Sashe 68
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
kalaman tsohuwa sunyi matuƙar girgiza angel, kafin ta yi yunƙurin buɗe baki ta furta wata kalma, tajiyo muryar parveen tana kuka tana faɗin Kada su bari a tafi da ita, mutuwa zata yi, ita bazata bi su ba ' a hargitse angel ta juya tana kallonsu, Kusan atare giants suka kai hannuwansu saman gadajensu Deeja da rubina da parveen, Wata irin ɗauka su kayi masu ta hanyar ruƙe waist ɗinsu suka yarfa su saman faffaɗan kafaɗunsu, bayin Allah Sai kuka suke Yi suna Bugun bayan giants da hannayen su, Nan take zuciyoyinsu Batool suka karaya Jikin kowan nan su yayi sanyi, har ma basu san lokacin da suka fashe da matsanancin kuka ba, Juyawa giants su kayi atare suka soma tafiya dasu ɗauke saman kafaɗunsu suka nufi stairs ɗin,
Da gudun gasken Angel ta tunkaresu Tana ƙarasawa bayansu Ta cafko hannayen parveen dake abayan giant ɗin dake ɗauke da ita, da iya ƙarfinta na ƙarshen ta janyota gaba ɗaya ta faɗo ta baya, baiwar Allah jikinta sai 6ari yake yi, ɗagowa tayi tare da rungume angel ta ƙanƙameta tana kuka tana faɗin"dan Allah angel kada ki bari su tafi dani, saboda basu dawowa da mu, bana so nabar Cikin ƴan uwana bansan inda zasu kai mu ba, Ina ji araina kamar na tafi kenan......." Giant ɗin dake a ɗauke da Parveen Ya tsaya Tsak wanda ko ba'a faɗa maka ba, zaka shaida cewar A fusace yake, domin su ba'a katse masu aiki, Da gudun gaske su Hanna da su Javed suka ƙaraso Inda su angel ke a zaune ƙasa suna kuka,
Kallonsu kawai take yi idanuwanta sun rune ita kaɗai tasan irin tashin hankalin da take ci, Na raba ta da ƴan uwanta da ake ƙoƙarin yi,
Cikin shessheƙar kuka Batool tace" Dan Allah ki daina kuka Parveen, tsohuwa ta faɗa mana cewa Cuta ba mutuwa bace, Sai in kwanan mutun ya qare, Zasu yi maki magani ne zuwa gobe idan ku ka ji sauƙi zasu dawo mana da ku," Ita kanta batool ta karaya sosai ta yi maganar ne kawai donta ƙarfafa mata gwiwa,
Zufa ta ko'ina Ajikin Parveen Muryarta na kerma tace"Koda ace ban dawo ba, Idan an kawo abinci, ku dinga ajiye mini nawa" Hawaye sharkaf akan fuskarta tayi maganar, angel dai takasa cewa komai, Zuciyarta ta gama karaya,
Kafin wani ya kuma cewa wani abu, Giant ɗin yakai Hannu da niyar ya ɗauki parveen, a tsorace ta ƙankame jikin angel tana faɗin" kada ki bari su tafi dani, bazasu dawo dani ba, idan har kuna sona dagaske ku taimake ni, kada ku bari araba ni daku......" ƙanƙameta angel tayi ajikinta, Giant ɗin ya damƙi qugun Parveen, ta ƙarfi ya fisgeta daga Jikin angel ya ɗaura ta saman kafadarshi Ya juya Cikin zafin nama Ya haura saman benan, Sauran Giants ɗin guda Biyu dake a ɗauke da rubina da Deeja suna abakin ƙofar fita suna jiran ƙarasowar shi, yana daga cikin dokar aikinsu Basa tafiya dole sai suna atare da juna, wani irin jiri ne Ya rufe idanuwan angel, anan ƙasa ta kwanta idanuwanta na zubar da hawaye, Suna Jiyo sautin muryar parveen cikin shessheƙar kuka take faɗin cewa"Angel dan Allah kiyi mini addu'a, Kuma idan gobe ba'a dawo dani ba, ku ajiye mini abinci na"
Wannan maganar ta parveen ta yi matuƙar kashe masu sassan Jikinsu, A nan suka wuni zuƙunne suna kuka, Mutun biyu ne acikinsu basu zubar da kwalla ba, Danish da Haris Saboda sun sa ma ransu cewa Za'a dawo masu da ƴan uwansu ne, duk da haka sun yi matuƙar damuwa da halin da su Parveen suka shiga, Na raɗaɗin ciwo ga kuma maraicin da zasu Yi na raba su da ƴan uwansu,
