← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 179

Sashe 66

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haris come out dakai zan fara, zaka gano mini deeja," fitowa haris yayi daga Jerin layin da yake yaje gabanta ya tsaya yana fuskantar sauran Æ´an wasan, Hanna ta tsaya daga bayan shi ta zagayo da hannayenta saitin fuskarshi ta rufe mashi idanuwanshi da tafin hannayen ta,

Tafiya su ka yi agaban layin na farko, Kowa yasha Jinin jikinshi, daga haris yakai hannu zai canko mutun, sai kaga suna girgiza kai, gudun kada yaja masu dundu, Cikin rashin sa'a haris Ya ruƙo hannun mubeen yace Itace, aikuwa gaba ɗaya suka fashe da dariya, mubeen kuwa rai a6ace yace"amma dai haris anyi hamago, kai baka gane hannun mace da namiji ne? Deeja ce fa akace ka kamo ba ni ba," Maganarshi tayi matuƙar basu dariya, hatta tsohuwa saida ta murmusa,

"Kamar yarda nace a dokar wasa, Idan mutun ya canko ba dai dai ba, Da shi da wanda ya canka kowa xaiyi masu dundune, don haka Mubeen da haris ku zuƙunna ku bamu bayanku,,

Mubeen yana Cika yana batsewa ya fito daga cikin layi, ya Duka shima Haris Ya duƙa, kowa ya naɗe hannun rigarshi, babu tausayi babu imani, haka suka jera layi, suka dinga kai masu dunduna abayansu, koda akazo kan angel dama haushin haris take ji, Muguwar da gwiwar hannunta ta daddage ta buga mashi ƙulli a baya, har wani sauti ya bata durum! nan take ya kife ƙasa, dama shi mubeen tuni ya zube yana mayar da numfashi ido sun ciko tab da kwalla, koba a faɗa mashi ba yasan wacece tayi mashi wannan dundun, idanuwanshi akan fuskar angel yaci alwashin sai ya rama idan idan aka zo kanta,

Hanna tace"the next person is, " kowa ya kasa kunne yana jira yaji su wanene,

Murmushin mugunta ta saki kafin tace"Batool! Ki gano mana Javed," Jiki ba ƙwari Batool ta fito daga Ciki layinta, Hanna ta rufe mata ido da tafin hannunta, suka soma tafiya suna Bin layin na farko, Duk wanda ta ruƙo hannunshi saita saki, harfa ta ruƙe hannun javed ta murza shi kamar tace shine sai kuma ranta ya bata cewar bashi bane, ƙasa ƙasa da murya yake ce mata ke ni ne, ki ce ni ne,' amma ina batool sai ta tsalleke shi ta ruƙo hannun Parveen, wadda tuni fitsari ya kamata, motsa lips ɗinta tayi tare da cewa"He is the one"

Hanna tace"you're wrong" tayi maganar tare da zame hannunta daga kan fuskar batool,

Waro ido tayi ganin parveen, gaba ɗaya suka fashe da dariya, Cikin shessheƙar kuka parveen tace"Ban yafe ba, Kinja min bala'e, "

Janyo kwalar rigarta batool tayi'hakuri zakiyi, dama kinfi kowa Cin abinci yau, Kizo kawai mu basu baya suyi mana dunduna, ba yadda ta iya haka suka duƙa, kowa yayi masu dundu abaya, parveen tasha kuka, ita kanta batool saida ta matse ƴar kwalla, don da mugunta suke yin dundun,

Komawa su kayi Cikin layi, next person da aka kirawo, Azeeza ce aka ce ta Canko masu Naufal, hanna ta rufe mata idanuwanta, Da yake Allah yayi mata baiwa, duk wanda ta ruƙe hannunshi saita shinshina kamar mayya, wai da ƙamshin jikinsu take amfani, tana zuwa kan hannun naufal ta shinshina, sai ce wa tayi"Shi ne" gaba ɗaya suka sanya sowa, " tsohuwa fa yau ta samu abun nishaɗi, sai faman murmushi take yi, har lokacin basu son cewa tana atsaye bakin ƙopar ɗakinta ba, tana kallonsu,

