Sashe 72
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ko zakiyi wanka ne? May be kiji daɗin Jikin ki," cikin sanyin murya tace"eh, xanyi, " tana rufe baki Azeeza tace"Angel me zamuyi yau"? Murmushi angel ta ƙaƙalo, yayin da take kallonta tace"Little Kome kike so Shi za'ayi, " ashagwa6e Azeeza ta bubbuga ƙafar tare da cewa"Ni kidaina ce mun little bana so," gaba ɗaya su kayi dariya, Hanna tace"Ae gaskiya ta faɗi, kallarki fa? Wata ƴar ƙarama dake, Ko kafaɗarmu baki kai ba, banta6a ganin wadda bata cigaba ba acikinmu irin ki, Duk yawan abincin da kike Ci sam baki ƙara auki, ba ƙiba ba tsawo," dariya suka saki gaba ɗayansu, Rai a6ace Azeeza Ta zuƙunna kasa tana yin kukan ƙarya, Angel tace"pls kudaina janta, Nima na faɗi ne kawai don ayi nishaɗi, amma azeeza ae itace babbarmu," ta yi maganar tana ƙyaftawa musu ido, atare suka haɗa baki wurin cewa"hakane Azeeza itace babbarmu, muma wasa muke Yi mata, don kawai ayi raha ne" Sunsan azeeza da son girma, jin wannan maganar tasu yasa ta miƙe tana gumtse dariya abaki,
Angel tace mata"Me kike so Muyi yanzu?
"Ki wanke mana gashin kanmu, Kuma ki gyara mana, keda batool kamar yadda ku kayi mana ran nan kin tuna'? Zaro ido angel tayi"Azeeza Baki ga yadda na farka ba yau, sam babu natsuwa atare dani, Taya zamu Iya wanke maku wannan uban gashin kan naku, Kuma mu gyara shi,? Ta6e baki azeeza ta yi, Itafa in taso abu to ayi mata kawai, idan ba haka ba yini zatayi tana faman tur6une musu fuska duk da tana da yawan fara'a kamar Gonar auduga,
"Kada Ki damu sister azeeza, Koda angel bata samu damar tayani ba, Ni xan gyara maku gashin kanku, Mu barta ta huta, tun da bata Jin daÉ—i, Kuxo muje toilet," Batool ce ta yi maganar, Ta juya ta nufi toilet suka bi bayanta,
Bayan tafiyarsu Cikin toilet, Angel ta sauke ajiyar zuciya, tare da jingina bayanta Jikin bango, Gefe ta juyar da kanta tana kallon Gadon danish, kamar dai kullum yana a kudundune Cikin bargo, Haris da mubeen da Javed hada naufal duk basu farka daga Bacci ba, sakamon daren da su kayi jiya batare da sun runtsa ba, Suna Xaman Jiran adawo musu Æ´an uwansu,
Saƙe saƙe ta shiga Yi acikin zuciyarta, game da wasu tambayoyi da suka cunkushe mata kwakwalwarta, sun hanata sakat, idan ta takura kanta akan tunaninsu Har wani matsanancin ciwon kai take ji, tabbas tana son Yin magana da tsohuwa duk da tasan zaiyi wuya tsohuwa ta amsa mata tambayoyinta, amma zata jaraba tunkararta, Yau ɗin nan,
A6angaren su Batool, sai da tabi kowannan su ɗaya bayan ɗaya ta wanke musu sumar kawunansu, Baƙaramar wahala tasha ba, domin kuwa Dukansu tsayin gashinsu Ya zarce midback ɗinsu, Ga uban yawa dake gare shi, bayan ta kammala wanke musu gashin, Sai da kowannan su Yayi wanka, Kafin suka dawo Cikin ɗakin, Kamar yarda suka bar angel zaune saman gadonta haka suka sameta, ganin sun fito daga wankan Yasa itama ta miƙe domin zuwa yin wankan, Shigarta da ƴan mintuna ta fito, A lokacin Danish dasu Mubeen duk sun farka daga bacci, saukowa su ka yi daga saman gadajen su, Atare suka Nufi Toilet domin suma suyi wankan ko sunji daɗin Jikin su.
