← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 179

Sashe 81

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin sun samu natsuwa yasa Ta fara jan hankalinsu zuwa ga addinin musulunci, Idan dare Yayi bata barinsu Yin bacci, Tarihin annabawa take basu tun daga kan tarihin Annabi Muhammad (SAW) Cikin hikma take Basu tarihin, Kuma ga dukkan alamu ba ƙaramin daɗin shi suke Ji ba, domin kuwa idan ta fara basu tarihin, Ko fitsari mutun ke ji sai kaji yace a jira ya dawo sai acigaba, idan kuwa tace ta gaji abari gobe zata ƙarasa musu kamar su yi mata hauka, Taci wahala sosai Wurin janyo hankalinsu duk da bata ci nasara ba saboda duhun jahilcin dake akansu, Suna Yi mata tambayoyin ƙural da suka fi ƙarfinta musamman haris, Da yace idan har akwai Allah wanda ya halicce su to meyasa bai ta6a zuwa ya kawo musu ziyara ba? Ire iren irin waɗannan tambayoyin sune kesa tana karaya wani lokacin, Ita dai tayi iyakar bakin ƙoƙarinta wurin sanar dasu gaskiya, Sauran kuma tabar ma Allah domin kuwa shi kaɗai ne zai basu ikon musulunta idan yaso, mutun huɗu ne acikinsu ta lura da suna matuƙar son Addinin, Batool, Azeeza da Javed, sai kuma parveen, sauran kuwa kokwanto ne Ya hana su yarda da ita saboda wasu tambayoyin su da ta gaza amsa musu, shi danish bama tasan a wata matsaya yake ba, Yana dai son tarihin annabawan da take basu, Sai dai Babu alamar yana da niyar kar6ar addinin nata, mutun huɗun nan da suka nuna suna da interest sune suka fara kar6ar addinin musulunci acikinsu, Ta biya musu kalmar shahada, Kusan Yini guda suka ɗauka tana ta fama dasu akan su maimaita sun kasa furta ta, Sai cikin dare Wani iko na Allah tana sake biya musu sai gashi sun maimaita lafiya lou batare da inda inda ba, Tayi farin Ciki sosai kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha, Duk da farin Cikin nata ragagge ne tun da sauran basu kar6a ba, Tafi damuwa akan danish saboda tana ji aranta idan har ya kar6i addinin zai taimaka ma sauran ƴan uwan nashi saboda suna jin maganarshi sosai, duk da haka bata ƙyale shi ba, ta addabi rayuwarshi ta hana shi sakat, Sai yana tsaka da yin bacci ya dinga jin muryarta acikin kunnanshi tana karanta mashi kalmatusshahada, wato da tsiya sai ya kar6i addinin, babu yarda batayi dashi ba, Amma Yaƙi bata haɗin kai a ƙarshe da ta gaji ta ƙyale shi badan ta haƙura ba, Ta dai bashi lokaci ne ya ɗan sarara, duk da haka bata yi fushi dashi ba, Sai ma ƙara janshi da take yi ajikinta, saboda sanin mahimmanci da yake da shi, dole saida shi wasu abubuwan zasu tafi dai dai, a 6angaren su batool da suka musulunta, tafara ƙoƙarin Koya musu addu'o'i da karatun kur'ani, sai dai wani abu dake ɗaure mata kai, Wahalar da suke sha wurin furtawa, Ita parveen ma hada amai take Yi idan angel ta matsa mata akan ta furta karatun kur'ani, ita kuma azeeza daga anfara sai ta kama bacci, ba ƙaramin takaici angel ke ji ba, daga bisani tayi wani zazzafan nazari, Acikin kwanakin kowani sati akwai wace rana da idan dare yayi tayi musu karatu suke amsawa lafiya lou batare da sun kakare ba, a irin ranar ne ta ta6a yi ma danish karatun kur'ani da daddare lokacin da giants suka dawo dashi kuma dai dai lokacin ne take basu tarihin annabawa batare da ta samu targaɗe ba, Kuma a irin lokacin ne su batool suka furta kalmatusshahada batare da sun yi inda inda ba, duk irin lissafin kwanakin da take yi Tun lokacin da daddynta Ya gudu da ita bata ta6a bari lissafin kwanakin wata sun ku6uce mata ba, Sai dai wannan karan ta kasa gane wace rana ce wannan mai tarin albarka? Meyasa take samun dama A ranar? Bata iya hasashen wace rana bace sai dai tana ganeta ne da alamominta, duk irin ranar ta zagayo bata bari ta tafi abanza, kusan kwana suke Yi da daddare tana Koya musu karatu tare da yi ma sauran ƴan uwan nasu da'awa kota samu suma Su kar6i addinin, Allah mai yarda yaso, Sai gashi ɗaya bayan ɗaya suna zuwa wurinta suna cewa suma zasu musulunta, cikin waɗan da suka kar6i addinin musulunci akwai, batool, azeeza, Hannah, Hibba, deeja, parveen, Eve, yasmin, Angel, Batool, rubina, Cikin maza mutun uku, Javed, Naufal da Mubeen, yanxu mutun biyu ya rage mata acikinsu, Haris da danish, Su kaɗai suka yi mata cikas, Duk da Tayi matuƙar yin farin Ciki, Da Allah ya bata ikon musuluntar dasu Hanna, Ranar da suka kar6i shahadar ko bacci bata yi ba, A tsakiyar gadonta ta zauna tana kukan farin ciki tare da Yi ma Allah godiya, daya bata wannan damar, Nima dai Na matse kwallata kuma na tayasu murna koba komai sun tsira da imanin da su ka yi, Allah zaiji ƙansu,

