Sashe 95
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cikin zolaya tace"dama ance mutun mai haƙuri bai iya zuciya ba, yau na tabbatar da hakan, danish yayi fushi da angelar shi," babu irin lallashin da bata yi mashi ba, amma yaƙi tanka mata a ƙarshe ranta ya 6aci a fusace tace"Kai ni fa ko daddyna bana zama in lallashe shi kamar yadda nake yi maka, don ma ka samu ina kula ka shine kake wani shamin ƙamshi, to shikenan, Nasan me zanyi, Zanje ne kawai in dura tagar nan ta cikin toilet, kome zai faru ya faru, " tana kai ƙarshen maganar, ta miƙe da sauri ta ɗauki fitilar dage ƙasa gefen gadonshi, Ta nufi sashen makewayinsu har ta kusa kaiwa bakin ƙopar shiga, Kamar walƙiya taganshi agabanta tsaye yana faman lumshe idanuwanshi, doguwar sumar kanshi duk ta yamutse, Tsananin mamaki ne ya kamata, da sauri ta ɗan juya ta kalli gadon shi donta tabbatar idan shine dagaske, bata ga kowa ba, sai taga kamar 6acewa ya yi daga saman gadonshi ya faɗo gabanta,
Kafin ta yi mashi magana ya riga ta cewa"zan ci shi kenan ko"? ÆŠaga kai tayi alamar eh, ya ruko hannunta acikin nashi yaja ta suka koma Cikin É—akin, a gefen gadonshi ya zauna, Suna fuskantar juna shi da angel, tana azaune saman nata gadon, ta tsareshi da ido tana jiranshi ya kammala Ci, kwandon Ya dauka ya É—aura shi saman laps dinshi, A tsanake ya kai hannu ciki ya É—auki yankan nama yana ci, Bayan ya gama taune shi duka, Ya É—auki sauran 6allin apple data rage mashi yakai baki yana gatsa, jefi jefi yakan É—an É—ago ya saci kallonta, Ko uwarsa Albarka yadda ta tsare shi da ido,
"Zaka sha ruwa"? Ɗaga mata kai yayi alamar eh, ta miƙe tsaye sai da tafara ɗaukar kwandon, Kafin ta nufi gadon batool, A ƙarƙashi ta tura kwandon ta ɗauko mishi robar ruwa guda ɗaya, Ta dawo ta miƙa mashi, yasa hannu ya kar6a ta koma saman gadonta ta kwanta tana facing ɗinshi, Buɗe murfin bottle ɗin yayi tare da kwafata abakin sa, kusan rabi ya sha, bayan ya gama shan ruwan, ya maida murfin bottle ɗin ya ajiye ta daga ƙasa, Sannan ya gyara kwanciyarshi, suna fuskantar juna, kallan ƙurulla suka shiga yi ma junansu, bakomai take tunawa ba, face yadda ya sha gabanta ɗazu saboda tace zata dura tagar nan, tarasa gane dalilin dayasa baison tasan komai dangane da kurkukun, Ta fahimci cewa danish yasan komai, shiyasa yake lalla6ata don kada ta gani taja musu wata matsalar, Abunda kuma bazai ta6a yiyiyuwa bane,
Da wannan zancen zucin bacci yayi awon gaba da ita, shima danish É—in tuni bacci ya É—auke shi,
A washe garin ranar, kafin kowa ya farka daga bacci, batool ce tafara tashi tana miƙa tare da Yin hamma, ta sauko daga saman gadonta, cikin sauri ta nufi toilet saboda wani irin fitsari daya matseta, Ya ɗaure mata mararta, hada ɗan gudunta wurin shiga toilet, batare data yi locking door din ba, hannayenta ta sanya wurin zame wandon jikinta ta zuƙunna tana Yin shi, bayan ta kammala ta kunna fanfo ta yi tsarki, Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa tsaye tana gyara wandon Jikinta, kafin ta nufi ƙopar fita, harta miƙa hannu zata buɗe sai ga azeeza ta faɗo cikin toilet ɗin. jikinta sai kerma yake yi, batool tace"lafiyarki kuwa kika faɗo mini Cikin toilet ba neman excuse? Batare da azeeza ta kalli batool ba tace"ke dallah fitsari ne ya matse ni, ni ina nasan da mutun a ciki, " tana faɗin hakan ta wuce cikin toilet ɗin, girgiza kai batool tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta fito daga waje, taja mata ƙopar ta rufe, tana ƙoƙarin shiga cikin ɗakinsu, Tajiyo muryar azeeza daga Cikin toilet tana kwala mata kira na fitar hayyaci, da sauri ta koma ta nufi ƙopar toilet ɗin, Fitowa daga Ciki azeeza tayi idanuwanta azazzare hannunta dafe da saitin ƙirjinta tace"Batool, naga ɗigon jini a cikin toilet wurin magudaji ke ce kika zubda shi"? Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce tazo ma batool, nan da nan walwalar fuskarta ta ɗauke, amatuƙar ruɗe tace"Bani bace, sai dai ko kece da kika shiga ciki yanzu, saboda ni har na fito banga wani ɗigon jini ba"aruɗe azeeza tace"Wlh bani bace, Ae ni yanzu na shiga, Ko tsugunnawa ban kaiga yi ba, naga jinin, hakan na nufin daga Jikin ki yake, " a tsiwace batool tace"Nifa bani bace na zubda shi ba, wlh bani bace" tuni hawaye sun wanke fuskarta, Azeeza ta fashe da kuka tana faɗin"Wlh kece, Ae ni ban kaiga yin fitsarin ba, Ki yadda ko karki yadda naki ne daga Jikin ki ya fito," shaƙo wuyan rigar azeeza batool tayi da hannunta biyu ta jijiigata, cikin shessheƙar kuka tace"You're lying to me azeeza, Kina so ki ƙala min sharri ne, Kiji tsoron Allah, ki faɗi gaskiya," Hankalinsu yayi matuƙar tashi, Kowa Ya haƙiƙance Yana ƙoƙarin kare kanshi,