A zaune ta samu batool gefen gado ta ruƙe Comb, Zata Gyara musu gashin kansu, hakanan taji tana sha'awar Tayi musu Kitson kalaba Guda Biyu akansu don ta Iyata, Kallon batool tayi tare da cewa"Ki bari In yi musu kitson Kalaba, Nasan ba'ata6a Yi maku ba, Yau zan jaraba mu gani idan zan iya" Cike da Jin daɗi Batool ta mika mata Comb ɗin, Tasa hannu ta kar6a, tare da samun wuri gefen gadon batul ta xauna, Ta ɗago ta kalli su Azeeza dake ta murna za'a gyara musu gashi tace Su zazzauna a ƙasa, zata fara gyarawa azeeza nata idan ta kammala mata zata Kira ta gaba da zata yi mawa,
A ƙasan gadon azeeza ta zauna tsakankanin ƙafafuwan angel, Hannu angel ta sanya tare da Ruƙo sumar kan Azeeza, Launin gashin kanta Dark blonde, mostly Turawa ne suke da irin wannan gashin kan, sharce sumar kan angel tayi, Kafin Ta raba gashin zuwa gida Biyu, a tsanake Ta soma yi mata kalaba, Tunkafin ta kammala su Hanna sai santin kalabar suke yi, duk sun ƙagara a kammala Yima azeeza suma ayi musu, Guda Biyu tayi mata shima daƙyar ta samu Tayi su saboda santsin gashin Ga tsayi da yawa, Tun da aka kammala Yima azeeza kitson, ta miƙe ta koma gefe tana ruƙe wutsiyoyin kalabar da hannayenta, Sai tsalle Take yi Wutsiyoyin kalabar suna yin sama da ƙasa, ita fa yau ta samu abun wasa,
Ɗaya Bayan ɗaya saida angel tayi musu kitson kalaba guda Biyu, Koda akazo kan Batool sai cewa tayi ta gaji bazata Iya ba, bakomai yasa tace haka ba face Fargabar Ta yadda zata Iya kama Gashin batool, Baƙar wahala zata Ci saboda yawan dake gare shi gashi kamar roba kuma Curly irin nata, a dole batool ta haƙura badan taso ba,
Danish Basu Jima da fitowa daga wanka ba, Giants suka zo Kawo musu abinci, Kamar Jiya haka Yau ma suka É—ibarwa Su Parveen Abincin acikin kwandonsu, Da niyar idan Allah yasa Aka dawo dasu Yau sai su basu su ci, gudun kada adawo dasu Da yunwa,
Bayan sun Kammala Cin abincin, Giants suka tattara Farantan suka Fuce daga Cikin É—akin,
Duk sun damu da rashin ƴan uwansu, hakan yasa suka kasa samun natsuwa especially angel, Zarya ta soma Yi acikin aɗakin, idan takai ƙarshen bango saita dawo ta sake zagayowa, Har saida ƙafafuwanta suka soma Yi mata raɗadi tukunna ta dakata da yin zirga zirgar, Ta nufi gadonta da niyar ta huta, gefen gadon ta zauna Zugudum, Zuciyarta acike fal da tunanin duniya, wuraren marece su ka Jiyo alamun motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa, Bayin Allah da gudu suka duro daga saman gadajensu, Jikinsu na 6ari suka ƙarasa ƙopar ɗakin nata suna jira ta fito,
Sandar hannunta ce ta fara leƙowa, Kafin ta zuro kai ta fito waje, Jikinta sanye da jan doguwar rigar nan ta gado,
Kusan atare suka haÉ—a baki Wurin gaishe da ita, Ta amsa masu fuskarta asake, Sai faman mamular baki take Yi kamar me cin goro, fuskarnan a jagwale saboda tsabar tsufa ta koma kamar aljana, hurhura ta ko'ina,
"Tsohuwa Ya jikinsu Deeja? Tun jiya muke ta tsammanin jiran dawowarsu amma shiru ba'a dawo mana dasu ba, Munyi kewarsu sosai, Bacci ma daƙyar muka Yi shi, Ko abinci bama Jin daɗin Cin shi saboda rashin ƴan uwanmu" yasmin ce tayi maganar cikin nuna damuwarta,
Mubeen Yace"tun daga Lokacin da aka ɗaukesu har zuwa Yau, kullum Cikin zullumi muke," Angel dai ta tsareta da ido kamar yarda itama tsohuwar idonta ke akan angel, Kowa da abunda yake saƙawa aranshi,
