← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 179

Sashe 134

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read

A washe garin ranar da safe, suna ta sharar bacci, wasu sun jingina bayansu jikin bango wasu kuma sun ɗaura kawunansu saman cinyoyin ƴan uwansu, Waɗan da suka kwana asaman gadonsu, mazan ne duka sai Jamima da azeeza, Cikin sa'a Gabriel ya riga Danish farkawa daga bacci, Ae yana buɗe ido ya hango Danish baje saman gadon shi, yai wuff ya duro daga nashi gadon Cikin sanɗa ya nufi bakin gadon unaiza inda suke zazzaune suna bacci, A hankali ya zuƙunna inda angel ta jingina bayanta jikin bango, hanna ta ɗaura kanta saman laps ɗinta, haka su kai bacci jiya, saitin kunnanta yakai bakin shi cikin raɗa ya shiga kwala mata kira "Angel! Angel" har cikin dodon kunnanta, ganin tana ƙoƙarin buɗe idanuwanta yasa shi yin sauyin ɗaura tafin hannun shi saman bakin ta, gudun kada ta razana ta saki ƙara Danish ya farka, tsantsar mamaki ne ya kamata ganin Gabriel, Zuƙunne agabanta, hada ƙoƙarin toshe mata baki, zazzare mishi idanuwanta ta soma yi, tare da kai hannu zata ka6e mishi nashi hannun daya toshe mata baki.

Da sauri yace"ina son magana dake, tun jiya, bana so kowa ya sani, pls ki bani haɗin kai, ki taso mu shiga sashen toilet ɗin mu" yana ƙare maganar ya zame hannun shi daga saman bakinta, Ya miƙe cikin sanɗa ya nufi 6angaren toilet ɗinsu, yana tafiya yana waiwayon shimfiɗar Danish, wata irin kasalace ta baibaye Jikinta, A hankali takai hannu ta ɗauke kan Hanna daga saman laps ɗinta ta kwantar da ita ƙasa, kafin ta miƙe ta bi bayan Gabriel, tana shiga sashen toilet ɗin ta same shi atsaye ya jingina bayan shi jikin bango.

Yana ganinta yai saurin ruƙo hannayenta biyu acikin nashi, kamar wani mara gaskiya, yana magana yana kallon bakin ƙopar shigowa sashen toilet ɗin, Nan take ta fahimci cewa akwai wanda baya son yaji abunda zai faɗa mata.

"Tun jiya nake son na yi magana dake amma É—an uwanki ya hanani sakat, na rasa gane dalilin dayasa baya son na tunkare ki"

"You mean Danish"? ÆŠaga mata kai yai alamar eh"

Tace mai ka ke son faÉ—a min ne"? Har ya buÉ—e ba ki zai yi magana ya ji ta yi saurin katse shi da cewa"Oh wai kana magana akan Unaiza da aka tafi da ita jiya? Nasan ka tsorata da ganin an É—auke ta, bawani abu zasu yi mata ba, za'a kai ta treatment room ne aduba lafiyar jikinta" tun da angel tai wannan maganar nan take Gabriel ya fahimci cewa DANISH yazo wurin, shiyasa tai saurin tarar numfashi shi, Saboda ita ta hango shi, kamar walkiya, ko yaushe ya tashi daga bacci.

ta wutsiyar ido Ya hango shi tsaye bakin ƙopar shigowa wurin ya goya hannayen shi saman ƙirjin shi, ya kafe su da ido.

Yatsina fuska Gabriel ye ba tare daya kalli fuskar Danish ɗin ba, yaji takaicin bayyanar shi, ɗan hana ruwa gudu, sauƙin ma Angel ta gan shi da baisan me zai biyo baya ba, idan ya faɗa mata ya shiga cikin kurkukun.

"Zan shiga toilet in yi wanka, yakamata kaima ka shiga ka yi" tana magana kamar batasan da zaman Danish a wurin ba, Ta juya ta nufi toilet ta buɗe ta shiga, duk akan idon Danish, Shima Gabriel ya nufi ɗayan toilet ɗin ya shiga Ciki, Ya datse ƙopa.

Sun so ace ya koma cikin ɗaki amma yaƙi tafiya, kowannan su sai da yae wanka time da suka fito daga cikin toilet ɗin, Yadda suka barshi haka suka same shi, Gabriel bai tanka mishi ba ya wuce ɗaki, Angel ce ta tsaya tana kallon shi fuskarta ɗauke da murmushi tace"ya ka ke? Fatan ka tashi lafiya"?

Wani irin kallo taga yanayi mata, kamar ba zai amsa mata ba, muryarshi da alamun kasala ya amabaci sunanta

"Angel, na tashi lafiya, ina fata kema haka" matsawa tai kusa dashi, jikinta da lemar ruwan wankan da tayi, Tace"jiya nashiga damuwa da aka tafi da unaiza, banma san time da bacci ya ɗauke ni ba, zuciyata ba daɗi" ta ƙarasa maganar kamar zata fashe da kuka, Ruƙo hannunta yae acikin nashi, ya ɗan janyota kusa dashi,

"Fuskarki harta kumbura, yakamata ki koma kiyi bacci, ko kin samu relief," girgiza mishi kai ta yi "a'a, baccin ya ishe ni, zan jira abinci ne, ka shiga toilet ka yi wanka zan jira ka anan"

(Angel sarkin wayau, tana so ne ya shiga don ta samu damar yin magana da Gabriel, ta ƙagara amatse take da taji me zai faɗa mata)

Maƙe mata kafaɗa Danish yai tare da cewa"Bana buƙatar yin wankan, mu koma ɗaki mu zauna, mu jira abinci nima yunwa nake ji," kallon shi kawai ta ke yi, wato ta fahimci wani abu agame da Danish, shegen wayau ne dashi, mutun sai yana da kaifin basira zai iya gane hakan.

