Sashe 97
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da angel ta datse ƙopar toilet ɗin, Ajiyar zuciya kowannan su Ya sauke, Haris yace dasu su koma ɗaki su zauna su jira su ga waye zaizo ɗaukarsu azeeza, Hada ja musu kunne akan karsu kuskura su bari tsoro yasa su faɗa ma giants inda suka 6oye su azeeza, duk runtsi duk wuya suja bakinsu su yi shiru, Suga iya gudun ruwansu, suka amsa mashi da toh,
atare suka nufi cikin É—akin, Idanuwansu akan danish dake kwance saman gadonshi, haushin shi duk ya kama su, wani sullu6iyo dashi,
Suna yunƙurin haurawa su zauna saman gadajenshi, kwatsam suka soma Jin motsin buɗe kofa tacen saman bene, wa'Iya zubillahi zoka ga tsantsar tashin hankali akan fuskokinsu, A matuƙar ruɗe suke kallon matattalar benan ,
Takun tafiyar giants suka soma Jiyo wa acikin kunnuwansu, kafin su bayyana su uku masu kawo musu abinci hannayen su ruƙe da farantai, wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya suka sauke ganin basu zo da shirin tafiya da wani ba, Bayin Allah hada murmushin su, saboda sun sa ma ransu cewa baza a ɗaukar musu ƴan uwansu ba,
Da ido suka bi giants da kallo har suka sauke musu farantan abincin, da sauri suka nufi saman dining carpet ɗin suka zazzauna, babu wanda yae tunanin yayi ma danish magana akan yazo yaci abinci, sai ma ta ƴan uwansu suke yi dake acikin toilet, ƙasa ƙasa da murya suke yin magana don kada giants su ji su,
"A ina zamu ɗibar musu abincin mu kai musu"? hibba ce tai maganar, hannah tace"ku daina magana kada Giants su ji mu, abunda za'ae mu ɗauko kwandon batool mu ɗibi abinci, sai mu ajiye, bayan sun tafi sai muje mu kai musu acikin toilet ɗin," haris yace"kin kawo shawara mai kyau," batare da 6ata lokaci ba, hanna ta miƙe taje ta ɗauko kwandon daga ƙarƙashin gadon batool ta dawo ta zuƙunna gaban farantan, ta yaye jan ƙyallan da aka rufe faranti na farko dashi, fried fishes ne aka kawo musu, manya manya sun soyu sai maiƙo suke Yi, a ƙalla kowa zai samu ɗaya, Kifin akwai tsoka jikinshi sosai, A hankali take kai hannu tana ɗaukar kifin tana ajiyewa acikin kwandon, ganin ta ɗauki uku, yasa haris yace"Ki ƙara ɗaya kodan saboda danish" duk da fushi da yake yi dashi hakan bai hana shi jin damuwa dashi ba, Hanna tace toh, tasa hannu ta ƙara ɗaukar ɗaya ta ajiye, Ta ɗibar musu fruits tare da robar ruwa guda uku ta ɗauka, miƙewa tayi hannunta ruƙe da kwandon taje bakin gadon batool ta ajiye shi ta dawo ta zauna, a tsanake suke Cin nasu fried fish ɗin, Suna ci suna satar kallon giants dake atsaye sun goya hannayen su saman ƙirjinsu yadda kasan Gumaka, ko gajiya da tsayuwa basa yi,
A 6angaren su angel dake acikin toilet, Tuni bacci yai awon gaba da azeeza da batool, duk suna akwance saman jikinta, itama angel É—in wani irin bacci take ji ga yunwa dake addabarta, sai faman lumshe idanuwanta take yi,
Daga wajen ƙopar toilet ɗin ta soma Jin ana yi musu knocking ras taji gabanta ya faɗi, hatta su azeeza dake baccin jin bugun ƙopar yasa suka farka a firgice suna faman zazzare idanuwan su,