Tsohuwa dake a tsaye Bakin ƙopar ɗakinta, Ko a ha6ar xaninta bata sanya damuwar Halin da yaran suka shiga ba, Sai da taga Sun sassauta da yin kukan tukunna Ta dogara sanda ta nufi inda suke a zuƙunne ta tsaya tana kallon fuskokinsu da suka jiƙe sharkaf da hawaye
"Idan ku ka yi haƙuri, Za'a dawo maku da ƴan uwanku ne da zarar sun samu warakar Lalurar dake damun su, Kuka bazai ta6a yi maku maganin komai ba, Illa iyaka ya ƙara haddasa maku wata damuwar, Shawarar da zan baku shi ne, Ku sanyawa zuciyar ku haƙuri da juriyar rashin ƴan uwanku, kada ku cusawa kanku damu......." bata ƙarasa maganar ba angel ta yunƙura ta miƙe zaune idanuwanta sunyi jawur gwanin ban tsoro, muryarta a zafafe ta soma magana
"Har kina da bakin zuwa ki bamu haƙuri akan mu yi shiru mu daina kuka? Wlh tun da nake 6anta6a ganin Muguwar mace azzaluma irinki ba!
Ɗan zaro ido tsohuwa tayi da kwala kwalan idanuwanta tamkar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa,
"Kince ke uwa ce agare su, meyasa da naje na faɗa maki cewa Cikinsu na ciwo, baki zo kin duba jikin su ba? Koda sannu ne kiyi masu Amatsayinki na mahaifiyarsu, Amma bakiyi hakan ba, sai dai wasu ƙattai suka zo suka ɗauke su da sunan zasu duba lafiyarsu, bayan ke ya dace kiyi hakan a matsayinki na Ƴa mace, duk da bani da ilmi akan abun amma auntyna ta ta6a faɗa mini cewa Menstruation lalura ce ta mata da suke yi a kowani wata, zaki iya taimaka masu idan kinso basai an kaisu wani wuri ba......" cikin shessheƙar kuka takai ƙarshen maganar, Su batul duk sunyi zugudum suna sauraronsu,
"Banta6a jin tausayin wani ɗan adam ba aduniyar nan ba, kamar wadannan bayin Allah, wai su haka rayuwarsu zata ƙare? A tagayyare basu da me share masu hawayensu, basu da kafaɗar da zasu ɗaura kansu akai suyi kuka a lallashe su, Wannan wata irin Makauniyar ƙaddara ce? Tayi tambayar idonta akan tsohuwa dake a tsaye ruƙe da sanda, baka Iya gane awani hali take Ciki, domin kuwa fuskarta a haushine take, tsufanta da muninta sun ƙara bayyana
Juyawa tayi da sauri tana dogara sanda ta nufi ƙopar ɗakinta, tana ƙoƙarin kai hannu ta buɗe ƙopar muryar angel ta katse mata hanzarinta
"Ba zaki ce komai ba? Saboda rashin gaskiya? Zuciyarki ta bushe baki ji baki gani zalunci kaÉ—ai kika sa agaba, wlh rantsuwar É—an musulmi idan har ba'a dawo mana da Æ´an uwanmu ba, SAI NA KASSARA RAYUWAKI, koda kuwa zan rasa raina ne'
Girgiza kai tsohuwa tayi batare data waiwayo ta kalleta ba ta soma magana
"Zaki Iya zagina ki ci mutuncina son ranki, saboda a yanzu ni kike ganin laifina, Unaisah ga shawara...." a ruÉ—e angel ke kallon bayan tsohuwa, Jin yau ta ambaci asalin sunanta,
Cigaba da magana tsohuwa tayi"ME ZAI HANA KIYI TUNANI AKAN WAƊANƊA SUKA SADAUKAR DAKU A GIDAN KURKUKIN ƘADDARA? mutun baya ta6a kasancewa acikin gidan kurkukun ƙaddara dole sai in Na JININSA NE YA SADAUKAR DASHI!!, nifa ba kowa bace agidan kurkukun nan face Ƴar Aiki me rainon Yara," tsohuwa nakai karshen maganarta, ta yi saurin tura ƙofar ɗakinta ta shige taja ƙopa ta garƙame, ta tafi tabar angel da tunani, Zuciyarta ta shiga ruɗani, Kenan dama Tsohuwa bakowa bace Agidan kurkukun ƙaddara? Su kuma prisoners dake rayuwa acikinshi na Jininsu ne suka sadaukar dasu?tayaya kenan? Wata irin sadaukarwace wannan? Meyasa aka sadaukar dasu? Me za'ayi dasu? danginsu basa ƙaunarsu ne shiyasa suka sadaukar dasu ko kuwa?
