← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 179

Sashe 114

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka yi tunani mai kyau, nima ina fata Wata rana Danish Ya canza ya zama kamar kai, tabbas zamu Ji daÉ—i," shiru suka yi na wani lokaci suna kallon juna. Kafin Haris yace"bakomai yafi damuna ba, face rashin batool, Deeja ya zamu yi? Sun É—auke ta almost one month babu alamar zasu dawo mana da ita, na damu sosai, duk in na tuna da batool baki ji yadda nake ji ba, gaskiya bai kamata ace mun yi shiru ba, mutanan nan fa mugayene azzulamai, zasu iya cutar da ita, kamar yadda suka yi maku," hawaye ne kwance acikin idanuwanshi, yayin da yake yin maganar.

Cikin karyayyiyar murya deeja tace"Ae batool sai addu'a, Har ƙwara mu da aka ɗauke mu an dawo damu within weeks, amma ita fa har One month! Wlh ji nake kamar sun kashe mana ita....." bata ƙarasa maganar ba, saboda kukan da ya tari numfashinta, da sauri ta kifa Kanta saman pillow taci gaba kuka. Hankalin haris duk yabi ya tashi, muryar shi araunace yake lallashinta, yana bata haƙuri, akan tayi shiru tadaina kuka kodan saboda ƴan uwan su dake bacci kada su farka, suji suma su shiga damuwa.

Abunda basu sani ba, tunda suka fara magana angel ta farka, ba tare da ta buɗe idanuwanta ba, duk da akwai tazara atsakanin gadajensu amma tana iya jiyo maganganun da suke tattaunawa, wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke mata fuskarta, zuciyarta sai tafarfasa take yi, Tamkar zata 6allo ƙirjinta, aduk lokacin da ta tuna da batool, saita dinga jin kamar ana tunzurata akan ta ƙara dura tagar nan akaro na biyo taje ta nemo ta, ko Allah yasa ta dace, Dama fa ba haƙura ta yi ba, akwai dalilin dayasa ta dakata da kudurin nata, saboda ta lura shiga cikin prison ba abune mai sauƙi ba, dole saita yi mishi kyakkyawan shiri na musamman, kafin ta aiwatar da aikinta, can ƙasan zuciyarta kalaman tsohuwa tamira ne suka shiga yi mata yawo acikinta kanta, tarasa gane dalilin dayasa Suka tsaya mata aranta, tabbas akwai abunda take nufi game da makullan farin cikin nan, kuma tace Idan suka Cigaba da nuna ma danish wariya to wata rana zasu rasa madafar su, ko dan saboda haka dole ta nemi hanyar da zata karya alƙawarin dake a tsakaninta dashi,

numfasawa ta yi tare da ƙoƙarin miƙewa zaune hannunta ruƙe da pillow, ta ɗan juya 6angaren hagu ta kalli su Deeja, har lokacin bata daina kukan ba, haris sai aikin lallashinta yake yi, tun yana akan gadon shi har ya kai ga dawowa gefen gadonta ya zauna, tare da kai hannu yana shafa sumar kanta, daƙyar ya samu Deeja ta yi shiru, ya kwantar da kanshi gefen ta, yana leƙen fuskarta da ta yi sharkaf da hawaye, Angel tana jiyo shi yana faɗi"Hakan ma bazata ta6a faruwa ba, ki daina zancen mutuwa, inaji araina ƴar uwarmu tana araye, zasu dawo mana da ita ne" Cikin shessheƙar kuka deeja tace"bayan sun gama amfani da ita ko? Sai sunyi mata kamar yadda su ka yi mana, ko ka manta yadda aka dawo dani ne? Tae tambayar tana kallonshi da rinannun idanuwanta waɗanda suka kaɗa Jawur dasu, Zuciyarshi ta karaya sam ya kasa magana