Babu rabon azeeza tasha dundu, angel dai sai fargaba take yi, ta ƙosa layi yazo kanta taji wa za'ace ta canko, Har Allah Allah take Yi acikin zuciyarta,

Mutane na gaba da aka kira, Deeja ce akace ta gano Danish!!, hanna ta rufe mata idanuwanta suka tafi suna bin layi, duk wanda ta ruƙe hannunshi saita saki tace bashi bane, hankalin angel yayi matuƙar tashi, fargabarta kada Deeja ta cankota, taja mata bugu, aikuwa dai deeja tana zuwa gaban angel ta damƙi hannunta, har kusan fitsari saida angel tayi, aruɗe take girgiza mata kai kamar tana ganinta, har ta buɗe baki zatace shi ne, sai kuma ta saki hannun angel ta ƙara gaba, nauyayiyar ajiyar zuciya angel ta sauke hada sanya hannu ta shafa ƙirjinta, taji daɗi,

Cikin rashin sa'a deeja ta canko Rubina tace shi ne" rubina taji haushi, shaƙo wuyan Deeja tayi tana jijjigata tace"saboda ke shashasha ce, ta ina hannuna yakai na danish tsayi? Ba ki ga yatsun hannayena guntaye bane? Ke baki banbancewa ne? Gaba ɗaya suka fashe da dariya, hatta danish dake a tsaye saida ya ɗan saki murmushin gefen fuska,

Hanna tana dariya tace"Ba faɗa bane wasa ne, Kuyi haƙuri kuzo ku xuƙunna, Ku kar6i la'adarku" rai a6ace Rubina ta fito daga Cikin layi, takai hannu ta jan yo wuyan rigar Deeja, suka shiga tsakiya, Suka duƙa, ɗaya bayan ɗaya kowa yazo yana yi masu dundu abaya, koda aka zo kan angel, saida ta naɗe hannun rigarta, dama haushin deeja take ji, ta daddage da iya ƙarfinta na ƙarshe ta Buga mata dundu abaya, har saida deeja ta kife ƙasa tana kuka,

Girgiza kai tsohuwa tayi ganin irin muguntar da angel ke yi masu wurin Yin dundu, ta kosa layi yazo kanta taga idan ita zata Iya tsira🤣

"Tun da naga mutane sun ragu, saura mutun huɗu suka rage, bazai yiyu abaku za6i ku canka ba, Sabo da za ku yi nasara Cikin sauki, don haka gaba ɗaya ƴan wasa su dawo Kan layi," hanna ce tayi maganar idonta akan su Haris dake zuƙunne suna jinyar bayansu,

Miƙewa su kayi kowa yana hura hanci, Suka Koma Kan Layi, Tofa su angel murna ta koma Ciki, ganin sun koma su goma sha huɗu,

"Adai dai ta natsuwa, Last 4 person da suka rage, zan fadi sunayensu, akwai Eve, Angel, danish and hibba, sai kuma Ni hanna cikon ta Biyar, Yanzu Zan koma Cikin ƴan wasa, Batool ke ce zaki wakilce ni, A matsayin alƙalin wasa, a dokar wasan Sabon alƙali zai Iya faɗin nashi sabbin dokokin,"

murmushin mugunta batool tasaki, harta hango haÉ—in da za ta yi, Fitowa ta yi daga kan layi, Ta koma ta tsaya a inda hanna take, Ita kuma hanna ta koma Kan layi ta jera da sauran Æ´an wasa

Idon kowa ya koma kan alƙalin wasa Wato batool, a tsanake ta soma magana" A matsayina na sabon alƙalin wasa, Ina da tawa sabuwar dokar, Mutane biyar da suka rage idan har na canko ɗaya daga Cikinsu, na bashi sunan wanda zai za6o mini, idan ya kuskura ya canko ba dai dai ba, dashi da wanda aka bashi sunan shi ya gano kowa Zai yi masu dundu A bayansu, Sa'an nan babu su babu Cin sauran abincin da muka rage, kason su za'a raba ma sauran Ƴan wasa ne su Cinye" tun da batool ta soma kora jawabi, hankalin angel ya ɗunguzuma, ba ita kadai ba hatta hibba da eve da hanna sai da hankalinsu ya tashi, Jin wannan Dokar ta batool, taya za'a raba ma sauran ƴan wasa abincinsu idan suka yi failing, akwai matsala babba,

