← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 179

Sashe 88

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Damuwar duniya ta ishi angel, Ga wani irin faɗuwar gaba da take ji, tarasa gane dalilin hakan, addu'o'i kawai take janyowa Acikin zuciyarta, Tana ji aranta kamar wani abune zai faru, wasa wasa suna kwancen nan har dare Ya ratsa hasken ɗakin Ya yi duhu, tun tana iya jiyo hirarsu suna faɗin har yanzu ba'a dawo da deeja ba, har tadaina Jin surutunsu alamun sunyi bacci, Aranta tace"ita kuma wannan Makauniyar rayuwar haka zata ƙare? Kullum muna ƙunshe a ɗaki Ɗaya tsawon shekara da shekaru, Gaskiya bazai yiyu ba, Nifa ina da burikan da nake son Cimmawa don haka bazan zauna in zuba ido ba, dole in nema ma kaina mafita, tana karasa zancen zucin nata, ta yunƙura ta sauko daga saman gadonta, Cikin duhu ta shiga laluban Fitilun ɗakin su, ko da ta ɗauko fitilar bata kunnata ba, saboda gudun kada Danish ya farka daga bacci Ya bi bayanta, Cikin sanɗa taci gaba da tafiya ko sautin tafiyarta baka Iya ji, tana shiga sashen toilet ɗin Abakin door ta kunna fitilar, Ta buɗe toilet ta shiga ta zura jamlock, A ƙasa ta sauke fitilar, Ta ɗauko bokitin ƙarfen nan, ta Ajiye shi jikin bangon da tagar Nan take, saboda ta sa mu tsawonta yakai, Daddagewa ta yi tare da haye saman bokitin, tana yunƙurin kai hannu ta zame glass ɗin muryar danish Ta ratsa kunnata
"Angel!" ras taji gabanta Ya faɗi, gaba ɗaya jikinta ya hau kerma, tsantsar 6acin rai ne ya bayyana akan fuskarta, a tsiyace ta juya saitin Da yake tana kallonshi, A tsakiyar toilet ɗin taganshi A tsaye, tun kafin yai magana ta riga shi cewa"kai nifa nagaji, Don me zaka dinga faɗo mini cikin toilet? Bayan ka yi mini alƙawarin cewa bazaka ƙara shigowa ba?

Cikin sanyin murya yace"Ina Bibiyarki ne saboda sanin ƙudirin da kike dashi na son shiga Cikin prison, wanda yin hakan zai iya haddasa mana shiga mummunan haɗari, " Har saida taji gabanta Ya faɗi, jin abunda yace, Da mamaki tace"Oh dama kasan abunda nake son yi kenan? Taya akai ka sani?

"kawai naji araina ne, kina son ki dura ta tagar, ko last time dana Sauke maki glass, Ban yarda da abunda kika faɗa mini ba, na cewa bakya son kallon glass yana affecting ɗinki, da ace dagaske ki ke, to da tun lokacin kin kawar da shi daga Cikin toilet ɗin amma sai baki yi hakan ba, " Ya ƙarasa maganar a yayin da yake tunkararta, Runtse ido ta ɗanyi tare da cizon lips ɗinta, Rai a6ace tace"wlh duk bala'in ka baka isa ka hana Ni yin abunda nayi niya ba, kada ka kuskura kace zaka ma dakatar dani, idan har ba so kake In yi maka Illa ba"

