Sashe 167
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun daga wannan ranar ba'a ƙara kawo masu abinci mai rai da lafiya ba, Faranti Biyu ake cuko masu Da ganye ganyen ma mai ɗaci, ga ruwan zafi har tiriri ya ke yi, saboda tsabar mugunta haka ake kawo masu shi don su sha, Rana ta farko da aka fara kawo masu ganyen babu wanda ya iya ci, ga yunwa suna ji kamar suci ƴan hancin cikinsu, suka rasa ya zasuyi, saboda bai ciyuwa agare su, basu saba cin ganye ba, Yadda aka kawo shi haka giants suka koma dashi, a cikon kwana na biyu ne da yunwar ta kusa yi masu Illah Kamar dabbobi suka zauna suna cin ganye, saboda mugun kamun da yunwa ta yi masu kamar zasu zauce, suna ci suna kuka maƙoshinsu na ƙaiƙayi ahaka suka cinye shi tass, Basu sha ruwan zafin da a ka kawo masu ba, sai dai su ka koma suna amfani dana fanfon da ke a cikin toilet ɗinsu,
Ganyen da su ke ci ba ƙaramar illa ya ke yi masu ba, saboda basu saba ba, hakan yasa cikinsu ya dinga 6aci, babu wanda bai yi gudawa ba a cikin su, duk sun rame sun fita hayyacin su, sun zama mahaukatan ƙarfi da yaji, addu'ar da suke samu suyi yanzu sun daina saboda Rashin lafiyar da suke fama da ita, Kullum ne sai an samu wanda zai kwanta jinya acikin su, sun jigata sosai, kamar ba za su rayu ba, tun suna ci yana 6ata masu ciki har ta kai ga yanzu sun daina yin gudawa idan su ka ci ganyen, sun fara sabawa da cin shi, cikin nasu ya daina 6acewa, Idan aka kawo masu shi zama suke yi suci shi kamar dabbobi, ruwan kuma Basu iya shanshan shi da tsafi don zai iya yi masu illah, sai sun hura shi da bakunansu kafin su samu su kora shi ta cikin maƙoshin su, yaushe rabon da su wanke uniform ɗin jikin su yau tsawon wata ɗaya kenan, babu mai yin wanka a cikin su, damuwa da baƙin cikin halin da su ke aciki sakamakon canza masu abinci da akayi da kuma rashin dawo masu da ƴan uwansu yasa duk sun rasa kwanciyar hankali.
Sai da Angel ta yi dagaske wurin ƙoƙarin danne zuciyarta dake shirin bugawa ta hanyar dagewa dayi masu addu'a tukunna suka ɗan samu salama, natsuwa ta shiga jikinsu, yanzu suna samun damar runtsawa su yi bacci sosai, amma fa dukkan su bana tunanin za'a iya samun ɗaya wanda bai fama da depression, wani lokacin idan ƙirjinsu yayi masu zafi zuciyoyinsu suka yi masu nauyi, haka zasu zauna su dinga karanta duk wasu addu'o'i da su ka san zasu Sanyaya masu zukatansu, kuma cikin ikon Allah da zarar sun yi komai su ke samun sauƙi, harma su samu damar yin bacci, yanzu sun fidda rai da za'a dawo masu da ƴan uwan su duba da irin tsawon lokacin da aka ɗauka babu su, Danish Yana acikin wata na biyar a hannunsu, Su haris suna acikin wata na huɗu, basu san awani hali su ke aciki ba, Allah kaɗai yasan irin azabtarwar da ake yi masu, suna raye ko sun mutu basu da tabbacin hakan....................."
💔PRISONERS💔
Dare ya nutsa sosai, babu mai motsi acikinsu, Bacci su ke yi kamar matattu, numfashin Angel ne ya soma canzawa, zufa ta soma wanke fuskarta, bugun zuciyarta ya ƙarfafa, yatsun hannayenta dana ƙafarta suka soma Yin kerma, Ga dukkan alamu mafarki ta ke Yi, wanda yasa ta shiga wannan yanayin da take a ciki, su uku ne a kwance saman shimfiɗar da ta yi masu a ƙasa, Ita da Jamimah sai Azeeza.