Ta ci gaba da cewa"A wulaƙance, aka dawo dani, ji lokacin da aka dawo dasu Hanna, Hada yakushin akaifa akan wuyansu, le6e duk ya bushe ya faffashe jini yana tsastsafowa, idanuwa sun jagwale da ruwan hawaye.....haris duk da bamusan me akeyi mana ba, amma munji raɗaɗin azaba ajikin mu, mun yi jinya, mun yi kuka tamkar rayukanmu zasu fita daga gangar jikin mu, Iya cuta dai ancuci rayuwarmu," tana faman jan majina ta ɗaura da cewa"Ina tsoron Awani hali za'a dawo mana da BATOOL! ita da ta ɗauki tsawon lokaci ahannun su, mugaye azzalumai Allah kaɗai yasan me su ke ƙunsa mata a yanzu haka......"

Deeja bata kai ƙarshen maganar ta ba. Sakamakon jin sautin kukan angel, A matuƙar ruɗe su ka ɗago daga saman mattress ɗin suna kallon shimfidarta, A lokacin harta duro daga saman gadonta, da gudun gaske ta nufi sashen toilet ɗinsu ta shige, damuwa ce ta bayyana akan fuskokinsu.

"Tun yaushe ta farka? da ace na sani da ban yi maganar ba, bari naje in lallashe ta, nasan dole taji raɗadi acikin zuciyarta," Deeja na yunƙurin miƙewa haris yae saurin katse ta, ta hanyar yi mata magana,

"kada kije, Ayanzu bata buƙatar kowa a kusa da ita, ganinki zai ƙara karya zuciyarta saboda kece kika yi maganar..."

"Amma tana buƙatar wanda xai lallashe ta, kana ji fa tana kuka"

"Nasani, kema yanzu kika gama kukan inata aikin lallashi, Ki koma ki kwanta, Zanji da ita" sai da ya samu ya kwantar ma deeja da hankali, kafin ya miƙe ya nufi sashen toilet ɗinsu, Har satar kallon shimfiɗar danish yai ta wutsiyar idanuwanshi ya hange shi kwance saman gadonshi, aranshi yace"Kaji haushin rayuwarka, wato baka ci abincin ba, sabbin uniform ɗin ma ba za ka sanya ba, saboda Taurin kai irin naka," Guntun tsoki yaja yayin da yake shigewa cikin toilet, tunkafin ya ƙarasa ciki ya same ta zuƙunne agaban tukunyar fulawar nan, Ta tasa ta gaba sai kuka take yi kamar ranta zai fita,

"Why angel? Wannan kukan fa da ku ke yi bazai kare ku da komai ba, Ina fama da deeja, kema kuma kin kama kuka, nasan saboda kinji maganganun da muke tattaunawa ne," a bayanta ya tsaya hannayenshi rungume saman ƙirjinshi,

Cikin shessheƙar kuka tace"Bazan Iya jurewa bane, Batool tana can Hannun fasiƙan mutanan can, Cikin mawuyacin hali, Nagaza zuwa in taimake ta, nasan Ta jira zuwana taji ni shiru, dole taji ba daɗi duk irin ƙaunar dake a tsakanina da ita," A gefenta haris Ya zuƙunna Ya soma lallashinta kamar yadda yayi ma deeja, A ƙarshe Ya ruƙo hannunta yace"Ki taso mu koma ɗaki" Maƙe mashi kafaɗa tayi"a'a Kabarni anan, Inaso zanyi ma furennin addu'a" gyaɗa kai yai tare da miƙe wa, da niyar yabar toilet ɗin, har ya juya zai fita sai kuma ya ɗan dakata tare da kallonta yace"Angel, badan halina ba, badan na isa dake ba, pls Ki karya alƙawarin dake a tsakaninki da Danish! Idanuwanta jawur ta juyo tana kallon haris, yaci gaba da cewa"Ki tausaya mashi, dama ba cikakkar lafiya ce dashi ba, yanzu kuma kin ƙara jefa shi cikin wani hali, duk fa saboda ke ya gaza sakewa acikin mu, yaƙi cin abinci yaƙi canza uniform ɗin jikin shi, ni bansan ya akai kika sa ya ɗaukar maki alƙawari fa" fuskarshi a yamutse yayi maganar, Hannu tasa ta matse tsinin hancin ta, yayin da take kallon shi, muryar ta ƙasa ƙasa tace"haris, Nasan ban kyauta ba, nima nayi regretting da na sanya shi ya ɗaukar min alƙawari, raina ne yake a6ace, Amma har ga Allah ni bana fushi dashi ayanzu, sai da nace mashi nafasa promise ɗin, Mu shirya amma yace min shi bai fasa ba......" kaf angel ta kwashe duk yadda su ka yi atsakaninta da Danish ta sanar mashi,