"Angel Na roƙe ki kada ki je, Zaki jefa rayuwarki da tamu Cikin hatsari, Ba'ayi musu leƙen asiri, Ki fahimce, yafi muyi rayuwarmu Cikin duhu akan musan ainihin abunda ke faruwa acikin prison, amma daga ranar da kika haura tagar nan, xaki ja mana ne gaba ɗayan mu ne"... Tamkar zai fashe da kuka Yake yi mata magiya akan karta dura, A ƙarshe daya ga ta kafe tasa naci akan saita dura, ai kuwa da ƙarfi Ya sanya hannu ya janye bokitin da tahau sama, Gaba ɗaya ta tafi zata kife ƙasa da sauri ya sanya hannayenshi biyu Ya tarbo ta, ta faɗo saman jikin shi, Suka rubza ƙasa atare, kanshi ba ƙaramar buguwa yai ba, ita kuwa kamar jira take yi su faɗo aikuwa ta daddage ta dunƙule hannayenta, Ta shiga kai mashi bugu a ƙirjinshi, Ya yi shiru batare daya dakatar da ita ba, zuciya ce ta fusgeta, a karshe ta kifa kanta saman ƙirjinshi tana kuka tana faɗin"Ya rabu da ita taje, Ita ta gaji da rayuwar kulle, Bazata Iya jure azabtar da ƴan uwansu da ake Yi ba, " Haƙiƙa Danish yaji tausayinta, Sai dai bazai Iya barinta taje yin leƙen asirin ba, saboda shi ya fita wayau da hankali, Ya kuma san Abunda sai biyo baya, Idan har ta dura ta tagar nan,

Tuntana yin kukan har tagaji tadaina muryarta ta disashe, Sai lokacin ya samu damar yunƙurawa Ya ɗago da ita a jikinshi, A saman kafaɗarshi ya kwanto da ita, ranƙwafa yayi tare dakai hannu ya ɗauki fitilar da tazo da ita, Ya juya ya fuce daga cikin toilet ɗin, Yana shiga ɗakinsu Ya kwantar da ita saman gadonta, Daga ƙasa ya ajiye fitilar hannun shi, Ya zauna daga gefenta yana kallon fuskarta, Wadda ta yi jaga jaga da hawaye, hannayenta ya ruƙo acikin nashi, ya soma lallashinta, ya ɗauki tsawon lokaci Amma ko kallo bai isheta ba, Sai da ya gaji don kanshi tukunna Ya ƙyaleta, Ya koma nashi gadon Ya kwanta, A daren ranar daƙyar bacci ya ɗauki angel,

Ranar da Deeja ta Cika 4 days da aka ɗauketa, A daren Ranar Giant Ya dawo da ita, Babu wanda ya sani duk sunyi nisa a cikin baccin su, A tsakiyar ɗakinsu Giant Ya sauke ta, Baiwar Allah duk ta fita hayyacinta ta rame ta fige, kamar wadda aka ɗibi naman jikinta, kasancewar sun kunna fitilun ɗakin su, Hakan ya bata damar bin Cikin ɗakin, Bata nufi ko'ina ba sai bakin gadon angel, a gefe gadon ta zauna, fuskarta sharkaf da hawaye, hannu takai saman shimfiɗar angel ta ɗan bubbuga kafadarta, Ƙasa kasa da murya take ambaton sunanta don kada ta takura ma masu yin bacci, koda angel taji muryar deeja acikin baccinta, a matuƙar ruɗe ta yaye bargonta, muryarta na kerma tace"deeja! Dagaske kece? Ko dai mafarki nake yi," jinjina kai deeja tayi cikin shessheƙar kuka tace"its me angle, am back, Giant ne ya dawo dani, na same ku kuna bacci, bana so na tashi kowa shiyasa nazo wurinki, saboda akwai abunda nake son faɗa miki," Tun da angel taji haka, Sai ta yaye bargon dake a jikinta, Ta kalli fuskar deeja da kyau, Gaba ɗaya ta zabge Duk ta bushe, janyota tayi zuwa jikinta ta rungumeta sosai, kamar zata maida ta cikin cikinta, Tayi matuƙar yin kewarta, Sun ɗauki tsawon lokaci, Kafin angel ta raba jikinta daga na deeja tace"Ki faɗa mini menene? Deeja tace"za'a iya jin mu idan muka Yi magana anan, amma zan shiga toitet, sai ki biyo ni" angel ta amsa mata da toh, Miƙewa deeja ta yi jiki duk ba ƙwari ta shige toilet, angel ta miƙe ta bi bayanta, bayan sun shiga, deeja ta sanya jamlock ta datse ƙopar, ta juyo suka fuskanci juna ita da angel,

