← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 179

Sashe 140

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

jiki na 6ari ya ƙarasa ciki, atare da Angel su ka ruƙo Danish, daƙyar daƙyar suke jan shi saboda jikin nashi ba ƙwari, kamar lagwanin fitila, A haka suka janyo shi har zuwa bakin ƙopar fita daga cikin sashen toilet din nasu, duk inda suka taka sai jinin shi ya ɗiɗdiga

Kamar jira ake su dira ƙafafuwansu saman floor ɗin ɗakinsu, Ba zato ba tsammani, Su ka soma Jiyo motsin buɗe ƙopa, A matuƙar gigice Gabriel da Angel suka kalli ƙofar, Wata irin zufa ce ta shiga wanke fuskokinsu, damuwa ce ƙarara akan fuskar Angel.

Wani gabjejen Giant Ne ya shigo ɗakin Yana tafiya Tsokokin Jikin shi na motsawa, zazzafan gaske Star biyu ce a gaban rigar shi, a gaggauce yake taka staircases ɗin benan tsabar sauri kamar zai tashi sama, Da zafin shi Yake taka ƙafafuwan shi.

batasan lokacin da ta fashe da wani sabon kukan ba, don tasan zuwa akai araba ta da Danish dinta, Sautin kukan Angel ne ya farkar dasu Haris, Hakalinsu a matuƙar tashe suka soma buɗe idanuwansu kusan atare Kowannansu ya yaye bargon da ya lullu6a da shi, sai dai kafin su yi yunƙurin saukowa daga saman gadonsu, Tuni wannan giant ɗin Ya jima da ƙarasowa ciki, tsabar tsoratar da Gabriel yai ne yasa shin Yin saurin sakin Danish yabar Angel da ruƙon shi, kamar amafarki su haris suke kallon Danish da Jini ya wanke ma fuska, ruɗu ya hana su gane wanene.

Yayin da wasu daga cikin su ke kallon Giant ɗin da ke tafiya yana tunkarar su Angel, Lamarin yai matuƙar ɗaure musu kai, Sun gaza yarda da abunda idanuwansu ke nuna masu, Tana ji tana gani, Giant ɗin nan ya sanya hannu biyu Duk irin tsayin Danish Kamar jinjiri Haka giant ɗin ya ɗauke shi tare da ɗaura shi saman kafadar shi, Cikin Zafin nama Ya juya dashi, Ya nufi Benan, Da gudun gaske Angel tabi bayan shi, tana kuka tamkar ranta zai fita tana ambaton sunan Danish, Adai dai bakin stair ɗin tai tuntu6e wurin taka staircases ɗin Gaba ɗaya ta kife kanta Ya daki ƙasa, ko motsi bata yi ba. Ga dukkan alamu ta sume ne, sai bayan da Giant ɗin Ya fuce daga Cikin ɗakin, Ƙopar na rufewa ta bada wanj irin sauti Garam!!

Shi ne silar dawowar su Cikin hayyacin su, Azeeza ta fashe da wani irin matsanancin kuka tun kafin ma taji meya faru, sautin rufe ƙopar ɗakin su ne yasa ta fahimci cewa Giants ne suka tafi da wani, shiyasa ta fashe da kuka, Jikin Haris har 6ari yake yi wurin saukowa daga saman gadon shi yana bin Fuskar Gabriel da kallo wanda Ya ƙame jikin bango tsabar tashin hankali ne akan fuskar shi, ɗaya bayan ɗaya kowannansu Ya sauko daga saman gadon shi, Tun kafin ma su soma tambayar Gabriel a ruɗe yake girgiza musu kai hawaye nabin fuskarsa,

Muryar haris aruÉ—e ya furta"wanene aka fita dashi? Meya faru ne naga jini a jikin ka? Meyasa Angel ta ke kuka tana ambaton sunan Danish? Allah yasa mafarki nake yi ba gaske ba, zaifi min kwanciyar hankali na, akan ace wani abu ne ya faru da shi"!

tsabar ruɗanin da Gabriel ya shiga ne yasa shi Yin su6ul da baka wurin furta"Bada son raina na aikata mishi hakan ba, bansani ba, Ku ƙyale ni ku rabu dani inji da abunda ke damuna! ' zuƙunnawa yai saman gwiwowinsa kamar ƙaramin yaro haka ya fashe da wani sabon kukan.

