Sashe 162
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gigice ta furta "Innalillahi...." ba tare da ta ƙarasa maganar ba, tsananin tsoro ne da firgice su ka bayyana a cikin akan fuskokin su, Hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, musamman parveen a ruɗe ta nufi gadon majnoon ganin daskararren jini asaman shimfiɗarsh, hannayenta biyu ta ɗaura saman bargon shi, yayin da zuciyarta ke tafarfasa.
Muryar Hannah na rawa ta furta"INA MAJNOON YA KE? JININ MENENE MU KE GANI A SAMAN SHIMFIÆŠAR SHI, DAN ALLAH KADA KU CE MANA YA MUTU SHI MA"!
Babu wanda ya iya buɗe baki ya basu amsa, hakan yasa su ka fahimci cewa Majnoon ya mutu babu shi, hawaye ne masu ɗumi su ka wanke fuskokinsu, A saman shimfiɗarshi Parveen ta kifa kanta da ke sara mata da ciwo, ta dinga kuka tamkar ranta zai fita, bakomai take tunawa ba face Irin rayuwar da su ka yi dashi, ta yi matuƙar tsaya mata arai, ta yi danasanin duk wani bugu da ta yi mashi, tun ranar farko daya fara kasancewa a cikinsu, Ya 6arar masu da Cake, Tana matuƙar son yaron tsanar da ta yi mashi a lokacin saboda 6arnar da ya ke yi masu ce, ɗago da hannayenta tayi tare da ɗaga su sama tana kallon fingers ɗin ta da ke kerma, Hawaye jaga jaga akan fuskarta, sautin kukanta ya cika ɗakin nasu, Muryarta da wani irin sauti ta ke faɗin"YA ALLAH KA ƊAUKI RAINA IN HUTA! BAZAN IYA JURAR TASHIN HANKALIN NAN BA! Bana fatan na sake yin tozali da gawar wani a cikin ƴan uwana, So nake na mutu in huta, Narasa Majnoon abokin Faɗa na ga Unaiza ma ta tafi tabar mu da kewarta, wayyo Allah nah! ' sosai ta rushe masu da kuka, kamar mahaukaciya haka ta cusa hannayenta cikin sumar kanta, ta dinga hargitsa gashin cikin ƙunar rai, kafin ta mayar da kanta saman mattress ɗin Majnoon.
Duk suna jin sautin kukanta, Jikin su duk ya yi sanyi, mutuwar mutun biyun nan ta raunata zukatan su, ta sagar masu da gwiwarsu, komai ya fita aran su, babu mai sauran walwala acikinsu, ba don zuciyar Imani ba da tuni wasu daga cikin su sun zauce, musamman Azeeza ta shiga halin ha'ula'u, tsoro da firgici sun hana ta sak, har zufa ke tsastsafo Mata saman goshinta, tun da ta farfaÉ—o daga suma ta zauna ko motsi ta gaza yi sai dai tabi su da ido.
Miƙewa tsaye Sarah Ta yi jikinta kamar zai 6alle, saboda rashin kuzari, fuskarta a bushe muryarta asanyaye ta soma magana"Idan har mu ka cigaba da zama ba tare da mun ɗauki mataki ba, za'a cigaba da yi mana ɗauki ɗai ɗai ne ana kashe mana rayuwa, Yakamata musan abun yi, wlh na tsorota Na firgita da ganin irin mutuwar da Unaiza ta yi, Tare da ita fa aka kawo mu cikin ku, bazan ta6a manta farkon gani na da ita ba, ban ta6a tunanin cewa zan shaida mutuwar ta ba, na girgiza sosai, please na roƙe ku, idan zaku iya ku kashe ni zaifi min kwanciyar hankali akan aƙara zuwa a ɗauki wani acikin mu, saboda na fahimci cewa rayuwar mu bata da amfani awurin su, mutuwa ta zamar mana dole yanzu ma aka fara yinta, bansan wanene next zai mutu ba, bana so na gani shiyasa nake so in mutu................" daƙyar ta ƙarasa maganar, saboda raɗaɗin da ta ke ji a cikin zuciyarta, miƙewa tsaye Hannah ta yi, idanuwanta jawur dasu ta soma magana tana fuskantar sauran ƴan uwan nasu da ke a zazzaune ƙasa
"Meyasa har yau Allah bai dube mu ba? Mu ma fa bayinsa ne kamar kowa, Angel ke da kan ki kika faÉ—a mana cewa wanda ya halicce mu yana sane damu, but why mu ke fuskantar irin wannan tashin hankalin? bawani mai taimakon mu, sau nawa muna hana idon mu bacci don mu kai kukan mu agare shi, amma shiru...!
Hankalin Angel ba ƙaramin tashi yai ba, jin maganganun da Hanna ke yi, duk da matsanancin halin da ta ke a ciki sai da ta girgiza, ganin sun soma ƙoƙarin kauce hanya, dama ba wadataccen ilmin addini gare su ba, ba lallai bane a yanzu da suka fara fuskantar tashin hankalin nan su iya jurewa ba, saboda suna da raunin imani da tawakkali, a haka ma sunyi ƙoƙari saboda basu ta6a ƙaryata maganar ba, sai dai awannan karan tana tsoron Su juye mata su canza ra'ayinsu.