Sai faman yin sambatu ta ke yi tana ambaton Sunan tsohuwa Tamira!
Wata irin firgita ta yi Sakamakon Ta6a jikinta da akayi, a hanzarce ta yi wuff ta miƙe zaune tana faman zazzare idanuwanta, gashin kanta duk ya tarwatse saman bayanta.
"Angel ni ce! Meyasa kike sambatu kina ambaton sunan tsohuwa Tamira? A tsananin tsorace ta É—aura idanuwanta kan fuskar batul da ke yi mata magana, Farkawarta kenan daga bacci, fitsarine ya matse ta bayan taje toilet ta yi shi ne ta dawo É—akin har zata kwanta sai taji muryar Angel tana sambatu acikin baccinta, wannan dalilin ne yasa ta nufi shinfiÉ—ar su don taga meke faruwa da ita.
Bata amsa mata tambayarta ba, saboda bata a cikin natsuwarta, ganin ta miƙe tsaye ne yasa itama batul ɗin ta miƙe tana tambayarta lafiya meya faru? Babu alamun zata tanka mata, sai faman bin ɗakin su ta ke yi da kallo kamar ranar ta fara ganin shi.
"Angel dare ne fa, Me ki ke kallo? Magana fa na ke yi ma ki amma kin share ni....." tunkan batul ta ƙarasa maganar, Angel ta damƙi hannun batul tare da Janta da sauri ta nufi sashen toilet ɗin hannunsu aruƙe dana juna, bayan sun shiga sashen ne Angel ta saki hannunta, aruɗe batul ke kallon fuskarta gani take kamar angel tafara haukacewa ne shiyasa ta janyota a tsakar daren nan zuwa sashen toilet ɗinsu.
Fuskarta da alamun ruÉ—i tace"kiyi min magana mana, meyasa kika kawo ni nan"?
Sai da ta fara tattara natsuwarta guri guda kafin ta soma magana
"Batool na yi wani mafarki da ban ta6a yin irin shi ba, dangane da wani kalami da tsohuwa Tamira ta ta6a furta mana......" daƙyar tayi maganar tana faman haɗiyar yawu, batul duk ta gama ruɗewa
"Wani kalami kenan"!? Ta jefa mata tambayar.
"Zan faÉ—a maki amma kafin nan inaso ki sanar dani, Kafin zuwana gidan kurkukun nan, a ina ku ke yin rayuwa? Meyasa aka canza maku É—aki daga asalin wanda ku ka baro"?
"Angel meyasa kika tambaye ni"? A tsiwace tace"nidai ki bani amsar tambayata"! Yawu batul ta haɗiya kafin tace"Ni kaina bansan dalilin dayasa aka dawo damu nan ba, kawai dai nasan tsohuwa Tamira tace zata sanya a canza mana ɗaki saboda asalin wanda muke aciki yayi mana ƙanƙanta, babu wadataccen filin da zamu sakata mu wala........" A dabarbarce take yin maganar saboda yadda Angel tayi mata rumfa kamar zata rufeta da bugu.
"Amma ranar da aka kawo ni kurkukun nan, Na tsinci kaina nikaɗai acikin ɗakin nan, sai daga bisani aka buɗe ƙopa sai gaku kun shigo Ciki, daga ina ku ke"!? girgiza mata kai Batul tayi"bazan iya tunawa ba Angel, bansan inda aka kaimu ba, " numfasawa Angel tayi tare da sanya hannunta biyu cikin sumar kanta, kamar akwai wani abu da take son ganowa, ganin yadda duk tabi ta ruɗe ne yasa Batul tambayarta"meke damun ki ne? meyasa ki ka tambayeni"?
"Saboda ina hasashen Akwai ƙopar da zamu Iya guduwa ta cikin ɗakin nan da muke rayuwa........." batul bata fahimci inda zancen nata ya dosa ba.
"Angel ƙopa fa kika ce a cikin ɗakin nan ta ina kenan? Anya kuwa kinsan me kike faɗa kuwa"?