"Hakan na nufin wani abu ya samu Danish! Kada ka ce min Jinin shi ne wannan a jikin ka," haris ne yai maganar tare da sanya hannu biyu ya damƙi gaban rigar Gabriel ya ɗaɗɗago dashi Ya buga shi jikin bango, Idanuwanshi tuni sun rikiɗa sunyi jawur dasu

"ka faÉ—a min Me ka aikatawa Danish? Jinin wanene a jikin rigarka!

Yana magana tsokokin fuskarsa na motsawa, Kasa buÉ—e baki Gabriel yai duk yabi ya firgice,

Hankalin su Deeja ya tashi sosai, Har sun fara sharar ƙwalla Saboda sunji a jikin su wani abu ne ya faru da Danish ɗinsu, Da gudu Su hanna su ka nufi Angel da ke baje saman matakalar bene A saman laps ɗinsu suka kwanto da ita, Sai ku ka su ke yi suna ambaton sunanta haɗi da bubbuga jikinta akan ta tashi ta faɗa musu meya faru da su.

Kukan azeeza yafi na kowa sauti, Ta cika ɗakin nasu, Takaici biyu ga rashin ido, Ga takaicin halin da take tunanin waninsu ya shiga, Na tashin hankali, Abun ba ƙaramin ƙona mata rai yake yi ba, tana matuƙar jin zafin makantar daren da take fama da ita.

Takaicin duniya ya ishe su, kamar su yi hauka, Gabriel ya ƙi buɗe ba ki ya basu amsar tambayoyinsu, kuma shi kaɗai ne zai iya faɗa musu abunda ya faru.

Ga Angel taƙi farkawa, Har ruwa suka yayyafa mata amma bata farfaɗo ba, Babu wanda ya iya runtsawa acikin su, Zuciyoyinsu sun karaya sosai musamman Haris da ya gane cewa An tafi da Danish din shi Cikin mawuyacin hali, tuni zazza6i ya kama shi mai zafin gaske, Ciwon kai mai raɗaɗi ya kama Azeeza da ke ta ku ka, Babu wanda bai ji jiki ba a cikin su, Bacci ya ƙaura ce wa idanuwansu, An rasa wanda zai lallashi wani acikin su, matan gaba ɗayan su asaman benan Suka kwana kewaye da Angel har ruwa suka ƙara yayyafa mata amma bata farfaɗo ba, Sun yi kuka har sun gaji sun gode ma Allah, Mazan cikin su A zuƙunne suka kwana, Yadda su ka rana haka su ka dare.

Kafin safiya ta yi kowannan su ya fita hayyacin sa, babu mai iya motsa la66ansa yai magana acikinsu, zazza6i duk ya lullu6e su, Don shi Gabriel ma suman zaune yai, bawan Allah duk ya damu kan shi, ga matsanancin ciwon kai da ya ke fama dashi.

A cikin su mutun É—ayane hankalin shi ya ke akwance, majnun dake ta sharar baccinsa, ko daren jiya da Angel ta ke ta kuka za'a tafi da Danish bai farka ba, hatta jamima da ta kasance autar cikin su saida ta tashi daga bacci hada ita cikin waÉ—anda suka kwana zaune saman benan É—akin su.