Idon batool akan Na Angel data cika ta batse, murmushi ɗauke akan fuskar batoo tace"Next person Is......." Gaba ɗaya sun baza ido suna sauraronta, hatta tsohuwa a ƙagare take da taji wa batool zata Canko,

"Danish! " a hankali ya É—ago da lumsassun idanuwanshi ya É—aurasu kan batool, Yana jiran Jin wa zata ce ya canko,

Tunkafin batool ta ƙarasa maganarta, angel ta shiga girgiza mata kai daga inda take a tsaye Cikin layi, Alamar kada tace ya gano ta, don tasan halin danish zaiyi wuya ya iya canko ta, ita da take da tarin maƙiya acikin wasan kowa so yake tayi failing don tasha dundun, expecially haris da Deeja, a ƙule suke da ita, don har yanzu basu daina jin raɗadin dundun da tayi masu ba,

"Danish zaka Canko mana ANGEL, kafin mu fara zan ƙara tunasar dakai dokar wasa, idan har kayi kuskuran canko wadda ba ita ba, Kowa zaiyi maku dundu, sa'annan babu ku babu Cin abinci an jima, za'a raba ma sauran ƴan wasa naku" wani irin murmushin mugunta haris da deeja suke saki, daɗi kamar ya kashe su, don sunsan cewa Danish bazai iya canko daidai ba, saboda halinshi da suka sani,

Cike da shaƙiyanci deeja tace"Ina fata Danish Ya gaza canko ki, Na rantse hatta spinal cord ɗinki sai ya amsa idan nayi maki wani mugun ƙulli" tayi maganar tana kwatanta yadda zata bugu bayan angel da hannunta, gaba ɗaya suka sanya dariya, angel kuwa ta ɗaure fuska babu walwala kwata kwata, duk tasha jinin jikinta,

Haris yace"ni kuwa Da gwiwar hannuna zan daki bayanta har sai ya 6urma, In yaso su Giants sunyi jinyarta a treatment room," gaba É—aya suka sanya dariya cikin nishaÉ—i, idanuwan angel tuni sun cicciko tab da kwalla, tabbas ta gama karaya domin kuwa tasan danish bazai ta6a iya gano ta ba acikinsu,

"Danish come forward" Batool ce ta yi maganar tana nuna shi, fitowa yayi daga Cikin layi, ya ƙarasa gaban Batool ya tsaya, saboda tsabar mugunta haris hada cewa ajira ya cire rigarshi, a ɗaure ma danish fuska da ita, don yasan tsayin Batool bazai kai na danish ba, hakan na nufin bazata Iya datse mashi ido da tafin hannayenta ba, batare daya samu ƙofar da zai iya kallonsu ba, jama'a kowa fa yaci burin bugun angela,

Hannu haris ya sanya tare da tu6e rigarshi, Ya wurga ma batool ta sanya hannu biyu ta ca6eta, idon danish akan na angel da tabi ta kame kanta, kamar ta fashe da kuka,

ÆŠaure mashi fuska batool tayi da rigar haris, ta matse mashi ido sosai har saida yaji zafi,

"U can Start" ta ambaci hakan tana kallon shi, tafiya ya soma Yi yana lalubansu, ya ruƙo hannun rubina ya saki, ya ruko na azeeza ya saki, ya ruƙo na eve ya saki, ya kuma ruƙo na parveen ya saki, Kowa ya zuba ido yana kallon shi, ya cafko hannun javed ya murza shi, Kowa yayi tunanin shi zai canka amma sai suka ga ya saki hannun,
Chapter 66 · 0% Book details