Jinjina kai ta É—anyi kafin ta soma magana" akwai wata magana da tsohuwa tamira ta ta6a furta mana, ban tashi tunawa ba sai Acikin mafarkin da na yi yau, abun tace mana shi ne tana so mu É—auka cewa mu kamar
*MUKULLAI NE NA MABUƊIN WATA ƘOFA GUDA ƊAYA WADDA ZATA SAMA MANA FARIN CIKI ACIKIN RAYUWARMU, TABBAS MUNA DA DAMA*
Amma fa dole sai Mun yarda da kan mu, mun haɗa hannu, domin kuwa Ƙofar farin cikin nan tana atare mu Sa'annan
*MU NE MAKULLAN DA ZAMU BUÆŠE TA*
Numfashi Angel taja tare da cigaba da yin magana
"Kalamaine tayi mana cikin hikma, a hasashe na, dama tun fil azal tsohuwa tamira tana son taimakon ku, shiyasa tayi silar da aka canza maku É—aki aka kawo ku nan, bayan haka tasan da zuwana gidan kurkukun nan........"
Ba ta kai ga ƙarasa maganar ba, Batul ta tari numfashin ta da cewa" kin manta wacece tsohuwa tamira, itama fa muguwace kamar sauran, banbancin kaɗan ne sannan ma'aikaciya ce ita agidan kurkukun nan, taya kike tunanin zata iya taimakon mu? ta yi mata tambayar tana bin da kallo.
"Mutun koda dutse ne a ƙirjin shi ba zuciyaba, idan Allah ya so ka da rahama sai kaga Ya rikiɗa daga mara tausayi zuwa mai tausayi, Zai iya yiwuwa tsohuwa tamira taji tausayin halin da ku ke acikine shiyasa ta nemi hanyar da zata ku6utar daku, Ita da kanta ta faɗa mana cewa tun da ta ke rainon prisoners bata ta6a samun waɗanda su ka kwanta mata aranta ba irin mu, da alama tun kafin zuwana kurkukun nan take so ta taimake ku sai dai tagaza gudun kada taja ma kanta, Shiyasa ta dakata har zuwa lokacin da aka kawo ni sai tayi amfani da kaifin basirar da nake dashi wurin sanar dani cikin hikma akan hanyar da zamu bi don mu gudu daga prison!"
Cike da ƙwarin gwiwa ta yi maganar, Nazari sosai batul tayi dangane da kalaman da Angel ta furta mata, Na ɗan wani lokaci babu wanda ya furta wani abu a cikinsu, can batul tace"Kamar fa akwai ƙamshin gaskiya a maganarki, Amma idan har ta tabbata dagaske ne tsohuwa tamira ta yi kalaman hikma donta fahimtar damu hanyar da zamu ku6uta, Tayaya zamu iya ganin ƙopar da zamu gudu? Sannan taya akai muka zama makullai
........................â“â—
Dai dai nan Na ajiye alƙalamina, Shin kuna ganin dagaske ne hasashen Angel akan kalaman tsohuwa tamira?
💋PRISONERS💋
Cike da ƙwarin gwiwa ta yi maganar, Nazari sosai batul tayi dangane da kalaman da Angel ta furta mata, Na ɗan wani lokaci babu wanda ya furta wani abu a cikinsu, can batul tace"Kamar fa akwai ƙamshin gaskiya a maganarki, Amma idan har ta tabbata dagaske ne tsohuwa tamira ta yi kalaman hikima don ta fahimtar damu hanyar da zamu ku6uta, Tayaya zamu iya ganin ƙopar da zamu gudu? Sannan taya akai muka zama makullai
Zama Angel ta yi dirshan a saman floor, ta jingina bayanta jikin bango, Hannayenta Biyu Dafe da kanta, Ganin ta zauna yasa itama batul ɗin ta zauna, Ya kasance suna fuskantar Juna ita da Angel, Kowa Da abunda Ya ke nazari a cikim kanshi duk a ƙoƙarinsu na su gano fassarar kalaman tsohuwa Tamira,