← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 179

Sashe 15

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read

sai da yabi komai asannu tukunna ya samu Tafara sabawa da kwana a ɗakinta, yanzu da kanta take yin wanka ta sanya kaya har ma tayi kwalliya, har lokacin angel batasan an bata gift din piano da Kayan zane ba, Saboda ya 6oyesu Laptop kaɗai ya bata, wayar kuma da aka bata shi yaci gaba da amfani da ita, don bazai bari ta ruƙe waya ba, Saboda wayon dake gareta, kuma zata iya ɗauke mata hankalinta daga yin karatu,

Acikin waÉ—annan kwanakin taj yaso yaje buzaye wurin Dangin shi, Amma Uzair ya dakatar da shi, Akan ya bari Su uncle su dawo Nigeria, in ya so sai su É—unguma su tafi a tare, ba don yaso ba Ya amince ma shi,

Tuni angel ta kammala primary school ɗinta a yanzu haka tana a Jss 3 Sunyi Exam na first term, tunda suka samu hutu ba inda take zuwa Kullum tana gida bata zuwa ko'ina, taj Ya damƙa mata Piano ɗinta, Idan ta zauna ta soma yi masu kiɗa ko gajiya ba ta yi, Sai in Lokacin Karatunta ya yi ko sallah take tashi, sam ya hanata Yin kallo In ba cartoon ba, Shima cartoon ɗin Sai ya tabbatar Baida wani abu da zai 6ata mashi yarinya tukunna yake barinta ta kalla, Ya sanya mata ido sosai, duk wani motsinta a tafin hannun shi, idan zai tafi wurin aiki, Gidan su Aneelerh yake turata, koda basa nan mai aikin gidansu Ana tana nan, A wurinta take zama kafin su dawo

Wannan kenan,

a gajiye ya ke driving a daidai bakin gate, ya soma dannawa mai gadi hon, Da hanzari baba mai gadi Ya fito daga ɗakinsa, ya buɗe ma shi gate ya shigo da motar Jikin gidan, Fitowa daga Cikin motar ya yi, Jikin shi na sanye da Shadda green Colour ba ƙaramin kyau tayi ma shi ba, Sai daya fara tsayawa suka gaisa da baba maigadi tukunna Ya nufi Cikin gidan,

Tunda yayi sallama a palour Yaji shiru ba'a amsa mashi ba, ran shi ya ba shi cewar Ko bata dawo gida bane, yanke shawarar zuwa bedroom ɗinta Yayi, walking slowly Ya nufi stairs ɗin ya haye, a tsanake ya ke tattaka steps ɗin benan harya samu Ya haye sama, Kaitsaye Ya nufi inda ɗakinta yake, Da sallama a bakin shi ya tura ƙopar ɗakin, Yana shiga idanuwanshi suka sauka akan gadon, wayam baiganta ba, Hakan na nufin bata dawo ba, tana agidansu aneelerh, Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da juyawa zai bar ɗakin, Karaf idanuwan shi suka sauka akan Zanen fuskar shi da angel ta yi a jikin bangon ɗakinta, Cike da mamaki Yaci burki tare da nufar Bangon yana kallon Zanunnukan da ta yi, da kuma rubuce rubucen da ta yi duk a jikin bangon,

Motsa lips É—insa ya soma yi yana karanta abunda ta rubuta a jikin bangon

_To my biggest hero_

_There's no better role model than you,_
_There's no one I'd rather look up to than you._
_I'm so proud to be your daughter_
_You're my one and only dad, and you'll always have a special place in my heart._
_Dad, you've made all my favorite memories._
_Dad, you've always been my hero._
_I'm so lucky to have your love and guidance in my life_

ya ma rasa mi zai ce lokacin daya kammala karanta Rubuce rubucen da ta yi ma shi, Wani irin tsantsar farin Cikine Ya bayyana akan Fuskar shi, Tuni hawaye su ka wanke ma shi fuskar shi, slowly ya zube saman gwiwowinsa, a yayin da hawayen ke cigaba da bin kuncin shi, kalamanta ba ƙaramin faranta ma shi rai su ka yi ba, maimakon Ya ji haushin 6ata bangon ɗakin da tayi sai ma yaji ya ƙara sonta a cikin zuciyar shi,

Haƙiƙa angel ta ba shi mamaki, ta san ya shi farin Cikin da bazai ta6a mantawa ba,

Da sauri Ya juya ya kalli ƙopar ɗakin Jin motsin mutun, Bakowa bace face angel
Jikinta na sanye da jallabiya, daidai tsayinta, Tayi rolling mayafi akanta,

"Daddy sannu da dawowa Nayi missing ɗinka sosai" ta ambaci hakan fuskarta ɗauke da murmu shi, buɗe mata hannayen shi ya yi alamar tazo gare shi, da gudu ta ƙarasa ta faɗa saman faffaɗan kirjin shi, Ya sanya dukkan hannayenshi Ya rungumeta sosai, Yana faɗin"kin sani farin Cikin da bazan ta6a mantawa ba angel, I luv u so much, bansan da wasu kalmomi zanyi amfani wurin bayyana maki irin ƙaunar da nake yi maki, Allah yabarnmin ke angel, Allah ya kare mun ke daga sharrin maƙiya da mahassada, Allah ya yi maki albarka"
Amsa ma shi tadinga yi da ameen daddy, kusan mintuna goma suna manne da juna, batare daya raba jikin shi daga nata ba, wani irin yanayi yake ji attare da shi, sam baya son yana tuna mutuwa, Saboda yasan ita kaɗaice zata Iya raba shi da angel, ko yana so ko bai so, dolene bayan ita kuma sai wata ƙaddarar rayuwar wadda baya fata,

ÆŠagowa tayi daga Jikin shi ta sanya hannu tana goge mashi tears É—in dake sauka akan fuskar shi"daddy kadaina pls, banason ganin hawayen ka na zuba"

Kallonta ya yi da runannun idanuwan shi waÉ—anda su ka yi jawur da su, sam ya kasa furta mata komai,

Huggin ɗinshi ta ƙarayi tana shafa sumar kanshi, bacci ya soma Ji hakan yasa shi miƙewa Ya lalla6a ya haye saman gadonta, ya kwanta duk da ya yi mashi ƙanƙanta,

Gefen gadon ta zauna tana kallon shi, jikinta duk ya yi sanyi tace"daddy baka lafiya"?