Muryar hanna suka jiyo tana faÉ—in"Ni ce angel, ku buÉ—e mini kopa, breakfast ne na kawo maku" Kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, duk sunyi tsammanin ko Giants É—in ne suka zo tafiya dasu,
"Ku jira na amso mana abincin" tai maganar tare da zame jikinta daga nasu ta miƙe ta nufi ƙopar, ta cire jam lock ɗin, ta janyo ƙopar tare da leƙo da kanta waje,
Hanna ta gani atsaye ita da haris, kwandon Yana a hannun hanna ta ruƙo shi,
"Angel Giants sun zo kuma sun tafi, Ni ina ganin kamar É—igon jinin nan ba jini bane. Tunda da ace shine, Giants zasu tafi da su azeeza ne, Amma kinga har sun kawo mana abinci sun tafi" shiru angel ta É—anyi tana nazarin maganar Hanna. Ita gani take kamar jini fa ne, kawai dai bai kai ga zuwa bane gaba daya shiyasa basu zo sun É—auke su ba
Muryar haris ce ta dawo da ita daga zancen zucin da take yi,
"Nima ina tunanin ba jini bane gaskiya, tun da ga shi har zunzo sun tafi batare da sun buƙaci tafiya dasu ba" abunda za'ae yanzu ku fito mu koma cikin ɗakin ku zauna ku yi breakfast ɗinku" Gyaɗa kai angel tayi badan taso ba tace"Allah yasa abunda muke hasashe ya zama gaskiya, bari nayi musu magana su fito mu koma daki amma kafin nan, zan taimaka musu su wanke fuskokinsu," haris ya amsa mata da toh .kafin ya kalli hanna yace"Mu jira su acikin ɗaki" juyawa suka yi atare suka koma ɗaki,
Badajimawa ba, Sai ga angel ta fito hannayenta ruƙe da nasu azeeza, Bayin Allah har faɗa wa sun ɗan yi saboda damuwa, Ƴan uwansu ba ƙaramin daɗi suka ji ba, da su kayi tozali dasu,
A saman dining carpet suka zauna su uku, Hanna ta ajiye musu kwandon. Angel da azeeza suka ɗauki fried fish ɗinsu A hankali suke Ci, Sauran ƴan uwansu duk suna a kewaye dasu suna kallonsu, ganin batool ta kasa ci ne yasa haris yi mata magana yace"batool meyasa baki ci? Muryarta na ɗan kerma tace"Hannuna Zafi yake yi mini" sai lokacin suka tuna da cizon da azeeza ta gartsa mata, Zuƙunnawa haris yai agabansu, ya kai hannu cikin kwandon ya gutsiri tsokar kifin ya mika mata abaki, ta ɗan buɗe shi tana Ci, sai ƙara kwantar musu da hankali ƴan uwan nasu suke Yi, bayan sun kammala Ci, suka sha fruit ɗinsu, tare da ruwa,
Angel tace yakamata suje suyi wanka, jikinsu duk zufa, suka amsa mata da toh, har tana cewa idan bazasu iya yin wankan ba zata taimaka musu suyi, batool tace ita zata Iya, azeeza kuma tace tafi son angel tayi mata wankan, hannun su aruke dana juna suka nufi toilet, bayan tafiyarsu, Haris ya É—auki kwandon yana kallon sauran Fried fish din daya rage na danish tare da Rabin gwanda, Ta6e baki ya É—anyi kafin ya nufi gadon danish, Ya ajiye mishi kwandon daga gefen shi yace"Idan kaga dama ka É—auka ka ci, breakfast É—in ka ne" ko motsi danish bai yi ba, ya runtse idanuwanshi, kuma ga dukkan alamu idonshi biyu ba bacci yake yi ba,