"Faɗa mini menene kikeson Gaya mini? Duk na ƙagara inji" Cikin shessheƙar kuka deeja tace"Angel yanzu na ƙara yarda da maganarki na cewa ana cutar da rayuwar mu, wani iko na angel, Duk da bakomai zan iya tunawa ba, Amma lokacin da giant ya tafi dani, ina Cikin hayyacina, Inata karanta addu'ar nan da kika koya mana acikin zuciyata, Har yakai ni wani part inda wasu jerin daƙuna suke, Bayan ya shiga dani ɗaya daga cikin su, duhu ya mamaye idanuwana, ban iya ganin komai sai dai biji biji nake gani, Har lokacin ban fita hayyaci na ba, Sai dai bana iya gani da kyau, Naga mutun shida wanda ba baƙaƙen kaya bane ajikinsu kalar na giants, naga launin Ja a ƙugunsu, angel daga nan ne na fita hayyacina, bansan me akayi mani ba, Sai dai naji ajikina an cutar da rayuwata, nayi kukan mutuwa, Na azabtu iya azabtuwa, " Deeja nakai karshen maganarta, Ta zube saman gwiwowinta, tare da fashewa da matsanancin kuka, kamar ranta zai fita, Hankalin angel yayi matuƙar tashi, duk da bata ji me mutun shiddan nan suka Yi mata ba, amma tana ji aranta cewa Lalata suke yi dasu, idan har zata iya tunawa, can lokacin baya,Ta ta6a yunƙurin guduwa daga islamiya zata je gida, Tazo giftawa ta ofishin head master ɗinsu, Tajiyo shessheƙar kuka, da kuma maganganun mutane, duk da ƙarancin shekarunta a time ɗin tana dab da shiga 11 years, Har zata wuce ta la6e ta kasa kunne tana sauraronsu, ɗaya daga Cikin ɗaliban makarantar ne aka samu wani malami yayi ma fyaɗe ya kuma cigaba da lalata da yarinyar da bazata wuci shekara sha bakwai ba batare da sanin kowa ba, idan tazo islamiya aka tashi sai ya ɗauketa saman mashine ɗinshi zuwa gidanshi da ya gina da niyar yin aure, amma sai ya 6uge dakai yara yana 6ata musu rayuwa tare da yi musu barazana, Mahafiyar yarinyar ce ta fara lura da canzawarta, Bata iya tafiya ƙafafuwanta sun gwame, ga yawan yin amai, da su ka kaita asibiti likita ya tabbatar musu cewa ƴarsu Cikine da ita, iyayen yarinyar sun shiga damuwa, bayan sun baro asibiti sun dawo gida, mahaifiyar yarinyar ta ɗauko wuƙa ta ɗaura akan wuyan yarinyar tayi mata barazana akan ta faɗa musu wa yake yin lalata da ita har ta samu ciki, in ba haka ba zata kashe ta, atsananin tsorace yarinyar ta faɗa musu cewa malaninsu ne na islamiya, Koda jin haka sai suka tasa ƙeyarta gaba suka zo makarantar don su tabbatar da abunda ta faɗa musu, A lokacin angel bata fahimci komai ba, amma ta naɗi komai a acikin kanta, sai yanzu da Deeja ke faɗa mata wannan maganar ta soma tariyo abunda ya faru da ɗalibar nan ta makarantar islamiyarsu, duk da bata da tabbaci akan hakan amma tana zargin Suma lalatar ake yi dasu, ' Zuƙunnawa ta yi agaban deeja, Ta sanya hannayenta biyu ta rungumota ajikinta, Lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, itama deejan kuka take yi sosai, ta ƙanƙame angel da hannayenta, Abun da ciwo idan har ya tabbata cewa lalata ake yi dasu saboda rashin imani kuma a lokacin da suke Yi jinin al'ada, 😭😭😭

*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Chapter 88 · 0% Book details