A wani dare Ne, dukkansu Sun kwanta bacci, Angel tana a kudundune cikin bargonta, kwatsam ta soma Jin shessheƙar kukan mutun acikin kunnuwanta, tun bata ɗauki abun serious ba har sautin kukan ya fara disturbing ɗinta, Sai kuma ta dinga jin hannun mutun asaman jikinta kamar ana bubbuga ƙafarta ƙasa ƙasa ta jiyo miryar mutun yana yi mata magana, A hanzarce ta yaye bargon jikinta ta ɗago da idanuwanta masu ɗauke da bacci biji biji take Iya ganin fuskarta, tana a zuƙunne gaban gadonta, fuskarta sharkaf da hawaye,

Mutsustsuke idanuwanta ta yi da yatsun hannunta don ta samu damar ganin kowacece, koda tayi arba da deeja sai taji gabanta ya faÉ—i rass! Tun kafin ma takai ga faÉ—a mata abunda ya kawo ta,

"Angel Jinin nan ne ya dawo mini, Na shiga toilet in yi fitsari shine naganshi, hankalina Ya tashi sosai bansan Ya zanyi ba," fuskarta a yamutse tayi maganar, dafe kai angel tayi tare da ambaton"INALALLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN! wannan wata irin masifa ce, mun shiga uku! Ni nayi tunanin Kun daina gaba É—aya, ashe da sauranshi," idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar,

Ruƙo hannunta deeja tayi acikin nata"Dan Allah angel, Ki san yadda za'ae ki hana atafi dani, wlh gani nake kamar idan aka ɗauke ni wannan karan baza'a dawo dani ba," tana kuka ta yi maganar, Hankalin angel ya tashi matuƙa, Saukowa Tayi daga saman gadon ta nufi gadon Danish, Hannu takai ta ruƙo bargon daya lullu6a dashi ta yaye shi, Bubbuga ƙafadarshi tayi tare da ambaton sunashi"Danishi!danish!" daƙyar ta samu ya farka, Yana faman yamutsa fuska Yace"menene"?