Tsawon lokacin babu wanda ya iya buɗe baki ya furta wata kalma, Jamima ce tai ƙoƙarin cewa"Bari naje na ɗebo ruwa a ƙara yayyafa mata asaman fuskarta" ba wanda ya kalle ta, miƙewa tai da sauri ta nufi sashen toilet ɗinsu, tun da ta shiga hankalinta yai matuƙar tashi ganin jinin Danish daya ɗiɗɗiga a saman floor ɗin ya bushe ƙamas, ɗago wa tai da sauri tana kallon Jikin ƙopar toilets ɗin da suke a jere guda uku, kafin ta tsayar da idonta akan ƙopar toilet ɗin da A kayi badaƙalar nan jiya, Jikin ta na kerma ta ƙarasa tare da turo ƙopar shi ta faɗa ciki, gabanta yai wani irin mugun bugu ganin uban jinin da Danish ya zubar a inda ya faɗi jiya yana birgima, a gigice Jamimah ta fasa ƙara wadda ta yi silar janyo hankalin su haris, da gudu suka shigo cikin toilet ɗin kaitsaye idanuwansu su ka sauka akan uban jinin, Lamarin yai matuƙar girgiza su, jinin duk ya daskare acikin toilet ɗin,

Zuciyarsu ta dinga azalzalarsu tana tunzura su akan cewa Gabriel ne yai mishi wani abu, shiyasa yaƙi faɗa musu, Ransu yai matuƙar 6aci don gani suke kamar ma kashe musu ɗan uwa yai, Hakan yasa suka koma ɗakin mazan dukansu, Suka tarar ma Gabriel sai da suka fara Farfaɗo dashi ya dawo cikin hayyacin shi, Su ka tasa shi gaba akan ya faɗa musu gaskiyar abunda ya faru idan har yana son zaman lafiya, a lokacin yaso ya sanar dasu sai dai yakasa motsa bakinsa, saboda halin da ya ke aciki, zuciyace ta fusge su, Su ka yi mashi jahilin bugu har sai da su ka ga ya suma, Tukunna suka ƙyale shi,

Babu wanda yabi ta kanshi, Kwance suka barshi ƙasa, la66ansa duk sun fashe, ƴan matan sai kuka su ke yi ba ƙaƙƙautawa, An rasa me lallashin wani acikin su, Haris ne ya je wurin da su ke zazzaune bakin benan, ya sanya hannayenshi biyu ya ɗauki Angel ya nufi tsakiyar ɗakin su da ita, Miƙewa su kai gaba ɗayan su suka bi haris, wanda ke ƙoƙarin kwantar da Angel saman floor,

Yace da azeeza ta ƙara ɗebo mishi ruwa ya watsa mata, ta amsa mashi da toh, Da gudu azeeza ta nufi sashen shiga toilet ɗinsu, shigarta ke da wuya, su ka soma jin motsin buɗe ƙopa, Saboda halin da su ke aciki babu wanda Ya kai idonshi ga ƙopar, Giants ne da ke kawo musu abinci, A jere su ka shigo hannayen su ruƙe da kayan abincin su, Ko ajikin su jin kukan da su Hanna ke ta yi, wuce wa su ka yi zuwa saman dining carpet dinsu, bayan sun ajiye kayan abincin basu tsaya jiran su taso su ci ba, a tare suka fice daga cikin ɗakin, Babu wanda ya kalli kayan abincin, hatta parveen damuwa ta hana taje taci abinci.

Badajimawa ba Azeeza ta shigo hannunta ruƙe da bokiti, Kusan rabi ta ciko, don a watsa ma Angel ko sun samu tafarka, Hanya suka matsa mata ta sauke bucket din gefen haris.

duk da hankalin su ba a kwance ya ke ba sai da su ka dubi fuskar azeeza ganin ta kawo musu ruwa a bokiti Sai nishi ta ke yi tana haki, Hannu biyu haris ya tsoma acikin bokitin Ya ɗebo ruwan da ƙarfin gaske ya watsa Ma Angel saman fuskarta, Nan take taja dogon numfashi ta fara mutsu mutsun buɗe idanuwanta.

Ajiyar zuciya kowannansu ya sauke, tunkan ta buÉ—e idanuwanta ta soma Æ´an buge buge tana ambaton sunan Danish tana kuka tana faÉ—in Wlh ba za ku rabani dashi ba, Duk inda zaku kai shi saina bi ku, Wayyo Allah na Danish shikenan sun rabani da farin ciki na, Gabriel kaine silar da ya rasa idon shi É—aya...."

Kalaman Angel sun girgiza su Har suna haÉ—a baki wurin furta Danish ya rasa idon shi É—aya!?
Chapter 140 · 0% Book details