Runtse idanuwanta ta yi sosai tare da cusa kanta a ƙirjin batul, ba ta yi tsammanin zata samu sauran hawaye a cikin idanuwanta ba, sai gasu sun soma tsastsafowa saman kuncin ta masu ɗumi.
zuciyar batul ba ƙaramin karaya tayi ba, Jin yadda Jikin Angel ya yi zafi sosai, tasan dole taji raɗaɗin a cikin zuciyarta,' ƙara ƙanƙameta ta yi a jikinta, hannayenta asaman sumar kanta, A hankali take shafa sumar Angel tana lallashinta, zuciyarta tamkar ta fashe saboda ƙunar da ta ke yi mata, gudun kada ta zauce ta rasa madafa, yasa ta soma furta duk wasu addu'o'i da tasan zasu kwantar mata da hankalinta.
A yayin da ta ke yin addu'o'in idanuwanta suna arufe, sosai ta matse su, tana jiyo muryar Yasmin tana faÉ—in
"Angel Kin yi shiru baki bamu amsa ba, har yaushe ne zamu tsara Jiran taimako daga wurin Allah! Kina ganin mun fara mutuwa, tsoro da firgici kaɗai kaɗai sun isa su sa mu zauce, Mun yi tunanin cewa idan muka kar6i addinin ki, Mu ka yi Imani da Allah, komai zaizo mana da sauƙi, Amma shiru sai ma ƙara shiga tashin hankali da mu ke yi, lokacin da kika zo cikin rayuwar mu Ba ki ji daɗin da mu ka ji ba, saboda alƙawarurrukan da kika ɗaukar mana na cewa Zaki taimaka mana wurin ganin mun ku6uta daga cikin kurkukun ƙaddarar nan, Ki ka sanya mana kwaɗayin son yin rayuwar ƴan ci kalar wadda ki ka yi awaje, Meyasa angel muke ganin ba dai dai ba? Idan da ace kinsan ba zaki iya taimakon mu ba, meyasa kika sanar damu hakan? Kuma kika bamu labarin rayuwarki har muka sanya rai da yin irinta........"
Yasmin bata ƙarasa maganar ba, ta rushe da kuka, Hankalin Angel idan yai dubu to ya tashi, Dama fa dole ta fuskanci wannan matsalar, cos itace mutun ta farko data fara sanar dasu komai agame da mahaliccin su, Nauyin komai ya rataya akan wuyanta! Duk idan su ka ji ba daɗi dole ita zasu tunkara, to ayanzu dai mutuwar Unaiza da Majnoon ta kwance notikan kawunansu, sun fara tsorota shiyasa su ke waɗannan maganganun.
"Angel idan har akwai abunda ya rage mana wanda ba mu yi ba dangane da addinin ki, to ki faɗa mana shi don muyi wata'ƙil Allah zai ji ƙanmu ya tausaya mana, ya dube mu da idon rahama ko mun samu mu tsira da ranmu!" Eve ce ta yi maganar, Duk sun mimmiƙe tsaitsaye Agaban Batul da ke a rungume da ita, sai ƙara tighting ɗinta ta ke yi a jikinta, ita kanta batul ɗin hawaye ne sharkaf akan fuskarta, cigaba da ambaton sunan Allah ta yi acikin zuciyarta, tana roƙonshi akan ya basu bafita kada yasa su ga gazawarta.
"Angel Mun san kina sauraron mu, kin yi shiru ba ki ce komai ba, kada ki sanya mana kokwanto A cikin zukatan mu, Mun yarda dake, Munsan kina ƙaunarmu, kuma kina son Farin Cikin mu, don haka Muna jiran amsar ki me ya rage mana wanda ba muyi ba a cikin addininmu wanda zaisa Allah ya jiƙan mu......" Cikin rauni na murya Hibba ta yi maganar, daga ganin fuskokin su a matuƙar tsorace suke.
Angel tana a cikin tsaka mai wuya, ta kasa ɗago da idonta ta dube su, saboda bata da ƙwarin gwiwar yi masu magana, to me zata ce masu? Itama fa A tsoroce take da abunda ya faru na mutuwarsu Unaiza.
Muryar Rubina a hargitse tace"Babban abunda nake jimawa, Ƴan uwan mu da aka kwashe Shin suna araye ko sun mutu, bamusan a wani hali su ke aciki ba, Tun da yanzu mun fahimci cewa kashe mu ake yi, Lalata rayuwarmu ake yi a kwashe wani sashe na jikin mu! Kamar yarda aka yi ma Unaiza, Da Majnoon......." Bugun zuciyar Angel ne ya ƙaru tunawa da Mazan su da aka kwashe, ba ita ba Hatta su Deeja damuwace ƙarara akan fuskokinsu, Tabbas Suna fuskantar barazana a cikin rayuwarsu.
"baƙin Cikin da mu ke ƙunsa da barazanar da muke fuskanta sun isa su sa zuciyoyin mu su buga mu mutu" Eve ce tayi maganar tana faman huci, idanuwanta a zazzare, ruwan hawaye ne kwance a cikinsu. Kowa Yana tofa albarkacin bakinsa, mutun biyar ne basu tanka ba, sai da su ka yi mai isar su tukunna Deeja ta miƙe cikin kakkausar murya ta soma magana tana duban kowan nan su.
"Na yi mamakin jin maganganun da harsunan ku su ke furtawa, saboda abun da ya faru ne yasa ku ke kokwanto Akan Addinin da Angel tazo mana dashi, Kun bani kunya duk da na fahimci cewa ba'a cikin hayyacin ku kuke ba, banaso mu yi abunda zamuyi danasani acikin rayuwar mu, Angel ba ita bace silar halin da muka shiga ba, Akan me za ku dinga ɗaura mata nauyin komai akanta! Yarinyar nan fa ƙanwar mu ce, babu wanda bai girmeta ba a cikin mu...."
Numfasawa Deeja ta yi a yayin da take bin fuskokin su da kallo.