Dafe goshi haris yae da hannun shi na dama kafin ya zame shi ya ruƙe qugu yana faɗin"Oh my God, Danish matsala, kin san shi da ruƙe alƙawari, idan har mu ka ce zamu biye mashi bamu san har tsawon wasu kwanaki za'a ɗauka ba, Yana Cutar da kanshi, Tun da ba mu san ranar da za'a dawo da Batool ba, kuma bamu da tabbacin cewa idan an dawo da ita zata yafe mishi," Dakatawa yae da yin maganar yana kallonta, itama shi take kallo,

"Yanzu ya zamu yi kenan? Alƙawarin Ya karye" Haris ne yai tambayar, shiru angel tayi na wani lokaci tana yanke shawara daga cikin zuciyarta,

"Kin yi shiru" a ƙagare yae mata maganar, har ya fara gajiya da tsayuwa,

"Kada ka damu haris, Ni nasan yadda zanyi dashi, In sha Allah a daren yau ɗin nan zan karya alƙawarin, " ajiyar zuciya haris ya sauke fuskarshi asake yace"Dama nasani zaki Iya!" ya ambaci hakan tare da juyawa da sauri ya fuce daga Cikin toilet ɗin,

Lokacin daya shiga Room ɗinsu, Su parveen duk sun farka daga bacci, sai surutu suke yi. Kamar ba waɗanda suka sha bacci ba, Kowacce Tana daga zaune saman gadonta, Hannah tana hamma tace"Wai ina angel ɗinmu take ne? Naga banganta ba" hibba tace"yanzu haka tana acikin toilet, wani uzirin ne ya kamata," saukowa daga saman gado azeeza tayi tare da cewa"Nima toilet ɗin xan shiga" takarasa maganar tare da wuce wa ta nufi sashen toilet, tuni haris ya jima da komawa saman gadon shi, ya zauna yana yi musu sannu da farkawa bacci, sarakan ɗumi yanzu xa'afara, gaba ɗaya suka kama dariya, Parveen na miƙa tace"Motsa Jiki zamuyi, Jiki na duk ya ruƙe, " Haris yace'ae dole, An cika ciki yayi haiƙam ta ko'ina babu space ai dole ki nemi motsa Jiki, ko kin samu Cikin ya kwance Aje toilet kamar yadda aka saba," Wani irin kallon harara take jefa mashi, Eve tace"Haris ka sanya ma sis parveen ido Allah, bansan me tayi maka ba" Ta6e baki yai"ae tunda tace ban da kyau saita gane kuren ta," Deeja dake kwance tana jin muryoyinsu Acikin kunnanta, taƙi motsawa ne don kada suga halin da take ciki na damuwa,

"Yakamata Baƙin prisoners ɗin nan su ƙaraso tunkafin Ku 6alla musu gadajensu" javed ne yai maganar idanuwanshi rufe, yana kwance saman nashi gadon,

"Idan ma akwai wanda zai 6alla musu gado to bai wuci ku ɗin nan ba, saboda kune ƙattai da kai da haris da mubeen da naufal, gadon ma yayi maku ƙanƙanta" parveen ce tai maganar tana gatsina mashi hanci,

Wani irin kallo haris da javed suke jefa mata jin abunda tace, Naufal dai bai tanka musu ba, tun da ya farka bai mike zaune ba, mubeen dai ne ya tada kanshi saman pillow,
Chapter 114 · 0% Book details