← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 179

Sashe 17

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_daga alƙalamin Boss Bature ✍️*_

dedicated to Aunty kubra❤

قصة حزينة جدا عن السجناء🥺💔

*E7*
Su na Cikin Maganar nan, Su ka ji yo wani irin gurnani, A ruÉ—e su ka É—ago suna kallon su,

Wannan dattijon ne Ya rikiɗa nan take ya zama wata halitta mai matuƙar tsoratarwa, Ya shiga girgiza jikin shi Yana wani irin gurnani,

Tashin hankalin da ba'a sama shi date, Wani irin tsoro ne ya bayyana a kan fuskokin su, Tuni zufa ta wanke su sharkaf, Don tunda Allah ya halicce su basu ta6a ganin mutun ya rikiÉ—a ya koma dabba ba, duk da suna Jin labarin Matsafan dake rikiÉ—a suna canza halittar su,

Ja da baya halittar nan tayi, Kafin Ya daka suka, Kaitsaye Ya faɗa kan Ƴa'ƴan malamin nan, Ya shiga yagar Naman Jikin su Yana ci, malamin na kuka yana ƙoƙarin ceton ran ƴa'ƴan shi da jini Ya wanke fuskokin su, Aikuwa nan take sauran Alhazawan guda biyar dake a kewaye da su, suka rikiɗa, gaba ɗayan su ka canza halittar su, Cikin lokaci ƙanƙani su ka handame malamin nan da ya'yan shi,

In taƙaice maku zance, Sai da Suka cinye namansu tass, Ko ƙashi basu bari ba, Tukunna Suka rikiɗa a lokaci ɗaya suka koma Mutane, Bakin kowannan su, Da6a da6a da jini,

A hanzarce bodyguards ɗinnan suka zura hannayen su Cikin aljihunan wandunansu kowannansu ya zaro Hanky mai girma. suka shiga goge masu jinin da ya 6ata bakunan su, Bayan sun kammala suka jefar da hanky ɗin Cikin ƙoramar dake a gabansu,

Batare da 6ata lokaci ba, suka koma Cikin motocin su, a guje suka bar cikin dajin 6aaat suka 6ace,

Jikin Taj na kerma Ya kalli Uzair wanda tuni ya jima da ƙamewa a tsaye kamar saƙago, Idanuwanshi sun firfito waje tamkar zasu faɗo ƙasa,Wani irin matsanancin tsoro ne ya ziyar shi zuciyoyin su, hankalin su ya tashi matuƙa,

A ruɗe Taj ya fisgi hannun Uzair suka Koma Cikin motar su, Aka rasa wanda zaiyi driving ɗin su, tsakanin su biyu, jikinsu duk yayi sanyi ga wata uwar zufa dake tsatstsafo masu, tamkar waɗanda aka tsamo su daga cikin ruwa sun haɗa uban gumi, daƙyar Taj ya iya tada motar, ya samu ya karya kwana da wani irin speed ya fusgi motar tamkar zasu tashi sama, Duk tsoro ya kama su ga tausayin malamin nan da ƴa'ƴanshi, abun ya yi matuƙar girgiza su,

A can gida kuwa, Sam bacci ya ƙaurace wa idanuwansu, Daga angel ɗin har aneelerh, Sun yi zugudum saman Gado, kowa da abunda yake ayyanawa a ran shi, Ganin har ƙarfe 12 ta buga amma ba su dawo ba,

"Aunty aneelerh, ni tsoro nake ji kada a ce wani abu ya faru da su daddy" Janyo ta Jikinta aneelerh ta yi Tare da shafa sumar kanta tace"in sha Allah ba a bunda zai faru da su, zasu dawo ne nan bada jimawa ba, ni inaji a raina"
"Allah bazan ƙara bari ya tafi ya barni ba, duk inda zai je ƙafata ƙafar shi, idan ba haka ba zan sa ce tayar motor shi kowa ya rasa" aɗan shagawa6e tayi maganar, tamkar zata fashe da kuka,
Fashewa aneelerh tayi da dariya daƙyar ta tsagaita da yin dariyar tace"Idan ki ka sa ce tayar motar shi ae yana da ƙafafu ko suma zaki guntule su ne? Kuma in banda abun ki, idan kika sa ce tayar motar shi, ae a kwai ta Uzair zasu fita a cikin ta shi ne,"
Tur6une fuska tayi, ba halin tace zata sa ce tayar motar uzair,