Watsa hannu haris yai alamar bai damu ba, Ya wuce abunshi, bayan wani lokaci, angel tafito daga Cikin toilet tare dasu azeeza, Wani irin sanyi suke Ji, asaman gadajensu suka kwanta, angel ta lullu6esu da bargunansu, Cikin ƙanƙanin lokaci bacci yai awon gaba dasu,
Ajiyar zuciya kowannan su ya sauke, yanzu sun ƙara tabbatar da cewa ba jinin gaske bane suka gani acikin toilet tunda har marece ya doso amma ba'a zo an ɗauki wani daga Cikin su ba,
Ita dai angel ta kasa samun natsuwa acikin zuciyarta, abu biyu ne ya dameta, na farko Jinin batool da danish yasha da niyar ya taimaka mata wurin dakatar da bleeding É—in da yake yi, amma wani abun mamaki bai zubda jinin ba sai ya shanye shi, hankalinta bai kwanta da hakan ba, abu na biyu daya tsaya mata arai shi ne wannan É—igon jinin dake acikin toilet na wanene? Dole akwai wanda ya zubar dashi,
Zuciyarta cike fal da tunani ta ɗan kishingiɗa saman gadonta, da niyar ta samu ta runtsa, juyawa ta ɗanyi tana satar kallon danish dake kwance saman gadonshi, yatsun hannunshi dana ƙafarshi sai kerma suke Yi, hakan ya tabbatar mata da cewa idonshi biyu, ta6a baki ta ɗanyi aranta tace"Haka zaka ƙare, mutun sam baya gajiya da hawan gado, mai matacciyar zuciya kawai" takarasa xancen zucin tana mai jan tsoki, ta ɗauke idanuwanta daga kan jikin shi, ta mayar dasu kan kwandon da haris ya ajiye mashi daga gefen gadonshi, yau kuma kowa zai lallashe shi yaci abincin shi? murmushin takaici ta dan saki, wani lokacin in yana abu kamar ƙaramin yaro, har mamaki yake Ba ta
*after some hours💔*
Kafin marece ya yi sai da kowan nan su ya yi wanka, Suka koma saman gadajensu suka kwanta, har lokacin danish bai motsa ba, Yana ayadda yake lafe saman gado,
Angel tana ƙoƙarin nutsawa cikin baccinta, ta soma jin motsin mutun a jikinta, aɗan firgice ta ware manyan idanuwanta akan fuskar wanda ke zaune saman gadonta, Tayi mamakin ganin batool, fuskarta duk a yamutse. Idanuwanta sun ƙanƙance, tunkafin ma batool tayi mata magana taji wani irin faɗuwar gaba,
Muryarta na ɗan rawa tace"Lafiya? Batool meke damunki"? Cikin sanyin murya ta soma magana"Bana jin ɗaɗin jikina angel, gaba na sai faɗuwa yake yi, na gaza jurewa, shiyasa nazo wurinki, don kiyi mini addu'a, ko na samu naji sanyi araina" ajiyar zuciya angel ta sauke a yayin da take yunƙurin mikewa xaune tace"Wlh har gabana ya faɗi dana ganki nayi tunanin ko jinin ne kika gani yazo miki ashe bashi bane" jinjina kai batool ta ɗanyi alamar eh, tace"Bashi bane, bana jin daɗi ne kawai"
"Tun da nake dake batool ban ta6a ganin ki cikin damuwa ba, irin na yau, kin canza sosai, duk sai naji ba daɗi jikina," daƙyar batool ta ɗan ƙaƙalo murmushin dole akan fuskarta tace"kada ki damu sister, zan dawo dai dai ne, just fargabar abunda ya faru ɗazu ce tasa duk na canza, Amma yanzu da ɗan sauki"
Ido cikin ido suke kallon juna. angel ta ruƙo hannayenta acikin nata tare da cewa
"Zanyi maki addu'a, amma nafi so naji ki ajiki na, don naji daÉ—in kwantar miki da hankali kamar yadda kika saba yi mini" murmushi suka sakar ma juna atare,