Wani irin matsanancin ciwon kai ne Ya taso mata, me raɗaɗin gaske, da sauri ta sanya hannu ta dafe kanta, Ɗaƙyar ta iya ɗaga kafarta ta juya tana kallonsu Batul, waɗanda ke zazzaune Cikin jimamin rashin ƴan uwansu, da alama Basu ji komai ba game da abunda tsohuwa ta tattauna da angel,
"Wa suke dashi A duniyar nan? Zuciyarta ce ta bata amsa da cewa "ALLAH"
biji biji take gani acikin idanuwanta, daƙyar ta samu ta iya zuƙunna agabansu, Muryarta a disashe tace"kuyi haƙuri dare yayi sosai, Ku zo muje mu kwanta, " miƙewa kowannansu Yayi, Suna jan ƙafa suka Nufi gadajensu Kowa Ya haye ya kwanta, sai da tabi su ɗaya bayan ɗaya tayi masu addu'a, taja masu bargunansu ta lullu6e masu Jikinsu, koda tazo saitin gadon Parveen sai da ta matse kwalla, bakomai take tunawa ba face kukan parveen da kuma kalamanta na karshe da take cewa Tayi mata addu'a kuma idan an kawo abinci su ajiye mata, angel tasha kuka kamar ba gobe, lokacin data zo kan gadon Deeja, tuni jikinta yayi sanyi tunawa da irin muguntar da tayi mata ɗazu da suna wasa, ta sanya gwiwar hannu ta daki bayanta harta kife ƙasa, cikin shessheƙar kuka angel ta furta "NAYI DANA SANI" Wuce wa tayi zuwa bakin gadon Rubina, Ta jima tana kallon shimfiɗarta, Kafin ta nufi gadonta ta hau sama ta zauna daga tsakiya, Hannayenta ta ɗaga sama Ta soma yi masu addu'o'i, Yayin da hawaye ke fita acikin idanuwanta, wasu na bin wasu,
A daren Ranar Kowa Ya runtsa banda Angel, Ta dage sai addu'a take yi masu ta hana idonta bacci duk don saboda su Parveen,
A washe garin ranar, dayawansu basu farka daga bacci ba, har lokacin tana a zaune tsakiyar gadonta, ta jingina bayanta jikin bango, fuskarta ta kumbura sumtun, tayi ja sosai, ga jirwayen hawaye,
Mutsu mutsun da taji ne yasa ta soma ƙoƙarin buɗe idanuwanta Sun kumbura ga raɗadi da suke yi mata, daƙyar ta samu ta ware idanuwan sosai, gefenta ta ɗan kalla don ganin wanene ya motsa, Danish ne ta gani zaune saman gadonshi, ya lumshe idanuwanshi fuskarshi babu alamun damuwa atattare da ita,
Zuro da ƙafafuwanta ƙasan gadon ta yi tare da gyara zama daga gefen gadon tana fuskantar danish,
Cikin sanyin murya ta ambaci sunan shi"Danish" a hankali ya buÉ—e idanuwanshi ya juyo yana fuskantarta,
"Ka tashi lafiya"? Jinjina mata kai yayi alamar eh, ajiyar zuciya ta É—an sauke kafin tace" Inaso na tambaye ka wani abu idan ba damuwa" ya amsa mata da toh,
Saukowa tayi daga saman gadon, taje bakin gadonshi ta ɗan zuƙunna daga ƙasa, ta ɗago tana kallonshi idonsu acikin na juna tace
"Shekaran jiya da daddare, lokacin da na shiga cikin toilet ka biyo ni, Taya akai ka shigo bayan na datse ƙopa ta ciki na sanya jam lock"? ta tsare shi da ido tana jiran jin amsar da zai bata, ɗan tahalikin nan yayi shiru yana binta da ido batare daya motsa lips ɗinsa ba balle ma tayi tunanin zai bata amsa,