Suna Cikin tattaunawar nan, Suka jiyo hon ɗin motar su, Da gudu Angel ta zabura Zata sauko daga saman gadon, Aneelerh ta ruƙo hannunta"ki bari su ƙaraso Ciki mana"

Komawa tayi ta zauna jikinta har wani rawa yake yi duk ta ƙagara taga daddynta,
Baba maigadi na buɗe masu ƙopar, A tsiyace suka shigo da motar bayan sunyi parking ɗinta Taj ya kashe motar,

Uzair ya kalli shi ganin yadda zufa keta tsatstsafo mashi ya haÉ—a uban gumi"banaso su gane wani abu ya faru pls, Ka daidaita natsuwar ka"

Kallon shi taj ya yi "natsuwa fa ka ce?tayaya kenan? akan idona fa mutane suka rikiÉ—a suka canza halittarsu, kuma akan idona suka handame mutun da ya'yan shi, wlh ko a film naga hakan saina girgiza ballantana kuma a zahiri, ni wlh ka cuce ni, danasani tunfarko ban biye maka ba, da duk banga wannan tashin hankalin ba" ranshi duk ajagule ya yi maganar,

"Amma ae koba komai, mun ƙaru ko?tun da kaga yanzu mun samu a bunda zamu taimaki al'umma,"uzair ne yayi maganar,
Wani kallo Taj ya jefa mashi"mu taimaki al'umma, ka yi hauka ne"?

Bai ba shi amsa ba, sai ma ya fito daga motar, ya nufi cikin gidan, Jiki a sanyaye taj ya fito daga motar yabi bayan Uzair suka nufi cikin palourn,

Kusan atare suka haÉ—a baki wurin yin sallama, jin muryoyin su yasa Angel da aneeleeh suka fito daga É—akin, da gudu angel taje ta faÉ—a ma daddynta,
"Nayi fushi sai yanzu zaka dawo,duk ka tayar mun da hankali, ko bacci na kasa yi"
Zuƙunnawa yayi saman gwiwowin sa, yadda tsawon shi zaizo dai dai da nata,
Sosai yayi hugginta ɗinta"Am sorry angel, Nasan nayi laifi, ayi mun afwa,"aɗan shagwa6e tace"shikenan amma kada ka ƙara," amsa mata ya yi da toh batare daya rabata da jikin shi ba, sam baiso ta gane halin da yake ciki, hawaye ne cike tab da idanuwan shi, tamkar ya rushe da kuka haka yake ji bakomai yafi tsaya ma shi a raiba fa ce yacce waɗannan Mutannan marasa imani suka fatattaki malamin nan da kuma ƴa'ƴan shi, Yanzu shikenan sun kashe su, Babu su a doran duniya, tabbas waɗannan mutanan sun san me suka taka,

Aneelerh da uzair tuni sun shige É—aki,
"Sannu da dawowa" batare da ya kalle ta ba, ya nufi toilet zai shiga,
"Wai meke faruwa ne? Nayi maka magana baka amsa min ba,"
Juyo wa ya ɗanyi Yana kallonta a lokacin ya ruƙe handle ɗin ƙopar toilet zai shiga, "To matar ɗan jarida, ba za ki bari na samu natsuwa ba" cikin zolaya ya yi mata maganar,

Murmu shi taÉ—an saki, shima ya mayar mata da martanin murmushin kafin ya shige cikin toilet É—in.

Tunawa da taj yasa Aneelerh miƙe wa Ta fito falon, Bata same su a nan ba hakan na nufin ya ɗauki angel sun tafi gida.

Ta so ace tayi ma shi sannu dawowa, ga shi kuma Ya tafi, Ta wani 6angaren kuma ji take kamar wani abu Ya faru ba daidai ba, Tun daga kan yanayin Uzair, da kuma shi taj É—in.

