo ki fisge ki yayyaga, Haka aka koya maki tarbiya a gidan ku,"?
Wuri ta samu saman Sofa ta zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, batare da tace mashi ƙala ba,
Sai da ta mula tasha iska tukunna tace"bansan meke damunka, duk kabi ka sanya damuwa kan wasu kucakai, ga wadda take jinin ka, Amma sam Baka damu da ita ba,"
Murmushin takaici yasaki kafin yace" Benzir don son ranta ta gudu kuma tana a raye tunda har ta iya ta turo mun saƙo a duk lokacin da taga dama, Su kuwa waɗannan bayin Allahn, Rana ɗaya aka neme su aka rasa, Har yau babu labari a kansu, taya bazan damu da su ba? Jikata ɗaya da nake da ita kwallin kwal, Narasa ta, ƙaramar yarinyar da bata mallaki hankalin ta ba, Wayasan a wani hali suke ciki"?
Ta6e baki Laila tayi"Laifinsu ne ae, kasan ƴan jarida da kafiya, ga shegen naci da bin ƙwaƙƙwafi, acan wurin neman labari suka tsokano abunda yafi ƙarfinsu gayanan ae yanzu wa gari ya waya,"? Yadda tayi maganar ko ajikinta,
Girgiza kai Alhaji ubaid yayi yayin da yake kallonta"Hada jikarki fa a cikinsu,"
"Jikarka dai, Ni ban haɗa komai da su ba, Auran benzir da yaron nan ƙaddara ce, kai ka sani nesa ba kusa ba, benazir tafi ƙarfin shi, Ni nayi tunanin ma ɗan Abdallan ne shima ashe ɗan wani faƙirin mutunne dake zaune a karkara....." rai a6ace Alhaji ubaid ya dakatar da ita"Cin mutuncin ya isa haka, Kuma ki iya bakin ki, mutumin da kike kira fakiri a yanzu haka baya a raye ya riga mu gidan gaskiya, ke wai baki tsoron Allah? Mace har mace ba kyan hali, silar ki ga shi nan duk narasa ya'yana saboda gur6ata masu tarbiyar da kike yi,"
Murmushi tasaki tana kallon shi,"Nifa komai zaka faÉ—i akaina bazan ta6a jin haushi ba, Ga Coffee É—inka nan Yana huce wa yakamata ka sha" tayi maganar tana nuna mashi Mug É—in dake ajiye saman table,
Banza yayi da ita batare daya furta mata komai ba,
Kashe murya tayi tare da cewa"Habibi fushi ka ke da Nooril ƙalbin taka"? Dariya taga ya saki kamar wani zautacce, mamaki ya kamata, ta ƙura mashi ido tana kallon shi,
Wayar shi dake ajiye saman sofa hand ta soma ringing,
Hannu ya miƙa ya ɗauki wayar tare da miƙe wa, still da dariya akan fuskarshi ya fuce daga Cikin gidan,
Girgiza kai lailah tayi"ɗan siyasa kenan, Jibi yadda ya mayar dani shashasha, Ina tunanin na harzuƙa shi ga shi nan ya fuce yana yi mun dariya wato nice mahaukaciyar, Allah ya kyauta, Ni ya dawo ma muyi magana ta fahimta, Tunda ciwon ƙafar ta shi yayi sauƙi, zan tunzura shi ya nemi takarar shugaban ƙasa, Wannan shi ne burin da nake da shi,' takai ƙarshen maganar tare da kwalawa mai aikinta Zainab kira, da sauri ta fito daga Cikin kitchen ta nufe ta, Balarabiya ce a ƙalla takai shekara arba'en, jikinta na sanye da kayan aiki,
Cikin harshen labaraci tace"ki sanar ma Sauran maids É—in Gobe A shirya Abinci kala kala na gargajiya dana zamani, Dr Shureim zai kawo mana ziyara daga egypt"
Jinjina kai zainab tayi cikin ladabi ta amsa mata da"Toh, in sha Allah za'a shirya komai, Allah ya kawo shi lafiya,"
Laila ta amsa mata "ameen"
Bayan fitar Alhaji Ubaid, A entry hall na gidan ya tsaya ya amsa Kiran da akayi ma shi daga gida Nigeria, Yana waya idonshi na akan Masu aikin gidanshi, dake ta aikace aikacansu,
"Ka kwantar da hankalin ka, Lokaci kawai nake jira, Ina nan ina shirye shirye dawowa Nigeria, Siyasa fa yanzu muka sanya ƙafa ba gudu baja da baya, Namiji da jarumta aka sanshi bada ragwanci ba, Wannan karan babbar kujera nake hari, Zanyi duk iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin Na siye zuciyar Dattijon nan, Kona samu ya sanya mun albarka Cikin lamurrana,"
On the other hand muryar Babban mutumin Da yake waya da shi ce ta soma bayyana" Da kamar wuya fa, kasan halin shi Kaifi É—aya ne, wani irin bauÉ—aÉ—É—an mutunne abunda ya yi niya shi yake aiwatarwa, Amma zamu yi kokarin shawo kanshi, Ko dan muyi nasara akan abunda muke son Cimmawa, yanzu dai dawowarka Nigeria shiya fi komai mahimmanci,"
"zan dawo In sha Allah, Kodan saboda Yaran nan da suka 6ace, Sunan ina zaune ne a Ƙasar nan amma tunanina gaba ɗaya yana a nigeria, nadamu da su," fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa yakai ƙarshen maganar, abokin nashi da suke waya yace"Wai har yansu babu labarin su? Ae ni da naji shiru nayi tunanin an same su ne," muryarshi da alamun mamaki
"kusan shekara biyu fa kenan babu su babu alamarsu, Ni tsorona ma kada ace abokan hamayyata ne suka Farmake su, kasan mutanan nan ba imani ne da su ba, Komai zasu iya aikatawa indai akan siyasar su ce,"
Jajanta ma shi abokin na shi ya yi, da ga haka su kayi ma Juna Sallama, Har ya juya zai koma Cikin falon, Yaji ƙarar shigowar mota, juyawa yayi yana kallon Motar da ta shigo, Danƙareriya mota mai numfashi, da alama Baki ya yi,
Bodyguard ne Ya fita daga Driver seat na motar, Ya zagaya ya buɗe mashi mota, Wata irin dariya Alhaji ubaid ya saki lokacin da yayi tozali da Alhaji badamasi, Mataimakinsa Lokacin da yana gomna a jihar jos, da sauri ya nufe shi yana faɗin"Marhaban bika Mutumina, Irin wannan zuwan bazata haka, Yaushe ka shigo ƙasar" Alhaji badamasi sai faman washe baki yake yi, yayi shigar larabawa, Ga wani ƙamshi dake fita a jikinshi,
Rungume juna su kayi kamar zasu haÉ—iye juna, A tsaitsaye suka fara gaisawa kafin Suka Nufi Cikin garden É—in gidan, A waya ya kira lailah yace Ayi ma mai aiki magana ta kawo masu kayan marmari su sha, A garden a kayi masu ShimfiÉ—a Saman Lallausar darduma suka zauna domin tattaunawa a tsakanin su,

Shin Ya rayuwar Angel ta kasance bayan An sace ta Cikin Mota?
Chapter 30 · 0% Book details