"Pls ka tashi deeja bata da lafiya, Menstruation ne Yazo mata" ware idanuwanshi ya yi jin abunda tace, Saboda ya gane me take nufi, tun da tayi musu bayanin komai dangane da jinin,

"Dan Allah Danish kada ku bari Giants su ɗauke ta, mu taimaka mata," yunƙurawa yayi tare miƙewa ya zauna saman mattress ya jingina bayanshi jikin bango, batare daya ce komai ba, idanuwanshi na akan deeja dake a zauƙunne sai kuka take Yi,

Ganin baida niyar tanka mata yasa ta wuce gadon haris, ta tada shi, daya farka ta sanar dashi abunda ke faru wa, Jikinshi har 6ari yake Yi, duk yabi ya ruɗe ya sauko daga saman gadonshi, Yana tambayarta Ina deejan take, Tun kafin ma ta bashi amsa sai ga deeja ta nufo su, Tana karasawa gabanshi ta fashe da kuka, Ruƙo hannunta yayi acikin nashi Ya janyota jikinshi Yana lallashin ta yana faɗin"ta kwantar da hankalinta, Ba wanda ya isa ya tafi da ita sai dai ahaɗa dashi atafi amma bazai ta6a bari giants su ɗauke ta ba, muddin Yana numfashi" Angel taji daɗin kalaman da haris yayi duk da tasan zaiyi wuya ya iya hana su tafiya da ita, Ga wanda taso Ya harzuƙa can saman gado Amma Yaƙi cewa komai, Haushin shi duk ya cikata, ta tsani halayyarshi ta lalaci da rashin son ta6uka komai,

"Haris Bari in tada su Naufal, In yaso sai mu haɗu mu duka mu hana su tafi da ita" Yace mata"toh" ɗaya bayan ɗaya tabi kowannan su saman gadanshi ta tada shi, duk wanda ya farka, Yaji abunda ke faruwa sai gaka ya zare ido saboda fargaba da tashin hankali, A tsakiyar ɗakin suka hallara su goma sha huɗu, sun sanya deeja a tsakankanin su suna jiran giants su ƙaraso, da alama yau sun shirya yin faɗa da Giants,

Motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa suka Jiyo, Da sauri suka kai idanuwansu kanta, a lokacin ta ƙarasa fitowa daga Cikin ɗakin Hannunta ruƙe da sanda, fuskarta a yamutse babu annuri babu walwala, Ɗagowa tayi tare da kallonsu

Babu wanda yayi yunƙurin yi mata magana, Sun ɗaure fuskokinsu, Saboda mugun haushinta da suke Ji,

Azeeza ce tace"ni dai bari in je in roƙeta kada ta bari atafi da deejan mu" har ta ɗaga ƙafa zata je wurin ta, Haris Ya damƙi hannunta tare da cewa"Ashe baki da hankali? Idan kinje kin roƙe ta me zata Iyayi mana? In banda ƙarya"? Wannan maganar ta haris tayi matuƙar girgiza tsohuwa,

Angel tace"Allah ya kamata ki roƙa ba ita ba, saboda shi kaɗai ne zai Iya taimakon mu amma waccan matar, Ba abunda zata yi mana," takai karshen maganar idonta akan tsohuwa,

Jinjina kai tsohuwa ta yi jin abunda haris yace, daga bisani ta Dogara sandarta zuwa inda suke atsaye taci burki ta tsaya, ɗaya bayan ɗaya ta shiga binsu da wani irin kallo, sun rasa gane kallon menene take Yi musu, Juyawa tayi tare da kallon danish dake zaune saman gadonshi, Dama shi kaɗaine baiyi yunƙurin miƙewa ba, da alama baya goyon bayan abunda suke shirin aikatawa,

"Saboda shi yafi ku wayau da hankali shiyasa bai biye maku ba," tsohuwa ce tayi maganar a lokacin da ta janye idanuwanta daga kan danish ta mayar dasu kan angel, Ido cikin ido suke kallon juna,

Murmushin takaici ne ya bayyana akan fuskar tsohuwa,

"Koda gigin wasa kada ku kuskura kuce zaku Hana giants tafiya da deeja!! ina gargaɗinku idan har kuna son zaman lafiya to ku daina yunƙurin shiga huruminsu....." Haris ne ya dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa yace"Wai ina ruwanki da rayuwarmu ne? Bakin nuna baki damu da mu ba? To ki fita sabgarmu mana? Idan ke bazaki Iya hana su tafi da ita ba, to mu ki barmu muyi da kanmu" rai a6ace yai maganar,
Chapter 81 · 0% Book details