"Dan Allah ka shiga ka yi wanka, inaso ne kaima ka ji irin daÉ—in da naji ajikina, idan ka kammala sai mu koma É—aki,"

kamar maroƙiya haka tadinga yi mishi magiya akan yaje yae wanka, hada bubbuga mishi ƙafa da shagwa6a, sai taga ya saki ƙayataccen murmushi akan fuskar shi, ta yi tsammanin zai amince ne hakan yasata sakin murmushi tace"Ka amince zaka shiga ka yi wankan"? Ɗaga mata gira yai tare da cewa"Eh amma atare zamu shiga, sai kiyi min, idan har baki amince mun shiga atare ba, to ki daina roƙona akan yin wanka don ba inda zanje INA ATARE DA KE!" takaici ne ya isheta

A ƙule tace "ai ni nayi wanka akan me zan bi ka mu koma toilet"? Tai maganar tana gatsina mishi hanci, yace"nasan kinyi ae, ni zaki yi mawa yanzu" tsoki taja tare da bi ta gefen shi ta wuce cikin dakin, Ya juya yabi bayanta, Suna shiga Ciki suka sami Gabriel zaune gefen gadonshi ya zabga uban tagumi, Takaicin Danish ne ya ishe shi, sam baya son aja tsawon lokaci ba tare da yayi gaggawar sanar da angel game da yarinyar nan ba, zata iya rasa ranta.

Saman gado Danish ya zauna, angel kuma ta nufi akwatin kayansu, ta ɗauko red vest ɗinta, tare da dogon wandonta baki, Ta nufi sashen toilet dinsu ta shiga, acan ta canza kayan jikinta, ta cire tsaffin ta maida sabon, Vest ɗin tabi jikinta ba ƙaramin kyau ta yi mata ba, duƙunƙune tsohon uniform din ta yi a hannunta.

Bata fito ba, sai ta tsaya tana leƙen Cikin ɗakin su daga cikin sashen toilet ɗin, bakowa take kallo ba face Gabriel, ranshi ne ya bashi cewar ana kallon shi, hakan yasa shi juyowa don ya tabbatar, Cikin sa'a su ka haɗa ido da ita, Da hannu ta dinga yi mishi alamar ya iya rubutu? Ta kwatanta mishi biro ta hanyar yin amfani da hannunta na dama kamar tana rubutu, nan take ya gane me take nufi, bai amsa mata ba saboda Danish daya tsare shi da ido, shiyasa ya kawar da kanshi gefe ɗaya, Fitowa angel ta yi daga cikin toilet din ta shiga ɗakin ta zauna gefen gadonta, ta daura idonta akan Gabriel, so take ya bata amsar tambayarta idan ya iya rubutu, tana so ta sanar dashi akan ya buɗe backpack ɗin Unaiza ya ɗauko jotter dinta da biro yae mata rubutu, Ya jiye mata, ta hakanne kaɗai zasu iya magana da juna, if not Danish bazai ta6a bari su ke6e ba, sai dai batasan koya iya rubutun ba, zaiyi wuya ma ace bai iya ba, tun da a hasashenta ba rainon kurkukun ƙaddara ba, Akwai wayewa atattare da shi.

Yaso ya bata amsa amma Danish Ya kafe su da lumsassun idanuwanshi, Su uku ne idonsu biyu acikin ɗakin, Sauran har yanzu basu farka ba, Sai daga bisani ne Ɗaya bayan ɗaya su azeeza suka soma tashi daga bacci, da tunanin unaiza suka farka, suna ta jimamin halin da aka tafi da ita jiya, abun ya ta6a zuciyoyinsu, Angel tace dasu suje suyi brush suyi wanka, idan suka fito zasu motsa jiki yau, hakan yasa suka miƙe atare suka nufi sashen toilet ɗinsu, kafin wani lokaci duk su kayi wanka, kowa ya sanya red vest din shi da dogon wandon shi na sabon kaya ba ƙaramin kyau, su ka yi musu ba.

Ba su kai ga fara motsa jikin nasu ba, Giants suka kawo musu abinci, Dama da yunwa suka farka, Kowa ya samu wuri ya zauna, tsiren nama ne aka kawo musu da kayan marmari, hada robobin lemu dana ruwa, suna cin abinci idon Gabriel akan fuskar angel, yana so ya bata amsar tambayar da ta yi mishi É—azu shiyasa ma ya zauna yadda zasu fuskanci juna, ko da ta É—ago suka haÉ—a ido dashi, saboda rashin gaskiya atare suka saci kallon Danish, shi da yafi su iyawa, ashe tun É—azu ya ajiye cin tsiren naman don kada ya janye mishi hankali daga kansu har su samu damar yin wani abu ba tare daya gani ba, kyawawan idanuwanshi na akan faces É—in su.

Danish bai ta6a bata mamaki ba irin na yau, ashe dama yana da wayau? Yake nuna kamar sakarai ne shi? yau dai ta shaida hakan, har tambayarshi ta yi meyasa bazai ci Abincin shi ba? ya ce mata kada ta damu, zai ci ne zuwa anjima.
Chapter 134 · 0% Book details