Hakanan taji hankalin ta bai kwanta dasu ba, sam babu natsuwa a tattare da su, Juyawa ta yi zuwa cikin É—akin a lokacin uzair Ya fito daga toilet É—in, da alama Ruwa yaÉ—an watsa ma jikin shi, short ne kawai ya bari ajikin shi,

"Sannu da fitowa" ta faÉ—i tana kallon shi,
"Yawwa madam,"
"Bari na kawo maka dinner É—in ka, nasan ka kwaso yunwa,"
Da sauri ya dakatar da ita "No bana jin yunwa, bacci nake ji" yakai ƙarshen maganar tare da nufar Cikin ɗakin wurin Closet ɗin shi, Ya buɗe cikin jerin jallabiyoyinshi ya ɗauko ɗaya Ya zurata ajikin shi,

Juyawa yai Still aneelerh tana a tsaye tana kallon shi, Ta gefenta yabi ya wuce ya kwanta,

"Nayi tunanin zaka yi missing É—ina," tayi maganar tare da takawa Ta koma gefen gadon,
"Kodai wani abu ya faru ne? naga duk ka sauyamun, Shima taj ko sallama banyi ma shi ba, Ya É—auki angel sun tafi gida"
Ganin zata takura mashi da surutu ne yasa shi yin saurin janyota jikin shi, wata irin runguma yayi mata, sai ga shi tayi tsit bata ƙara cewa uffan ba,

Taj kuwa bayan Sun koma gidan, Upstairs Ya wuce da angel, Yakaita bedroom É—inta, Yasan aneelerh bazata barta da yunwa ba,

Dawowa down Yayi a hanzar ce ya shiga bedroom É—in shi Ya faÉ—a toilet, shaf shaf yayi wanka ya fito, wuri ya samu saman kujerar gaban mirror ya xauna, wasu zafafan hawaye ne su ka soma yin zarya akan fuskar shi, Uban tagumi ya zabga tamkar marayan da ba shi da ma fadi aduniya,

"Daddy"muryar angel ce ta katse shi, ta cikin madubin yake hangenta, tana a tsaye bakin ƙopar,
Da sauri ya share hawayen dake a kan fuskashi cikin sanyin murya yace"Ba ki yi bacci ba?
Ƙarasa shiga cikin ɗakin tayi"daddyna ba ka da lafiya ne?

"Lafiyata ƙalou me kika gani ne"?yayi tambayar tare da ɗan juyawa yana kallon ta, a lokacin ta ƙaraso in da yake zaune,
"Ni dai inaji araina, baka da lafiya,"
daƙyar ya ƙaƙaro murmushi yace "Waya faɗa maki bani da lafiya?
"Naji a jikina" ta yi maganar tana ƙare mashi kallo,
"Bana hana ki yawo da daddare ba kallabi ba"? da biyu ya yi mata maganar don ya mantar da ita wancen zancen,
"Mantawa nayi,"
Nuna mata hanyar fita yayi da hannun shi"Oya go back to ur room ki É—aure kanki da kallabi, before ki kwanta"
Maƙe mashi kafaɗa tayi"Ni dai zan kwana anan, muyi bacci a tare"
Ɗaure mata fuska ya yi"Za ki wuce ko sai nayi ball dake" a faɗa ce ya yi mata maganar,nan da nan yanayin fuskarta ya canza, ƙwalla ta ciko tab a cikin idanuwanta, cikin shessheƙar kuka tace
"Dan Allah daddy ka bari in kwana anan yau kawai" ta ƙarasa maganar tana matsar ƙwalla,
GyaÉ—a kai yayi"Shikenan Ki fita waje Ki jirani zan kira ki" juyawa tayi da sauri ta koma daga waje, ta jingina bayanta jikin wall,

Miƙewa ya yi jiki ba ƙwari ya nufi wardrobe ya ɗauko kayan baccin shi, ya soma sanya su a jikin shi,

"Daddy in shigo" jin muryarta ya sa shi yin murmushi tare da cewa"ban kammala ba"

Sai daya ƙarasa zura kayan a jikin shi, tukunna Ya kira Sunanta Angel, Shigo wa tayi cikin ɗakin A kwance ta same shi saman gado, Ƙarasawa tayi ta haye saman gadon, Can kusa da shi ta kwanta,
Addu'a ya shiga jerowa yana tofa masu, Kafin Ya janyo ta jikin shi, a daren ranar da ƙyar ya samu bacci Ya ɗauke shi,

****Boss Bature****
Chapter 17 · 0% Book details