*Jinin wanene AZEEZA OR BATOOL â“â“â“*
*â¤â¤â¤PRISONERSâ¤â¤â¤*
Saboda tsabar firgicin da azeeza ta shiga nan take ta saki fitsarin da take ji ya soma gangarowa ta cikin wandonta, an rasa me lallashin wani acikin su, kowa sai kuka yake yi, Kuma har lokacin Batool bata saki wuyan rigar azeeza da ta shaƙe ba, bayin Allah su kaɗai suka san Fargabar da suke aciki, babban abunda suke jima tsoro shi ne azo araba su da ƴan uwansu, Basu da tabbacin za'a dawo dasu ko baza a dawo dasu ba,
Cikin shessheƙar kuka ta wanda ya galabaita azeeza ta kware maki tana faɗin"Wayyo Allah na, Na shiga uku, batool kin shaƙe min wuyan rigata, Ki sake Ni, inji da abunda ke damu na....."daƙyar ta kai ƙarshen maganar, tana kiciniyar ƙwace wuyan rigarta da ga ruƙon da batool tayi mata, wata irin zufa ce ta wanke fuskokin su, Sun yi jawur, idanuwansu sun kumbura luhu luhu saboda tsabar tashin hankalin da suke aciki.
Waɗan da ke acikin ɗaki basu san meke faruwa ba, babu alamun zasu farka daga bacci, Wata irin gigitacciyar ƙara batool ta saki sakamakon Cizon da Azeeza ta gartsa mata a hannunta, kaitsaye sautin ƙarar ya daki dodon kunnuwan su, Aikuwa a firgice kowannan su Ya farka, at same time suka ya ye bargunansu tare da yin wurgi dasu, Kowa yana faman zazzare ido, fuskokin su da alamun ruɗani, lokacin da suka ankara daga inda sautin ke fitowa, Jiki Na rawa kowannan su Ya sauko daga saman gadonshi, da gudun gaske suka nufi sashen toilet ɗinsu, kamar an jeho su suka faɗo Ciki, Kowa yana faman baza na muzurinsa, Angel ce farko sai Hanna da hibba, kaf matan da mazansu hada danish da haris,
Hankalin su yai matuƙar tashi, ganin Jinin dake ɗigowa daga hannun batool sai yarfa shi take Yi, ta runtse idanuwanta sai kuka take yi kamar ranta zai fita, Tun da suke a rayuwar su basu ta6a ganin batool tana kuka mai sauti ba irin na yau, saboda tsabar hakurinta da juriyarta, Ita kanta azeeza data gartsa mata Cizon, duk tabi ta ruɗe jikinta sai kerma yake yi, ta manne jikin bango, Sai zazzare idanuwanta take yi fuskarta sharkaf da hawaye,
"Innallallahi wa'inna ilaihirraji'un! Batool meya faru dake? Me kuke yi anan keda azeeza? Badai faɗa kuke yi ba"? Angel ce ta jefa musu tambayar, a yayin da take matsawa kusa da batool, takai hannunta tare da ruƙo hannun batool dake bleeding, Hanna tace"ashe dama kune kuke faɗa? Tun ina bacci nake ta jin hayaniya cikin kunne na, amma kun bani mamaki, yanzu batool ki rasa da wa za ki yi faɗa sai azeeza"? Hannah na rufe baki haris yace"Ku faɗa mana meya haɗa ku da har kuke ƙokarin illata junan ku, wannan wani irin abun kunya ne, " Lamarin duk bai yi musu daɗi ba, sai tambayar su suke yi akan su faɗa musu dalilin yin faɗan na su amma sun kasa tanka musu, saboda kukan da suke yi.
"Hannunta yana zubar da jini, Ya zamu yi? Ko dai muje mu faɗa ma tsohuwa"? Mubeen ne yai maganar, muryar danish da alamun bacci bai ishe shi ba yace"Basai an faɗa mata ba," ya ƙarasa maganar tare da matsawa ya tsaya gefen angel dake a tsaye gaban batool, ya miƙa hannu ɗaya ya damƙo hannun batool dake zubar da jini, tare da kaishi saitin bakinshi tamkar zai gartsa mata cizo, ya kama wurin, kamar yana tsotsar jinin, duk suna kallon shi, Musamman angel da mamaki ya kamata ganin wani sabon salon treatment da bata ta6a gani ba,
Sosai batool ta runtse idanuwanta, tana faman cizon brownish lips ɗinta, a hankali danish ya zame bakinsa daga saman hannun batool, wani iko na Allah jinin ya tsaya da zuba, sai dai a bunda ya ɗaure ma angel kai, ganin bai zubar da jinin daya sha ƙasa ba, A ruɗe take bin fuskarshi da kallo batare daya lura da ita ba, Sauran ƴan uwan babu wanda Ya kawo komai aranshi sai ita data ankara da abunda ya yi, zuciyarta ta shiga ruɗanin, taya akai ya ke iya swallowing ɗin jini!?