"Kinyi shiru baki bamu amsa ba? Yaushe za'a dawo mana da ƴan uwanmu? Idan mensturation ne Yanzu ya isa ace jikinsu Yayi sauƙi," Fuska aɗaure angel ta yi mata maganar,
Jinjina kai tsohuwa Tayi, Sai da ta mula tasha Iska Tukunna tace"Ƴan uwanku suna acikin koshin Lafiya, Bazan Iya sanar daku lokacin da za'a dawo dasu ba, Saboda bani da masaniya, amma nasan bazasu wuce Cikin week ɗin nan ba," A ƙagare Azeeza tace"Dagaske Su parveen Sun Ji sauƙi? Kuma Suna tambayar mu? Suma sunyi kewarmu"? Murmushi tsohuwa ta sakar mata tare da cewa"Eh mana, sun damu daku sosai, Kuma suna tambayarku, da zarar Sun ƙarasa Jin sauƙi za'a dawo maku da su" wani irin murmushin farin Ciki ne Ya bayyana akan fuskokinsu, In ka cire mutun Huɗu Batool Angel da javed sam babu walwala akan fuskokinsu, Baka iya tantance awani yanayi suke ciki, da alama suna kokwanton kalaman Tsohuwa, sun dai yi shiru ne kawai,
"Just for today, Ki kaimu inda suke domin muyi musu Ya jiki, Tunda Kince Suma sun Yi kewar mu, hakan zai rage musu damuwa" angel ce tayi maganar
Girgiza kai tsohuwa Tayi tare da cewa"Ba'a bada iznin É—aya daga Cikin ku, Yaje inda suke ba, Idan Ku ka yi hakuri zasu dawo ne" batare da angel ta yi mata musu ba tace"Shikenan zamu zuba ido mu gani idan za'a dawo mana dasu"
Kallon su Batool angel tayi tare da cewa"Ku koma kuje ku zauna, inaso zanyi magana da tsohuwa" Jin wannan maganar yasa tsohuwa tayi saurin kallon angel fuskarta da alamun mamaki,
Juyawa su batool suka Yi atare suka tafi izuwa saman gadajensu, duk wannan abun dake faruwa danish Yana a kwance saman shimfiÉ—arshi, ko sarki bazai nuna mashi Jin daÉ—in gado ba, Ya cancanci da akirashi da MAJI DAÆŠIN GADO,
"Ƴar nan ina sauraron ki, wata Irin magana ce ki ke son Yi dani kuma? Yau ke da kanki"? tsohuwace tayi maganar, fuskarta akwa6e,
cikin sanyin murya angel tace"Inaso mu shiga daga Cikin É—akin ki, Muyi magana" zaro ido waje tsohuwa tayi jin abunda angel tace, Can kuma saita yamutsa fuska tace"Ba dole sai mun shiga daga Ciki ba, Kome Ki ke son tattaunawa dani, Kiyi mini magana anan ya wadatar"
"Meyasa baki son in shiga É—akin ki"? Ko akwai wani abu da bakya son in gani ne? Da tuhuma angel tayi mata maganar, girgiza kai tsohuwa ta yi tare da cewa"Babu abunda nake 6oyewa kawai dai bana bada iznin A shiga É—akina, idan magana zakiyi dani to mu yi ta anan, babu wanda zai ji mu,"
Ta6e baki angel ta ɗanyi still idanuwanta akan tsohuwa tace"yau tsawon shekarata Biyu agidan kurkukun ƙaddara, Ban ta6a ganin wani ya shiga Cikin ɗakin ki ba, Bansan me kike 6oye mana ba, Amatsayinki na uwa agare su, meyasa baki bari muna leƙawa cikin ɗakin ki? Kuma bakya zama acikin mu domin Yin fira, Ko hakan ya sa6awa dokar prison ne"?
Bazawarin murmushi tsohuwa tasaki kafin ta Juya Tana dogara sanda tace da angel"Ki shigo daga Ciki," tsananin mamaki ne Ya kama angel, Jin ta amince mata akan ta shiga Cikin É—akin nata,
Sai da angel ta fara juyawa ta kalli su batool, ganin hankalinsu gaba ɗaya baya akansu Yasa ta bi bayan tsohuwa, Kafin ta shiga ɗakin tsohuwa Sai da takaranta addu'o'in neman tsari, sannan ta zura ƙafarta Cikin ɗakin, bakinta ɗauke da sallama,