Eyes É—inshi arufe yace"kinci abinci"?

"Naci a wurin aunty aneelerh, Ko inje in kar6o maka naka" girgiza mata kai yayi"a'a,Bana jin yunwa, kizo mu kwanta muyi bacci"

Ƙarasa hawa saman gadon ta yi a gefen shi ta kwanta, Ya sanya hannu ya janyo ta jikin shi, Cikin ƙankanin lokaci bacci yayi awon gaba da su,

Wuraren ƙarfe 4 ya farka daga Baccin, Lokacin a nata kiraye kirayen sallar la'asar, saukowa daga saman gadon yai tare da nufar toilet ɗin ɗakin ta Ya shiga ciki,

After some minutes ya fito yana share ruwan alwalar dake a fuskarshi, Kafin ya nufi inda angel take a kwance tana bacci,

Cikin sanyin murya ya soma kiran sunanta"My angel!"shiru bata motsa ba, hannu yasa tare da ɗan bubbuga ƙafarta, nan take ta farka tana mutsu mutsun bude idanuwanta,

"Lokacin Sallah yayi, Ki ta shi kije ki yi alwala, ni zan tafi masallaci"

Muryarta a disashe tace mashi"a dawo lpy daddy,"

Bayan tafiyar shi, ta sauko daga saman gadon ta shiga toilet,

Jim kaÉ—an tafito É—aure da alwala, ta É—auko carpet ta shimfiÉ—a, Ta zura hijab ajikinta a tsanake ta soma Yin sallah,

Lokacin data idar da sallar zama tayi saman dardumar tana karatun alqur'ani mai girma daga cikin kanta,

Tana cikin yin qira'ar, Ya dawo daga masallaci, murmushi yasaki Yayin da ya ke shigowa Cikin ɗakin, Ba ƙaramin daɗi yake ji ba aduk lokacin daya sameta, Saman darduma tana Yin sallah ko tana yin karatun al'qur'ani mai girma,

Sai da takai ƙarshen ayar da ta janyo tukunna ta juyo ta kalleshi"daddy sannu da dawowo"

"Yawwa daughter, Kin daiyi mana addu'a ko"? jinjina mashi kai tayi"eh,Ae kullum sai nayi"
"Haka nakeson ji, My daughter"

Shiru ya É—anyi kafin Yace"Zamu fita tare da daddy uzair É—inki, Zaki zauna a gida ko In kai ki wurin aneelerh"?

"Daddy bazaka tafi dani ba" aÉ—an shagwa6e tayi maganar,
"Am sorry, Ba cikin gari bane bazan iya yin tafiya mai nisa dake ba,"

Tuni idonta sun Ciko tab da kwalla sam bataso yana tafiya yana barinta a gida, musamman yanzu da babu school, islamiyace kaÉ—ai yau kuma Alhamis ne basa zuwa da juma'a,

"Dan Allah daddy......."tunkafin ta ƙarasa yayi saurin katse mata hanzarinta"yi mun shiru nace maki ba cikin gari bane,"

Shiru tayi Ƴar kwallar da take 6oyewa ta soma gangarowa akan fuskarta,

Ƙarasawa Yayi tare da sanya hannayen shi gaba ɗaya ya ɗauketa, yana ɗan bubbuga bayanta"Idan kikayi mun kuka Allah zan fasa zuwa buzaye dake ne"
Cikin shessheƙar tace"bazanyi ba"
"Haka nakeson ji my angel"
Sauke ta ƙasa ya yi tare da ruƙo hanunta, suka fito daga ɗakin ya ja ƙofar ta rufe, Kaitsaye suka nufi gidansu aneelerh, lokacin da suka shiga falon gidan a tsaye suka gansu shida Aneelerh, Ya kammala shirin shi cikin boyel, aneelerh kuma na sanye cikin Turkish dress, Riga da wando blue, ta ɗaure kanta da mayafin kayan.

Gaisawa suka fara yi da aneelerh kafin Ya damƙa mata angel,

Batare da 6ata lokaci ba, su ka yi mata sallama atare a cikin motar Uzair suka tafi,

Saman Sofa suka zauna ita da aneeleerh,
"Kina jin yunwa"? É—aga mata kai tayi alamar eh,
"Hawayen menene akan fuskarki"?tayi tambayar tana kallon fuskarta,
"Daddy inata roƙon shi ya tafi dani amma ya ƙiya"
Murmushi aneelerh tayi"Shine kike kuka? idan ki ka yi haƙuri ae ba kwana zasuyi ba," ta ambaci hakan tare da miƙewa ta nufi kitchen,

Kishingiɗawa angel tayi tana jiran dawowarta, fitowa aneelerh tayi daga Cikin kitchen ɗin hannunta ɗauke da plate, mai ɗauke da farfesun naman Kaza, da alama ba'ajima da kammalashi ba, don sai huci ke tashi ga ƙamshi,

A saman table ta É—aura plate É—in,tare da samun wuri gefen angel ta zauna,
Chapter 15 · 0% Book details